Showing 63001 words to 66000 words out of 294767 words
Chapter 22 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
duban Metron asabe. Hannu ta sanya ta yafitota,dan jim tayi sannan ta fara takawa tana nufarta.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 33
"muje kiyi wankan kafin lokaci ya qure" Metron asabe ta fadi tana amsar mata bucket. Ba musu ta miqa mata,Metrom tayi gaba sultana na biye da ita. Duk sai su fatima suka bita da kallo,can qasan ranta itama sultanan tana mamakin yadda metrom din ta kebeta ita daya.
Toilet dinsu da iya su yasu ta sanya muqulli ta bude ma sultanan ta shiga. Duk da a tsaftace yake amma sai ta dinga jin wani bawai. Sam baiyi koda rabin toilet din da ma'aikatan gidansu ma ke shiga ba. Hakanan tayi wankan a gaggauce saboda jaddada mata iya sauran lokacin da ya rage da Metron tayi.
Koda ta isa hostel an fara counting an kusa kaiwa qarshe,hakanan tabi lafiyar gadonta ta kwanta. Bata wani matsawa kanta can bama baccin ya dauketa kasancewar tana da buqatar yinsa,don tsahon rayuwarta bata taba daukan lokaci haka yini guda tana a tsaye ba,bata jurewa wahala aam,shi yasa take gudun islamiyya kamar me?. Babban abinda ya sanya ta tsani boko kuwa baccin safe da take hana mata,ta tsani tana bacci a yanke mata shi,yanzun zakaga bacin ranta.
Ilai kuwa tana tsaka da baccin sautin muryar fatima ta ratsa kunnenta. Bata gama wartsakewa daga bayanin fatiman ba taji wannan kakkaifar muryar wadda tamkar an halicceta ne don qididdige musu mintuna ta fara musu lissafi. A kasalance ta jawo hijab dinta na house wear ta zura,ta sauke qafafunta qasa tana saukowa daga saman gadon tana jan wani mugun malalacin tsaki. Kanta gaba daya sara mata yakeyi,wannan wanne irin stress ne haka?.
Sallah suka sake wucewa sukayi cikin jam'i kamar dai ta azahar,sukayi dukkan azkar sannan suka wuce babban filin da suke zama don maimaicen karatun da akayi a ranar. Yana daya daga cikin dokoki da qa'idan makarantar. A bisa radin kansu kowanne zaiyi muraja'ar karatunsa,cikin rukuni,idan kuma anso awarwartsasu kowa shi kadai. Ajinsun ta lura suna da himmar karatu,team guda sukeyi suna yiwa juna tuni da qarin haske,a yanzun ma hannunta saman habarta,littafinta a bude amma kuma idanu ne nata. Ta baza dukkan hankali da nutsuwarta amma har yanzun bata fahimci komai ba,sai ta sauke ajiyar zuciya,wani abu yana darsuwa cikin zuciyarta,wani abu da bata taba jin irinsa ba sai a wannan karon.
Sha'awar taga ta iya karatunta kaman kowaacce daliba,tana karantashi sosai kamar yadda taga Fatima ahmad da ameena aleeyu nayi,bisa dukkan alamu ma sune jagororin zaman,ta fahimci suna ganewa matuqa,sai suka dinga bata sha'awa ta dinga binsu da kallo.
