Showing 111001 words to 114000 words out of 294767 words
Chapter 38 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
da ita. Gyara zamanshi yayi sosai cikin kujerar,sam yama manta da waje ko muhallin da yake,don sai yanzunne yakema sultanar kallon tsanaki kuma kallon tsaf,yake kuma ganin canji ga rayuwarta me mugun nisan tazara,irin sauyin da yayi mata kwadayin samu,irin canjin da ya dinga fatan ta samu,amma kuma komai sai ya sauya,komai sai yazo ta bahaguwar hanyar da baiyi zato ba.
Gilmawar wani ta gabansu da kuma dawowarsa gurin tsaiwarsa yaja hankalinsa. A nutse ya maida dubansa sashen,har zaya dauke kai saboda baiga wani abun kallo a wajen ba sai idanunsa suka hango masa mutum uku cikinsu. Mutum ukun da suka hade kai waje guda suna qus qus,dukkansu idanunsu suna inda houda da sultana ke tsaye. Tashi yayi ya zauna sosai sanda zuciyarsa ta fara bugawa,adadin gudunta yana son ya sauya daga yadda qa'idarsa yake. Kallo suke mata irin kallon nan da ake kira na qurilla
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fada yana jin yadda numfashinsa yake rawa. Ko shakka babu ita suke kallo,maganarta kuma sukeyi,yana da saurin fahimta da kuma nacin gane me kake fadi koda daga nesa ne ta hanyar karantar motsawar labbanka. Ya fuskanci shirin tunkararta suke ba shiri ya miqe don baya jin zai iya tsaiwa ya kallesu koda a gefenta ne bare suyi mata magana,bayajin zai kasa taka musu burki koda kowa zaiji bai cancani yayi hakan ba.
Murmushi ne ya kubce daga fuskar Goumar wanda ya gama karantar komai daga fuskar maina,duk kuwa da cewa yana nesa kadan daga inda yake din,ba kuma lallai ya ganshi. Wani irin zazzafan abu yake gani a fuskar maina din,mahaukacin baqin kishi,tun kafin yau,tun yana haidar dinsa dan makaranta a niamy.....tun yana saurayinsa me qananun shekaru dama mutum ne shi me matuqar kishi na gaske,wannan dalili ya sanya yayi ruwa yayuntsaki wajen kula da tarbiyyar qannensa mata kamar me?......wannan dalili ya sanya tyj suna da qananunnshekaru ya haranta musu sanya qananun kaya saidai atamfa da manyan riguna masu rufe jiki......wannan dalili kuma still shine ya zama silar samun rashin jittuwa tsana da qiyayya me gurma tsakaninsa da SULTANA.....yana kishin dukka yan uwansa mata qwarai,yayin da ita kuma sultana take kallon hakan a matsayin takurawa da kuma tsangwama,don a sannan hankalinta baikai ta gamo girma da matsayin gatan da yakeyi musu ba.
Taku biyu kacal yayi sai ya hangi goumar har ya isa gabansu sultana din. Maganar da takewa houda ta katse,ta daga kai tana duban goumar da kallo me kama da hararara harara
"Me kuma ya faru?" Ta jefa masa tambayar tana hade girar sama data qasa. Tun kafin ma ta ajjiye harshenta maganar data tsani ya fada mata ita ya gaya matan
"Kefa matar wani ce,duk wajen nan kuma kusan mazan wajen ke suke kallo" sosai ranta ya baci,yakai qololuwar baci ma
"Baqin buzu......wai oncle umar baiyi mana tsakani dakai ba?"
"Don yayi mana tsakani saina tsaya na kasa tunasar dake girman nauyi da haqqin dake kanki?"
