Showing 6001 words to 9000 words out of 294767 words
Chapter 3 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
MOHMOUD da HAMIDOU sune yaran da bibi ta haifa da tazarar shekara hudu a tsakaninsu,batayi haihuwa ta uku ba kuma sai data shekara biyar ra haihuwar HAMIDOU(ABA) sannan ta haifi MUHAMMAT,sai oumar bashar sannan issoufou autah.
Babban tashin hankalin da suka fuskanta bayan rasa nadeeya shine na rasuwar mahaifinsu alhaji ABDALLAH wanda gaba daya sunansa yafi fice da sunan kakansu na ainihi wato MAYAK'I. Rasuwar da tayi mugun girgiza su,ta kuma daga musu hankali,don shi dinma kamar dai nadeeyan,babu wani ciwo,face dai tunanin da suke rasuwar mahaifiyar tasa ya maqale a rai har ta zame masa ajali. Hakanan cikin wani irin ciwo da rashin rabo sukaci gaba da rayuwa,cikin rashin jin dadi da kuma walagigi saboda basu saba rayuwa haka ba su kadai,don kuwa a sannan baaba ABDURRA'UF yayi nisa da agadez,bama agadez ba gaba daya nijer,tun bayan rasuwa granny da aka bashi gadonsa ya lula duniya fatauci.
Tun bayan tafiyarsa sai matsalolin rayuwa suka dinga taso musu,wadansu mutane sabbin fuska da basusansu ba,kowa yazo zaice yana bin nadeeya ko abdallah abu kaza,sai sunyi duba da wani abu me qwari cikin dukiyarsa suce yayi jinginarsa a garesu. Babu wanda bibi ta tsaya ja'inja dashi,ta barsu kawai,a sannan mohmoud yaso ya taka birki duk da kwata kwata shekarunsa a sannan basu goma sha biyar ba amma bibi ta hanashi
"Zukatan mutane a yanzu sun qeqashe da son abun duniya,komai na duniya a nan aka sameshi kuma a nan za'a barshi,yau ina wanda ya tara dukiyarma?,ka barsu nafi buqatar taka rayuwar akan abinda aka tara muku,watan watarana sai kaga Allah ya albarkaceku da abinda yafi abinda kuka rasa" qananun shekaru da kuma zantukan bibi ya sanya hakanan suka zuba ido,basu qyalesu ba saida suka tabbatar sun rabasu da manyan kadarorin da mayak'i ya mallaka.
Shekarar da mohmoud ke aji na biyu na university,hamidou (aba) yake ajin qarshe na secondry school rayuwa ta tsananta a garesu,gidan da suke ciki ma ya soma niyyar gagararsu zama a ciki. MOHMOUD wani irin halitta ta daban Allah yayi masa,bibi tasha daga hannu ta godewa Allah da ya bata kyautar mohmoud a matsayin d'a. Yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya yin kuka saboda kawai wani yayi dariya. Yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya hanawa kansa saboda wani ya samu,yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya wanzuwa cikin radadi rudani da firgici muddin wani zai wanzu cikin walwala nutsuwa da kuma sukuni. Wanna dabi'a tasa bawai iya cikin gida ba har zuwa ga mutanen waje.
Ranar da abun yaci tura ranar da ya kammala jarabawarsa ne daga aji biyu zai shiga aji uku,sakamakon jarabawar hamidou kuma ya fito,an gama komai na cuku cukun tafiyarsa jamia,amma kudin da ake da buqata don yiwuwar hakan basu babu dalilinsu.