Karfe biyar suka koma hostel,masu wanka gyaran gado,saka net duka suna aikinsu,tana zaune tana sake nazarin kowa tare da bin kowa da kallo. Ameena aleeyu ta taba kafadarta tana kallonta
"Ki gyara gadonki sultana,kinsan komai namu yana da qayyadadden lokaci,qarfe shida zamu fita a nan,idan ka wuce haka kuma sai kayi zaman istigfari,ga punishment" ta qarasa fada tana dariya saboda tuna makarar da Fatima ahmad tayi wata rana da lokaci ya qwace mata
"Wai dama istigfari din da ake tsareka kayi shima wani azabar ne ban sani ba?,saika bude duk muryarka ka qwala da qarfi kamar wanda kake saka ran mutanen sama su tayaka lissafawa?" Maganar ke sanya ameena aleeyu dariya har yau,duk sanda kuman tayi dariyar fatiman tasan da ita take,to in sha Allah sai takai mata duka. Kamar yanzun ma dundu ta bita dashi tana sauke net dinta,ameenan ta qwace tana gocewa,sai Fatiman ta zarto gadon sultana tana cewa
"Tashi na kama miki mu gyara muyi mu fita da wuri" ta fuskanci duk irin gatan da suke taqama dashi sultanan ta damesu,ta sake tabbatar da hakan sanda sultana ta kasa tabuka komai. Batasan ta yadda zata kama zanin gadon ta zaunar dashi sosai saman katifar ba ballantana net din da bata taba bacci qasan net irinsa ba,na saman gadonta ba irin wannan bane sam sam sam,aba ne ya siyo mata shi musamman daga turkey,daga gadon har net din,shi kansa duk da kyau da tsadarsa bata fiya shiga ciki ba,don gidan kwata kwata basusan wai wani abu da ake kira sauro ba bare sauran qwari,gida ne dake bisa tsari yake samun cikakkiyar kulawa daga ma'aikata kowanne lungu da saqo na gidan
"Kaman haka a irin wannan lokacin muke gyara makwancinmu,duk lokaci irin wannan sai na tuna da talatu" fateema ta fadi tana dariya dariya
"Suna qoqari sosai,a lokacin bakasan zafin abun ba,sai yanzu da rayuwar makaranta ta gaya maka" ameena itama ta fadi tana tata dariyar. Lokaci lokaci sukan zauna suyi hirar masu aikin gidajen nasu,zuwansu makarantar ya sanya suka qara ganin kima da matsayinsu da kuma girman hidimar da suke musu.
Hannu kawai sultana ta sanya ta dafe goshinta,itama tanja ce ta fara fado mata,sau daya kuma koda wasa bata taba daga tsintsiya da sunan share dakinta ba,hatta suturarta idan ta cire tanja ke killace mata,me taci?,me zataci,dukka suna wuyan tanja,hatta panties nata washing machine ke hidimat wanke mata su,yau gata cikin rayuwar yiwa kai komai,ba kuma cikakken 'yancin lokaci,sai iya abinda aka qayyade maka.
"Ya Allah" karon farko ta furta sunan ubangiji da a lokacin zuciyarta ke ayyana mata shine zai dafa mata,ta waiwaya ta sake kallon gadon tana mamakin yadda fateeman ta gyarashi tsaf,ita dinma kamarta kenan take ada?,dole ta sanyata koya?,ta yaya ta kuma ina ita zata fara nata koyon?.
A masallacin sukayi magariba,suka sake komawa kitchen sukaci abincin dare,sukayi isha'i sukayi tilawar litattafan addini sannan suka wuce makwanci.
Kamar jiya din,yauma da farko juyi ta dinga yi,gaba daya yininta na yau take nanatawa cikin ranta. Wata irin rayuwa data banbanta da rayuwarta,ta banbanta da rayuwar data saba yi,yau gata tsundum cikin makaranta, makarantar da babu abinda ta tsana sama da ita,yau sai gashi ba jeka ka dawo bama makarantar kwana ce. A Hankali tunaninta ya gangaro kan yadda rayuwar karatunsu take. Kowa kusan gwanine za'a ce cikin daliban,tana hangen yadda kowa ke zagewa ya kuma dage don ganin ya kai maqurar iya karatunsa,ta tuna yadda a kowanne darasi ta dinga baza idanu,nan da wani lokaci idan batayi da gaske ba zata zama cikin sahun dalibai na kashin baya,wadanda kowa zai fahimci qarancin ganewarsu. Wannan tunanin ya sanyata hantsilowa daga gadonta,wani abu yana dasa mata qaimi cikin zuciyarta,tana jin ba zata lamunci faduwa ko rashin iyawa ba. Ta saka hannu gefan gadonta inda qaramar locker dinta take ta fidda jakar makarantarta,ta zazzage dukka litattafan da a yau sukayisu,ta soma budesu daya bayan daya tana dubawa.