"Nauyi?,haqqi?, dukka na waye?,ba haqqin kowa kaina, goumar ka dameni......ka shafamin lafiya,wai idan nace aure zan daura yau ko gobe ka isa ka hanani?" Shi dinma dan uwan maina dinne wajen kishi,maganar tata sai yaji ta zafafeshi tamkar shike da igiyar auren nata a hannunsa
"Baki isa ba.....kema kin sani,saidai kiyi aure akan aure,wanda kuma badai cikin family dinnan ba"
"Haka kace?,zaka gani kuwa yanzu,badai taqamarka igiyarsa ba?,to yau zata zo qarshe naga da meye zakamin taqama" ta fadi a zafafe sannan ta zagaye houda tana nufar hanyar ficewa,tanata qoqarin riqe fushi da hawayenta amma ta kasa,ita kanta batasan meye ya zafafi zuciyarta har haka ba.
Bayanta houda tabi tana kiranta, kiran nata da takeyi sai taji ya qarasa karya mata gwiwa,don haka ta soma takawa da sasaarfa tanason kubucewa ganinta.
Tunda aba da oncle issoufou suka nufo wajen,wadanda barinsu gurin sunje suyi sallama da wasu baqin aba dinne su dawo suka hangi tahowar sultana da houda. Sam sultana bata gansu ba saboda yadda idanunta suke a qasa,har sai data ci tuntube da aba sannan ta dakata. Saurin riqo hannunta aba din yayi yana fadin
"Subhanallahi.......lafiya kike?" Idanunta da suka cika taf da qwalla ta daga suka hada ido dashi,sai kuka kawai ya taho mata gaba daya,ta sanya daya hannun nata ta riqe hannun aba da kyau tana sakin kuka me sauti.
"Subhanallah......ya salam......ke houda.....me yake faruwa?" Aba yayi mata tambayar yana jin tuhumar maina cikin ransa. Dan daburcewa tayi saida oncle issoufou ya maimaita mata sannan ta gaya masa komai.
Sosai ran aba yaji ya baci matuqa.....ta kowanne fanni gani yakeyi kaman basa yiwa yarinyar adalci,zuwa yanzu ko a musulunci tana da haqqin zabawa kanta abinda takeso,to don me yasa su zasu tauyeta?,me yasa zasu bari a dameta akan abinda bai zame mata dole ba?,me yasa za'a dinga dukanta kuma ana hanata kuka?,shi me laifin waye ya dameshi?,waye yake sanyashi kuka tunda ya shigo gidan kusan awani arba'in da takwas?. Hannunta ya kama yana juyawa zuwa hanyar sassansa,oncle issoufou yana biye dashi. A yadda aba din ya fusata ya sani zai iya kowanne hukunci shi yasa bai barshi ya wuce shi kadai ba. Yana ganin aba din ya zaro wayarsa daga aljihun babban rigarsa shima ya zaro tashi,a gaggauce ya turawa oncle bashar tex
_"mu hadu a falon yaaya yanzu yanzu don Allah karka wuce wadannan mintunan komai na iya faruwa"_ ya tura masa ya maida wayar nasa aljihun,dai dai lokacin yaji aba din yana magana
"Kazo inason ganinka yanzu yanzu,ka taho da kuma wanda ya sanyaka ka gaggaya mata maganar.... Eh aliyyun nake nufi" ya fadi a hasale sai ya maida wayar aljihu yana jan wani dogon tsaki zuciyarsa na masa zafi.....
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 59
"koma ka dauko mata ruwa me sanyi" aba ya fadi sanda suke shiga falon,atta da ya gama sanya masa turaren wutar da ama ta bashi ya saka din yana shirin fitowa sukayi kacibus. Da kallo yadan bisu sannan ya koma ya ajjiye kwalbar turaren ya bude fridge ya ciro ruwan,ya hado da kufunan gilasan da suka zamewa saman freezer din ado,ya qaraso gaban sultana da kanta ke duqe a qasa,hawaye yana layi saman fuskarta. Fuskartata har ta dan hada ja,abinka da farin mutum
"Gashi aunty sultana" atta ya fadi yana miqa mata ruwan. Cikin ransa tausayinsu dukka yakeji,duk da baisan har yanzu ainihin abinda ya sanya ya maina barin gida ba,bai kuma san abinda ya hadasun ba,amma yadda suke ganin komai ya sauya a shekarun sun tabbatar ba na dadi bane.
