Showing 90001 words to 93000 words out of 294767 words
Chapter 31 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
cikin gida daya,kamar a nan zasu dawwama da yaran. A kullum bayan sallar isha'i sai ya zauna ya jirayesu. Duk irin yadda yake girmama lokaci......duk irin yadda ya tsani jira cikin rayuwarsa,duk kamewa irin tasa da rashin shiga sharafin kowa.......duk uban miskilanci da tsananin ginshira irin nashi amma bayan sallar isha'i saiya bata wananna awa daya zuwa biyun. Ko yana zama su iso,ko yazo ya samesu zaune a wajen suma suna jiransa. Ice cream da chocolate sun sha har babu iyaka,masu tsada ya koma siya musu irin wanda canjin da ama ke sanya musu cikin jaka bazai isa su siya ba,babu kuma me biyewa ciye ciyensu a cikinsu bare ya bisu ya siya musu da nasa kudin,don dukkansu sunsan girman wajen,zaman masallacin yafi komai cinye lokacinsu a wuni guda.
Tunda benazeer ta fahimci a ranar zuwa azahar jirginsu zai bar makka hankalinta ya soma dagawa,tasan dai ba zasu kai lokacin da suka saba haduwa da uncle ba bare suyi sallama,ta kuma gaya masa zasu tafin. Gaba daya sai ta kasa sukuni,tana cikin kujera a kwance tana ta kallon batoul dake cin chips da fork,tana ta son ta kalleta suyi shawarar yadda zasu ga uncle su gaya masa zasu tafi,shima yaushe zai tafi?,yaushe kuma zasu sake ganinsa?.
Yawan surutu kuzari da karsashin batoul ya sanya kusan kowa ma ya fahimci tana da damuwa. Tuni sultana ta fahimta,amma saboda kawaici da batason fiya zaqewa cikin lamuran yaran bayan ga qashin bayansu nan jigonsu a gurin saita kauda kai,saidai kuma tanata monitoring komai nata,ta kuma karanci tsaf akwai abinda yake damunta ya kuma hana mata sukuni.
Qaramar akwatinsu da ama ta shirya musu tsaraba a ciki tazo ta ajjiye,saita juya kadan tana kallon benazeer
"B....me yake damunki yau?" Tayi tambayar cikin salon nuna muhimmancin tambayar saman fuskarta. Zamewa tayi ya sakeyin lamo cikin kujera,sannan ta motsa qaramin bakinta
"Ba komai"
" Da gaske?" Kai ta gyada a hankali
"Ko kuma kayan shaye shayen sanyin nasu takeso ba,tunda na fahimci duk sun zama shazumamu,sunma fi uwarsu son shan jarabbaben zaqin nan ai" Dariya ama ta danyi,ta jawo purse dinta data shigo da ita ta fidda riyals tana cewa
"Su kenan suka ragemin dama......aje a siyo na bankwana" ta furta tana murmushi. Idanu sultana ta dauke gefe zuciyarta na motsawa,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin soyayya tsakanin kaka da jikokinta ba irin ta ama da su batoul. Haqiqa bibi ta sota,ta qaunaceta,ta kuma nuna mata soyayya me yawan gaske.....amma akwai wasu kusakurai da ramuka masu yawa a hanyar,wadanda tasan ta tsallakesu ne kawai saboda qilan taci albarkaci ko darajar wani ne.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 48
Da sauri benazeer ta miqawa ama qaramin hijabinta ama din ta sanya mata, batoul ma ta ajjiye abincin tana sanya lausasan wasu rufaffun takalma masu kyau suka sanya kai suna ficewa riqe da hannun juna,ama ta bisu da
"Ayi addu'a"
"In sha Allah" suka hada baki wajen fada.
Sai da benazeer ta tabbatar sun sauka sannan ta kalli batoul
"Nifa uncle zan nemo na gaya masa mun tafi fa" ido batoul ta zaro tana kallonta
"A ina zaki ganshi?"
"A inda muke zama,muje mu siya ice cream sai mu dawo mu wuce ta wajen ko zamu ganshi" dan jim tayi kaman me nazari,sai kuma tayi murmushi
"Muje to".
