Showing 72001 words to 75000 words out of 294767 words

Chapter 25 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

da benazeer tana sakinta. Fuska benazeer din ta kyabe tana duban bibi

"Wai aunty ce uwarmu?"

"Da dawa nake ja'ira?" Dariya ta qyalqyale dashi sannan ta nufi hanyar lobby din da zai kaika dakunansu da gudunta.

Awa guda cur ta kashe akan internet ta system din da ama ta bata kyautar graduation. Bincike kawai takeyi akan abinda ya shafi aikin jarida,haka kawai cikin kwanakin data tsananta addu'ar neman zabin Allah kan makarantar da zata tafi da kuma abinda zata karanta din taji ba abinda yafi kwanta mata a rai irin aikin jaridar. Lokaci guda ta tsinci zuciyarta hankalinta da dukka tunaninta ya karkata ga zama shararriyar 'yar jarida.


Tayi d'ai d'ai a tsakiyar gado,tana sanye da wata maroon abaya,daya daga cikin dressing dinta da tafiyi a yanzu,dankwalin abayar me santsi ne wannan ya sanya ya gaza zama saman lallausar sumarta. Wani qamshi jikinta da dakin dukka yake fiddawa,a yanzun ba abinda ke burgeta sama da turare,komai nata qamshi yakeyi,hatta da abubuwan amfaninta na yau da kullum muddin tana ta'ammali dashi ko da yaushe sai kaji yana wannan sassanyan qamshin nata. Hutu da zama guri daya ya sanya fatarta yin matuqar yin fresh. Gazar gazar din gashin idanunta da na girarta sun sakeyin baqi sidik sun kuma kwanta a fuskarta luf,kamar yadda gefe da gefan fuskarta keda wani irin lafiyayyen kwantaccen gashi me santsi da duhu.

K'ofar taji an murda sannan an budeta da qarfi ta daga fararen idanunta da sukayi laushi saboda kallon allon computer tana duban me shigowar. Idanu ta zubawa yarinyar sanda take shigowa,abinda ya sanyata nutsuwa da shiga taitayinta. Sam bata musu wasa kwata kwata,idan kaga warginsu to suna jikin ama,ko suna tsakanin aba ama bibi ko tanja,wani irin discipline take musu sosai wanda kallo kawai da idanu sun isa su sanyasu shiga taitayinsu.

"Koma kiyi sallama" tace da ita cikin bata fuska da kuma dake rai. Sum sum ta saki qofar ta kuma koma da baya,saiga zazzaqar qaramar muryarta tana jero sallama fes. Amsa mata tayi tana sake qare mata kallo,kullum qara girma sukeyi suna wayo,wayonsu yafi qarfin shekarunsu sosai

"Wai ki fito inji Bibi,za'a yi dinner"

"Ok" tace mata tana gyada kai,sai ta juya tana komawa

"Zonan" ta kirayi benazeer din,haka kawai taji tausayinsu yana saukar mata,hannu ta sanya gefan bedside drawer ta jawota ta fidda wani pink box me cike da chocolates. Tana siyansu ta ajjiye ne kawai saboda su,duk da ba ita da kanta take basu ba,duk sanda tayi niyya kawai tana dauka ta bawa tanja ta basu. Abun yana bawa tanja dariya,itakam ta rasa wannan abu na sultana,anaso ana kaiwa kasuwa?,ko cikakken kallo bata iya yima yaran idan cikin jama'a ne,saidai kuma duk burger banza ce,idan kayi tsinkaye da kyau xaka fahimci dukka motsin yaran bisa idanunta da lurarta yake.

Hannu biyu tasa ta karba da qaramar muryar nan tata tace

"An gode"

"Madalla" ta amsa tana binta da kallo,saita cilla da gudun murna tana fita daga dakin,tana iya jiyota tana qwalawa batoul kira

"B...B" murmushi yadan qwace mata ta girgiza kai,sai kuma a hankali murmushin ya soma bacewa fuskarta,ta miqe da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskarta,ta dawo.ta shafa turare kaman yadda ta saba ta daura dankwalinta tana fita daga dakin.