Idanunsu jajur yayi zaune gaban bibi yana gaya mata ya ajjiye karatunsa,ya yanke shawarar bidar kudi kota halin qaqa kota kuma wacce hanya muddin wannan hanyar halastacciya ce don ya kula da ita ya kuma kula da rayuwar qannensa
"Amma mohmoud ta yaya?,karatun naka dake sake nisa ta yaya zaka ajeshi?" Kai ya girgiza
"Sam sam karatuna a yanzu bashi da amfani,koda na yishi bazanyi farinciki ba mahaifiyata da qannena da basu da kamata suna cikin matsi da buqatar rayuwa" daga bibi har hamidou tsit sukayi suna duban mohmoud,ya fadi maganar ne har tsakiyar rai da zuciyarsa. Daga kuma randa ya furta wannan batu ya fara aiwatar da abinda ya tsara din kamar yadda yace.
Tinja tinja aka dinga yi tsakaninsa da hamidou,yace shi kuma sam bai yarda ba,bazai zama silar rujewar farinciki da kuma burikansa da shi yafi kowa saninsu ba. MOHMOUD bashi da wani babban buri a duniya da ya wuce ya zama cikakken likita,ya shaidawa bibi shine zai tallafi karatun yayan nasa,idan yayan nasa ya gama shi yayi nasa.
Wani kallo sheqeqe ya watsawa hamidou,har yanxu wannan kyakkyawar soyayyar da qaunar da granny nadeeya ta dasa musu yana biye da jinin jikinsu
"Saboda gani babban banza ko?, bakaji mr bahausa suka ce ba?, babban wa magajin uba ko?,to gwara ka soma shirin tafiyarka makaranta,don ko bakaje din ba dama karatuna tangal tangal yakeyi ai, karatun lafiya sai dan wane da wane kai kafi kowa sanin haka,ni ba babbabn kwabo bane ra zan zauna qanina ne zai tallafi buqatun qannena dana mahaifiyata ba,indai nayi hakan meye amfani na?,meye amfanin girman da Allah ya bani?".
Tun daga lokacin da ya ajjiye karatunsa ya shiga neman kudi idanu rufe saidai bisa tsaftatacciyar hanya,baya raina abinda zaya kawo masa kudi komai qanqantarsa koda kuwa kwasar kashi ce. MOHMOUD dan gayu dan gata sai gashi tashi daya rayuwa na tamaula dashi tana sauya masa kamanni da tsarin rayuwa. Yasha dawowa gida ya kasa bacci saboda ciwon jiki ciwon kai ko ciwon qafafu,amma baya bari kowa ya sani. Saidai kuma wannan dashashiyar qaunar tana nan tana kewayawa,duk wani motsin MAHMOUD din bisa idanu da kiyayewar HAMIDOU ne, hamidou din yasha boyewa yayi kuka saboda ganin yadda yayan nasu ke bautar da kansa saboda su,iya yadda yake tunanin yaa mohmoud yana sonsu sai a yanzu ya tabbatar abun ya zarce haka,ya kuma shallake hankali da tunaninsa. MOHMOUD ne faskare, MAHMOUD ne tura ruwa, MAHMOUD ne dako, MAHMOUD ne share share goge goge da wanke wanke a gidajen saida abinci duk don kada karatun hamidou ya samu tangarda,kada karatun su oumar ya tsaya,kada bibi ta buqaci wani abun ta rasa,ya gwammace shi yayi kuka muddin su zasuyi dariya. Ranar da ya gaza jurewa ganin dan uwan nasa ahaka cikin wani darene da MAHMOUD din ya kasa bacci saboda radadi da hannunsa ke masa saboda yawan itacen daya faskara duk don ya qarasa hada kudin registration din hamidou.