Da qur'ani ta fara,ta dinga hada baqin yana guduwa,ta dinga qoqarin maimaita shafukan daidai,a haka ta kashe awa daya kusan da rabi kafin taji ta fara kama hanyar karatunta bisa qa'ida. Bata sare ba bata kuma gaji ba,tayita nacin maimaitawa har sai da taji ya zauna mata a harshenta,ta tabbatar zuwa gobe koda za'a ci gyaranta kadanne. Kowanne subject sai da tayi maimaicinsa,tun bata fahimtar abinda take ta faman karantawar har sai da taji kamar qwaqwalwarta tana budewa ne a hankali. Sanda ta duba agogo awa uku kacal ya rage lokacin tashinsu dsga bacci yayi. Sai ta zauna tsakiyar gadon tana son tuna addu'a daya daga cikin tarin addu'o'in da taji suna yi,yayin tashi a bacci,kwanciya bacci,cin abinci,shiga bandaki,shiga aji da komai ma na rayuwar daliban makarantar. Ba wani abu guda da taga wani dalibi yayi bs tare da yayi addu'a ba,tamkar ma ta shiga jinin jikinsu ne sun kuma saba. Duk sallolin da akayi yau din cikin jam'i abinda bata taba yi ba tsahon rayuwarta......duk sanda aka idar suka hada baki duk yawansu suna addu'o'in da akeyi bayan idar da sallah,sai taji wani sanyi dadi da nutsuwa suna shigarta,sai taji wani sukuni yana ratsata,har sai taji kamar ma kada lokaci ya cika, kamar kada su daina addu'ar.
Waiwayawa tayi ta dubi su fatima dake bacci abinsu. Cikin ranta ta ajema kanta zasu zame mata mudubi in sha Allah cikin rayuwar makarantar,zata kuma yi qoqari tayi catching up na dukkan abinda suka tsere mata.
Abunda ya bawa su fatima mamaki a yau ita ta tashesu maimakon jiya da sune suka tasheta,kafin kace meye ta kammala komai da sukeyi kafin fita masallaci sallar asuba. A bakin hostel din suka cimmata tsaye da metron asabe tana gaidata
"Ina fatan baki da wata matsala ko?,idan kun kammala karatu kina da sha'awar wanka kafin ki wuce aji kiyimin magana saiki shiga kiyi"
"Ba komai,zan jira har lokacin da kowa yakeyi,idan ban samu toilet ba zan miki magana sai nayi s gurarenku din" ta amsa mata tana rungume da qur'aninta cikin wata murya me sanyi. Da kallo metron asabe ta bita,bata taba zaton zata sameta da sauqin kai har haka ba,bata taba kawowa cewa zatayi saurin daukan shawararta ba,sai gashi daga jiya zuwa yau kacal tana qoqarin kiyaye dokar makarantar.
Yadda ta dinga nacin bibiyar kowanne harafi da ake qara musu ya sauqaqa mata qwarai. Kafin akai ga tashi sai gashi ta iya karatun fes kamar kowa. Dadi sosai ta dinga ji cikin ranta,har kuma hakan ya nuna a fuskarta,duk da ba murmushi takeyi ba amma fuskarta a washe take sarai.
Gurin sharar compound na hostel dinsu kuwa kamar kowa ta karbi tsintsiya. Metron asabe na cewa ta bari amma tace zata iya. Tana sharar tana mamakin meye dalilin metron asabe nason dauke mata wasu wahalhalu na makarantar ne?,me yasa take kawo mata hanyoyi sauqi da sauqaqawa?,ahalinta ne fa da hannunsu suka danqata a makarantar,komai na ama bisa manufa da tsari yake,ta tabbatar ba a banza ama ta aikata hakan ba,ba shakka akwai dalili,kuma akwai hujja.