Hannun tasa ta karba,muryarta na rawa tace dashi
"Na gode" bai iya amsawa ba ya miqe,ya dauki turarensa yana barin falon.
Ko zama aba baiyi ba sai kai kawo da yakeyi tsakanin oncle issoufou da sultana da suke zaune,zuciyarsa na masa lissafin wahala fadi tashi dawainiya da mohmoud yayi dasu,jininsa bai cancanci zubda hawaye ba.
Baiji ko d'ar ba sansa goumar ya gama gaya masa saqon aba yana kiransu
"Amma ya maina......me zai hana ka fice,zan gaya masa yanzu yanzu kuka fita dasu tahir" idanunsa ya daga ya watsa saman fuskar Goumar
"Na fita goumar?,na sake fita a gidannan?,na gama fita goumar......kasan sunan da nafi tsana a duniya?,kasan abinda nafi tsana a wajen d'a namiji?,RAGWANTAKA.....kalmar da ban yarda a kirani da ita ba kenan......don meye zanta guje guje akan halas dina?,meye zai sanya na yita guduwa?,kasan meye ma'anar sunan HAIDAR?,fassararshi na nufin jaririn ZAKI,ka taba ganin zaki ya gujewa wata masifa?,to haka nake goumar.....wancan da ya faru na yarda yana cikin babin qaddarata.....ba kuma wai nayi GUDUN K'ADDARA bane...... a'ah.....rubutacce ne dole sai na fita nabar gida na wannan shekarun kafin na zama abinda na zama a yanzu....muje goumar,zan iya fuskantar aba" bai sake bawa goumar second chance da zaiyi magana ba ya fusgi hannunsa,har cikin ransa yana jin wani karsashi yana cikashi. Shima ya gaji,yafison ayita baro baro......yafison su fidda duk kalar hukuncin da suka yanke masa,yafison yaji meye matsayinsa?,yasan daga inda zaya fara.
Mamakin tsananin jarumta da yadda yake takawa ta kama goumar,sai ya kasa tabuka komai sai kallo da yake binsa dashi,ya kuma ci gaba da binsa tamkar raqumi da akala.
Sai da suka isa qofar falon sannan ya saki goumar din,ya durqusa ya sabule takalman qafarsa ya sanya qafars a falon bakinsa dauke da cikakkiyar sallama,dukkan wata gaba ta jikinsa tana bayyana nutsuwar zuciyarsa.
Oncle issoufou ne ya amsa masa yana binsa da kallo. Bai tsaya ko ina ba sai daya dangane da gaban aba sannan ya durqusa, goumar ya biyo bayansa shima ya tsugunna gabansa. Cak aba ya tsaya a gabansu su dukka biyun,saidai kuma goumar yake kalla
"Ina cewa kwanaki umar ya maka gargadin kiranta da matar wani?,wanin da ba'asan a wacce nahiya yake ba?,......ko yanzun kuma da akasan nahiyar da yake bashi da nagartar rayuwa da d'iyata....... inason naji shi ya aikeka ka sake maimaita mata?!"
"Nine aba" maina ya furta cikin qanqan da murya da kuma nuna tsananin girmamawa
"Goumar kai nake tambaya!" Aba ya kuma maimaitawa fushinsa yana motsuwa. Abun ya taba oncle issoufou sosai,bai taba ganin zallar madarar fushi akan fuskar aba irin na wannan lokacin ba,don haka ya sake fidda wayarsa. Wannan karon direct ya kirayi bashar,akayi sa'a ya daga,baice masa komai ba yabarshi speaker bude,yadda yasan zaiyi sautin aba din. Yaji din kuwa take hanakalinsa ya dawo jikinsa,ya katse kiran, oncle issoufou din yana ganin ya katse sai ya sake rubutawa oncle umar gajeran saqo yasan shi din zaiyi wuya bai gani akan lokaci ba saboda yana yawan mu'amala da waya
_idan zai yiwu ka shigo da bibi da kawu_ ya rubuta masa daga qarshe. Ya nemi tallafinsu ne saboda yana gudun kada ayi aika aika,yadda yau din fushin aba ke hauhawa bayajin shi daya a matsayinsa na autansu zai iya controlling nasa.
