Showing 234001 words to 237000 words out of 294767 words
Chapter 79 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
ya kunnata,ya tasheta suna fita a layin sannu a hankali.
Cikin motar ya dauki shuru,ba kuka takeyi ba,amma kuma baya iya ganin fuskarta,ta cure waje daya kaman maijin sanyi,wannan ya sanyashi miqa hannunsa ya kashe ac din motar gaba daya,ya kuma sake dage glass din sama.
Tana iya jin kowanne motsi nashi kaman yadda qamshin turarensa daya cika motar yake shiga hancinta cikin kowanne numfashi da zata shaqa. Idanunta ta dinga lumshewa,tana mamakin yadda takejin matuqar dadin qamshin fiye da kowanne lokaci. Maganganun da sukayi da ama suna dawo mata daya bayan daya tana sarrafasu cikin kanta. Bata taba tunanin haka ama ta shahara wajen kara ba......haka ama ke kallonta dama?,amma koda a motsin 'yan yatsunta bata taba nuna mata komai ba..... kullum tana bayanta.....kullum goyon bayanta kuma takeyi,hakanan kullum farincikinta takeso.
Duka duka tafiyar minti goma ya bulla wani titi,titi ne dake dauke da wadatar shops iri iri da ke saida abubuwan buqata iri daban daban. Ya ganganara muhallin da aka kebance don yin parking ya ajjiye motar a hankali sannan ya kasheta,ya zare key din,yadan waiwaya ya kalleta. Har yanzu taqi kalonsa,taqi juyawa sashen da yake gaba daya.
"Zaki magantu,zakiyi bayani" ya fadi qasan ransa yana tunanin me ama ta gaya mata haka da ya tsaida kukanta a lokaci guda haka?.
A nutse ya bude murfin motar ya fice,saita samu kanta da satar kallonshi. Yadda yaketa dake mata da yadda fuskarshi keson koma mata aliyyun nan na maradi ke bata mamaki
"Hey madam.....gani ta nan" taji an fadi daga gefanta. Juyowa tayi ga mamakinta yana ta bakin window din da take zaune. Suka hada idanu saita dauke kai don nashi idanun duka suna kanta. Ita batasan ya zagayo ba,da ba yadda za'a yi tabi bayanshi da kallo.
Rumfa taji ya mata gaba daya,ta daga idanu a dan tsorace tana tunanin me zaiyi mata?. Oily eyes dinta suka hadu da lion eyes dinsa suka sarqe waja guda. Tana jin dumin numfashinsa sosai yana sauka saman fuskarta yana kuma gogayya da nata numfashin. Hannunsa ya miqe yana sauke mata kujerar sosai yadda zata iya jingina ta huta yadda ba zata takura ba,faffadan qirjinsa yana gugar nata a hankali,ya lumshe idanun nasa yanayin numfashinsa yana sauyawa. Shi kadai yasan idanunta kadai ke iya illata dukka jarumtarsa.....ina ga kyakkyawan jikinta dake dauke da wani irin sinadari dake kassara duk wani qwarin gwiwa nashi
"Bi a hankali 'yammata,idanuna basu da kyau......kince baki sona.....so ina baki shawara karki yarda ki fada tarkon so na" yayi maganar softly kaman me rada. Kanta ta kawar gefe saboda yadda zuciyarta ke wani irin bugawa. Tana iya jin sautin fitar murmushinsa,ya miqe yana maida mata qofar ya rufe
"Mugu" ta fadi cikin zuciyarta tana lumshe idanunta,qamshinsa yana sake sanya mata nutsuwa a ranta,maganarta da ama tana sake kwantar mata da hankali,duk quncin da take tunanin shiga tana jin babu kaso hamsin cikin darinsa.
Duka duka bai wuce mintuna ashirin ba taji ana bude butt din motar. Ta glass din motar take hango sanda ake zuba siyayya a ciki,ya sallamesu ya dawo ya tayar da motar.
Tafiya suke a nutse kaman bai shirya zuwa inda zasuje din ba. Sun kusa mintuna talatin saman hanya kafin su isa inda suka nufa din.
Daya daga cikin unguwanni ce dake dauke gine gine masu irin wani fasali dake da ban sha'awa kaman cikin qasar turkey. Idanunta qasa qasa amma tana kallon unguwar da duk wani tsari da yanayinta me kyau. Kaman ko ina cikin qasar,itama a tsaftace take cikin tsari,sannu a hankali har ya isa qofar wani madaidaicin gidan dake da madaidaiciyar harabar me qananun katangun da kana iya hangen ainihin ginin gidan dake tsakiya,harabar da aka qawatata ainun kamar wani qaramin garden.