Koma meye ita dai ta barma ranta zata rayu kamar kowa,tayi alwashin zatayi irin rayuwar data samu cikin makarantar,zata rungumi kalar sabuwar K'ADDARAR da ta risketa. Can kuma qasan ranta takejin kamar dai ama ta kawota ne don tasan rayuwa?,kamar dai ama ta kawota ne don ta fahimci bayan duniyar da take rayuwa a ciki akwai wata duniyar ta daban?,kamar dai ta kawota ne saboda wasu abubuwa masu yawan da ita kanta bata gama fahimtarsu ba.
Tana ankare da yadda labour prefect huda keta wani fusge fusge da sanya mutane aiki cikin izza da gadara. Duk wanda ta kira ita da team dinta da sassarfa yake isowa ya kuma zube yana kiran
"Aunty gani" ladabi ne wannan na makarantar da dole kowanne dalibi ya koya ya kuma ginu akai,amma batajin zata iya zube musu har haka,hasalima batajin tana da LOKACIN shiga sharafinsu.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 34
Lokacin data sake kame kanta tare da takatsantsan da lamarin huda da sauran maqarrabanta ita kanta sai tayi mamakin kanta,har batasan sanda qaramin murmushi ya subuce mata ba abinda ta jima bata yishi ba,wai yau ita sultana ita ke kaucewa rigima da wasu,ita sultana da batajin tsoron rigima da ko waye,mace ko namiji,yaro ko babba,bata tsoron tunkararka ko qaddamar maka,lallai giwa tayi lafiya ta fadi qasan zuciyarta tana shafar gefan fuskarta,to ko hankali ta soma yi?,ta yiwa kanta tambayar data sanyata sakin wani murmushin.
*****A hankali A hankali cikin wani irin yanayi sauyi na bazata ke ruskar rayuwarta. Ingatacce kuma gamsashen sauyin da yayi nasarar taba ainihin ruhi da zuciyarta. Cikin ba zatar da ita kanta bata sani ba ta tashi daga SULTANAn bibi,sultanan aba sultana ta nijer zuwa sultanan Nijeria,sultanan hassan Ibrahim gwarzo,sultanan fateema Ahmad da kuma ameena aleeyu. Ba wanda take bari ya huta tsakanin fateema Ahmad da ameena,kowannensu ta samu ta riqeshi to tabbas sai yayi mata qarin dukkan wani kwantan karatu da aka tsere mata,tashin cikin dare ya fara bin jikinta,a lokacin da kowa ya sanya haqarqarinsa yake bacci.....a lokacin take tashi bita da tilawar katatuttukanta. Cikin kowanne mataki na karatunta batajin akwai ya kamar ALQUR'ANI. Tana jinta wani fresh a sanda take karantasa,tana jin wani softness cikin zuciyarta,tana jin kuma nutsuwa tana shigarta,shi ya sanya cikin lokaci qanqani ta kamosu ta kuma hade da izifin baya da suka wurwuceta,abinda ya baiwa kowa mamaki,sauri da kaifin basirarta,duk da a farko sun mata kallon hadarin kaji,kallon dalibar da bazata wani basu matsala ba. Tana da rivals da yawa a ajin,matan da sukaci buri suke ganin sune na gaba gaba wajen samun yarda da amincin malamansu,sai gashi cikin dare daya wata baquwar haure na shirin yi musu shalll. Wata irin murya Allah ya mallaka mata me dadi,sai take sake qawatuwa da sautin karatun qur'ani da wani irin daddadan sauti.
Bata da lokacin kowa,ba wanda take bi ta kansa,bata kuma hulda da kowa idan ka debe fateema da ameena. Muddin kaga hirarta sosai to da sune,idan kaga motsawa kumatu da labbanta to da ameena dinne,sun dinke sun zama kaman wasu 'yan uwa, dabi'a da yanayin sultana din su ke burgesu,suna mata kallon wadda gayu gata da shagwaba suka yiwa yawa shi yasa komai nata ya fita na dabanne.
