Showing 240001 words to 243000 words out of 294767 words

Chapter 81 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Wani abu me tauri taji ya tsaya mata a wuya,mode dinta na neman attention daga wani ya sake hauhaww,taji zuciyarta kaman zata zautu,kana zaune da mutum daki daya amma baka monitoring mode dinsa?,meye hakan?. Hawaye zuciyarta keson zubarwa amma ta dake,tayi gyaran murya kadan wai ko zai daga kanshi,amma tamkar tana zaune da kurma a dakin. Ta sake motsawa kadan tana jefo pillow qasan qafafunta,nan ma dai duk ko a jikinsa,saima qafafunsa daya dauke daga qasa ya aza saman sofa yana sake gyara zamanshi alamun zama ya masa dadi.

"Ni ban iya bacci da wuta a kunne ba" ta furta cikin qufula alhalin bata da abu guda daya da zata ambata yayi mata da sunan laifi.

Shanyayyun idanunsa da suka rusuna ya dago ya zube mata su a nutse,dan hasken dake dakin yana haske farin kwalbar computer glass din daya maqala a idanunsa. Kallon kallo suka fara yiwa juna,kowa da abinda yake rayawa cikin ranshi. Ita tafara janyewa don nan da nan taji ba zata iya jurewa dogon kallo a tsakaninsu ba,ko a iya haka aka tsaya ya sake rusunar mata da zuciyarta da wani irin mode da rauni me yawa. Kaman bazai magana ba saboda qasaitarsa data lura ta motsa sai kuma yace

"Me kike buqata?" Yayi tambayar a taqaice

"A kashemin hasken dakin" ta amsa masa tana lumshe idonta don batason qwallar da taji ya fara taruwa ya samu nasarar cika mata idanu. Qafafunsa ya sauke qasa ya sake tashi ya zauna sosai yana kallonta

"Ikon Allah,nan dinfa dakin aro ne......dakin matar gidanne me zuwa,aro na baki zuwa wani lokaci,so kinga dole kiyi haquri da isa da dakin da zakiga ana nuna miki" bata shirya zuwan kuka ba amma sai gashi ya taho,ta juya da sauri tana saka kanta cikin pillow tana jin wani irin loneliness yana mamayarta.

Gilashin fuskarsa ya zare yana fidda idanu waje

"What?.....me kuma nayi?,daga magana?,kince baki sona,na miki alqawarin zama dake a matsayin uncle.....yanzun don nace dakin akwai maishi nayi laifi?" Maganarsa kamar tiri ta zame mata,ba wadda ke yawo a kanta sai laila....laila yake nufi kenan?,ita kuwa me zataci da dakin laila?. Tanaso ta miqe tabar dakin amma kuma kunya ta dabaibayeta,kunyar yadda akayi ta bari har ya fahimci wai taji haushi don yace aron daki ya bata.

"Withtime yarinya.....muje zuwa" ya fadi yana miqewa a hankali gami da rufe littafin,ya dora eye glasses dinsa akan littafin. Ko batayi magana ba ya gama karantar me takeso,skin to skin contact. Shi take mutuwar buqata a lokacin,ya gama karantar mode dinta,tun juyinta na farko ya gama fahimtarta,yana sane yayi biris da ita.

Pyjamas dinsa ya zare yana murmushi ya wuce toilet ya daura alwala ya fito,har yanzu tana kife ya kuma tabbatar hawaye takeyi. Ya dauke kansa yana qunshe dariya. Wahala bata sakata giving up da wuri,ya lumshe idanunsa yana sake sakin boyayyen murmushi,wala'alla ubangiji ya dubi zuciyarsa da haqurinsa ne ya sanya mata wannan yanayin. Wani irin yanayi ne da ciki zai iya kawoshi duk dare tattare da wasu matan. Zuciyarsa yaji tana sake sanyi,yayi amanna komai yana kusa da zuwa qarshe.

Wutan ya gama kashewa gaba daya,sai ya haura gadon ya dage blanket din yana shigewa ciki,ya sanya dukka hannuwansa yana jawota cikin jikinsa. Zamewa ta soma yunqurin yi,sai ya gwada mata banbancin mace da namiji,yayi mata wani kyakkyawan riqo da hannunsa,ya saka daya hannun nasa yana yage rigar baccin jikinta,ya manna fatar jikinsu guri daya.

