Showing 207001 words to 210000 words out of 294767 words

Chapter 70 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

da bakinki......wallah.....indai na haifu jinin aba......saikin qaryata kanki cikin mutane sababin yadda kika fadi maganarki a sirrance" ya fadi a fili murya a qasa. Ya fahimci abu na qarshe da bataso shine asan yana cikin gidan cikin dakin,kanshi tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa ya fara dosar fita daga dakin gaba gadi,kanshi kuma tsaye,duk da yana jiyo muryar ama benazeer da batoul daga falon.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 110


Cikin nutsuwar data roqa Allah ya bata kada wani cikin gidan ya gano komai tattare da ita take fitowa a dakin. Ayana itace ta farko da suka fara kacibus,tana tsaye tana kurbar wani abu cikin mug,jikinta sanye da pajamas masu dogon hannu da dogon wando,kanta sanye da qaramar hula. Sultana ce ta fara dauke idanunta daga kan ayana din. Haka kawai batason wannan kallon da take tsireta dashi,kuma sam tana jin jininta dana ayana bai hadu ba kwata kwata,tana da zaqewa hali guda daya da sultana taqi jininsa kenan.

Ci gaba tayi da fitowa cikin falon,ta gota ayana din ba tare data waiwayeta ba. Wani abu me tauri ayana ta hadiya hade da madarar da takesha,ita kadai tasan yadda takejin matsanancin kishin sultana cikin ranta,bayan kishi tana kishin yadda ta fita da komai,duk kuma yadda taso gano makusar sultana ko aibunta ta gaza ganowa,hasalima duk wani move nata sai yakeson ya dinga burgeta,kama daga yanayin takunta,salon yadda take magana da kums kallo,komai bisa aji da wani irin tsari.

"Good morning" ayana tace da sultanar sanda take giftata, saboda tayi imani ama zatace ta gaida matar yayanta ne,sunan matar da ama ke bawa ayana yana sanyata a nazari,da auren ko babu?,idan da auren bataga alamar wani good relationship tsakaninsu ba.

Adan dake sultana ta juya tana qoqarin dora murmushin dole kan fuskarta

"Kin tashi lpy baquwar Paris?"

"Alhamdulillah" ayana ta amsa tana lumshe ido jin yadda sunan PARIS din ya fita a bakin sultana tarwai kaman don ita aka sanyama garin sunan. Daga haka sultanan bata qara ba tayi gaba wajen yaran da ama.

Tana riqe da hannun benazeer da batoul suna gaidata,amsa musu takeyi amma kaf hankalinta ba'a kansu yake ba. Gani takeyi kaman zai fito yabar dakin,tasan halinsa komai ma zai iyayi,bashi da tsoro,hakanan ba abinda yake canza masa maganarsa.

Waiwayawa tayi suka hada idanu da ama,saita samu kanta da sulalewa har qasa tana gaidata,duk da saita rusuna sosai din take gaidata kullum kwanan duniya,amma gaisuwar yau din ta banbanta da ta kullum.

"Lafiya alhamdulillah" ama din ta amsa mata tana dauke kanta daga gareta

"Batoul riqewa aba wannan muje" ama ta fadi tana miqawa batoul wasu qananun cups biyu

"Ni ba za'a bani na riqe masa ba?" Benazer ta fada tana karya wuya gami da maqale kafada

"Batoul yace a bawa,next time sai a baki kema" ama ta amsata tana daukan warmer ta soma yin gaba.

'Yar qaramar sautin da qofofin dakunan ke bayarwa a duk sanda aka budesu yaja hankalin ayana dake zaune cikin falon tana satar kallon sultana da yaranta cike da kishi. Mutuwar zaune tayi ganin wanda ke fitowa daga dakin sanye da kayan bacci da suke bada tabbacin ko a nan ya kwana,ko kuma ya shigo da asuba yayi bacci cikin dakin,don yanayin fuskarsa ta nuna lallai daga baccin ya tashi. Kasa motsi tayi,sai idanu data zuba masa,qwaqwalwarta ta kasa tuna ko tantance komai. Ya haidar ne ya fito daga dakin sultana, dakin da tana a tsaye itama sultanar ta fito daga ciki?. Wani irin abu taji yana mata yawo dukka sassan jikinta,ta kasa controlling yadda zuciyarta ke mata zafi,saita dinga qoqarin dauke kanta daga sashen da yake don tana gudun abinda zuciyarta zata iya ci gaba da raya mata a kansu.

