Showing 288001 words to 291000 words out of 294767 words
Chapter 97 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Sai daya kammala cin abincin ama tana gyara wajen ya kalleshi
"Ya akayi angon qarni?" Da gaske kunyar aba din yanzu yakeji,yadan murmusawa yana dan basarwa,sai yayi gyaran murya
"Aba cewa nayi kaman ya kamata a bawa yaran nan suna ko?" Idanu aba ya zuba masa sannan ya saki murmushi
"To kai banda abinka aliyyu ina ruwan aba a nan?,shine uban?,na baka wuqa da nama,ka saka musu duk sunan da kaga ya kamata"
Kunya ta sake kamashi,har yanzun halin aba yana nan na bawa yara 'yancinsu,ba takura ba shiga haqqi muddin baka sabawa addini ba.
Yayi shuru kaman bazaiyi magana ba,akwai sunayen da yawa da suka cancanci ace an sanyasu,baisan wanne zai dauka a ciki yabar wani ba.
"Feel free,yancinka ne,kada kaji nauyina" aba ya fadi ya jawo wayarsa yana budewa. Zamansa ya gyara sannan yace
"Mohmoud da hamid,sai kuma khadeejatou(bibi)"
"A'ah,mohmoud hamid da hamdiyya dai aliyyu" suka tsinci muryar bibi da basusan ta fito ba tana fadi.
Dukkansu suka waiwaya suna kallonta tana takowa a hankali saboda ciwon qafafunta. Aba ne ya miqe yana gyara mata kujera,daidai fitowar ama itama
"Bibi ya za'a miki takwara kice bakiso?" Ama ta fadi bayan bibin ta zauna. Kai ta daga ta kalli ama
"Ke kikafi cancanta a yiwa takwara hamdiyya,kece jarumar.....kece kika sauya komai daga inda yake zuwa yadda ya zamana a yanzun.....ke kikayi gwagwarmayar hamdiyya....ke kikafi cancanta......a yanzu na yafe takwara,na amince a yiwa hamdiyya" ta fadi cikin raunin murya. Zuciyar ama itama raunin tayi,ba shakka bibi ta nuna dattako ta nuna kuma karamci
"Shikenan kai aliyyu kaji,saika maye hamdiyya a madadin khadeeja,Allah ya rayasu yayi musu albarka".
Dukkansu sai suka kasa barin gurin,sukayi zaman hira ana tuna abubuwa da suka wuce,wasu ayi dariya wasu a jajanta.
A washegari ne najma ta baiwa kowannensu wakilin suna,ta zauna ta duba sunaye sannan ta daga Mahmoud daya kasance babban
"Mohmoud aseem" ta daga usaininshi
"Hamid Waseem" ta ajjiye ta daga gambonsu
"Hajiya ama kenan,hamdiyya BIRRA"
"ASEEM,WASEEM,BIRRA" Goumar dake zaune yana biye mata ya maimaita sunayen a jere.
Kwanaki bakwai jikinta sultana yayi kyau,ta fara maida jikinta saboda samun isashiyar kulawa da takeyi. A zagayowar sati na biyu gaba daya yaran suka fara wani hawa,wanda yake nuna zaiyi wahala idan ba irin jikinsu batoul suka dauko ba. Daga benazeer har batoul sun maida dakin wajen wuninsu da kwanansu,wani irin so sukewa yaran,kamar su hadiyesu,qauna sosai irin ta dan uwa da dan uwansa.
Watansu biyu suka kammala komai dukkaninsu suka dunguma zuwa Nigeria.
Hutu sosai suka sakeyi a Nigeria din,ta fahimci kuma akwai abinda ya saukar dasu Nigeria din,saidai bata zafafa sanya kanta akan abubuwan da ba'a nemi ta shiga ba.
Zaman da sukayi a nan ayana tazo musu sosai,da farko babu sakewa tsakaninta da sultana,saidai kuma ita ayana gaba daya ta kasa jurewa,don sosai 'yan ukun sultana ke tafiya da ita. Yara ne masu wani irin farinjini kamar 'yan uwansu,musamman da yake abune da ba'a saba gani ba a al'umma,yan uku abune me matuqar jan hankali a cikin al'umma,bare yaran lafiyayyu ne,ga tsananin tsafta da suke samu. Duk kayan da zasu sanya kuwa designer ne wanda mafi yawa sabon design ne da bai gama shigowa cikin jama'a ba. Rainon mamarsu ya amshesu sosai,komai na yaran dabanne.
Koda tazo bata iya cikakken kwana biyar bata dawo gidan ba saboda yaran. Sannu sannu hira tadan fara shiga tsakaninta da sultanan,don dama ita sultanan tun bayan faruwar abun bata riqi waninsu a rai ba,ko laila ko ita.
