Showing 75001 words to 78000 words out of 294767 words

Chapter 26 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Sosai taji dadin xuwa nijer,ta ji har cikin ranta lallai a gida take,abu daya ke yawan takurata,duk sanda ta gilma wani guri da tasha dabdala a baya,ko guraren da maina yafi yawan zama sai taji duk walwalar da take ciki ta gushe,wannan ya sanya ta dinga kame kanta daga shiga wasu guraren,ciki harda nahiyar dakunan dake sassan bibi wanda anan me akkuwa ta auku.

Wata guda ta shafe a nijer,daidai lokacin kuma muqamin aba ya tabbata,tafiya ta tabbata daga nijer to nijeria har zuwa qasar FRANCE!.

*_TOFA MASU KARATU,DAB MUKE DA ISA GURIN😄,muna dab da mu qarasa gurin da na tabbatar kowa ya qagauta a isa_*

*_FRANCE......NEW CHAPTER UNLOCKED_*🥰


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 40



*FRANCE _(PARIS)_*

*Charles de Gaulle Airport*


*Avenue champs elysees*

_8th arrondissements_


Cikin awa daya da saukesu da jirgin qatar airways yayi a airport din Charles de Gaulle suka iso champ elysees avenue. Unguwar dake da matuqar kyau tsari da kuma dadin zama,wadda take dauke da dukkan nau'ikan shop shop,malls restaurant da coffee shops harda makarantu. Unguwa ce me kyau qwarai da dadin rayuwa,wannan ta sanya aba ya zaba musu zama a cikinta. Cikin daya daga cikin apartment dake unguwar wanda gwamnatin nijer ta bashi.

Babban apartment ne dake qunshe da dakunan bacci guda hudu,biyu ta gaban gidan inda zaka bulla har balcony zuwa harabar gidan, biyu kuma ta cikin gidan wanda suke hade da backyard na gidan. Kowa yasan ginin bature gini ne me matuqar kyau da daukan hankali,komai na gidan a tsare yake a kuma killace,sun iso cikin gidan bisa jagorancin wakilan qasar nijer a nan din da suka tarbesu a hukumance,suka yiwa aba duk wata tarba data kamata.

Karfe hudu agogon paris suna cikin gidan,sun gama zagaya ko ina da duba ko ina. Sultana kam da ido take bin komai tana sake tabbatar da maganar hausawa da suke cewa tafiya mabudin ilimi,tun daga abuja zuwa gidan da suke ciki a yanzun take ganin mabanbantan al'amura. Benazeer da batoul kam sai tsalle tsallensu sukeyi,suna biye da ama duk inda ta sanya qafarta. Walwalar yaran data qaru kawai ta sanyawa ama farinciki,tana ji a ranta zaiyi wuya tabar qasar nan nan kusa,har sai yaran sun samu kalar ilimin da take musu kwadayin samu. Tanason su fita daban,su zama na musamman,kamar yadda gatan da suke samu ya banbanta da gatan duk wani d'iya dake familyn MAYAK'I,kamar kuma yadda suka zamo jikokin farko a wajensu aba din.

A nutse ta taka izuwa babban curtains daya suturta babbar qofar glass na dakin da zai iya baka daman ganin cikin unguwar da kuma duk wanda ke zirga zirga ta street din nasu. Qofar ta murda ta fita zuwa balcony din,sassanyan yanayi na la'asar sakaliya dake gauraye da qamshin tsirrai da suka wadaci unguwar ya daki fuskarta,iskar ta shiga sosai cikin hancinta ta isa hunhunta ta sauketa a nutse tana kuma fidda wata me zafi. Ajiyar zuciya ta sauke,tana fatan taji ruhi da zuciyarta ta nutsu amma. Ta lumshe fararen kewayayyun idanunta da suke da wani irin qwalli kamar an diga mai a cikinsu,haka kawai taji bugun zuciyarta yana dan sauyawa a hankali yana qara gudu. Da hanzari ta ware idanun nata cikin mamakin abinda ya haifar mata da hakan,sai ta aza hannun nata saman qirjin nata tana qoqarin controlling sabon yanayin data tsinci kanta a ciki.

Tsahon wasu mintuna babu sauyi,sake maida idanunta tayi zata lumshe karadin benazeer ya cika mata kunnuwa

"Aunty......aunty kinga" hannayenta ta sauke tana waiwayowa zuwa ga yarinyar. Da gudunta take nufarta tana nuna nata wata qatotuwar teddy. Murmushi ta saki dan siriri tana tuna rayuwarta,yadda tayi yayin tara teddy kaman hauka,batajin cikinsu ma akwai wanda zai qaunaci teddy din yadda ta sota

"Kizo inji ama" benazeer ta sake fadi tanata qoqarin ganin ta goya Teddy din,sai kuma ta juya da gudu gudu tana sauka hadi da kiran

"B.....B" Juyawa tayi tana komawa cikin dakinta ta dauki mayafin gown din jikinta ta yafa tana bin bayansu.

