Showing 126001 words to 129000 words out of 294767 words

Chapter 43 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ko ta rakata da harara sannan ne zata ja bakinta tayi shuru. A zaman da takeyi ta maida kai sosai wajem research yadda zata zama good presenter akan program dinta, research akan abubuwan da suka shafi al'adun qabilu daban daban,saidai ta fi bada qarfi akan qasarta ta nijer,don da ita take son farawa,wannan ya sanya duk sanda ta fahimci bibi ita daya ce a zaune zata je ta dameta da tambayoyi da son sanin wasu tsaffin al'adu da ita batasan su ba.

Duk wata magana da maina din ya gaya mata a wancan ranar ta azata a mizanin qarya ne,don bataga wata hanya guda daya zancansa zai zama gaskiya ba. A yanzun ba maina take kallo ba,aliyyu take kalla,duk wata kalmar damuwa da ita da yake furtawa tana kallonta ne a mazaunin labarin qanzon kurege,ko kadan zuciyarta ma bata qaunar wani lamari da ya shafeshi,a yanzun da zai sake bacewa bat kaman wancan karon tayi imani dari bisa dari itace number ta daya a gidan da zata fara murna da hakan.

Su aminata sunyi mita sun kuma yi qorafin rashin zuwanta gidansu har sun gaji,abinda basu sani ba shine,ita ba zuwa gidansu ne matsalarta ba,damuwarta ta fita farfajiyar gidan tsautsayi ya hadata dashi.


**********K'arfe takwas na daren ranar tana tsaye cikin kitchen din ama tana qoqarin kammala miyar tuwon aba. Tun safiyar yau data shigo gaida ama don ba'a sassanta take kwana ba kwana biyu ta karanci ama din bata jin dadi,wannan ya sanya da yammaci liqis ta fito ta karbi girkin aba wanda bata baiwa kowa yayi masa sai ita da kanta sai kuma sultanan. Bata kuma baro sassan bibi ba sai data tabbatar baya gidan shi dasu batoul da a yanzun suka zama qafar yawo,kowacce rana akwai inda suka nufa,guraren shaqatawa daban daban cikin marad'i harma da niamy kamar wadanda suka kawo yawo duniya. Abun yana bata haushi, musamman yadda taga kowa cikin gidan ya xuba musu idanu,kamar ma sun samu goyon baya kenan,wani gun idan sunje su kwana,wani su dawo a ranar, goumar idan yana free kuma shima ya zama dan rakiya dan iza wuta. Haka zata zauna tayita baqin rai,abun da yake sake bata haushi hatta da bibi tana yin kamar bata san me yake damunta ba,kusan tanja ce kawai ke tankata,ita dimma tana bin tanja da ba komai,don tana ganin idan ta furta wani abu game da yaran kaman tayi rashin kunya ne,amma yana da kyau a dinga duba mata basai tayi magana ba.

Lafiyayyen tuwon shinkafa tayi masa miyar shuwaka da taji agushi. Tadan qara yawan abincin saboda ama tace tana da buqatar tuwon itama. Ta kammala komai tana shiryawa cikin warmer's tanja tana tayata.


A nutse yake takowa zuwa sassan ama daga nashi sassan don yayi dinner,yana sanye da wata baqar hoodie abaya ta maza wadda aka yiwa adon golden din zare,bai sanya hular saman kanshi ba,wannan ya sanya baqin nannadadden gashinsa na asalin buzaye ya bayyana bisa tsari saman kansa. Suma ce da ba'a gajiya da gyaranta da kuma kashe mata muggan kudade gurin siyan kayan gyaranta,kama daga mayuka hair mist da sauran tarkacen kula da gashi na maza.