A nutse ta iso wajen,zuwa sannan aba da bibi sun fara cin abincinsu, benazeer da batoul kuma anata faman rikici ama tana sharia,saidai isowar sultana kawai ya sanya suka kama kansu suka hau cin abincin ba tare da sun sake koda tari ba.

Sai datakai har qasa dukkansu tayi musu barka da gida sannan ta miqe taja kujera ta zauna. Da kanta tayi serving kanta,ta fara kai abincin bakinta amma kuma zuciyarta cike fal da tunanin ta inda zata fara sako zancan data quduri aniyar yau din zata fadeshi don a sauke mata nauyin dake bisa kanta ta huta,ta kuma sake cikin tabbaci da yaqinin ba wata alaqa tsakaninta da wani.

Aba ne ya fara gamawa,sai ya koma bawa benazeer da batoul,muddin kuwa ya bawa batoul kafin yazo ga benazeer ta soma rigima,haka ya dinga dariya yana rarraba basu. Yana jin dadin irin wannan yanayin sosai,yaran sun zame musu wani tushe na farinciki da walwalarsu,yaran sun zama tamkar wani budi na alkhairi wa rayuwarsu,tunda aka haifesu al'amura daban daban na alkhairi ke samunsu,komai nasu yana sake bunqasa da ci gaba tamkar dama ragiwar rabonsu yana hannun yaranne sune zasu iso musu dashi. Duk lokacin da ya tuna da haka,ya kuma tuna da yunqurin zubda su da aka soyi a baya sai yayi istigfari. Yaga maganar malamai qarara da suke fadi,kowanne yaro da arziqinsa yake zuwa,hakanan bakasan wanda arziqinka ke a jikinsa ba,hikima ce wannan ta ubangiji.

Sai daya gama da rigimarsu yana goge musu baki sannan yace da sultana

"Kaman naga sanarwar fitowar exam dinku ko?" Kai ta gyada a nutse tana dan ture plate din abincin daga gabanta,duk da ba wani abinci taci me yawa ba

"Eh aba,don fateema Ahmad ta fadamin dazun da safe ta dubo nata"

"to ma sha Allah,Allah yayi jagora,kema sai amanki ko goumar wani ya duba miki naki,tunda sun fini iya shige shigen computer"

"Ama din dai" ta fada qasa qasa yadda ba wanda zai jita,saidai duk da haka ama din ta jita. Ta rasa wanne irin rashin jituwa ne irin haka tsakaninta da goumar din,tana iya kashe wuninta dashi batace masa kanzil ba,shi kuma da yake ya saba a baya abokiyar dabinsa ce to in sha Allah sai ya samu abun tsokanarta,idan taga ya fara sai ta tattara ya nata ya nata tabar masa wajen,takance

"Kaci kanka da kanka".

"Alhamdulillah,yanzun wanne ecole kike buqatan yi?,kuma wanne cours(course) kike sha'awar yi?" Ajiyar zuciya ta sauke,aba ya soso mata inda yake mata qaiqayi,ya kuma dauko mata mafarin maganar da take juya ta inda zata fara yinta

"journalisme(aikin jarida) shi nake so aba" murmushi aba din yayi,itace mutum ta farko kuma qwaya daya tal a cikin gidan mayak'i data zabi wannan aikin

"To ma sha Allah,saidai kuma munyi magana da bibi,ina kyautata zaton akwai tafiya da zata samemu ni da ama dinku,kuma tafiya ce bata kwana daya ko wata daya ba,tafiya ce ta shekaru biyu ko uku,na samu kujera cikin gwamnatinmu duk da ba'a sanar ba officiellement (a hukumance) ba amma abun tabbatacce ne,so sai a tayamu da addu'a,duk abinda yafi alkhairi Allah ya zabar" kai ta jinjina

"Allah yayi jagora aba ya zaba abinda yafi zama alkhairi"