Daga qofar dakin da ama ke ciki din ta tsaya saboda rashin ganin dacewar shigarta dakin,don daki ne da ama ta zabawa aba,duk da cewa aba dinma baya nan ya fita tare da mutanen da suka yo masa rakiya zuwa nan din.

Knocking tayi ama dake ciki tace ta shigo. Hakanan cikin jin nauyi ta murda qofar dakin tana shiga. Babban dakine da yafi kowanne girma da kyan furniture,aman tana tsaye da wani folder a hannunta tana dubawa,ta amsa sallamar tana kallon sultana sannan ta miqa mata takardun tana cewa

"Ba hutu,ba zama,sun kusa gama daukar dalibai,aba yace ki duba,cikin universities din wacce ce tsarinsu yayi miki?"

"Allah sarki ubana na kaina" ta fada hawaye yana cika idanunta. Hannu biyu tasa ta karba tana kallon folder din. Itakam dai kawai tayi rashin mahaifinta hamani ne,amma zata iya cewa iyayenta sun maye mata gurbinsa har fiye da haka,batasan wani abu waishi maraici ba,bata taba ji ko ganin zumunci irin nasu ba,tasan indai ana batun dacewa da family itakam ta dace

"Amma ki kula ki duba location na kowacce university ki zabi wadda ba zaki dinga shan doguwar tafiya ba"

"In sha Allah ama". Ta fadi farinciki yana cika zuciyarta fal,burinta ya kusa cika na zama 'yar jarida,ta rungume folder din tana fita daga dakin.

Tsabar zumudi ya hanata tsaiwa ta kintsa dakin ta zauna duba jami'o'in,tanayi tana browsing a wayarta da babu layi a ciki duk kuwa da tsadar wayar,akwai wifi da suka samu a gidan don haka bata buqatar komai don research din.

Har tanja ta gama abinda ya dace tayi ta biyo ta dakin tana nade tsakiyar gado tana aikin canki canki. Cikin zolaya tanja tace

"Wai sultee kamar yanzu zaki fara zuwa makaranta a rayuwarki,wannan zumudi haka?,xuwa makarantar ma kamar yafi komai yi miki dadi" tashi tayi ta zauna tana yatsina fuska saboda yadda bayanta ya riqe sakamakon rub da cikin da tayi na kusan awa daya tana cewa

"Ji nakeyi kamar yanzu aka haifeni tanja,kaman yanzu ne na soma rayuwa,ai da can ba rayuwa nakeyi ba tanja,rayuwar da babu ilimi a ciki?,meye marabarka da gawa?"

"Irin wannan lokacin maina yakeson gani,shi yayita burin gani tattare da ke,ya Allahu ko ina wannan bawa naka ya shiga?" Qwaqwwaran motsi sultana batayi ba,sai tayi kaman bataji abinda tanja tace ba,inda sunsan adadin dimuwa da qyamatar da ruhinta ke yiwa sunansa kawai bama shi din kansa ba.......da babu wanda zaiyi kuskuren sake kiran sunansa a gabanta

"Bari na kintsa miki wajen kafin ki gama" a hankali ta motsa labbanta tace

"To" tana maida hankalinta ga wayarta cikin tsananin nutsuwa,yayin da zuciyarta taci gaba da motsa da wani irin sautin tsana da qiyayya duk sanda kunnuwanta suka tuna mata sautin kiran sunansa da tanja tayi.

Satinsu daya suka gama huce gajiya,sai ama ta fara diban jikokinta suna fita shan iska. Kullum da inda zasu,sai idan sun dawo kaji labari cakwai a bakin benazeer,don ba kasafai batoul ke da surutu haka ba. Hasalima ita saita nema debo dabi'un abbanta sak da sak,tana da wani irin miskilanci da kuma basarwa. Haka kawai idan taso saita tashi da 'yan shirun, benazeer tayi hirar duniya taqi kulata,idan taga haka tasan tana nufin yau ba zasuyi wasa ba ko ifce ifcensu da suka saba ba sai tahau tsokanarta,ba kuwa zata qyaleta ba har sai ta sakata kuka,sau tari sai ama ta shiga tsakani,ko kuma idan suka cikawa sultana kunne ta leqo shikenan sai benazeer din tayi laqwas ta shiga taitayinta.