Shop din da ya saba kaisu suka shiga,suka zabi kowa flavor din da yakeso,har ma'aikatan wajen suna tsokanarsu
"Yau babu fada?,ina uncle din nasu?" Dariya sukayi, benazeer tace
"Baizo ba?,nemansa muke" daya balaraben yace
" Tare kuke zuwa, sai dare yake zuwa tare daku" basu wani fahimta ba,sundai gane kawai baizo ba don haka suka sanya kansu suka fice benazeer na cewa
"Ma'assalama". Suna riqe da ice cream din suna sha suna kuma bin duk hanyar da suke ganin zasu iya ganin uncle haidar amma babu shi babu dalilinshi,har batoul ta gaji,taja tunga sanda aka soma kiran sallar azahar
"Kizo mu tafi gida tunda bamu ganshi ba,kada aunty tayi mana fada,ama ma kuma tace fa mu dawo da wuri" juya idanuwa benazeer tayi kaman me shirin sakin kuka,ta sake waiwayawa bayanta kamar me fatan ta bude idanunta ta ganshi a wajen,saita dawo da kallonta ga batoul wadda itama dinma duk ranta ba dadi
"Muje" ta fadi a sanyaye. Haka suka jera suna komawa hotel din ba um ba um um. Sanda suka isa dakin duk sun fice zuwa sallar azahar,amma kuma kayansun sun gama hadasu tsaf,kowacce saita samu waje tayi lamo ba wani me magana ko kuzari a cikinsu.
Koda suna shirin fita a dakunan saida ama tayi qorafi
"Anya lafiya kuke kuwa.yau dinnan?" Ta fadi tana taba wuyansu,sanyi taji ba alamun zazzabi ba komai,batoul ce tace mata ba komai
"To Allah yasa alkhairi" aman ta furta,saboda tsahon tarenta da yaran bata taba ganin jikinsu ya mutu haka ba.
Nannauyan numfashi ta sauke tana furzar da iska daga bakinta. Cikin ruhinta takejin wani salama da nutsuwa suna saukar mata,zuciyarta kuma tana gaya mata tayi masa nesa ta tsere masa. Ta window din take kallon fadin sararin airport din,tana jin kewar barin qasar kamar yadda ta saba,amma tana jin farinciki idan ta tuna ta tserema idanun maina,sannan nan gaba kadan zata dawo ta sake ziyartar dakin Allah.
Tafiya miqaqqiya daga birnin makka har zuwa qasar nijer. Tafiyan awanni goma sha daya suka sauka a niamy,daga nan wani jirgin suka sake hawa suka wuce marad'i.
Iska ta shaqa sosai ta qasar nijer sanda tayi relax cikin daya daga cikin lafiyayyun motocin mallakin aba da ama. Wasu emotions suna cakuduwa cikin zuciyarta,qamshin qasartata yana motsata tare da tuna mata abubuwa masu yawa,wanda kusan fiye da rabinsu quruciyarta ne......yarinta da zallar wauta da ta tafka a rayuwarta,wani abun ya sanyata murmushi wani ya bata takaicin da shima din dai murmushi ne na dole ke qwace mata.
Tun barinta nijer zuwanta daya kacal......wannan shine zuwa na biyu da tayi,zuwan daya banbanta da zuwanta na farko. A yanzun ta sake dawowa qasarta a matsayin cikakkiyar sultana,me yara har guda biyu,wadda ta mallakin hankalin kanta......sannan masaniya cikakken sani a harkar ilimin jarida. Sultanar da a yanzun kai tsaye zaka iya kiranta da madam. Dukkan wata sura da halitta nata na kyawu ya gama cika,ya kuma cakuda da zallar kwarjini da hasken ilimi. Ta zama classy qwarai,ta banbanta da girman tazara da wancan sultanar me rawan kai yawan surutu fitsara da rashin kunya. Yanzun ta zama wata sultana me yawan shuru shuru,wadda ba shirgin kowa take shiga ba,abinda ya shafeta ma ba kowanne take daga idanu ta kalla ba har ta bashi lokutanta.
Isowarsu qofar makeken gate din mansion house din mallakin MAYAK'I ya sanyata daga tsintsiyar hannunta tana gyara zaman siririn agogon gold din dake hannunta,lokaci ta duba murmushi ya subuce mata sanda hancin motarsu ke shiga harabar gidan. Ba wani abu ta tuna ba illa lokaci irin wannan da take hada dabar hira,sam qawaye mata a sannan ba damuwarta bane,maza ma sunfi mata dadin qawance qwarai,saboda su din zata musu tsiwa tayi musu fitsara kuma su daga mata qafa don suna kallon ita macace kamar sauran mata. Idanunta cikin farfajiyar gidan da ta sake qawatuwa qwarai,anyi mata gyara sosai,da alama kuma dukkan gyaran yana da nasaba da bikinsu aminata ne. Ko ina yayi fes,tamkar sabon gini,tamkar ba wannan tsohon ginin da qarfi d kuma qoqarin NADEEYA ya samar dashi shekarun baya ba. Ko kusa ko alama mamallakan gidan basu taba barin tsufa ko shekaru su cimmasa,saboda kusan koda yaushe cikin aikin gyaransa suke,duk wanda ya samu dama a cikin kawunnan nata saidai kawai mutanen gidan suji ana shelar a kwashe ko za'a yi aiki.