"Ameen ya rahman" kusan dukansu suka amsa. Shuru yadan ratsa tana ta dan juya hanunta. Cikin qasan ranta takejin kamar abinda zata fadi akwai nauyi,to amma komai nauyinsa abune daya kamata ta tunasar dasu idan sun manta. Dukkan juriyarta da qwarin gwiwarta ta tattaro sannan tace

"Amma aba ina neman alfarma a wajenku" hankalinsa ya bata da kyau da ganin yadda tayi maganar,bama shi ba hatta bibi da ama,saboda baqon abune a wajensu,tun faruwar abun sultanar bata taba neman komai daga wajensu ba

"Ina jinki sultana,fadi duk abinda kk son ki fadi,karkiji komai nidin mahaifi nake a wajenki kuma uba" kai tadan jinjina sannan tace

"Inason a rabani da igiyar auren......ya maina dake kaina" ta danyi dabur dabur wajen furucin saboda yadda furta sunanta kadai yake haifar da wani abu me daci daga saman harshenta.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 39




Dif wuta ta daukewa kowa dake dakin. Tun daga tsakiyar kan ama har tafukan qafafunta sai da taji wani ya tsarga mata,ba wanda ya taba hasashe ko tunanin maganar da zata fada kenan. Kaf cikinsu kowa ya kasa furta komai,kimanin wasu sakanni har sultana ta debe tsammanin wani a cikinsu zaiyi magana sannan aba ya sauke ajiyar zuciya,kafin yace komai bibi ta furta

"Sultana?.....me kike fada haka?" Hannu aba ya dagawa bibi yana kallonta,sai tayi shuru,tsam ama ta miqe ta zagayesu tana barin wajen,saboda batason jin duk wani hukunci da zai fito daga bakin aba,don ta tabbatar zaiyi wahala hukuncin ya dace da abinda ita takeson ji ko son ya kasance

"Kinyi qoqari qwarai sultana da kika iya zama da igiyar auren mutumin da har yau ba wanda yasan inda yake,a raye ko a mace duk ba wanda ya sani,kika raini cikinsa kika haife,kika shiga makaranta kika gama,don yau kin buqaci hakan ba laifi bane,tashi kije zan nemeki in sha Allah,Allah ya yiwa rayuwarki albarka,idan kuma goumar ya shigo ya duba miki sakamakonki"

"To aba,na gode qwarai" ta fadi tana miqewa daga zaman durquson da tayi. Tana shirin juyawa sashen dakunansu suka hada idanu da goumar dake tsaye daga can bakin qofar falon jingine da qofar,hannayensa goye a qirjinsa,da alama kuma yaji komai,don abinda ta gani cikin idanunsa ya karanta mata haka. Harara taso watsa masa amma saita shareshi kaman itama bata ganshi ba ta juya ta wuce lobby.

"Amma dai hamid,kada kacemin ka amshi zancanta da gaske kana nufin yi mata abinda takeso din?" Bibi ta tambayeshi murya qasa qasa tana duban qwayar idanunsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa

"Komai a musulunci bibi yana da iyaka,yana da doka,a shekarun da maina yayi baya nan ba wanda ke da tabbacij yana raye fa,kuma ko a musulunci miji yayi irin wannan bacewar ba tare da ya sake waiwayar matarsa ba ya halatta alqali ya raba auren ayi ma matar GAIBA ta auri wani.....bibi sultana yanzun ba qanqanuwar yarinya bace,ta iya yiwuwa tana da buqatar tayi aure shi yasa ta bijiro da wannan batun da ya kamata ace mu muka fara dubashi" zama tayi sosai tana jifan aba din da wani irin kallo hadi da gatsine fuska

"Hamidou......ka fara kasheni tukunna saika tsinka auren maina kaji"

"Subhanallahi bibi,abun baikai har can ba"

"Ah to,yo Allah na tuba,don qaniyarta nawa take duka duka da har za'a ce waiko tana da buqatar aure?, ina cewa kwata kwata sha tara shekarun nata suke?,to ko labarin mutuwar maina aka samu ai bata isa tayi wani auren ba sai tayi masa idda"

"Ya maina ma yana raye......" Goumar ya fada

".........in sha Allah,jikina yana bani haka" ya qarasa fadi ganin dukka sun waiwayo sun zuba masa idanu,sai ya sauke hannayensa yana ci gaba da takowa cikin falon

"Bazamuyi masa fatan mutuwa ba aba baiga jininsa ba diyoyinsa,kai din ubane,a duk inda yake kaci gaba da yi masa addu'a Allah ya bayyanashi,ko kuma ubangiji ya karkato da hankalinsa gida" shuru sukayi su dukka jikinsu a a mace,saidai maganganun goumar dake cike da nutsuwa da kuma hankali sun ratsasu.