A irin wannan lokacin ama kan zauna kawai tana binsu da kallo, zuciyarta tana mata haske tana kuma mata fari,wani lokaci kuma damuwa ta cika zuciyarta,dukkansu su biyun sun dauko attitude na mutum biyu ne, benazeer sak SULTANA tana yarinya,batoul kuwa MAINA ce har yabar gabansu.

Duk da garine dake da ababen kallo sosai,gari ne dake da ababen sha'awa amma ita bata sha'awar fita ko ina. Zaman kadaicin da taketa yi ya sanyata karance karance a matsayinta na wadda keson fadawa harkar karatun jarida,a hankali har abun ya zame mata jiki. A nan taga wata makarantar koyar da girke girke na qasashe daban daban,koda ta duba kudin registration din sai taga yayi yawa,don haka ta maida site din ta rufe bata sake budeshi ba. Ranar ama ta karba aron ipad dinta taga ta soma register,ta fahimci yawan kudin ya hanata qarasawa. Murmushi ama tayi,sultana..... sultana,akwai barin kashi a ciki,ba zata taba bude baki tace ga matsala ko damuwarta ba,sai ta shiga site din ta qarasa komai ta biya kuma kudaden,sai gayawa sultana tayi ranar da zata fara zuwa.

Nauyi da kunyar ama suka sake kamata,tana kunyar yadda ta azama kanta dukkan nauyinta,komai nata itace,bata qyashin kashe mata ko nawa ne, ba'a maganar su benazeer da suke fuskantar wani irin gata,idan akace gata ana nufin gata na qarshe,irin gatan da ake kwatance dashi. Komai nasu me tsada ne,komai nasu kuma na musamman ne,hatta kuwa da brush da zasu wanke haqoransu. Amma kuma duk da gatan da ake gwada musu hakan bai sanya sunyi lako lako da tarbiyyarsu ba. Sosai suke samun kulawa da tarbiyya,don ama da kanta take koya musu qur'ani. Da yake sunyi gadon kwanya,sai gashi da qananun shekarunsu sunyi nisa a alqur'ani,hadda kuma tartilan cikin qwaqwalensu. Ta siya musu kayan karatu kala kala da zasu taimaka musu, harshensu kuma ya fara juyewa da qira'ar sheik imam khusari.

Makaranta me kyau aba ya duba ya sakasu,inda suke karatu da dukka harasa biyun, French da English harda qarin larabci.

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂


*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 41



Cikin watanni biyu aba yayi settling komai ta fara zuwa makaranta. Qaramar mota ya siya mata daidai d'iya mace,ta kaita makarantar koyon tuqin mota ya zube kudi ta koyi tuqi da kyau suka bata license. Hakan ya mata dadi qwarai,don ta huta da tafiya railway ko kiran taxi.

Shigarta makarantar ya sake sanya idanunta suka bude da rayuwa,ta qara sanin mece duniya?,tarin al'umma mabanbanta masu mabanbantan halaye da dabi'u. Ta sake sanin tabbas duniya tana da girma da fadi,taga kalolin tarbiyya iri iri al'adau dabi'u da kuma halaye,wanda kusan kullum idan ta dawo sai ta bawa ama labari. Murmushi kawai ama keyi,itama sai yanzu take sake tabbatar da quruciyarta,lallai a baya in banda quruciya da tabara babu abinda sultanan ta sani. Duk da haka suna biye kuma suna kula da ita,ko don girman igiyoyin dake saman kanta,wanda tun wancan lokacin da bibi tayi magana ba'a sake tada zancan ba.

Suna exam semester farko aba ya ajjiye musu visa dinsu na zuwa umra. Ranar kasa bacci sultana tayi. Hakanan Allah ya jarabceta da son zuwa madina da makka,tun daga sanda ilimin addininta ya fara zurfi ta fahimci muhimmancin gurin gaba daya zuciyarta ta tafi can.

Washegari goumar ya dira a Paris,sai a sannan tasan dashi za'a yi tafiyar. A sannan tana parlor tana duba wasu litattafai nata door bell tayi qara,tanja ta bude masa ya shigo riqe da jakarsa. Daga benazeer har batoul yarda abun wasan hannunsu sukayi sukayi kansa kamar zasu shide saboda murna,shi kuwa ya tattarasu duk da girmansu ya dagasu yana zagaye dasu.

Har suka gama abinsu tana zaune bata daga kai ba,sai da suka nutsu suka zauna tanja ta ajjiye masa drinks da snacks tana gaya masa ama tana bandaki,sai ta fara tattare litattafanta da zummar barin wajen idanunta na kallon litattafan nata tace dashi

"Ina yini,kana lafiya?"

