Showing 237001 words to 240000 words out of 294767 words

Chapter 80 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

jikinta game dashi?.

"Ya Allah.....ya assamad" ta fadi tana kama kanta da hannunta. Me yasa zata tsinci kanta a haka?,bata shirya ba sam sam.....meye ya kawo mata wannan yanayin?,ta shiga tuhumar kanta tanason maida kanta mode dinta na ainihi ta qarfi da yaji. Dole daga qarshe ta gaji,ta hada ruwa me dumin da har ya wuce yadda take wanka ta soma zubawa jikinta duk a qoqarinta na ganin ta fidda komai daga jiki da zuciyarta.

Babban towel ta dauro ta kuma yafa wani saman kanta sannan ta fito daga bandakin. Tana tafe tana jin yadda kasala ke luguguitata,hakanan jikinta dake da wani buqata shima yana sake taimakawa wajen wanzuwar kasalar.

Ta samu abinci a jere a wajen saman wani dan zagayyen rug,sai ta dauke kanta gefe,don gaba daya bata da wani buqatar abinci a a yanzu,hasalima tasan bata isa taci ba,koda taci kuwa sai ya dawo.

Ruwan jikinta ta goge tas sannan ta tsaya gaban dressing table tana binsa da kallo. Komai akwai akai,abun mamakin ma duk wani nau'in product da take amfani dashi ne. Ya akayi yasan zabinta?,hatta da turare irin nata ne bare powder qaramin alhaki. Ta miqa hannu ta daukeshi tana juyawa,irinsa ne tabbas,amma tsadarsa ya zarta nata.

Daga gefe taga nashi turaren,ta miqa hannu a hankali ta dauka tana dubawa. Qaramin murmushi ya subuce mata ba tare data shirya ba,dole turaren ya dinga tsaye mata a rai da zuciya,ba qaramin turare bane. Bude murfin tayi tana sansanawa kaman ranar ta fara jin qamshin. Ido ta lumshe tana jin wata nutsuwa tana shigarta, cikin duhun idanunta ta dinga ganin tamkar shine a gabanta,batasan me yasa ta jarabtu da son qamshin ba,sai kawai ta fara fesa turaren qirjinta zuwa wuyanta ba tare data bude idanunta ba.

Caraf taji an riqe hannun nata tare da hana mata damar ci gaba da fesa turaren,wannan ya sanyata bude idanunta da sauri.

Shine a tsaye a gabanta taba duban face dinta. Fuska a hade,ya kama hannun nata ya riqe cikin nasa da kyau,sannan ya saka daya hannun yana zare turaren daga hannunta

"Irin wannan fesa turare haka?" Ya qarasa maganar yana dage mata girarshi duk biyun. Nauyi da kunya suka kamata,bata fiyason yana kamata tana shiga shirgin lamuran da suka shafi rayuwarsa ba,wannan ya sanya ta motsa nata kambun,ta zare hannun nata tana jin nauyi da takura da yadda yakebin qirjinta da kallo

"Ni bansan turarenka bane......shi yasa naji baimin dadi bama....."

"Ashe?......me qarya,?......" Yayi maganar dariya na taso masa amma ya kanne. Qin bashi amsa tayi fafur,saita juya zuwa wajen wardrobe dinta tana. Tana jin yadda idanunsa ke binta da kallo. Batayi qarya ba,don gaba daya ya sauke zazzafan kallonsa a kanta,qugunta yana juyawa a hankali tamake wadda keyi da gayya,yayin da ita kuma taji ta qagu ta isa ga wardrobe din,tana jin baiken kanta ma,me yasa ta saki jiki cikin dakin bayan tasan cewa ko yaushe yana iya shigowa.

Bayansa ya jingina da dressing table din yana harde hannunsa a qirji yana ci gaba da jifanta da mayataccen kallon nan nasa tamkar maye yaga nema. Ko Ina ajikinsa take aikewa saqo ba tare data sani ba. Yana jin inama zai iya riqe lokaci su tabbata a haka?.

Kayan da hannunta ya fara kaiwa kawai ta zaro,ta riqesu a hannunta tana juyawa kawai ba tare data waiwayo ba. Tayi imanin kallonta yake,kuma muddin ta juya tabbas qirjinta zai fara aza idanunsa akai. Batasan me yasa sam bashi da kunya ta wannan gefen ba,waishi baya ma kunyar tabasu?,baya kunyar kusancin dake tsakaninsu?,me yasa yake manta shi din kamar uba ko kawu yake a wajenta?.