Kowanne kwanan duniya sai metron asabe ta tambayeta ko tana da wani buqatar?,amsarta daya ce A'ah,a nata tunanin tanason gwadawa ama zata iya rayuwar data zabar mata,zata kuma wanzuwa a kowanne bigire ko muhalli da rayuwa ta gangarata cikinsa.
*_VISITING DAY_*
Tun daren jiya daukacin daliban makarantar ke cikin farinciki da walwalar ganin ahalinsu a goben,kamar yadda fateema da ameena aleeyu suka bi sahun sauran dalibai.
Safiyar yau din kowa shiryawa yakeyi don 'yan gidansu su ganshi fes..... sultana na zaune kusan sai da kowa yayi nisa wajen nashi shirin,wasuma suka soma fita sannan ta shiga tayi nata wankan da yau ta zabi tayi cikin tsaftatattun toilets dinsu ba nasu metron asabe yadda ta saba yi ba.
Komai nata cikin wani sanyi da nutsuwa ya koma,babu sultanan nan ta anihi,haka ta tsaya gaban gadonta ta shirya kanta cikin house wear kaman kowa,bayan ta daure jelar manyan kitson da fateema da ameena sukayi taron dangi sukayi mata,saboda sulbinsa da tsahonsa ya sanya ba kasafai take kitso ba,koda anyim ma baya dogon zango yake warwarewa.
Tayi kyau sosai,don sabbin house wear ta sanka,dinkin kuma ya zauna sosai ya qara fidda tsaho data qara,saidai kuma tadan fada kadan wanda hakan baya rasa nasaba da sabuwar rayuwar da take qoqarin daidaita kanta taga ta hauta bisa tsari.
"Sultana mohmoud mayak'i" aka maimaita kiran sunanta har sau uku. Waiwayawa tayi tana duban me kiran nata,senior dinta ce cikin wadanda zasu fita makarantar a shekarar da ake ciki
"Kina da baqo" ta fadima sultana din tana juyawa. Turarenta ta miqa hannu da sauri ta dauka ta fesa ta maidashi,sannan ta zura house shoe dinta ta soma tattakawa cikin wani irin zumudi tana ratsa hostel din nasu
"Tacan zaki zagaya" dalibar ta fadi tana mata nuni da hannu sannan ta wuce gararin gabanta.
Sosai take takawa da zumudinta shiyyar da ta nuna matan,qasan ranta cike fal da dokin ganin ama da aba,tasan kuma zaiyi wuya ace bibi batazo mata ba,BATOUL da BENAZEER......taji an kira mata sunan yaran daga can qasan zuciyarta,ta lumshe idanunta murmushi na subuce mata,wata irin mahaukaciyar kewar yaran ta taso ta lullubeta,karon farko daga can qasan ranta taji wani irin tausayinsu ya saukar mata.
Tsaiwa tayi cak ganin tana ta cusa kai area din da babu motsin kowa babu kai kawon kowa. Ta tayi ta tsaya cak,wai mema dalibar tace mata ne
"Kinyi baqo" ta tuna da abinda tace
"Baqo......baqi...." Sai taji kwanyarta ta rikice. To ko aba ne shi daya ya samu zuwa?,idan hakane ai ba za'a barshi ya qaraso har gate na biyu na sashen mata ba,akwai askar da basa bari maza su wuce gurin,kuma bata nan ya kamata ya tsaya ganin nata ba.
Wani mummunar bugawa zuciyarta tayi. Cikin jini tsoka da jikinta taji kamar ana fusgar hankali da kuma numfashinta sakamakon shaqar wannan qamshin.......wannan qamshin dai da hanci zuw qwaqwalwa ba zasu iya gaza fayyaceshi ba,wannan qamshin dai da yake da taushi dadi