Da kanshi ya sauka ya bude motar,sannan ya saka wani siririn key ya bude gajeran gate din,sannan ya dawo ya shiga da hancin motar ya kuma ajjiyeta daga hannun hagun harabar inda aka saka qaramar rumfa mara girma don ajiye motaocin da bazasufi biyu zuwa uku ba.
"Alhamdulillah" taji ya furta cakude da fitar numfashinsa yana zare key din motar.
A nutse ya ciro wayarshi,yadanyi danne danne sannan kuma yayi kira. Cikin qasa da second biyar aka daga kiran. Kiran sunan suhail da yayi ya tabbatar mata suhail ne
"No...je n'ai besoin de rien(bana buqatar komai)" ya fada a taqaice
"Near Rue de rivoli" ya sake fadi. Dan satar dubanshi kadan tayi,ta fahimci kaman yana gaya masa adress na unguwar ne,don a hanya taga symbol na wannan sunan,saita mayar da kanta gefe. Zuciyarta na qiyasta mata wanne bigiren kuma rayuwa zata kaita yanzu?,a ina rayuwa zata ajjiyeta?,ta yaya zata zauna dashi?,yaya zasu rayu?,a matsayin miji?,ko a matsayin yaaya kaman yadda yayi iqirari?.
Tana jinsa ya bude motan ya fita bayan ya gama wayar,da idanu dai take ci gaba da satar kallonshi har ya isa qaraman veranda,ya sanya maqulli ya bude qofar da zata sadaka da ainihin cikin gidan ya shige.
Ko ina lullube da duhu,sai ya dinga takawa a hankali yana kunna kowacce fitila ta gidan.
Ko ina na gidan tsaf yake kuma fes kaman yadda ya zata,don ya ajjiye me kula dashi na musamman duk bayan kwana bibbiyu. Sai daya gama zagaye ko ina ya tabbatar komai yana kan order sannan ya dawo tsakiyar falon. Yayi tsaye hannayensa cikin aljihun wandonshi yana kallon babban hoton benazeer da batoul da ya mamaye kusan rabin bango ga tsaho ga fadi kamar zasuyi magana. Saidai kuma ba ainihin photo bane,qwararren me zane ne ya zanasu irin zanen da kana kallon frame din kawai kasan yaci kudi bare akai ga farashin zanen kansa.
Wani irin tsarin gini me matuqar tsari da dukan hankali aka yiwa gidan. Gida ne daya ginashi da guminsa da kuma jinin jikinsa. Gida ne daya ginashi tun bai sanya ran ci gaba da rayuwarsa kaman kowanne mutum ba,kamar yadda hoton dake maqale a bangon hoto ne da aka zanashi tun baisan benazeer da batoul mallakinsa bane.....jininsa bane ....kuma 'ya'yansa bane. Tsananin soyayyar da yakewa yaran ya sakashi aka masa zanen ya sanya a cikin gidan da ko sau daya bai taba kwana a cikinsa ba. Sardauna yasha tambayarsa me zaiyi da wannan gidan da har ya kashe maqudan kudade don ya mallakeshi a qasar da ba tasa ba?. murmushi kawai yakeyi,don shi kansa a lokacin baisan me zaiyi dashi din ba,saidai kuma zuciya da gangar jikinsa suna yawan gaya masa ya gina gidanne don iyalinsa
"Wanne iyalin?,iyalin da babu su?" Sai wani sashe na zuciyarsa ya tuhumeshi da wannan,saidai kuma bai taba sarewa ba......yau gashi ashe akwai ranar da wannan tunani nasa zai cika.
Gidan yasha burgeshi shi a karan kanshi,yasha jin kaman ya kwana a gidan.....amma kuma hakanan sai yaga bai cancanci kwanan a ciki ba. Gini ne daya dace da dukka tsarinsa da yanayin rayuwarsa,don ko suhail ma bai taba zuwa gidan ba.
Juyawa yayi a nutse yana fita a falon bayan ya kashe dukka ac din gidan,don ya fahimci kaman sanyi yana takurata.
Yana fitowa ta maida idanunta ta rufe,ya ganta amma sai yayi shima kaman bai gani ba,don yasan meye ya shirya mata,ya saka hannu ya bude murfin motar,sai kawai ya zura jikinsa gaba daya ya daukota cak daga cikin motar.