Ta tabbatar tsaiwar ba zata haifar da d'a me ido ba,don wala'alla su dauki dogon lokaci haka baice mata ci kanki ba. Tun a wancan shekarun ta sani miskilancinsa yafi gaban haka,don haka ta cije tace

"Ina buqatar dakin zan sauya kaya"

"Me na tsare miki?,ki canza abinki mana,beside ma ni banda abun kalla a nan wajen" yayi maganar yana dan tabe baki kadan hadi da nuna halin ko in kula saman fuskarsa.

" A gabanka?" Ta fadi cikin jin haushin maganarsa

"Yes......me kike boyewa?,kin manta na miki tsarkin fitsari na cire miki majina.......ni nake siyo miki pant..... boom short,har aka fara half vest aka koma bra......."

"Na shiga uku" ta fada a mugun raunane,don duk iya tsiwarta akwai abubuwan da yayi mata da batason tunasu,suna sakata taji kaman ta nutse,amma shi sai ta fahimci abun dadi yake masa.

"Baki shiga ba tukunna" ya raya a ransa yana wassafa randa zai manna mata haukan da zata fito da bakinta ta bayyana masa ta kuma bayyanawa duniya matsanancin son da take masa.

Lallausan busar piano dake a mazaunin ring tone dinsa ne ya katse muhawarar. Ya juya gefansa a hankali ya kalli me kiran. Laila ce,sai yadan tada idanunsa kadan ya saci kallonta. Ya dauke idon nasa yana cije lips dinsa hadi da sakin murmushin mugunta.

"Bazan lamunci wasa da abinci ba ko don lafiyar baby na..... ki shirya ki zauna kici abinci" ya fadi yana daga kiran,ya kara a kunnensa hankali kwance yana fadin

"Hi laila....." Dai dai sanda yake fita a dakin..

Kaman wadda ya fusgi hankalinta da kiran sunan kadai da yayi,ta bude kyawawan fararen Idanunta da kyau tana binsa da kallo sunan LAILA yana amsa kuwwa cikin kunnenta. Ta tsani sunan tsana ta haqiqa,kuma bata da tabbacin tsanar data yiwa sunan bai shafi me sunan ba.....bata ko qaunar jin sunan da yayi mata da wannan sunan......wai wacece ita?,tambayar da har yau bata sani ba kuma takeson tasan amsarta. Dumin da taji saman fuskarta ya sanyata miqa hannu,data shafa sai taji hawaye

"No sultana.....kuka?,me yasa?" Ta fadi a fili wasa qasa tana mamakin kanta da dalilin fitar hawayen idanunta duk da tana jin radadi kamar ana tsaga zuciyarta.

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 127



Komawa tayi ta zauna a wajen tana ci gaba da girgiza kai.

" Bai kamata na damu ba tunda na amsa bana sonshi,bai kamata naji ciwo ba......na barshi yayi rayuwarshi nima nayi tawa" ta dinga fadi qasa qasa ita daya

"Da cikinsa a jikinkin?' wata zuciyar ta jefa mata tambayar,abinda ya qara raunin zuciyarta kenan,ta miqa hannu saman plate tummy dinta tana shafawa.

"Yanzun wata halittar ne a nan?,me kama da benazeer ko batoul?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana jinjina lamarin a ranta. Tanason tasan wacece lailan nan,ba wata diya mace da ta taba tsaya mata a rai sama da laila din,sai ta miqe tana qoqarin baiwa kanta jarumta da qwarin gwiwa,ta sauya kayan jikinta,ta koma inda ta tashi ta zauna still hannunta saman mararta kamar tanason taji motsi ko alaman wani abu da xai tabbatar mata ciki ne manne a jikinta. Yunwa takeji sosai,amma ta kasa samun qwarin gwiwar da zata kalli abincin ma,ta lumshe idonta tana tura tarin wahalhalu da tiri tiri da tayi da kanta da rayuwarta lokacin cikinsu benazeer,sai taji wasu sabbin qwalla na zubo mata,don bata da tabbacin wanne hali zata shiga a yanzu?.

Saman daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana fidda iska a bakinsa

"You know what?" Ya yiwa laila tambayar a dake. Mamaki ya kamata,yanzun nan ya kira sunanta da kulawa da taushi,har tanajin hakan cikin zuciyarta,to meye kuma ya sauyashi nan da nan?