Sam baima lura da wanzuwarta a wajen ba,dukka hankalinsa yana kansu,yana jingine jikin qofar dakin yana murmushi gami da kallon dukka drama din da akeyi tsakanin ama dasu din hannayensa nade a qirjinsa. Dama haka akeji duk safiya sanda ka wayi gari cikin familynka?. Baya benazeer taja alamun taji haushi,sultana da takeson kowa da kowa yabar falon koda zai fito ta juya tana zare mata idanu

"Ba za'a gaya miki magana ki haqura ba?,oya wuce muje" baki ta kyabe kaman zata saki kuka sannan tayi gaban,sultana ta bita da kallo ta soma takawa tana bin bayansu itama. Bakin qofar ya bari shima yana nufar hanyar fita,saidai kuma kafin takai ga bacewa cikin jikinta ta dinga jin kaman ana kallonta,wannan ya sanyata waiwayo babu shiri.

Mutum biyu ta gani a falon,tanja dake fitowa a kitchen da kuma maina din dake qare mata kallo tamkar yau ya fara ganinta,sai ayana da itama ke kallonsu kamar idanunta zasu fado d wani mahaukacin kishi. Wani gumi ya yanko mata,ta firgice gaba daya tana fidda fararen idanunta

"Barka da safiya" tanja ta fada tana dan rusunar da kanta

"Ina kwana tanja,mun tashi lafiya"

"Lpy alhamdulillah" ta amsa masa tana wucewa dining area da dan sauri sauri da alama tanason aje abun hannunta ne ta wuce tabar musu falon,hakan ke alamta kenan ta fahimci daga inda ya fito?, sultana ta tambayi kanta da kanta. Ga ayana da tayi imanin taga fitowarsa,don ta karanceta da alama zatayi qwaqwafi da sanya idanu akan lamuran da basu shafeta ba.

Kallonta ta maida kan tanja,amma sai taga tanja din fuskarta bata nuna komai ba,bata gamsu ba,tunda tasan tanja farin sani,daga ita har maina din tanja ta haddace halin kowa,tunda ba wai yau ko jiya take tare dasu ba,tun tale tale da quruciya cikin jikkunansu. Ganin tanja ta soma barin wajen ya sanya itama ta qara sauri da zummar barin wajen,sai kuma muryar benazeer tayi mata birki

"Laaa.......daddy a nan ka kwana?" Faf ta buge bakin benazeer ba tare data shirya ba,ta kuma juyata da sauri tana saita mata hanya. Tayi imani idan ta bari wannan akun ta isa wajenshi to ba wanda ya isa ya rufa asirinsu sai Allah.

Idanunsa ya runtse har cikin zuciyarsa yana jin zafin bugun da ta yiwa benazeer din,ta riga da tabar wajen,koda yayi magana ta bacewa ganinsa bazaiji ba. Ya kusa minti biyu tsaye a wajen sannan ya juya yana ficewa daga gidan,amma ranshi yana masa susa har yanxun na dukan yarinyar da tayi. Ji yayi ya kasa jurewa,har ya isa bakin qofar gidanshi suhail ya bude masa sai yace