"Abokin wasanku zaku maidani kai dashi din?......." Ya fada yana sake fusata saboda yadda kowa ke son maida laifin kansa kusan minti biyu kenan. Basu amsa masa ba don haka yayi taku biyu baya ya dauki qaramar jotting paper da pen dake maqale a jiki ya wurgawa maina,ba bata lokaci ya sauka a fuskarsa
"Maza maza rubutawa diyata saki......saki ukku kuma nake buqata bawai daya ko biyu ba".
A razane ya dago kansa,karon farko ya kalli fuskar aba da idanunsa da suka sauya launi
"Eh abinda na fada din nake nufi...... girman idanunka ba zasu razanani da komai ba,ka rubuta mata sakinta guda uku......"
"A'ah yaaya ba za'a yi haka ba,wannan hukuncin ai yayi girma da yawa" oncle issoufou ya taso yana son riqe hannun aba
"Kada ka dakatar Dani issoufou.....me za'a jira?,meye amfanin igiyarsa?,ya gama shekarunsa dai ya dawo ba?,to ya sallamarmin diya zan zaba mata miji na kere sa'a,me tarbiyya wanda yasan mutuncin na gaba dashi" kamar ya zanya tsinin qaho ya caki qirjinsa haka yaji,wannan radadi da ciwon da qirjinsa keyi masa lokaci bayan lokaci.....ciwon da tunda ya fara zuwa gaban ka'aba yana shan zam zam shi da azababben ciwon cikinsa suka shafa masa lafiya a yau din kalaman aba sai yaji suna shirin tayar masa dasu
"Don Allah yaaya ka daina....."
"Sai ya saketa don bata dace dashi ba" ya sake maimaitawa,kalaman da suka sanyashi zamewa ya zauna sosai saman carfet,sallamar oncle umar da oncle bashar ta baqunci wajen. Oncle umar ya duba bibi din bai ganta ba,don haka sukayo gaba shi da oncle bashar,don saqon issoufou din ya nuna musu ba lafiya ba
"Bazan iya sakinta ba aba.......bazan iya sakin diyar NAFESSA ba!" Ya furta cikin dakiya da jarumta. Sak aba din yayi,don bai taba tunanin maina zaiyi masa musu ba.
"Sai yanzu kasan diyar nafessa dince?,sai yanzu kasan da haka?"
"Na yarda da dukkan wani laifi da kuke tuhumata dashi aba.....na yarda da duk wani kalar suna da zaku laqabamin......na kuma yarda da kowanne hukunci amma na roqeka da girman mahaliccinmu banda saki"
"Saboda?" Ya tambayeshi yana matsowa gabansa
"Bazan iya sakinta ba!,ina qaunarta.......ina qaunar jinin nafessa!" Ya fadi wasu siraran hawaye na biyo gefan idanunsa
"Zan yita baku haquri ku da ita iya adadin numfashin da ya ragemin.......aba koda nayi ma sultana laifi banajin yakai a yankemin hukuncin rabuwa da ita........naku laifin da nayi muku gani a qasa ina roqon afuwa da yafiyarku!"
"Kasan yadda ta rayu tsakanin shekarun?,kasan da yadda aka samu rayuwarta?,ka tafi ka barta da dawainiyar cikin yara har biyu?,don bakasan yadda mata sukeyi ba idan suna tare da juna biyu?,baka da tausayi bakasan ya rayuwarsu take komawa ba?,yara biyu da qananun shekaru irin nata?,wannan shine qaunar?,wannan shine tausayin?"
A hautsine ya daga jajayen idanunsa yana kallon goumar
"Yara biyu?,twins?" Ya yiwa goumar tambayar idanunsa a kanshi,da alamun ya zaqu matuqa yaji cikakken bayani,kamar ma ya manta a gaban waye yake,kamar ma ya manta cikin kotun aba yake. Ganin goumar bai dago ya dubeshi ba sai ya dafa kafadarsa da qarfi
"BENAZEER DA BATOUL?" Ya fadi muryarsa tana shacking
"Ka bani amsa goumar!...... benazeer da batoul?,nadeeya da BINTOU?" Ya kuma fadi cikin yanayin matuqar rudewa,rudewar da sai data sanya kowa dake wajen zuba masa idanu.