Yana ganin hamidou din ya motsa yayi saurin boye hannuwansa,saidai kuma tuni shima ya kama hannuwan yana kalla. Wasu hawaye suka zarto daga idanunsa yana dubansa
"Hamma....wannan abun da kakeyi a kanmu yayi yawa,ka sassauta gangar jiki da zuciyarka don Allah hamma" hamidou ya fada yana hawaye. Jawoshi kawai mohmoud yayi yana bubbuga bayansa
"Inajinku ne tamkar 'ya'yan da suka fita a ciki na,zuciyata da ruhina ba zasu taba samun nutsuwa ba muddin dayanku na cikin buqata" sun jima a daren hamidou yana gasa masa hannunsa,tun kuma daga ranar yasa ya masa alqawarin daina boye masa wasu abubuwan,sannan wasu lokutan tare suke fita ayyukan,amma yanayin karatu ba kasafai yake barin hamidou din binsa ba. Shima kuma MAHMOUD din yafison hakan,yace yafison yayi zamansa ya maida hankalinsa akan karatunsa shi shine farincikinsa.......*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
*BOOK 02 PAGE 04*
_________________________________
*_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_*
*_SUTURA ABAR TUNQAHO_*
*_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_*
_Magana akeyi ta_
*UMMU MAHNOOR LUXURIES*
*UMMU MAHNOOR LUXURIES*
_GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_
*_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_*
*_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_*
*_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_*
*KYAU*
*QUALITY DA DAUKAN HANKALI*
*LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA*
*GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA*
*_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*
08135142610
*INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES
*FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA
*_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_*
*_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_*
*_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_*
*TASTED AND TRUSTED*👌👌👌
_________________________________________
*HAMDIYYA ABDU ME KANO*
Yarinyar da tafi kowa kyau cikin school din,ajjiye kyau a gefe,idan ana batun gata za'a iya cewa kaf makarantar babu diyan da ya kaita gata wala mace ko namiji.
Ita din diya ce ga attajiri alhaji abdullahi me kano,mashahurin dan kasuwa wanda inda arziqi yana yawa za'a iya cewa nashin har yayi yawa. Arziqi da aka nemeshi da zuciya da kuma qwanji,aka tara shi cikin albarka iyaye data al'umma. Yaranshi uku kacal a duniya,tajuddeen da ake kira da taj,sai mebi masa abdulhakeem sai kuma 'yar daya daya 'yar gatansu kuma 'yar gaban goshin kowa wato hamdiyya(ama). An haifi hamdiyya ne a lokacin da kowa ya fidda rai daga sake samun haihuwar mahaifiyarta hajiya aisha a duniya,bayan wasu shekaru harsu abdulhakeem sun fara yin hankali,don a qalla a cikinsu babu wanda ya bata qasa da shekara goma. Tazo a dai dai sanda suke da kwadayin qananun yara a gidan,kuma tazo a jinsin diya macen da basu da ita,wannan ya sanya gata yayi mata rubdugu tako ina,kowa kawo nashi gudunmawar gatan yakeyi. Idan akace gata ana nufin gata me sunan gata,gatan da ya sanya take cike da haushin yadda rayuwar sultana take,domin kuwa idan za'a dora mizanin gatan da sultana ke samu da wanda ita ta samu a zamanin quruciya zata iya cewa sultana din bata samu kaso daya cikin goman nata gatan ba,saidai natan bai hanata samun cikakkiyar tarbiyya da kulawa ba. Sam sam alhaj abdullahi da aishatu matarsa basa cikin jerin sahun mutanen da suka aza dukiya a gaban tarbiyya yaransu. Sau da dama yanayin tarbiyya yaran alhaji abdullahi na bawa daruruwan mutane mamaki. A yadda mahaifinsu keda kudi ruwa ruwa kamar su kasheshi,ko kadan ba zaka taba tsammatar samun tarbiyya haka daga yaransa ba,sakamakon yadda ya zama kamar wani tambari ko al'ada na yaran da iyayensu ke da hali,sukan tashi a sangarce,babu ganin girman babba bare akai ga sanin haqqin qarami,gaisuwa ma kam ba kowanne ke tashi da iyata ba,wanda wannan babban kuskure ne ga rayuwa,domin da 'ya'ya da dukiya dukka amana ce kuma jarrabawa ce,idan ka jagorancesu ta hanya me kyau kaci moriyarsu cikin kwanciyar hankali da farinciki,idan ka jasu kuma ta akasin hakan lallai bone da nadama yana nan tafe.