Gwanin tsokana baya fasa halinsa,tabe baki yayi yana cewa

"Nidai ban roqi gaisuwa ba bare a wulaqantani ehe,meye wani ina yini kana lafiya?" Tsaiwa tayi da abinda takeyi ta xuba mishi fararen idanunta, kwanyarta na mata tariyar tarin kamanceceniyar halayya dai da uban dakinsa sarkin zalunci da mugunta wato maina kaman yadda ta rada masa

"Kaidai ba'a iya maka wallahi,Allah ya sawwaqe" saita dauki kayayyakinta a hannu tana yin gaba

"Ya kyauta mana gaba daya,mutum se shegen qunci da dacin rai kamar wanda aka kashewa diyan fari" ya qarasa fada yana galla mata harara. Tasan halin goumar,baiqi su kwana sunayi ba,don haka ko waiwayoshi batayi ba ta shige dakinta,amma ranta cike fal dashi,tana kuma tunanin hanyar da zata bi ta taka masa burki,yadda yake shige mata sharafi ya soma isarta hakanan.

Bata qara bari sun gamu ba sai ranar da zasu wuce. Tafiyar tasu dukkansu ce,harda tanja,amma sai ya zamana duk cikinsu sultana din tafi zumudi saboda a wajenta tamkar zuwan farko ne.

Tafiyar awanni tara bayan yada zango a wani qasar Wizz Air Malta ya saukesu a filin tashi da saukar jiragen sama dake garin madina don can suka fara sauka. Wata ajiyar zuciya me qarfi ta sauke kamar wadda aka finciki zuciyarta. Ta furzar da iska daga bakinta tana jin daukin ganinta cikin masallacin ma'aiki. Daga wankansu cin abincinsu a masaukinsu zuwa fitowarsu masallacin duk sai taji kaman basa sauri,ji take kamar duk duniya ita daya keda buqata,kamar duk duniya ita keda damuwa a qirjinta,kamar kowa baya da matsala sai ita kadai. Tana ganinta a raudha kuwa kuka ta saki sosai,saidai qasan ranta taji nutsuwa tana saukar mata,wannan ya taimaka ta samu nutsuwa tayi addu'a sosai.

Dukka kwanakin da sukayi a madina babu wanda bata amfaneshi ba da tarin addu'o'in da ita kanta batasan adadinsa ba. Sai gata a yau wai itace da yiwa ummanta NAFESSA da mahaifinta HAMANI addu'ar samun rahamar ubangiji,lallai hankali da nutsuwa ya samu,madalla da wannan rayuwa data samu sauyinta.

Randa suka sauka a garin makka kuwa kayanta kawai ta ajjiye tayi wanka ta fice,ko ama su benazeer ta barwa sallahu su gaya mata ita ta wuce harami. Ta kasa nutsuwa don masaukin nasu daga nan idan ta bude window din dakinsu tana gano harami sosai,saita dinga ji kamar ana fusgarta.

Sanda suka fito ma ita ta bace cikin masallacin,don haka ama ta fara tata ibadar, benazeer da batoul ma sukayi nasu waje,wanda ama batasan ma ina sukaje ba sai da suka dawo hannu dumu dumu da siyayyan kayan zaqi,tunda kafin su fita dama already aba ya basu kudi a hannunsu.

Da rigima suka dawo,mutuniyar batoul tayi kicin kicin da fuska tana harara benazeer,tambayar duniya taqi bayani sai ice cream da ta saka a gaba,ita kuwa benazeer ba abinda ya shafeta ta zauna ta bude abinta ta fara sha tana dariya. Da kallo ama ta bita,sak yadda sultana ke cakar da yara zamanin quruciyarta da shegen tsokana da yiwa yara dariya. Daqyar ama ta lallasota ta gaya mata

"Mutane take kulawa ama,sai kuma tayita basu labari mu 'yan nijer nigeria da paris ne" waiwayawa aman tayi tana duban benazeer,suna hada idanu jikin benazeer din yayi sanyi saboda tasan kalar wannan kallon na ama

"Bana hanaki dogon surutu irin haka ba benazeer?,kina so na saka wuqa na rage miki tsahon bakinki?" Da sauri ta girgiza kai idanunta na hada hawaye

"To daga yau na hana,idan zakuje siyan abu kuje ku dawo,ba ruwanku da kowa kina jina?" Kai ta gyada mata tana lanqwashe qafafunta taci gaba da shan sanyinta. Dariya taso qwacewa ama,wato tsoratar da itan da tayin bazai hanata qarasa shan kayanta ba

"Gado ba karambani ba" ta furta can qasa tana sake tuna mata da sultana da qananun shekarunta cikin qasar nijer mansion house na MAYAK'I family.

Da wata irin kasala mutuwar jiki data zuciya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login