"Ina zuwa" ya juya yana komawa cikin gidan,duk da yaci alwashi bayason aba yasan da zamansa cikin paris ko zuwansa cikin gidan,amma yau yana jin bazai bar gidan ba sai ya mata gargadi na gaske,tafiya zaiyi na sati uku,haka zai tafi tana dukan masa yara?. Da qyar ayana taja numfashi takai hunhunta,ji tayi babu sauran space da zata iya zama cikin falon tana kallonsu,bayan ba abinda take ganowa cikin idanuwansu illa zallar soyayya me masifar zafi da akan jarabci zukata da ita,saidai kuma qasan zuciyar akwai wani abu da yakeson lallai saiya murqushe soyayyar ya hanata bayyana kanta. Duk kuwa da idanuwa suna qaryata hakan,ta cikin idanunsu kawai zaka iya karantar kome,saita miqe da sauri saurinta tana wucewa daki tun kafin ta rasa ragowar numfashin da zata shaqa,zuciyarta tana karyewa,tana jin kamar tana dab da rasa dukka damarta ne.

Tunga taja ta tsaya a hanya tana tsare batoul da ido,ta tabbatar sukaje wajen aba a haka tana kuka zai tambayi ba'asi,kuma lallai indai benazeer ce me bakin bada labari ba zata kasa gaya masa ba, musamman ita din,tatabbatar indai ta fadi aba zaya lallasheta ne,yakuma hadata da chocolate ko sweet

"Bana hanaki surutu akan duk abinda kika gani ba?,ban hanaki bada labarin abu koda tambayarki akayi ba bare ba'a tambayeki ba?" Ta fadi tana tsare yarinyar da idanu fuskarta a daure.

"Kinaso na daina kulaki kwata kwata?" Da sauri benazeer ta girgiza kai kukanta yana tsayawa tana duban sultana a tsorace

"To daga yau indai baki bar wannan halin ba ruwana dake"

"Na daina mummy" ta fada tana qwalla

"Naji......goge hawayen" ta fadi mata tana dubanta. Da kanta ta saka gefan hijabinta ta goge mata fuskar,ta tabbatar ta koma normal sannan suka wuce.

Ta samu aba tuni ya fara breakfast shi da batoul, benazeer tayi joining dinsu,ita kuma ta zauna suna hira kadan kadan da aba din tana tattare duk inda su batoul suka bata har suka kammala.

Aikenta yayi saman study table dinsa ta dauko wasu takardu,ya budesu ya miqa mata

"Wadannan fa aba?" Ta tambayeshi idanunta a waje

"Nakine sultana, mohmoud baya raye,duk abinda na raya a raina inda yana raye zanyi masa to ke ya cancanta na yiwa" jikinta gaba daya yayi sanyi,ta kasa cewa komai sai ama datake kalla kamar tana jira ta bata umarnin yin magana

"Kinga ama" ta fadi tana dorawa ama takardun a cinya. Murmushi ama ta saki,duk duniya batasan me zasuyiwa jinin mohmoud su saka masa ba,alkhairi keta bibiyarsu ta sanadin sadaukarwarsa da kuma jininsa daya bari a duniya,ita ko da benazeer da batoul ta tsira daga jinin mohmoud bata da abun cewa

"Na gani sultana,aba muna godiya Allah ya qara budi da arziqi" tayima aba godiya don ta bawa sultana qwarin gwiwa. Qwalla taji ta cika mata idanu,batasan adadin dukiyar data mallaka ba daga hannun aba,komai ya rarumo sai ya rubuta mallaka da sunanta,tamkar baisan ciwon kudin ba. Muryarta na rawa take masa godiya,yayi murmushi yana janta da tsokana,bari barta ta tashi a wajen ba sai data sake.

Ita ta fara fitowa ta barsu,don muddin aba yayi irin wannan zaman benazeer da batoul na gefansa to tashinsa a wajen ba yanzu ba. Dam bata lura dashi ba,don hankalinta yana kan takardun hannunta tana sake shiryasu,saidai kuma abinka da aikin jini,tana qarasa fitowa falon dukka jikinta ya dauka,saita dan rage saurin tafiyarta tana maida hankalinta gabanta.

Ya nutse sosai cikin kujera yana fuskantar tv,a haka idan ka kalleshi zakayi tsammanin bacci yake,amma kuma ba baccin yakeyi ba,yana kallon komai fes,yana kuma ankare da kowa. Fitowarta ya sanyashi dan qarawa idanunsa girma,wannan ne ya bata daman sake tantance idanunsa biyu.