Idanunta ta janye sanda suka sauka a wannan bigiren....muhalli ne da kusan yafi zama a cikinsa akan ko ina cikin gidan,waje ne da yake zama yana kula da shige ficensu yana kuma monitoring motsinsu da tarbiyyarsu. A duk sanda zata kalli wajen koda sau dubu ne sai taji ranta ya baci sau dubun,shi ya sanya zabinta daya kauda kai a irin wannan lokacin.
Motarsu na tsaiwa kusan duk wanda ke wajen ya ankara da isowarsu. Kafin kace meye wannan mutanen dake cikin gida ma sun fara fitowa tarbarsu. Kusan kowa ya fito ta batoul da benazeer yake. Batoul sarkin rashin yarda da shegen miskilanci da taga ama ta kutsa kai cikin jama'a sai ta koma jikin sultana ta lafe. Abun sai ya soma baiwa sultana kunya,saboda idanuwa data ja mata,kowa sai ya matso ya tsokaneta ya kuma tsokani sultanar,wadda a sannan idan kaga batoul dake jikinta zatayi rantsuwa yayarsu ce bawai uwa mahaifiya ba. Ko kusa ko alama duk qwaqwafinka baka isa kaga alamun sultana ta isa ta mallaki tiqa tiqan yara har guda biyu kamar benazeer da batoul ba.
Wata motar ce ta shigo,najma aminata da yasmine ne a ciki amare. Najma ke driving aminata da yasmine da houda cousin dinsu suna baya,a kujerar gaba kuma djamilla ce itama dukka kakanni daya suke dasu sultana.
A gaggauce najma ta tsaida motar,dukkansu cike da farinciki suke qoqarin fitowa,saidai ta rigasu ma qarasowa,fuskarta dauke da nutsatsen murmushin nan nata,da muryartannan me sanyi tace
"An fara yawon amarcinne?,amma ko a jirani?" Junansu suka kalla da dan mamaki,ba wanda ya kawo zata nema sakewa a cikinsu shi yasa wasu abubuwan ma basu tsara da sunanta ba
"Zaki iya yawo a cikinmu?" Houda ta fadi tana 'yar qaramar dariya. Waiwayowa tayi tana dunan houda da murmushin da ya tsaya saman kumatunta tace
"pourquoi pas?(me zai hana?)" Ta fadi tana kallon houda
"Yar jarida ce ke yanzun a qasar France...... kinga dole muyi takatsantsan karmu shiga ajin da ba namu ba" dole ta sanya sultana sakin siririyar dariya,siraran jerarrun haqoranta suna bayyana
"Banason sharri houda.....har yanzun baki sauya hali ba?"
"Inaaaa......wannan canjin saiku......na rantse bada wasa ba ko.......ban ganeki ba sai da kika matso sosai" kada kai tayi tana murmushi,tasan halin houda da kyau,tun suna qanana,tasu tafi zuwa daya saboda halin tsokana irin nata na da da take dashi
"Amma sœurs(yan uwana)su ba zasu kasa ganeni ba ai"
"Nima canzawarki ta jawo"
"Ku bani hanya naje naga babies dina,don idan aka biye taku naga alama zamu jima tsaye a nan" aminata ta fada tana maida headphone dinta qaramar handbag din dake hannunta. Rufe qofofin motar sukayi suka fara takawa gaba dayansu zuwa cikin gidan,suna tafe suna tattaunawa akan dame dame aka tsara yi a bikin.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 49
Sake duba agogon wayarsa yayi don bai fito da agogo ba. Wannan dubawar yana irge ita ta zame masa cimakin dubawa na goma sha biyar kenan. Zubawa fuskar wayar idanu yayi wadda ke dauke da hotunan yaran,yaja godon numfashi daya sauka har cikin huhunsa. Kanshi ya sake dagawa yana duban jama'ar dake shige da fice cikin haram din wai ko zai ga gilmawarsu,saidai ko twins guda daya bai gani ba bare ya sanya ran dasu a ciki.
Ya fara sarewa da ganinsu yau,saboda tun wancan ranar da suka hadu din basu taba kaiwa warhaka basu iso wajen ba,basu taba latti kaman haka ba,kamar yadda basu bata fashin zuwa ba.
Dauke kansa yayi ya maida idanun nasa qasa,sai ya samu kanshi ya tsawaita a addu'a cikin zuciyarsa na zuwan yaran a nan kurkusa. Bayajin zai samu nutsuwa ko qanqani idan bai gansu din ba,zuciyarsa da rayuwarsa a kwanakin jinsu yakeyi a rikice gaba daya,hatta da suhail da sardauna da basu kusa dashi suna iya fahimtar haka cikin mu'amalarsu dashi.