Birra na kwance cikin jikin ayana din tana barci abinta lakadan cikin tattausan kayan bacci. Sultana na gefe tana amsa wayar maina wanda duka kusan qorafi yake mata akan me yasa zata yarda ama tana boye masa ita?,koda bata fama warkewa ba yana buqatar kulawarta. Da qyar ta samu ta lallabashi,ta sauke wayar tana sauke numfashi gami da furzar da iska.
Murmushi ayana ta saki tana duban sultana
"Duk macen da tayi gigin auren maina tasha wahala,don zata zama 'yar kallo" idanu Sultana ta daga tana kallon ayana,sai dariya ta kubce mata
"Innalillahi,ya kike haka?,so kike ki kashema mijina kasuwa?"
"Ai gwara na gaya musu gaskiya wallahi.....mijinki na dabanne kamar yadda soyayyarku take ta daban,ko mu a baya rashin sani ya sanyamu gigin son saka kanmu a muhallin da ba namu ba......amma mu kanmu mun fahimci gangan ce" dariya sosai ta bawa sultana,daga nan sai kuma hira ta barke a tsakaninsu.
Bayan komai ya kammala ta fahimci katafaren kamfani ne na hadin gwiwa tsakanin aba maina da ama sai saddi da almu. Basu bar Nigeria ba sai da komai ya daidaita,yaran suka fahimci komai duk da qarancin shekarunsu bisa jagoranci uncle tahir. Kafin su wuce saida maina ya tabbatar da kammaluwar ginin mansion house dinsa daya bawa kowa mamaki. Yanason Nigeria kuma yana sha'awar zama cikinta shi yasa ya aje irin wannan gidan,wanda a nijer dinma irinsa yake dab da kammaluwa.
*_CONCLUSION_*ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½*_GUDUN ΖADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 155
*_Bayan shekara BIYU_*
K'arfe hudu na yammaci jirgin saudi airlines ya sauke jerin gwanon fasinjojin daya dauko daga qasa me tsarki zuwa qasaf nijer cikin garin maradi.
Cikin iyalan daya samu nasarar debowa,akwai familyn hamdiyya abdu me kano(ama),sannan kuma iyali jinin Aliyyu hamidou MAYAK'I(maina).
Lokacin da aka sauke matakalar da zata sadasu xuwa ga shakadeden filin,Bintou aliyyu hamidou(batoul),Nadeeya aliyyu hamidou(benazeer), khadeeja aliyyu hamidou(BIRRA),hamid aliyyu hamid(waseem),mohmoud aliyyu hamid(aseem) haka suka biyo baya daya bayan daya.
Kyawawan 'yammatan twins din masu tsananin kama da juna sune xaka fara gani a gaba,daya a gefan daya. Daga nesa kawai zaka fahimci me yawan surutun wato benazeer, batoul me halin daddynta kuwa nata saurare,sai fararen qwayoyin idanunta da suke kama dana mamanta wanda ta boyesu cikin brown sunglasses daya qara musu kyau su duka biyun.
Sai da suka kai qasa sannan birra ta juya bayan taja tunga ta tsaya, batoul ce ta fara ganinta ta waiwaya a nutse cikin tataccen harshen faransanci daya kama bakinsu take mata magana
"Wuce mana muje". Kafada tadan maqale ta narke fuskar nan me tsananin kama data maina,tamkar an dauko fuskarsa an aza a tata
"Mummy nake jira"
"Eh na sani ai maqalemata.....kinsan tare zasu fito da daddy ko?" Ta qarasa maganar akwai seriousness dinnan irin na maina akan fuskarta.
Kafin su qarasa cewa komai ma'auratan guda biyu suka fara sanyo qafafunsu zuwa qasa. Aliyyu hamidou MAYAK'I da sulthana hamani mohmoud. Ma'aurata mafiya dacewa da juna ta fannin halitta....kamanni halaye da kuma dabi'a.
Mummy sultana......wadda a yanzun duba daya zakayi mata ka kirata da CIKAKKIYAR MACE,wadda auren wuri da haihuwar wuri suka zame ma rayuwarta ado da kuma gata. Da za'a yi maka tambaya su waye benazeer da batoul a wajenta?,tashin farko cike da qwarin gwiwa zaka bada amsa da
"Qannenta ne" ba wata alama ta kusa kota nesa da zata sanya kayi zaton cewa daga jikinta suka fito.