Yunqurawa yayi ya zauna sosai,daidai sanda ama ke fitowa daga wajen aba din. Fuskarshi a matuqar daure,daurewar data haifar mata da tsoronsa,irin tsohon tsoron nan da take masa a baya,sanda yake tamkar wani mai gadin motsin kowa na gidan,ya zamewa gidan katanga,idanunsa akan tarbiyya da shige da ficen kowa.

"Daga yau......kada ki sake gangancin dukarmin yarinya a fuska ko a baki,idan ba haka ba zakisha mamaki na wallahi" ya fadi mata yana bude dukka idanunsa. Saida gabanta yayi mummunan faduwa,don ta jima bataga fuskarshi da idanunsa cikin irin wannan yanayin ba. Kanta ta kawar da sauri, zuciyarta na raya mata kodai maganar daxun itace ta tunzurashi?,banda haka dukan data yima benazeer baici ace ya dagi hankalinsa ko ya bata masa rai har haka ba.

Sum sum ta wuce zuwa ciki,sai a sannan yaga ama dake tsaye a bayanta. Idanunsa ya lumshe sanda suka hada idanu da ama din,yanajin bacin rai sosai cikin zuciyarsa

"Ina kwana ama?" Ya fadi cikin rusunawa da girmamawa

"Lafiya qalau" ta amsa masa tana nazarin fuskarsa. Zuwa yanzun tana jin zuciyarta tana quntata da yawa,haqurinta yana shirin gazawa,ta fahimci daga maina sultana har aba zuru da zuba idanu ba zatayi musu aiki ba,wacce irin rayuwa ce suke shirin tanadarwa gobensu?.

"Ka gaida aba?" Tayi masa tambayar tana zama saman kujera tana kuma qureshi da kallon nan da yake sanyashi jin shi din tsantsar me laifi ne

"Zanje ama,kiyimin afuwa sai na dawo daga tafiya,ina buqatar adduarki,yau zan wuce los Angeles,sati uku kawai zanyi in sha Allah,idan na dawo komai zai daidaita......na miki alqawari,amma da taimakon adduarki" shuru ta danyi tana karatu akan muryarsa, muryarsa tayi rauni da yawa,ta tabbatar akwai damuwa sosai cikin zuciyarsa

"Allah yasa,Allah ya tsare ya bada sa'a"

"Ameen ya Allah na gode" ya fadi yana tashi,hanyar waje ya kama,kamar tace ya tsaya yayi breakfast dasu amma ta sani ba lallai ya iya ci din,ranshi a bace yake,kuma muddin yana cikin bacin rai irin haka baya iya cin komai.

"Aliyyu" ta kirashi da sunansa,sai ya dakata ya waiwayo

"Ka dinga qoqarin rage bacin ranka akan sultana......karka manta har yanzun rainonka ce ita,kafi kowa sanin yadda zaka tafi da ita" karon farko ta sanya baki akan abinda ya shafeshi shi da ita,sai yaji cikin tsakiyar zuciyarsa kaman an cire wani dutse an maida gurbin wajen da dutsen qanqara,har ajiyar zuciya tana subuce masa. Wato har yanzun dai sultana nada wannan matsayin cikin rayuwa da zukatansu,har yanxun basa ganin laifinta cancan,harda ita kanta ama din ma,bata taba yaba ma juriyarsa da kawaicinsa ba,amma ya yiwa diyarta fada sau daya ta kasa haquri?. Murmushi ya subuce masa yadan girgiza kai

"In sha Allah ama,na gode" ya qarasa fada yana ficewa da sassarfa.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*


BOOK 02 PAGE 111


Binsa da kallo suhail yayi sanda yake shigowa,yana kwance a qaramar kujera

"Wai a ina ka kwana ka barni ni kadai cikin gida?" Yana balle bottoms na rigarshi ya kalli suhail din