Shi da ita ba wanda yasan ya fidda ajiyar zuciya sai bayan ta fita daga jikkunansu a lokaci guda,muryarsa nadan sarqewa yace

"You are not strong enough at all madam......don xan taimakeki na baki relief ma sai kinyimin taurin kai,taimako ne fa?,a qa'ida ma saikin biya" kaman ta mutu saboda haushi,saita cusa kanta qirjinsa ala dole tana son goge damshin hawayen idanunta cikin gashin qirjinsa. Haushin kanta da kanta takeji,me zai hana tayi kwanciyarta ita daya?,da datake kwanciyarta shekarun baya meye ya sauya?,me yasa yanzun ta damu da son jinta jikin wani?,yanzu ba gashi yana gaya mata baqar magana a fakaice ba.

Minti guda yayi yawa nutsuwa ta fara saukar mata,kukan da take tsammani zata dade tana yi sai gashi yana yin nasa guri. Shuru ya ratsa dakin,sai sautin bugun zuciyoyinsu da wani irin dumin jikin juna dake ratsasu. A hankali wani irin ni'imtaccen bacci yayi awon gaba da ita,ya gyara mata kwanciya sanda ya fahimci bacci ya dauketa,ya leqa fuskarta kadan yana kalla. Duk da baya iya ganinta da kyau amma sai da qaramar dariya ta subuce masa. Ta riga ta fada ruwa tsundum amma tanata yunqurin qaryata kanta da kanta,taqi bada kai.....amma a sannu a sannu zaici gaba da matsata har sai ta bayyanawa duniya bama shi kadai ba.

Sake mata mazauni yayi sosai cikin jikinsa,ya cusa kansa tsakiyar gashinta yana shaqar daddadan qamshin hair mist da take using dashi. Wani irin scent me laushin qamshi,ya lumshe idonsa tana jin feeling din da yaketa qoqarin dannewa tana tasowa.

Ko ina na jikinsa ya soma amsawa,ya sakeyi mata kyakkyawan riqo ainun. Shi daya yasan me yakeji a jikinsa,sati ukun nan ba qaramin qoqari da kuma yaqi yayi da kansa ba tsahon kwanakin. Ba gangar jikinsa kadai ba,hatta jinin dake zagayawa a jikinsa yayi kewarta. Bayason ya karya shirginsa......yanasin ya nisanci neman komai daga wajenta saboda ya wanke zuciyarta yadda ya kamata daga tunanin gangar jikinta kawai yakeso......yanason ya tabbatar mata da sahihiyar qaunar da yake mata......yanason ya bata tabbacin ita sultana yakeso gaba dayanta bawai wani abu daban daya danganceta ba.

A hankali ya dinga murza fuskarsa cikin gashinta yana sauke zazzafan numfashi,kowanne saqo na jikinsa ya shiga fidda gumi,kaman yadda numfashinsa ya dinga fita a wani irin birkice.

A hankali dumin numfashin ya dinga ratsa fatar kanta yana aika saqo zuwa qwaqwalwarta. Wannan ya sanya katsewar baccinta,ta bude idanunta a hankali,turarensa kuma daya gauraya da nata ya zama abu na farko data fara sheqa.

Yadda numfashinsa ke fita wani iri ya bata tsoro sosai,tayi qoqarin banbarewa daga jikinsa don ta kalli fuskarsa don tabbatar da lafiyarsa saidai kuma ya hanata wannan damar,don wata wawiyar runguma yayi mata jikinsa ko ina ya dauki rawa. Mararsa ke murdawa sosai,ya lumshe idanunsa yana ambaton

"Ya Allah......ya rahman" gabanta ya fadi sosai,tsoro ya kamata jin yadda hatta da gashin qirjinsa ke fidda damshin gumi

"Kada dai wani abune ya sameshi mummuna,idan hakan ta kasance ya zanyi dashi?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan cikin zuciyarta.

Samun kanta itama tayi da karanto addu'o'i,ta sake yunqurin zame kanta a karo na biyu,muryarsa cikin rawa har labbansa suna rawa yace

"No.....please......stay with me,don't......" Sai ya kasa qarasawa yayi mata wani kyakkyawan riqo yana sauke wani numfashi me matuqar qarfi da nauyi.

Idanunta ta lumshe tana cije lips dinta itama tana sakin nishin wahalar tsatstsauran riqon da yayi mata,don sai da taji kaman qashinta zai amsa. A hankali kuma ya sassauta riqon yana sake cusa fuskarsa cikin gashinta,jikinsa ya saki gaba daya,gumin jikinsa kuma yaci gaba da tsatstsafowa,sai ya sassauta riqon sosai amma saita kasa matsawa daga jikinsa kunnenta saman qirjinsa tana sauraren bugun da zuciyarsa keyi wadda sannu a hankali ya fara daidaita.