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 66


Duk inda ya gifta sai yabar sassanyan qamshin nan nasa me kwantar da zuciya wanda yakan jima a waje kafin yabar wajen. Tunaninsa da kuma hankalinsa suna karkasuwa,ya gama noticing nata tsaf,duk wani zaman daki da boyewar da takeyi ya tabbatar don saboda shi ne,shi kuma yana ji cikin jikinsa akwai wani abu da zai girgizashi ko ya sanyashi janyewa daga qudurinsa. Duk kuwa da cewa ba wani sauyi daga wajen aba,gaisuwa ce kawai take hadasu, gaisuwar ma zaya amsa masa ita ne da qyar,bibi kuwa tana ji tana gani ya mata qarfa qarfa,duk abinda zaiyi wanda zai saka ta kulashi shi yakeyi,to kuwa koda batayi niyyar kulashin ba sai ta kashi. Ama kam zata amsa masa gaisuwa ne ba yabo ba fallasa,daga haka koda zaman awa nawa zasuyi a wajen muddin dai bai sake cewa komai ba itama bata sake cewa. Zuciyarsa ba zata iya daukan hakan daga ama ba koda kowa zaiyi masa,don haka ya soke kawo mishi dinner da akeyi har sassansa,ya tsiri zuwa suyi dinner tare koda ba abinda zai hadasu har su gama. To bare zaiyi wuya su gama dinner din sun tashi haka,musamman da yake su benazeer suna zuwa ayi tare dasu,sai ya soma ganin alamun zuciyarta tana sanyi daga daukan zafin da tayi,saidai tanata boyewa ne taqi ta bayyana hakan akan fuskarta,to koda bata bayyana ba shidai hakan ma ya masa dadi,ya sani kuma tsakanin uwa da danta sai Allah,tabbas zata sassauto kaman yadda yake fata.

Sanda ya shiga falon babu kowa,baiyi mamaki ba saboda dukka masu aikin cikin gidan daga kowanne sashe daga magariba tayi suke komawa sassansu,saidai idan kuma an buqacesu,sai na jiki sosai irinsu tanja da ba'a rabo dasu. Fes falon yake wanda girmansa ya sanya yake dauke da rukunin kujeru biyu,amma duk da hakan sai yake neman rainsu,ko ina qamshi yake fiddawa dake gauraye da sanyin a.c. qatuwar tv plasma din dake girke ce kadai keta aikinta. Takawa yayi a hankali ya dauki remote yana rage sautin ta,yayin da hancinsa ke shaqo masa daddadan qamshin miyar shuwakan. Ajjiye remote din yayi yana duba lokaci. Bakwai da hamsin da takwas,masallatai dake sallah da wuri dukka sun idar. Kewar yaran gaba daya ta isheshi,tun dazun suka fita da goumar da yammaci yawonsu saboda yau din shi bai samu fita ba yana daki yana duba wasu takardu da sardauna ya turo masa ta email dinsa,gashi har yanzun basu dawo din ba. Bude wayan yayi ya kira goumar din

"Mun kusa da gida,nasan yaranka ka biyo" abinda goumar ya furta kenan yana qaramar dariya cikin salon tsokana. Qaramin murmushi ya subuce masa,yadan cije lips nashi kadan yana katse wayar. Shi goumar din baisan banda shi ba ba wanda zai iya lamuncewa yaran har a fita dasu daga gidan har haka su dade ba?. Number ama ya laluba ya kira,bugu biyu ta daga,muryarta a qasa tayi sallama,ya amsa mata cikin tsananin kulawa a ladabce

"Na shigo ban ganki ba ama" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke. Haidar dinnan dai me tsananin nuna mata kulawa da kuma kula da damuwarta,har yanzun shine dai,komai har yanzun halayen da dabi'unsa game da ita da take tunanin sun barshi suna nan ba inda suka je

"Zan fito yanzu zan shiga wanka ne"

"A fito lafiya" ya bata amsa yana komawa saman kujerar dake facing dining area ya zauna yana dan sauke idanunsa a wajen. Yanason duba me suka dafa din yau amma sai yaji yana gandar haka,ya bude wayarsa ya kunna data dinsa,sai ya shiga IG yana duba hotunansu benazeer da baya gajiya da kalla.