"Wajen matata.....ko ance maka kowa ma gauro ne irinka?" Hantsilowa suhail yayi ya zauna dai dai tana dubansa

"ne dis pas de bêtises(kada ka gayamin maganar banza),yaushe kayi matar?,ko leqe leqe ka fara ban sani ba nayi saurin gayawa ama a nemo maka mata?.don ni......." Bai samu qarasawa ba saboda saukar maqullin maina a fuskarshi. Yaji zafi sosai ya dafe wajen yana kallonsa baki bude

"Na lura baqin kishinka ya fara yawa,na samu labarin crush dinmu daya dakai,shine kakeson yimin tabo a fuska salon idan ta tashi tace kai takeso bani ba?" Yana kaiwa qarshe hucin naushin maina ya wuce ta fuskarsa,mugun hantsilawa suhail yayi yana salati ya dira ta bayan kujera

"Anya ba gamo kayi ba?,see dis man jama'a,ko sai na nemo taimako?" Sosai maina ya nunashi da dogon yatsansa

"Zan maimaita maka amma a karo na qarshe,idanma iya shege kakeyi kaida bibi da kuka qulla abinku ku kiyayi kanku,sultana matata ce..... benazeer da batoul 'ya'yana ne.......daga yau koda wasa ka sake kiranta da crush dinka......kasan Allah saidai a saka maka wasu haqoran badai baka na haihuwa ba" yana gama fadi ya sauke qafafunsa qasa.

Dariya sosai suhail ya saki harda kama cikinsa,lallai bibi ta iya hada tsiya,ya tabbatar duk yadda bibi ke zaton maina din ya wuce haka akan sultana. Ya miqe yayi caraf ya kamo maina dake shirin wucewa bedroom dinsa

"ne dis pas de bêtises(zo abokina)" waiwayawa yayi ya watsa masa harara

"viens mon ami(sakeni)" zagayowa suhail yayi gabansa ya tsaya

"Karmuyi haka dakai,daga yau bani da wani crush da ya ragemin,ko dama can baya na cire haka a raina,a baya dai na sota sanda bansan wacece ita ba,amma daga ranar da ka gayan matsayinta a raina,babu sauran soyayya sai respect da nake bata.....inda da gaske ita din nakeso ta yaya zan zauna Ina fadi iya baki ba'a aikace ba?...... shirin bibi ne,itace tace naci gaba da aikina" ya qarasa fada yana sake qyalqyalewa da dariya. Hannu maina ya sanya ya turashi gefe yana wucewa daki.

Yana cire kayanshi yana tuna maganar suhail,yayi tsaye a gaban madubi sai murmushi ya subuce masa,shi bibin zata yiwa haka?,banda Allah yasa ya fahimta abun da wurwuri kenan da sai sun haukatashi ita da suhail din zasu barshi?. Tabbas bibi bataci bulus ba,daga ita har suhail din sai ya rama abinda suka masan.

Toilet ya shiga ya sake wanka da kyau,ya dawo dakinsa ya duba luggage dinsa,zama yayi ya shirya komai,abinda yake buqatar ya saka ko ya cire dukka yayi hakan. Yana aikin amma fiye da rabin hankalinsa yana kanta,duk wani daqiqa guda daya da suka share a daren jiya da ita ba wanda bai tuna ba.

Tsaf ya gama gyaran,ya wuce closet dinsa ya shirya cikin wani lafiyayyen trouser da shirt dinsa dukkansu na kamfanin gucci. Yayi kyau qwarai kai kace wani jarumi ne daga cikin jerin jaruman qasar india.

Idanunsa ya sauka kan dan qaramin frame daya kafe me dauke da kyakkyawan hoton benazeer da batoul,ya miqa hannu ya dauka yana kallon fuskokinsu,diyoyinsa abubuwa mafi soyuwa a ranshi,kyautar da ubangiji yayi masa kaf rayuwarsa ta ba zata, kyautar da bai taba tunani ko tsammanin samuwarta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login