"A'ah ya haidar"

"Daga yau banaso kici gaba da wahalar kirana......magidanci ne ni yanzun,kina iya kirana sanda iyalina ke kusa.....i will call u duk sanda buqatar hakan ta taso" wani tsawa taji ya fashe mata saman kanta. Kada dai ace da gaske hasashenta ne zaya zama gaskiya,kada dai ace SULTANA HAMANI MOHMOUD MAYAK'I,sabuwar 'yar jaridar gidan tvn nan matarshi ce kaman yadda ta soma ji da ganin qishin qishin din haka?. Muddin ko haka ne......ita laila bello ina zata iua goga kafada da ita,sultana ake magana fa?,matar data shiga media da wani irin mugun farinjini?,matar da ko ke mace idan kika kalleta saita burgeki?,indai itace matarsa,BB twins yaransa lallai bata da wani gurbi ko muhalli cikin rayuwarsa.

To amma ta yaya zata bari tayi loosing hope har haka?,ta yaya zata bari ya subuce mata a dare daya?,ta yaya zata kashewa kanta qwarin gwiwa alhalin bai fito qarara ya bayyana mata hakan ba?. Salube wayar tayi tana jin kamar wani zazzabi zai saukar mata. A duk sanda tayi tunanin akwai wata mace a rayuwarsa,kwanyarta tafi hasko mata ayana tahir cousin dinsa,don ta tabbatar indai ta hangi sultana a wannan gurbin bata da wani sauran abinda zata nuna a gabanta.

Wayar ya dinga juyawa a hannunsa. Yana buqatan Peace zuwa yanzu,ayana da laila dukka zasu zame masa matsala su hanashi sukuni su kuma dagula lissafinsa. Yadan waiwaya kadan yana duban bakin qofar dakin,dukka hankalinsa yana can,yana kanta,yanason komawa ko don ya tabbatar taci abinci,amma kuma yayi wuri ya koma yanzun,don haka yaci gaba da zama a wajen hankalinsa yana rarrabuwa,ganin haka sai kawai ya danna numbers din goumar ya kirashi.

Su batoul ya buqaci ya bashi,suna kusa dashi don haka ya hadasu ya koma gefe ya basu wuri. Hira da yaran ya dauke hankalinsa,a qalla sai da ya kwashe musan mintuna ashirin sannan ya katse kiran,ya miqe yana wucewa dakin.

Qamshinsan nan daya soma zame mata jarraba zuwa yanzun shi ya fara gaya mata shigowarsa,daga inda take zaunen kamar wadda aka dasa ta daga idanunta da suka sauya launi saboda yunwa da kuma tabuwar da zuciyarta tayi ya zube masa su. Dauke kai yayi yana basarwa,saidai kuma idanun nasa yana kan hannunta dake saman cikinta.

Cikin qasaitaccen takunsa ya qarasa gaban kayan abincin,ya kallesu sannan ya maida dubansa a kanta,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya tsugunna a hankali,ya buda komai ya zuba daidai yadda ya dace ya hada saman tray ya isa inda take ya sabule takalmin qafarsa ya zauna sosai saman rug din wajen

"Oya......sauko kici abinci" idanunta ta aza a kansa sai kuma ta janye,wani irin zafinsa takeji,waya yaje yayi da wata ya jima haka,ya barta zaune a daki bayan ya rabota da ama dinta,ya kuma danqara mata cikin da ta tabbatar shi yake sanyata jin gigitacciyar yunwar da tunda tazo duniya bata taba jin yanayi irin wannan ba.

"Bana ci" ta bashi amsa murya a dakushe. Cikin qasa da second biyu yanayin fuskarta ya sauya tas.......wannan lion eyes din nasa ya zube mata yana maida fuskar nan ta ALIYYU HAIDAR saman fuskarsa

"Nasan ke kin qoshi......ki sauko ki bawa baby na abinci,that's what i wanta......." Zuciyarta taji na neman karyewa,wato bata tata yake ba,ta d'ansa yake,tunda ita din ba diya bace kota mutu ko tayi rai ba damuwarsa bace.

Yadda ya zuba mata nauyin idanunta da kwarjininta ya sanya ta kasa cewa komai,ta zamo qasa a hankali har yanzu tana dafe da cikinta ta zauna sosai. Hannun ya sake bi da kallo,wanne irin tsaro takewa cikin haka?,Allah yasa soyayyarsa ce ta shigeta da gaske ba qiyayyar data gwadawa cikin benazeer da batoul bane.

"Hope ba damunki yayi ba...... don babu batun abortion a nan" ya fada cikin salon basarwa. Da sauri ta daga kai ta kalleshi,suka hada ido sanda yake tura mata dukka palates din gabanta. Kau da kai tayi gefe zuciyarta tana raurawa,waishi waye yake bashin labarin komai?,labarin abubuwan duk da akayi alhalin baya tare dasu?.