Tsoro ya kamata sosai irin tsoron da yaro kanji a sanda babba ya daukeshi yana gudun kada ya yada shi,ba tare data shirya ba ta saqalo wuyansa da duka hannayenta tana zaro idanu waje zuciyarta kuma tana karyewa.
"Shshshs" yace da ita ba tare daya kalli idanunta ba,don yasan me yiwuwa dole tace wani abu. Kanta tayi qasa dashi,tana tuna alqawarin data yiwa ama ba za tana musu ba don yanzun matsayin yayanta kuma uba yake a gareta,tsohon matsayi ne da bai canza ba yanzun ya dawo sabo.
A nutse ya dinga wuce gurare har sai daya dangana da daya daga cikin bedroom din. Dream bedroom dinsa ne a duniya ya tabbatar da wanzuwarsa a wajen. Ya kashe kudade ba qananu ba wajen ganin bedroom din ya zama kamar yadda yake a yanzun. Saidai ko sau daya bai taba iya dogon zama a ciki ba,saboda duk inda ya juya yana reflecting masa rayuwar auren da a wannan lokacin bashi da wanda zai tayashi rayata. Yana da tsananin kamun kan da ba abinda ya tsana irin zina,don haka ya nisanci dakin gudun galabar shedan.
Duk da idanunta suna kulle amma suna shiga dakin ta tabbatar ta shigo wani guri na musamman daya banbanta da duk guraren da suka gilma cikin gidan.
Saman wata zagayayyr sofa ya ajjiyeta wadda ta nutse sosai saboda laushinta. Bai tsaya ba ya juya yana ficewa a dakin.
Taji alamun fitarshi wannan ya sanyata bude idanunta a nutse tana qarewa dakin kallo.
"Ma sha Allah" ta fada a zuciyarta duk yadda take basarwa. Iya canopy bed din dake dakin kadai ya isa ya sanya maka sha'awar kayi bacci. Ta gama bin ko ina da kallo,ko ina din yana burgeta.
Har yanzu maina din na dabanne,ba abinda ya sauya nashi saima sake gaba da yayi. Yasan me gayu yake nufi kaman yadda tsafta da ado suka zame masa jinin jikinsa,yadda ya fita daban a family din MAYAK'I haka ya fita daban da dabi'unsa dama komai nasa.
A qalla mintuna arba'in yayi kafin ya dawo,duk lokacin nan tana jiyo motsinsa a can babban falo,wanda daga shi zaka taras da matsakaicin falon da aka shiryasu saboda zaman karatu ko shan coffee ko kuma shan iska ko hantsi,sannan kabi lobby din dake shirye da dakunan bacci har guda hudu dake nesa da juna.
Ba kayan dazu bane a jikinsa,yanzu wata shirt ce a jikinsa wadda bata da nauyi ko kadan,hakanan wandon jikinsa ya sauko amma baikai masa idon sahu ba,kayan duka black ne wannan ya sanya suka haskashi sosai.
"Kina buqatan wani abu?" Ya fadi gently muryarsa na nuna rauni da gajiya a cikinta.
"Babu" ta fadi qasa qasa tana yin qasa da kanta. Idanu yadan zuba mata,gajiya yakeji yanzun bayason debo rigima,amma da tabbas yadda take amsashin da sai yayi maganinta,sai kuma ya birkitata.
Sakin wannan tunanin yayi ya tako ciki,ya isa gaban build in wardrobe din dake dakin,ya zugeta a nutse,take komai dake ciki ya bayyana.
Kayan sawa ne cike a ciki na mata,takalma,mayafi harma da hijabai. Ya riga ya zuba komai a gidan,don dama ya qudurce a ransa muddin ya dawo daga tafiyar zaiyi terminating komai,sai kuma Allah ya taimakeshi komai yazo a sauqi.
"Kiyi wanka ga kaya nan ki saka....... banason qazanta aikin sani?" Ya qarashe maganar da sigar tambaya. Fararen Idanunta ta daga tana dubansa cikin mamaki,ita zai cewa bayason qazanta bayan yafi kowa sanin halinta tun ba yau ba?,kuma ya wani hade rai yana gaya mata umarni,kamar ma itace tayi masa laifi ba shine yayi mata ba?,bayan ya rabota da gida tana tsakiyar rayuwarta da mutane......ya finciketa da qarfi ya sanyata barin gida a lokacin da ko da wasa tunaninta bai taba kawo mata irin haka zata faru ba.