Hajiya aishatu mahaifiyar ama itace haifaffiyar qasar NIJER, CIKAKKIYAR buzuwa gaba da baya wadda har rayuwa tayi mata zurfi cikin nijeria bakinta baya fidda hausa tar kamar yadda ya kamata.
Sun rayu kuma tashi da tsananin zumunci,daga dangin mahaifi har na mahaifiya babu wanda suka bari a baya wajen sada zumuncinsu,wannan ya sanya alaqa me qarfi tsakaninsu da dangin mahaifiyarsu dake nijer. A duk sanda suka samu hutu suna ware lokaci sosai da zasuje ga dangin mahaifiyarsun suyi masu kwanaki su juyo,wannan ya sanya nijer taso janye hamdiyya banda tsananin son da suke mata da tuni zamanta a Nigeria ya zama labari,saidai duk da hakan bayan ta kammala secondry school kakarta ta dauketa da zummar hutu kawai zatayi ta dawo,sai gashi zama ya miqa,duk da yadda abbanta dama su abdulhakeem ke jelen ta dawo gida
"Yo ku meye naku ne bayan kowannenku yana nashi gidan da iyalinsa?,ku jiyemin yara da sanabe?" Hajja kakarsu ta fadi tana kama haba
"Gidan ne ba kowa fa,daga maama sai masu aiki" tajuddeen ya fada
"Sai kuma kayita yi,amma tabbas jikina ya bani nijer saita janye hamdiyya" ta fadi saboda yadda taga tana sha'awar qasar sosai da son zuwa tare da son zama a cikinta.
Kai tsaye qanin mahaifiyarta ya soma mata cuku cuku sanda aka fara diban dalibai a matakin karatu na gaba da secondry. A tsarin jami'ar hamdiyya bata da wani aibu ko nakasu da zaya hanata samun gurbi. Results dinta sunyi kyau har abun ya dinga basu mamaki,saidai kuma ba abun mamaki bane,saboda baiwar wata budaddiyar kwanya Allah ya bawa ita hamdiyya din,abun kuma sai ya hadu da nacin son karatu da take dashi.
Sanda ta shiga makarantar hamidou(aba) yana aji uku,kuma shine president na makarantar gaba daya. Ranar data fara zuwa ranar ta fara ganin aba din, saboda a ranar sun gudanar da zanga zangar lumana cikin makarantar. Tana zaune daga qasan bishiya tana jiran driver ya iso ya dauketa,tanata zumbura baki irin na yaran da gata ya yiwa yawa,tana jin yadda zafin rana ya bude a sararin makarantar ya hadu da rairayin yashi yake bada wani hucin zafi har saman fatarta,daidai sanda dandazon matasan makarantar suke yowa ta area din da take.
Tsaki taja me qarfi tana qorafi cikin ranta na yadda ko zafin ranar sukam basuji?. Tana zaune har suka qaraso inda take suna wucewa da ifce ifcensu wanda yake cikin tsari ne ba hauka bare sauka daga tsari.
Da idanu take binsu kawai bakinta a tabe daya bayan daya,tanason gano waye shugaban wannan wahalar?,sukam me suka rasa da zasu damu kansu da surutai haka da rally cikin makaranta?. Caraf idanunta ya sauka saman fuskar kyakkyawan matashin buzun. Sanye yake da wasu jajayen kaya da baqar p cap wadda duk da ta dan rufe fuskarsa kadan amma hakan bai hanata hango gumi da yadan jiqa goshinsa ba,ya kuma bada damshi saman kyakkyawar fuskarsa dake da wani irin sassanyan kyau me matuqar jan hankali.
Kaf yawun bakinta ya katse,ta qifta idanunta ta sake budesu duka lokaci guda tana hadiye busashen miyau din da yayi saura a bakinta. Tunda take zata iya cewa idanuwanta basu taba tozali da namiji me kyan aba ba.