_"a sannan duk wani motsinki,faduwarki da nasararki a gaban idanuna kika yita,ba wani second na rayuwarki da ya wuce ba tare da nasan me yake gudana ba.....baccinki da tashinki.....kukanki da kuma sakewarki don ba dariya a dairy din qwaqwalwarki a sannan"_ ta tuna da maganar daya taba gaya mata. A sannan ta dauka ya fada ne kawai don ya wanke kanshi,amma yanzun ta tabbatar da gaskiyar abinda ya fadi din.

"Bismillah" taji yace. Koda ta waiwayo sai taga abincin ya debo cikin spoon ya biyo bakinta dashi. Duk yadda zata masa bayanin ba zataci ba bazai gane ba,bazai kuma yarda ba,don haka ta cire idanunta daga cikin nasa,tasa hannu zata karba spoon din.

Kansa ya girgiza yana janye cokalin baya

"For my baby......idan ya gama ci sai na baki kici naki da kanki......amma yanzun dai ki barni nayi aikina,ke kyaci naki da kanki,don dama bazan iya aikin mutum biyu ba"


"Ahaaaann" ta fadi qasan ranta,indai xaiyiwu harara me zafi takeson watsa masa,komai baby komai baby?,ita ba mutum bace wai?,me yasa bazai nuna kulawa a kanta ba?,me yasa ya daina nuna mata kulawa?,me yasa ya daina nuna damuwa da ita?" Wannan ya tsaye mata a rai,amma haka ta daure,ta buda qaramin bakinta tana karbar abincin kadan kadan.

Yadda lips nata ke juyawa sanda take tauna abincin ya tayar masa da tsigar jikinsa,all the way kawai yaji yana muradin siraran lips nata masu sulbi,saidai kuma yanason ya bata tazara tsakaninsu don ta sake aminta ta kuma gamsu ita yakeso ba gangar jikinta ba.

Yadda yake bata abincin tana karbar wani tana kuma qin karbar wani har sai ya hade rai sai ya tuna masa da some years ago.......sanda tana baby sultanarshi da sai ya lallasheta zataci abinci,sai ta kuma zabi irin abinda takeso taci dina. Abincin da taci a lokacin ita kanta tayi mamaki,tanata fatan kada ya dawo mata kaman yadda ta cishi,saidai har sanda ta gama shirin kwanciya ta kwanta tana qudunduna a blanket bataji alamun xai taso mata ba.

Idanunta lumshe zuciyarta na bugawa kadan kadan. Ta lumsassun idanunta take satar kallonshi. Bashi da niyya ko alamun fita a dakin,don ya nade abinsa cikin sofa bed yayi kyau cikin wasu pyjamas da suka bayyanar da kwantaccen lallausan gargasar dake lullube da qirjinsa. Idanunsa duka akan wani dan qaramin littafi da bata iya gane na meye ba saboda yadda qarami ne. Tadan sauke numfashi kadan tana motsawa,har yanzu yana nan da dabi'arsa ta karance karance kenan. Tun tana zaton zataga yayi wani motsi har ta gaji. Haka kawai ta samu kanta da juyi daga wannan hannun zuwa wani hannun,tana jin wani eagerness a hankali yana ratsata,cikin jiki da zuciyarta ta dinga jin wani feeling kaman she's waiting for something.....akwai abinda take jiran tsammani.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 128



Sake qara yawan motsinta tayi daga hagu zuwa dama duk bayan wasu mintuna. Cikin ranta taji ta kasa samun calmness........

Yadda yake zaune cikin nutsuwa yana buda littafin shafi bayan shafi ya bata mamaki,ta kasa jin ta yarda da cewa baiji motsinta ba,baiga duk wani juyi da takeyi ba. Yadda taketa mutsu mutsu koda ba daura da ita yake ba ya kamata ya fahimci ai ba'a kwance take waje daya ba,kodai halin ko in kula din daya koyi nuna matanne yake sake nuna mata a yanzun?,sai ta jawo pillow ta qanqame,tana ji har cikin bargonta runguma takeso,tanaso wani abu da zatayi hugging nashi ko shi yayi hugging nata,zuciyarta tana da buqatar home..... abinda ake kira da ainihin home bawai wannan da take ciki ba.

Tsuka taja qarama wadda bata shirya fitowarta ba,da sauri ta kalli inda yake zaunen tana dan ware idanunta kadan,don ta sani babu abinda ya tsana irin tsaki,fata take baijita ba,tana kuma fata koda yaji kada yace dashi take. Ga mamakinta baiko motsa ba bare alamu su nuna ya jita. Ta matsar da idanunta zuwa ga kunnuwansa tana dubawa wai ko earpiece ya sakawa kunnen nasa?. Ba wani earpiece,sai hankalinsa daya tattarawa littafin.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login