Tunda ta shiga daki take nanata kowacce kalma data fita a bakinta,saida zuciyarta ta gamsar da ita bata aikata wani abu me muni ba,hakanan batayi amfani da tsauraran kalamai ba wajen bayyana musu yankewar igiyar aurensu takeso,hannu ta daga tana addu'a Allah yasa aba ya yanke hukunci da wurwuri,ta yadda zata samu cikakken 'yanci kamar kowacce mace,tayi karatunta iya yadda takeso ta kuma gamsu.

Agogo ta dinga dubawa har sai data tabbatar da lokacin da goumar yake zama babban falon ama shi dasu benazeer su cikawa mutane kunne da karadi,sai ta dauki hijabinta ta sanya saman kayan baccinta donta gama shirin kwanciya,kasancewar bata fiya kaiwa dare can can batayi bacci ba.

Takardunta ta diba ta sanya loppy tana fita a dakin. Yau din sabanin kullum ne,zaka samesu ko yaushe sun cika falon da hayaniya da wasanninsu,amma a yau din sai ta samu yaran duka sunyi bacci zube a tsakiyar ama da goumar din. Daga goumar din kuma har ama idanunsu na bisa tv.

Motsinta ya sanya ama da goumar din juyowa duk suna kallonta. Idanun goumar bai sanyata jin komai ba,amma sai idanun ama taji sunyi mata mugun nauyi. Ta dinga jin kamar ana dabaibayeta,cikin gangar jikinta ta dinga jinta kamar me laifin da aka tsare.

Miqewar ama din kafin ta iso tana daukar benazeer ya sanya ta dan sake ji wani iri tana cewa

"Tanja zata zo ta dauki batoul,sai da safe"

"Allah ya bamu Alkhairi ama" ta fada a kunyace

"Ameen sultana" yadda ta amsa matan a sake sai ya rage mata tsarguwar da tayi,ta samu waje ta zauna tana duban fuskar batoul dake bacci. Bakinta gaje gaje da chocolate,tasan kuma ba aikin kowa bane sai na goumar,shi yasa yaran kullum qara habaka suke suna qiba mul mul abinsu,duk wanda ya gansu saiya tanka,wannan ya sanya duk sati ama ke sanyawa ana sauke musu qur'ani.

Hannu ta sanya ta shafi cute face din batoul tana dauke mata gashin daya warware daga band din kanta don suma sunyo gadon gashi me tsaho da santsi irin na iyaye da kakanni

"Ah waima,unuhunn......wai a haka fa sonta kikeyi ko?,bayan kin gama kashe musu uba da baki,kina kuma neman a sakeki" goumar da bakinsa baya shuru muddin shi da sultana ne ya fadi. Miskilin gaske ne a zahiri da fuska,amma indai shi da sultana ne dama tun tale tale sun saba. Idanuwa ta dago ta zabga masa hararar da bata samu daman sakar masa ba dazu

"Wai kai meye yayi maka zafi da shiga sha'anina ne baqin buzu?"

"Fadi ki sake fadi,baqin buzu nake me farar aniya da zuciya"

"A hakan?,kaga ma ni ba wannan bane ya kawoni,don bani da lokacin wannan maganar,aba ne yace idan ka shigo ka dubamin exam dina"

"Zan duba miki yanzun kuwa,don ni din me jin maganar magabatansa ne......exam kuma dai saidai a cirota a ajjiye don ba inda zaki sake tafiya,sanda akeson kiyi karatun bakiyi ba sai yanzun da kike matar wani?" Ya fadi kansa tsaye ba tare da damuwa da abinda zataji ba yana sanya hannu ya dauko laptop dinsa dake ajiye a gefansa wadda bai jima da gama aiki da ita ba.