Shuru yaci gaba da wanzuwa,bai sake motsawa ba har kusan mintuna biyar. Ajiyar zuciya ya saki yana miqewa,a hankali ya zareta daga jikinsa,ya dora mata kanta saman pillow ya maida duvet ya rufeta sosai sannan yaja jikinsa yana sauka daga saman gadon a sanyaye.

Da idanu ta bishi ta qasan duvet din,har zuwa sanda ya isa toilet ya tura qofan ya shige ya maidata ya kulle. Idanunta ta dauke daga wajen,gaba daya kanta ya kulle,me ya sameshi haka?,yana da wani ciwo ne da ba'asan dashi ba?,yadda bugun zuciyarsa yake da kuma fitar numfashinsa da irin riqon tsaurin da yayi mata ya bata tsoro. Ta maida idanunta ta lumshe tana jin qarar ruwa daga bandakin.

Mintuna kusan sha biyar taji alamun fitowarsa,tadan ware idanunta tana kallon fuskarsa a sace. Yana daure da rigar towel wadda ta fidda ingarman qirjinsa waje,gargasar duka ta jiqe da damshin ruwa kamar yadda sumar kanshi ke digar ruwa, qaramin towel ne a hannunsa yake rage ruwan yana matsawa zuwa gaban stool.

Caraf ya kama idanunta tana satar kallonshi,a gigice ta dauke idanunta wata matsananciyar kunya tana kamata. Basarwa yayi kamar bai gani ba,ya juya yana ajjiye towel din hannunsa,ya kuma kama zaren bathrobe din yana warewa,ya sanya boxers ya feshe jikinsa da turare sannan ya sake dawowa zuwa gadon.

Kaman dazu haka ya maidata jikinsa,ya dora hannunsa a hankali saman sumarta yana shafa sassalkan gashinta. Yadda yayi matan ya haifar mata da faduwar gaba,muryarsa can qasan maqoshi taji ya furta

"Shshshsh......relax......relax" idanunta ta maida ta lumshe tana qoqarin daidaita bugun zuciyarta.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 129



Daga ita har shi ba wanda yasan lokacin da bacci yayi awon gaba dashi ba. Saidai lokaci yana yi na sallar asuba suka farka kusan lokaci daya.

Ita ya fara yiwa umarni ta shiga tayi alwala sannan shima ya shiga yayi,ya jasu jam'i sukayi sallar asuba bayan kowa yayi raka'atanil fajri. Ya juyo ya zauna sosai yaja duban fuskarta,ya xube mata idanunsa dake a lullumshe wanda suke nuna akwai alamun bacci a cikinsu. Taqi yarda ko sau daya su hada ido,saboda duk sanda ta tuna yadda suka kwana jiya saita dinga jin kamar ta aikata wani babban zunubi ko laifi.

Wani kasalallen miskilin murmushi ya saki na gefen baki. Ta gama cukuikuyeshi ta gama sunnewa a jikinsa amma yanzun tana wani basarwa kaman ba ita ta aikata ba, ya tabbatar da zai nuna mata yadda ta dinga maqalewa cikin jikinsa tana matsowa a duk sanda ya motsa tana sake shigewa jikinsa.....ya tabbatar sai ta kusa narkewa.

Zara zaran hannunsa ya miqa mata kaman meson suyi musabaha. Ta daga ido a hankali ta kalli hannun sai ta dauke idanunta tana boye hannuwanta cikin hijab kamar me tsoron kada ya kamata

"Good morning mom twins" ya fadi da muryarsa can qasan maqoshi da tayi wani irin laushi yana lullumshe ido,saboda shi daya yasan irin feelings da yanayi da kuma lokaci irin wannan yake saka masa.

"Ina kwana?" Ta fadi qasa qasa itama,sai ya maida hannunsa yana hadesu guri guda idanunshi a kanta

"Lafiya qalau alhamdulillah" ya bata amsa a nutse har yanxu ya kasa dauke idonshi a kanta. Sosai ta kuma dauke kanta,kunya yake sanyata ji abinda batayi niyya ba. Saita kwantar da kanta saman cinyoyinta tana lumshe ido.

Yunwa takeji sosai,amma kuma batason ta nuna masa,batason ta bayar da kanta,saidai kuma da gaske yunwar qara gaba takeyi. Qara qudundunewa tayi,tana shirin jingina jikinta da sofa din dake kusa da ita,sai taji ya sunkuya ya dagata cak. Idanu tadan fitar qamshinsa yana shiga hancinta. Bai ajeta ko ina ba sai gefen gadon,ya sauketa a hankali yana mata rumfa da faffadan qirjinsa,ya miqa hannu ya dauko pillow ya saka mata a bayanta,ya jawo mata blanket yana lullube mata qafafunta.