Kiranta shi ya katse masa kallon hotunan da yakeyi

"Sister" shine sunan da ya bata,wanda ya tabbatar bata taba ganin hakan ya sanya mata ba. Doguwar numfashi yaja ya sauke qafansa da a dazu take daya saman daya ya gyara zamansa yana tunanin yadda zai kaucewa doguwar waya da ita,don a yanzun yana da buqatar lokacinsa qwarai,akwai abubuwa kuma masu muhimmanci da har yanzu bai gamasu ba. Yana shirin dagawa ta katse,yana kuma yunqurin bin kiran wani kiran nata ya shigo,sai ya daga yana saka wayar a kunnensa

"Hello" ta fada cikin karyayyar muryarta

"Assalamualaikum" ya furta kaman yadda ya saba a duk sanda zai daga waya. Gyaran murya tayi kadan tana tuno kuskurenta,yasha gyara mata amma saboda sabo tana mantawa.

"Wa'alaikumussalam........zuciyata tanata gayamin cewa da gaske yaa maina bai damu dani ba" ta fadi har tsakiyar zuciyarta kalaman suna fita,tana kuma ji da gasken bai damu da ita din ba.

"Kada kice haka mana.......ya mummy take?"

"Tana lafiya,amma wunin yau na cikata taf da qorafi a kanka,har sai da daddy ma yaji hakan" idonsa yadan rufe kadan,bayason abinda mahaifinta zai ga kaman bai damu da rayuwar diyarsa ba,diyarsa mace guda daya daya dorawa dukkan buri da gatan duniya

"Me yasa?" Ya tambayeta shima

"Saboda abinda idanu da zuciyata suke gani kenan.......yaa maina......inaso ka bani dama na shiga rayuwarka sosai......nayi maka alqawarin baka dukkan farinciki da kuma soyayya,ka bani dama na soka yadda ya kamata,soyayyata kadai zata samar maka da kalar farincikin da baka taba riskar irinsa ba" A yadda take maganar ya shanshano tana fesar dasu ne da gaske daga zuciyarta,yaji mata babu dadi sosai,ya kuma kasa gane sai yaushe zata fahimci inda shi yafi karkata ne?,sai yaushe zata fahimci pretending da reality?.

"Wannan damar da kike magana a kanta sai nake gani kamar na baki ko?......but duk da haka kiyi tunani da kyau laila....karkiyi pushing kanki zuwa abinda zai dinga hurting mind dinki..... please laila" ya fada cikin kwantar da murya yana fatan kalamansa masu harshen damo zasu warware cikin kwanyarta har ta fuskanci ina ya sanya gaba.

"Ya maina" ta furta a marairaice

"Laila" shima ya kirata da salon murya kaman me begging wanda ya furta sunan ne yana bude dukka idanuwansa,idanuwan da basu sauka a ko ina ba sai a kanta sanda take fitowa da qawataccen kwandon da aka saqashi da wani kalar ciyawar turawa me azabar kyau kalar green.

Sanda ta sanya dukka qafafunta waje zuwa cikin falon taji fitar sunan fes daga bakinsa,bata gama fahimtar waye a wajen ba sai data kammala fitowar daidai lokacin da ya aza nasa idanun cikin nata. Janye kallon nata tayi daga kansa,ta kuma dauke kanta zuwa gefe zuciyarta na ayyana mata yau tayi baqar rana.

"Zan kiraki later" ya furta a nutse

"Is okay....... but ka cika alqawari"

"Zan qoqarta" ya sake amsa mata a gajarce yana zame wayar daga kunnensa. Zuwa lokacin har ta kusa qofar falon da nutsatsen takunta tamkar ma batasan da wata halitta a falon ba. Bai debe idanunsa daga kallonta ba har sai data kammala ficewar,sai ya maida idon nasa ya lumshe yana jin wani iri a zuciyarsa. Ko ba komai,koda bata kuma sanshi ba gaba ai take dashi ko?,kuma ya cancanci gaisuwa

"Kana nan har yanzu?" Ya tsinci muryar ama abinda ya sanyashi ware idanunsa a hankali sannan kuma ya miqe tsaye yana duban ama din

"Ina jiran fitowarki ama"

"Lafiya" ta jefa masa tambayar tana duban qwayar idanunsa da ta sauya launi,alama qwaya daya tak dake nuna somi somin bacin ransa kenan

"No.....ba komai, I can't take my lunch bakya kusa" ya fadi yana shafa sumar kansa.