Wannan tunanin ya sanya qwalla ta tarar mata,amma duk da haka sai ta miqe tana zare takalmin qafarta,ta sanya wasu lausasan flipflops data gani a gefan wajen tana dosar qofar da ta tabbatar toilet ne.
"Wait" taji yace yana qare mata kallo. Kukanta wani irin horo ne da takewa zuciyarsa ba tare data sani ba,baisan me zaiyi ya tsaida wadannan hawayen daga idanunta ba,duk da a yanzun bai shirya zuwa mata da lalama ba,amna dole ya hanata yawan wannan kukan ko don saboda abinda take dauke dashi.....ya qarasa raya hakan yana sauke idanunsa akan shafaffen cikinta da yake kaman zai manne da bayanta.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 126
Murmushi ya subuce masa can qasan ransa ba tare da ya bari fuskar ta nuna ba. Duk second daya da zai wuce muddin zai tuna cewa yana dab da sake zama baba sai farincikinsa ya sake ninkuwa. Yana burin ganin wannan tulelen cikin a jikin sultanarshi kaman waccan lokaci. Yanason yaga shagawabbiyar sultanarshi dinnan da juna biyu irin na kowacce diya mace,yanason ya bata daman baje kolin dukka sauran tabararta da batayi ba a shekarun baya,dum wata shagwaba da shine ya zama silar yankewarta da manna mata juna biyun benazeer da batoul da yayi ba tare da dukkansu sun shirya ba.
Bayanta ya tsaya,sai ya duqa a hankali ya zura hannayensa ta bayantan ta qasan mayafin nata. Jin hannunsa tayi kawai saman fatar bayanta, numfashinta ya fusga da qarfi yana shirin qwace mata saboda wani irin abu da yayi tasiri cikin gangar jikinta.
Qaramar sheshsheqa ya saki da dumin skin dinta daya ratsashi ta tsakiyar tafin hannunsa. Lullubin kanta ya fara warewa a hankali yana duban fuskarta. Hannu ta daga kaman zata riqe mayafin,sai kuma ta tuna da alqawarin da ama ta sanya tayi mata,don haka ga sauke hannu a hankali tana maida idanunta masu zara zaran eye lashes ta kulle.
Sai daya gama cirewa ya ajiye gefe,sannan ya sake hade tazarar dake tsakaninsu yana dora hannunsa saman zip din rigarta,idanunshi saman fuskarta yana kallon reaction dinta. Hakan bai masa ba,qwayar idanunta yakeson gani,itace fitilarsa dake fallasa masa halin da zuciyarta ke ciki,bayason kulle idamun da tayi,yanaso ya gani da gaske tayi kewarsa koda tanason qaryata kanta da kanta akan hakan?,yanaso ga gani da gaske tana da feelings a kansa kamar yadda yakejin wani mahaukacin feelings a kanta ko kuwa?,don haka ya matsa da bakinsa daidai fuskarta ya busa mata wata sassanyan iska saman fuskarta.
Kaman zata shide haka taji,taja numfashi me qarfi ta kuma dinga fesar dashi a hankali a hankali tana jin zuciyarta na wani riqewa. Boyayyen murmushi ya saki,kafiyarta da taurin kanta wani zubin suna burgeshi,alamu ne na inda an barta takai shekarun da maza zasu shiga gasar neman aurenta......tabbas zata jasu a qasa,hakanan ba za'a iya juya akalarta ko samun zuciyarta cikin sauqi ba.
"Bude idanunki kije kiyi wanka......na fadi ba qazanta a gidan nan" ya fadi yana shan mur..... shima yanason ko yaya ne yadan taba zuciyarta,a yadda ya zura hannunsa yana zare zip din rigarta yayi imanin zuciyarta sai ta raya mata samun romance ko yaya daga wajensa,sai gashi yabar mata zip dinta cak tsakiya baikai qasa ba bai kuma rufeshi ba gaba daya,yayi sauri ya juya yana hadiye yawun bakinsa,bayason ta fahimci yana da feelings a kanta yanzun,yanaso ko yaya ta dandani abinda yake dandana.
Idanun nata ta ware a hankali da suka sauya launi tana kallon hanyar daya fita. Haka kawai qasan ranta taji wani iri da hakan da yayi,jikinta a mugun mace ta sabule rigar ta maida gurbinta da towel taja qafafunta zuwa bandakin.
Tsaye tayi a gaban madubi tana kallin fuskarta tana kuma jin yadda kowacce gaba a jikinta take aiki,ta lumshe idanunta ta kuma bude tanason tabbatarwa da kanta da gaske ne abinda takeji a