Bata cika buri cikin rayuwa ba,bata da wulaqanci sai son jama'a da take dashi,bata da daukan rayuwa da zafi saboda ta fito daga gidan wadata,amma kuma tana da wani buri qwaya daya da kaf gidansu hatta da abbanta da wasu makusantanta na kurkusa sunsan dashi,wato tana son KYAKKYAWAN NAMIJI. Ba wai abu bane data tsireshi bayan ta girma ba,ko kuma bayan ta fahimci ita dinma me kyau ce ajin farko, a'ah tun tana qanqanuwarta take da wannan dabi'ar. Mama mahaifiyarta bata zafafa mata ba tun daga quruciyar,saidai ta zafafa wajen addu'ar idan ta isa munzali qaddarar aure ta zowa diyartata ubangiji ya hadata da nagartaccen miji salihi kuma managarci. Tun su abdulhakeem suna tsokanarta har suka fahimci da gasken gaske a jininta ne kuma raayinta ne hakan,sai suka daina tsokanar suma sai lokaci bayan lokaci.
Akwai tarin maza da suka amsa sunansu,masu kyau irin kyan nan abun kwatance da suke maqurar qaunarta da neman soyayyarta,to amma sai Allah ya sanya mata wani irin hali na shariya da miskilanci. Duk son jama'arta da haba haba dinta miskilar kanta ce idan taso.
Bada umarnin da aba yayi wajen dakatawa aje a bada faralin sallah ya sake fusgar hankalinta,tana nan a zaune taron ya watse,ya nufi hanyar masallacin makarantar bangaren maza yana zare pcap din kansa shi da 'yan tawagarsa suna tattaunawa,cire hular kuma da ya sake bayyanar mata da asalin kyansa.
Tun daga ranar bata sake ganinsa ba,hakanan zuciyarta bata huta da tunanin waccan ranar ba. Bata kuma sake ganin nasa ba sai bayan watanni shida,karatunta ya soma yin nisa,ana shirye shiryen fara exams da tafiya hutu. A sannan ne dalibai suka qirqiri wasu programs da sukan gabatar a lokuta irin wadannan,ciki harda zaben sarauniyar kyau ta makarantar.
A lokacin sai kawai gani tayi sunanta ya fita cikin list din wadanda zasu tsaya a matsayin. Ranta ya baci hankalinta kuma ya tashi. Tana da qawaye tunda ita din macace me kirki,bata raba dayan biyun a cikinsunne wata ta bada sunanta,kuma tunaninta ya tafi kan mutum daya data tabbatar bazata wuce ita bace wato ummuhani mammadou. Koda ta tuhumeta din kuwa ita dince. Fada ta balbaleta dashi akan ba zata shiga ba,tace kuma tun wuri su zame sunanta don ba abinda tazo yi ba kenan.
Lokacin aba na zaune cikin 'yan kwamitin tsare tsare ummahani ta shaidawa hafeez wanda shi ya qirqiri abun cewa hamdiyya na buqatar a zame sunanta,ta kuma baiwa hafeez haquri,wanda koda bayan ummahani ta wuce bai fasa qorafi ba
"Ita daya ce zata sanya makarantarmu taci wannan competition din,yanzun wace zata maye mana gurbinta?"
"A soke wannan cikin tsare tsarenmu hafeez, banason irin wadannan abubuwan" shine kawai abinda aba yace.
Bai taba ganinta ko lura da wanzuwarta ba sai ranar da aka fara programs din. Sai kuma a ranar program din da aba yace a soke yaji basu soke din ba,don a wajen aka fara neman 'yammatan da suka shiga suzo su fara rehearsal.
Ko motsi hamdiyya batayiba sanda aka kira sunanta saboda tasan tuni ta bada sanarwar fita daga lamarin. Aka dinga maimaita kiran sunanta amma ko motsi,abinda ya sanya MC pointing dinta don shi ya hangota,take kuwa idanu sukayi caaa a kanta. Adadin idanuwan ya sanya kanta sarawa,sai kawai ta miqe tsam ta dinga ratsawa ta cikin jama'a har ta fice