Ko a yanzun da hannayenta ke cikin na masoyinta kuma mijinta da baya gajiya da dawainiya da ita,da kuma jurewa wasu halaye nata da dama tun usul yasan kayarshi dasu. Sanye take cikin wata baqar abaya me azabar kyau da sulbi saqar qasar oman,budaddiya da bata fidda wannan kyakkyawan shape din nata ko kadan ba. Idanunta itama saye cikin baqin sun glasses daya sake qawata fuskarta ya kuma fidda kyawunta da quruciyarta muraran.
Qaramar handbag ce ta kamfanin Hermes a daya hannun nata da kuma carbin counter.
A yadda take din,macace me matuqar sakewa da barkwanci ga iyalanta,me yawan jansu a jiki,musamman benazeer da batoul da a qalla zuwa yanzu suka doshi shekara sha uku,amma girman jikinsu yasa zakayi zaton sunkai shekaru sha biyar,sun doshi shekarun fara girma,shekaru masu hadari a rayuwar yarinya. Tasan illar irin wannan lokacin,tasan kuma matsalolinsa,wannan ya sanya ta sake musu ainun duk da cewa basu hannunta,suna hannun matar da ita kanta fiye da rabun tarbiyyarta a wajenta ta tsotsa wato AMA da suka maidawa suna AMOUR wato LOVE a turance. Ta cancanci sunan,don ta zame musu bango abun jingina,ita din madogara ce ta gaske.
Wani irin matsanancin so takewa jikokin nata,soyayya fiye da son da takewa kanta,son da take musu bata hadashi dana kowa,soyayyar da take musu a bayyane take,gata take musu irin gatan daya amsa sunansa gata,saidai kuma duk da hakan.....bata yarda ba,bata kuma lamunci sangarta ko sauka daga hanyar data kamata ba.
"Soulsis" maina ya kira sunanta qasa qasa. Idanunta dake saye a glass ta daga ta kalleshi
"Are you okay?" Yayi mata tambayar da daga jiya zuwa yau batasan adadin sau nawa yayi mata ita ba. Qarfin hali tayi sosai wajen tattaro dauriyarta ta sakar masa murmushi
"Am okay daddy" idanun nan nasa ya kafeta dasu yanason gano gaskiyarta ko akasin haka,sai ya kasa jurewa,ya miqa hannu ya zare glass din fuskarta,take qwayar idanunta da take hanashi gani tun jiya suka bayyana.
Da sauri tayi qas dasu,saboda tasan muddin ya kalla din zai fahimci bata jinta daidai,wanda hakan kuma daidai yake da zuwan tashi nutsuwar
"Qarya soulsis?" Ya tambayeta a sanyaye
"Ba qarya nayi maka ba daddy......bansan me yake damuna ba.....banajin dadin zuciyata gaba daya,jikina kuma ina jin wani irin zazzabi ta cikin qashi na" ta bashi amsa takai tsaye.
"Ya salam.......ko rashin lafiyar bibi kika saka a ranki?,amma kin manta ama tace jikinta da sauqi sosai?,saboda wanann damuwar taki ya sanya na rage kwanakin zamanmu a makka fa?" Haka kawai taji zuciyarta ta karaya,amma ta hana kanta bayyana hakan,ta dubeshi da guntun murmushi saman fuskarta
"Nafi tunanin zazzabin dake damun jikina ne fa bloodline" dan zuba mata idanu yayi sannan kuma ya janye daga kallon nata badon ya gamsu ba
"Asibiti zaka wuce damu" ya furta ta hanyar amsa kiran driver dinsu ta Bluetooth din kunnensa.
"Asibiti kuma daddy?" Ta furta a shagwabe. Da idanu yayi mata nuni da yara dake tsaye daga gabansu kadan wadanda sukka suka zuba mata idanu cikin damuwar ko wani abune yake damun mummyn nasu. Tun suna can batoul ta fara yiwa benazeer complain na daukewar fara'ar mummyn nasu da kuma raguwar kuzarinta.
Suna hada idanu da yaran sai tayi qoqarin komawa kan control dinta,ta waiwayo suka hada ido sai ya kashe mata ido daya gami da daga mata gira. Ta fahimceshi,dole kenan ta bada kai su zarce asibitin.
Sam baya wasa da lafiyarsu,ko yaya abu yake zaice aje aga likita,wannan ma ya sanya abubuwa da yawa bata gaya masa saboda gudun daga masa hankali akan ciwon da baikai ya kawo ba.
Babbar motar dake da wani irin kwarjini da daukan idanu ta daukesu gaba daya. Sabuwar qira ce da duka duka bata kai watanni uku da bayyana ba daga qasar Dubai.
Duk abinnan birra na jikinta, batoul tayi tayi amma tace ita tana wajen momma dole ta rabu da ita.