Duk wata tattaunawa da ya shirya zasuyita through video call ya kasa halarta,wani lokacin ma sai sunyi sun gama zaiga miscal nasu. Idan sun matsa da yabi sai yace musu duk yadda suka yanke yayi. Duk kawaici na sardauna sai daya magantu
"Kafi kowa sani daddy bazai amince da dukka abinda zamuje masa dashi ba saiya tabbatar bisa yarda da sahalewarka ne tunda dai kaine jagora......kuma ma,ta yaya zaka jagoranci harkar lafiya a qasar dake da tsari da doka kana cikin dimuwa haka? what's wrong with you ne maina?" Sumarshi kawai yakan shafa duk sanda suka masa tambaya irin wannan,don baisan amsar da zaya basu wadda zasu fahimceshi su kuma gamsu ba,abu daya ya sani,Allah yana sonshi da ya kawo masa irin wannan yanayin a wajen da dukkan dimautacciyar zuciya ke samun nutsuwa,a muhallin da amsa addu'a bashi da shamaki da ubangijin dake amsa roqon bayi,banda hakan shi kansa baisan a wanne yanayi zaya kasance ba.
Miqewa yayi bayan ya fahimci ya sake qara wasu mintuna ashirin din masu kyau,ya zube hannayensa a aljihun kaftan abaya dinsa ruwan bula(navy blue)wadda ta sake fidda ainihin kyawunsa na cikakken ba'abzine kuma bafulatanin buzu,sai ya tsinci kansa da gangarawa bangaren shops din dake hada hadar saida ice cream da sauran kayan zaqi,wajen da yasan duk dare shi dasu suna zuwa.
Kai kawo ya dinga yi yana duba ice cream din zuwa chocolates din,saidai kawai yana zaba ne shi kansa baisan me zaiyi dasu ba. Nan dinma ya kashe kusan awa guda amma baiga alamarsu ba,har yakai lokacin da.ya tabbatar a irinsa ne suke ce masa sun tafi,daha qarshe ya fidda riyals ya biya uban chocolate da ice cream din da ya zaba yace su kyautar wa duk yaran da suka shigo.
Cikin wani irin nauyin jiki da na zuciya yake komawa swissotel, zuciyarsa a mugun quntace da wani irin rashin dadi,duka ya rasa target dinsa,ba sultana ba kuma yaran,sai ya dinga jin kamar lokaci yayi shima da zai bar wajen,lokaci yayi da zai cimma sultana,cikin nijer......cikin gidansu.
Yana fitowa daga elevator wayarsa ta dauki tsuwwa,sanda ya fiddata yaga me kiran sai da yaji kamar ya kyautar da wayar,don baya cikin mode na amsa kowanne kira. To amma hausawa sukace wata fuskar tafi gaban mari,ko don sardauna kawai kafin akai kan daddy,dole ta sanya ya daga kiran ya kara a kunne.
A yangance tayi masa sallama,da qyar ya hada kalmomin amsa sallamar tata,yana jin kamar numfashinsa baya sauka cikin hunhunsa da kyau
"Am sorry,zan kiraki wani lokaci" dan jim tayi,kamar bataji dadin furucin nasa ba,amma kuma sai tace masa
"Okay" a taqaice sannan suka ajjiye wayar kusan a tare.
Kasa haquri yayi,kafin ya isa daki ya lalubi suhail. Komawa yayi ya jingina da qofar dakin bayan ya maida ya kulle,idanunsa a kulle,kunnuwansa na sauraron yadda kiran ks gangarawa wayar suhail,gefe daya kuma yana sauraron bugun zuciyarsa.
Sama sama suka gaisa,kai tsaye ba kwana kwana ya gabatar masa da uzurinsa
"Banason na wuce kwanaki biyar suhail ban isa nijer ba"
"Why?,me yasa kake caccanzawa kamar wani wahainiya ne maina?"
"je ne sais pas non plus(nima ban sani ba)"ya fadi da harshen faransanci
"Me kace?" Suhail din da yaren turanci yafi yawa cikin nasa harshen ya tambayi maina abinda yace din
"I don't know suhail...... I don't know why"
"But amma kasan a yadda muka tsara zakayi koda one week ne a Paris a gama komai koda a tsaitsaye ne sai ka wuce"
"Noooo suhail,no.....bazan iya ba,koma meye ya jiraci dawowata......na gaya maka.....kwana biyar kadai zan qara a nan din.....bazan canza ba" daga haka ya katse wayar don kada ma suhail din ya sake kawo masa wani hanzarin,don bayajin akwai wani abu a yanzun da zai iya dakatar dashi kai kanshi nijer din.
*********Tunda suka sauka a nijer shirye shiryen biki