Tsam ta miqe,ba goumar ba,har wajen da take zaune a kansa sai da taji ta tsanesa. Hawaye fal idanunta tana dubansa dishi dishi,tana shirya kalaman da zata gaya masa da zata fanshe wannan maganganun da ya yaba mata,abu biyu ta iya gaya masa taji muryarta ta soma rawa,saita juya bata ida gaya masan ba,tana jinsa yana cewa ta kawo takardun ya cika aikin aba,ko waiwayoshi batayi ba bare ta saurareshi. Ko a jikinsa yaci gaba da aikinsa yana dariya qasa qasa cikin ransa hadi da cije lips dinsa na qasa.

Tun daga lokacin bata sake bi ta kansa ba,bata kuma sake bari sun hada koda hanya cikin gidan ba bare mazauni,rainon maina ne,tasan kuma zai aikata abinda yafi hakan,duk zuciyar tasu iri daya ce ta gayawa kanta,shi yasa ta yanke hukuncin nesanta qwarai dashi.

Aba ne da kansa ya kirata ya miqa mata hard copy na result dinta. Sanda ta karba hawaye ne ya kwance mata,ta samu fiye da marks din da ta tsammaci zata samu,ta cinye kowanne subject,abinda tayi hasashen zata samu ta samu fiye da hakan,ta kifa takardun saman fuskarta tana kiran sunan Allah,yau sultana ita keda wannan result din da abaya kaf gidansu koda cikin mafarki ba wanda ya taba kawo mata kwatankwacinsa saboda zallar qiyayyarta da karatu.

Ba ama ba hatta aba abun ya faranta masa rai matuqa da gaske,bai kuma yi sanya ba ya bata option ta zabi duk kalar kyautar da takeso yayi mata,ya bata dogon takarda yace ta rubuta list. Hannunta rawa ya dinga yi,ta kasa rubuta komai,sai daga bisani cikin rawar bakin bayan ama ta matsa mata ta rubuta din tace

"Umra nakeso aba"

"Sau nawa?" Hawaye ya biyo kuncinta tana tuna adadin zuwanta,sau uku ne,amma saidai duk sanda taje din tana cikin rudu,tana asalin sultanarta,batasan muhimmancin wajen ba,batasan kuma dimbin falala da wajen yake dashi ba,taje ne kawai taji dadin jirgi,ta kuma shaqata a kantunan dake daura da harami,tasha chocolate laban da ice cream har sau babu adadi. Amma a yanzun da tasan muhimmanci da girman wajen sai shauqinsa yaketa kamata,yanzun da ilimi ya ratsata burinta kawai shine zuwa wajen sau babu adadi cikin rayuwarta

"Sau nawa kikeson xuwa?" Aba ya tambayeta

"Sau babu adadi" ta qarasa fadi tana rushewa da kuka

"Kin samu in sha Allah" ya fadi yana nufin hakan har cikin zuciyarsa kuwa. Diyar mohmoud ce tafi qarfin komai,uwa uba ya samu sanyin idaniyarsa halittu mafi soyuwa a gareshi da silarta BENAZEER DA BATOUL. A arziqin da Allah yayi masa inda ana zuwa kullum kuma tana da buqatar zuwa din zai iya kaita.

Ya mata alqawarin muddin yana raye din zata yita zuwa har sai sanda tace ta gaji. Ita kuwa tasan zata yita zuwa kenan muddin ranta,muddin akwai wadata wa aba,akwai lafiya cikin jikinta,saboda bata tunanin akwai ranar da zatazo tace ta gaji da zuwa wannan gurin.


**. **. **. Randa bibi zata juya nijer sai taji haka kawai tana sha'awar zuwa. Tare suka tafin,da harda goumar ta kafe indai tare zasuyi tafiyar ita ta fasa,dole yayi gaba daga baya aba ya basu driver da escort uku.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login