A nutse ya miqe,saita daga idanunta,suka hada ido,shima ita yake kallo yana aje mata kallon nan nasa da kowacce rana yake barazanar sauke zuciyarta gaba daya. Baice komai ba sai ya juya yana fita a dakin.

Ajiyar zuciya ta sauke tana rungume pillow da kyau a qirjinta,ta kuma kanta ta kwantar. Batasan tunanin me takeyi ba,amma dukka hankalinta yana tare dashi bayan fitarsa, zuciyarta ta dinga bugawa a hankali kunnuwanta kuma sukayi nisa da sauraren kowannw motsi dake gilmawa cikin gidan,kamar dai tana qididdigen takunsa daga inda ya fita din zuwa cikin dakin.

Sanda taji an bude qofar dakin sai data sauke qaramar ajiyar zuciya,duka duka fitarsa da mintuna kadan amma sai take jinta ta takura,duk dakin takeji kamar an sauya masa yanayi.

A nutse ya iso gabanta,ya tsugunna a hankali daga gefe ya dauko wani abu. Koda ya bude saiga dan madadaicin tray table. Hannu ya miqa ya bubbuga pillow din da take kai. Ya sani idanunta biyu,don koda qafa tayi motsi yana fahimta,amma har zuwa sannan taqi daga idanunta a kanshi.

Kunyarsa takeji sosai ta yadda batason hada idanu dashi,yana jifanta da wani kallo ne da zuciyarta bata iya jurewa,shi yasa take matuqar qoqarin kaucewa duk wani eye contact dashi,don abune da bashi da sauqi sam.

Da ido ya mata nuni ta gyara zamanta. Bata musa ba ta gyara,saboda qamshin da takeji daga tray din da ya ajjiye yana qara mata kwadayi,yawunta ya shiga tsinkewa shi daya ba tare da taga meye a ciki ba.

A nutse ya saka table din daga saman qafafunta,ya dauko tray din dake dauke da qananun cups da bowl ya ajjiye ya fara buda mata komai. Ya kammala ya hau saman gadon ya zauna sosai,ya dauki qaramin spoon yana cewa

"Haaaa" sai data kalli spoon din sannan ta kalleshi. Ya dage mata dukka girarshi biyu yana fadin

"Aikina na uncle nake cikawa,sannan duk kina cikin baquncina ne......baby na nakema kuma.....banason zama da yunwa right?" Yayi maganar gently da irin dakiyar nan tasa dake qara masa kwarjini. Bata tsaye sa'insa dashi ba ta bude bakinta ya fara bata,kaman jiya sai daya tabbatar takai geji sannan ya tattara komai ya fita dashi.

Bayanta ta mayar jikin gado ta jingina tana fidda numfashi,bata san wanne sihiri bane a hannunsa?,wacce baiwa gareshi da ya haddace duk abinda take matuqar so,hakanan duk abinda taci din baya dawo mata,ba kaman a gida ba da bata isa taci solid abu ba,gashi daga jiya zuwa yau taci abinci da kyau ba tare da ya dameta ba.

Minti biyar goma ashirin taketa tsammanin sake jin dawowarsa,saidai ko motsinsa bata qara ji ba. Kasala takeji gadan gadan da wata irin mahaukaciyar kewa da takeji kamar ba zata barta ba. Tana buqatar ta jita jikin wani abu......tana da buqatar dumi a tattare da ita.

Sannu sannu sai gashi ta buge da duba agogo,har zuwa sanda lokaci yayi nisa, zuciyarta ta dinga zafi,ta kasa zama guri daya,sai ta miqa hannu ta jawo wayarta.

Numbers ta dinga bi tana tunanin waye zata kira?,a hankali a hankali har ya isa kan number bibi,sai kawai hannunta ya zarce da kiran bibi din.

Tayita ringing kamar ba za'a daga ba,wannan ya sake sakawa zuciyarta tazo iya wuya,ta cika ta cika tayi fam,dai dai sanda bibin ta daga wayar da sallama a bikinta.

Bakinta ta bude zata amsa sallamar amma saita kasa,wani abu ya tsaye mata a wuya,sai kawai ta fashe da kuka,kukan da ya daga hankalin bibi ainun.

"Ke meye ne haka da fara safiyar nan?,.......ke sultana?.....me ya faru?,waye ya mutu?" Tanason buda bakinta ta yiwa bibi magana amma ta kasa

"Na shiga uku,me ya samu diyar mutane?" Bibi dake zaune saman abun sallah ta fada.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login