Komai da ya faru kusan a kan idanunta ya kasance,tun fitowar sultana daga kitchen har zuwa ficewarta daga falon. Idan akwai abu daya da ama keson sultana da gyara a yanzun shine gaida maina,badon komai ba sai don idanun su batoul,kuma batajin zata bar haka yaci gaba da tafiya kodon tarbiyyar yaran

"To bismillah mana" ta furta tana nuna masa table din ba tare da tasan tayi hakan ba. Da sauri ya daga idanunsa ya dubeta,yau din ama ke masa magana haka a tausashe tamkar shekarun baya da yake little maina dinsa?. Wani abu me sanyi ya tsarga ta tsakiyar bacin ransa,sai yaji zafin da zuciyarsa ta fara yana raguwa.

"To mu qarasa ama" ya amsa mata yana janye mata wata qaraman kujera daga hanya. Fuska yaga tadan bata

"Ka fara yin gaba mana". Yadda tayi maganar ya kusa bashi dariya,wato ta gano kanta da kanta,wannan tausayin dake danqare a zuciyarta yana don fallasa kanta,ita kuma ba yanzu ba,yanzun bata shirya barinsa ya fahimci haka ba,tanaso yasan martabar sultana sosai.....tanason yaji ciwo akan 'ya'yansa,tana so kuma PLAN dinta da zai kaishi ga jin wannan ciwon ya tafi dai dai.

Shikam ko iya haka a wannan daren ta biyashi,don haka ya soma takawa har zuwa wajen dining din,yaja mata kujera yana jiran isowarta ba tare da shi ya zauna ba.

Key ta zura ta bude sassan aba tunda tasan baya nan,ta dauki kwandon tana shiga falon da sallama duk kuwa da tasan ba kowa a ciki. Tana qoqarin jera ma aba abinci fuskarsa tana mata yawo cikin idanunta

"Ya salam.....ya salam" ta furta tana yarfar da hannu,ko kadan ko alama batason tunawa da sunansa bare ta dinga ganin gilmawar fuskarsa,wannan ya sanya take jin dadi sosai yadda take killace kanta

"Mugu" ta fadi qasa qasa tana murguda qaramin bakinta,tamkar wanda takeyi don shi yana zaune a wajen.


_"Laila........zan kiraki later"_.ta tuna kalaman guda biyu da taji yana furtawa sanda take fitowar. Siririn tsaki taja tana tabe baki

"Yo daman mutumin da yabar gida ya tafi yawon duniya shekara biyar aiba abun mamaki bane hakan ta faru dashi" ta samu kanta da fadi qasan zuciyarta. Sai kuma ta sake jan tsakin zuciyarta na mata wani sabon qunar

"Me ya kaika jiyo abinda bais shafeka ba?" Tace da kunnenta cikin jin haushi jiyo sautinsa ma da tayi har ta jiyo wadannan kalaman. Tsakin dai ta kuma,ita in banda ama da bata jera mata nata tuwon ba bataga abinda zai maidata sassan ba,amma dole ta koma din,ama ta cancanci dukkan wata kulawa,domin itama babu wani nau'in kulawa da bata bata ba sanda take da matuqar buqatar hakan.

"Ama me zan zuba miki?" Ya tambayeta bayan ya tabbatar ta zauna. Wannan din al'adarsa ce dama tun ba yau ba,daya dawo kuma bai manta da ita ba yaci gaba

"Nan duk abinda zanci yanzu diyata zata kawomin tuwon data yi min". Maganarta kaman jirwaye me kama da wanka tayi masa,ko bata fada ba yasan tana nufin sultana,don haka sai ya koma ya zauna ya rungume hannayensa yana jiran dawowarta.