Kiran sunayen nasu da yayi sai ya zamana kamar kiransu yayi,sai gasu da gudu daya tana bin daya, benazeer ce ta qwace Sweet din nadeeya ita kuma ya biyota kan lallai sai ta bata. Sun cire duk wani kayan adon da aka saka musu dazu,kama daga abun hannu sarqa harda takalmansu,sai wani sock's me kyau da aman tace a saka musu don tasan ba lallai su iya wuni da high hill ba. Ko dankwalin kansu dukka sun yar,gashinsu kawai da yasha gyara yake matse a band ne jelar keta yawo a bayansu.
"Benazeer,batoul" ya kirasu yana kallonsu da idanunsa da zuwa yanzu suka koma kamar an diga musu jini. Suna hada ido dashi suka manta da rigimar da sukeyi sai kawo sukayo kansa kowacce nason ta riga 'yar uwarta isowa. Tafukan hannayensa ya bude musu,ba bata lokaci suka shige,ya maida hannuwan nasa ya lullubesu tsakiyar qirjinsa,ya matsesu gam yana boye fuskarsa tsakanin kafadunsu,sun lullubeshi da surutu,yayin da shi kuma wani zazzafan hawaye ya qwace masa,hawayen da bazaiso kowa ya gani ba.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 60
"ka sake mata yara ka rubuta mata takardarta" aba ya fadi yana hadiye abinda yake taso masa
"Bazan iya ba aba..... I can't" ya fadi da rawar murya,yayin da benazeer da batoul sukayi tsuru tsuru a jikinsa,don basusan abinda yake faruwa ba,basu shaida komai ba
"Baka isa ba kuwa......ba abinda zai hana ka sakarmin diya" aban ya furta cikin hargagi
"Kai hamidou,meye hake faruwa ne?" Muryar kawu ta halarcin gurin yana takowa zuwa falon bayan ya cire takalmansa. Dubansu suka maida kansu,har cikin ran aba baiso shigowar kawu a wajen ba,don yasan zaiyi wuya bai karya masa budget ba. Yanaso a barshi ne shida maina kadai,akwai lesson da yawa da yakeson ya koya masa.
"Samu waje ku zauna.....kai aliyyu,ku zauna sosai" kawu ya fadi yana zama kujerar dake tsakiya.
Dole kowa din ya zauna,shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna,sai batoul da benazeer dake faman kallon fuskar maina,kaman yadda shima yake kallon nasu fuskokin,yana jin wata soyayya da qauna da qaunarsu na ratsa kowane sassa na jikinsa.
Kiran sunan maina din kawu yayi,ya amsa masa kanshi a qasa.
"Abinda ka aikatama matarka baikai girman kuskuren barinka gida da kuma rashin waiwayosu ba" ya fada shima yana nuna bacin ranshi sosai
"Akwai dalili kawu.....ba haka kawai bane ba" ya fadi muryarsa a karye.
"Wanne dalili indai har kana raye kuma cikin hankalinka?......" Fada sosai ya tsinke dayi masa,har sai daya fidda dukkan abinda ke zuciyarsa dama wanda ya fahimci yana narke cikin zuciyar aba din.
Tsahon wasu mintuna ya dauka,har ya gama ba wanda yace komai a cikinsu,sai daya kammala sannan ya maida dubansa ga aba
"Hamidou,abinda ya faru ya riga ya faru,tunda har Allah ya dawo dashi lafiya,fatan kawai da za'a yi shine, ubangiji ya sanya hakan yaci gaba da zama silar alkhairi wa kowa....."
"Nifa dama kawu ba abinda yayimin,d'a dama idan ka haifeshi ai ka gama naka.......abu daya nakeso