Suna cikin motar amma haka kawai tunaninta yake lulawa wajen bibi. Kwana uku kenan da sukayi waya da ita,doguwar wayar da bazata iya tuna kaf tsahon rayuwarta yaushe suka taba irinta ba,tun tana sultanar bibi har ta koma ta maina. Sunyi wata irin hira data tsayawa sultana a rai,ta kuma kasa mancewa da kowacce kalma data gaya mata. Haka kawai hirar ke yawan fado.mata a rai,take kuma nanata kowacce kalma dake ciki.
Me abu da abinsa,asibitin nasu ne,don haka da shigarsu da gama ganinta duka ba'a haura minti arba'in ba. Sakamako kuwa ya fito da kyansa,ta samo tsarabar saudiyya,juna biyu na iya dadin watanni biyunsu a can.
Baisan alaqarsa da son yara ba,baisan me yasa Allah ya jarabceshi da son haihuwa ba,ko don ama bata da yara da yawa?,ko don itama ama din hakanan Allah ya halicci zuciyarta a wajenta sukayi gado?.
Duk yadda yaso daurewa saida idanunsa suka fidda qwallar farinciki. Ya tsugunna gabanta,ya riqr hannunta sosai yana hadiyar wani abu ya kasa cewa da ita komai,at last muryarsa ta fita bakinsa ya budu
"Allah yayi miki albarka,ya jiqan mahaifanki" shine abinda ya iya furta mata.
Ita kam jin komai take kaman a mafarki,ta zaci haihuwar sunyi sallama da ita,tunda gasu birra nada shekara biyar a duniya. Ta sani zata ga farinciki fiye ma da wanda ta gani a tattare dashi,don tsahon shekarun su birra da waseem da aseem kullum zancansa
"Soulsis.......i need more"
"Name bloodline?"
"Twins ko triple" sau da dama dariya take masa,har ranar ya gaji bayan ta fito daga wanka tana daure da towel,ranar duka sun wuni ne wajen ama,data masa dariyar ya riqota sosai
"Zakisan kinmin dariya,in sha Allah a watannan saina tabbatar na baki ajiyar 'ya'yana" kaman ya fadi da bakin mala'iku,bat samu a watan ba,amma watanni biyun kenan da wanann maganar sai ga cikin.
So yayi yayi mata lallabawar daya saba mata shekarun baya,suna isa gida yaso ya fara killaceta yana bata kulawa,ta kama qugunsa ta riqe kaman yadda yake riqe da nata
"Daddy kullum fa girma mukeyi,yanzun nidin uwa ce,mother of five,zan iya kula da kaina na kula da yarana na kuma kula da mijina da gidana.....bare ma meye aikin daddy?,gidan duka cike yake da ma'aikata,ka wadatani da masu yimin komai,nauyin dake kaina bashi da yawa". Sai data masa dabara da kyau sannan ya fahimceta.
Zagewa tayi ita da yaran suka gyara dukka sassan da bata bari masu aiki su shiga mata,duk zirga zirgar da takeyi idanunsa da hankalinsa suna kanta,yayin da nata hankalin gaba daya yake kan bibi.
Bayan kowanne minti sai taji ta fado mata a rai,ta dinga qoqarin yakice aikin ta kira ta gaya ma ama sun sauka ta kuma ji jikin bibi amma bata samu dama ba. Don tanason ta kammala komai da tasan maina zai buqata.
Sanda ta kammala komai din kuma tana yin wanka sai zazzabi ya rufeta,daga bisani wani nannauyan bacci mara dadi yayi awon gaba da ita.*_GUDUN ΖADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 156
Tsakiyar dare baccin nata ya yanke da wani irin mafarki da ya sanyayar mata da jiki. Ta miqe a hankali tana kiran sunan Allah, jikinta sosai ya jiqe da gumi,ta juya da nufin canza side na kwanciyarta sai idanunta ya fada a kansa yana zaune sosai saman abun sallah.
Ido suka zubawa juna ita dashi,ta sani ma'abocin tashi sallar dare ne,jajirtacce wanda addu'arsa kullum kan iyalinsa suke,baya gajiya da musu addu'a da nema musu kariyar ubangiji,amma a yau din sai yake ganin wani abu na daban saman fuskarsa.
Tanason masa magana sai ta kasa,taja jikinta a hankali ta sauka daga saman gadon ta wuce toilet,fitsari tayi ta daura alwala wai ko zataji dadin jikinta,ta dawo ta bude ruwa tasha sosai,sannan ta taka ta isa gabansa ta zauna. Hannuwansa ta kama ta riqe sai taji sunyi sanyi,ta kalli tsakiyar idanunsa saita hangi wani