Da wannan muryartata dai da bata taba bacewa kunnuwansa da kuma mafarkansa ba ta sake sallama a falon. Dukka tsokar zuciyarsa ta motsa,don kafin ta iso jarabbaben qamshin nan nata da baisan yaushe ta juye haka ba y soma riskarsa. Kamar zuciyarsa tana narkewa haka yaji sanda takunta ke isowa inda suke,yana muradin juyawa ya kalli takunta da kyau......yanason ganin takun tafiyar wannan sultanar shine har yanzu ko kuma ya sauya?,amma haka kawai cikin jikinsa yake jin kamar ama na ankare da duk motsinsa,wannan ya sanya dole ya cinye wannan da jawo wayarsa ya buda yana ci gaba da duba Instagram dinsa.

"Kin kammala?" Ama ta tambayeta sanda ta iso wajen tana maida al'amarinsa gefe guda gami da tattara hankalinta akan ama kawai

"Eh ama" ta bata amsa tana ajiye na ama din data fito dasu daga kitchen ta ajjiye qasan dining din

"Sannu da qoqari,ban kula bama ashe abincin yana kusa dani" dan qaramin murmushi maras sauti tayi tana bude warmer's din

"Sultana" ama ta kira sunanta da wani sauti da yaja hankulansu dukka su biyun,saidai still dai shi din bai kallesu ba yana ci gaba da danna wayarsa tare da qoqarin kokawa da sabon yanayin da yakeji a dukka sassan jiki da zuciyarsa

"Naama ama"

"Kin tuna?,duk garin kafiran da ma'aiki yaci da yaqi yana ci gaba da girmamawa dattawan kafiran?,ya kuma ce maja duk wanda baya girmama manya baya kuma tausayin qanana na qasa dashi tabbas baya cikinmu?" Fes ta karanci karatun ama din,saita sadda kai a karon farko taji kunyar ama din ta dan kamata

"Kiyi haquri ama"

"Ba laifi kikayi ba" ta tareta da wannan amsar fuskarta Na bayyanar da zallar jin dadinta. Cikin jin wani irin nauyi da takura tadan juya jikinta sassansa kadan. A zahiri wayarsa yake dannawa,yanayinsa sai ya tuna mata da shekarun baya,sanda take gaidashi yake bawa banza ajiyarta,bata gaidashi ba kuma ya zam wani laifi me girma,a zuciyarta ta dinga jin kamar ta bace daga wajen don ta kubucewa gaidashin,amma kuma ama tafi gaban haka daga gareta

"Barka da dare.....ina yini" ta hada gaisuwar dukka gaba daya. Kansa ya daga yana kafeta da lion eyes dinsa

"Barka kadai alhmdlh" ya amsa mata shima,sai shigowar batoul da benazeer ya kawo qarshen gaisuwar qeqe da qeqen.

Kamar ko yaushe da rigimarsu suka shigo,ama ce ta karbi rabiyar fadan. Tanaso ta wuce tabar wajen amma sai taga rashin dacewar hakan. Da qyar ama ta raba fadan,yana zaune yana murmushi,saboda hakan bai tuna masa komai ba sai fadan attah da almu. Bata ko bi ta kansu warning daya take basu a sannan,amma sai gata yanzun tana lalacewa wajen raba fadan jikoki,wannan kadai ya isa ya gaya masa yawan adadin son da take ma yaran.

Ta qasan idanunsa yake satar kallonta yana kuma qare mata kallo son ranshi ba tare da kowa dake wajen ya karanci hakan ba. Totally wannan ba sultana bane hatta da zara zaran yatsun hannunta sun sauya. Ta zama wata miskila ta gaske ba da ruwanta da abinda ke faruwa a kewayenta,don ko yanxun ma a zaune take tsaf saman kujera tana danna waya sanda ama ke rabon rigimar yaran.

Qarar wayarsa ne ya katse masa daddadan yanayin,iya morewa kallonta kawai daya fara ya saukar masa da nishadi. A kasalance ya sanya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login