Showing 54001 words to 57000 words out of 294767 words

Chapter 19 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

son ranta take bata maman ba. Tasha kuwa sosai,bibi ta dauketa ta saka batoul itama ta kama guda daya.

Kafin su gama hawaye shabe shabe akan fuskar sultana

"Yauwa to ma sha Allah" bibi ta furta tana daga yaran. Sai yanzu zuciyarta ta samu nutsuwa,ta sanya batoul a kafada tayi gyatsa sannan ta saka benazeer. A nan saman gadon sultana din ta kwantar dasu,tanayi tana qananun mitoci,abun ya qonawa sultana rai sosai,yanzun kenan ko damuwa da damuwarta bibi ta daina?,bibi da bata barinta tayi kuka yau itake kallonta tana kuka amma bata ko dubeta ba bare ta lallasheta?.

Bibi na fita ya tura qofar dakin ya shiga da sallama. Tana tsaye bakin mirror tana daura towel,tanason shiga tayi wanka tunda ta samu bibi ta dauki yaran kafin ta dawo mata dasu. Sau daya ta juyo ta kalleshi ta dauke kai tana ci gaba da abinda takeyi din. Ya taka ya matsa gabanta yana dubanta

"Hamdiyya" ya kirayeta qasa qasa

"Na'am" ta amsa masa ba tare data juyo ba,sai kuma shuru ya biyo baya

A nutse ya qaraso,ya jingina ta a jikinsa ta baya

"Har yanzu kina fushi ne?,kin daina ta tawa gaba daya sai ta jikokinki?" Bata dai waiwayo din ba ta bashi amsa

"Fushin me zanyi?, bayan nina muku laifi?,amma aina wanke kaina ko?,tunda ga diyarku nan na dawo muku da ita ban gutsireta ba"

"Ya isa" ya fada cikin son katse zancan,don gaba daya bayason ana maimaita maganar. Hannunta ya kama ya zaunar da ita sannan ya zauna a gabanta

"Haqiqa kinyi abu me kyau,kinyi abinda kika cancanci a yaba miki da kika tseratar da Bibi daga rudani da kuma fadama nadama,na gode miki qwarai,kuma ina fata zaki yafemin bisa duka kusakurai na" ta tsammaci zaya sako zancan maina amma sai taji bai sako din ba,ya zuwa sannan zuciyarta ta qeqashe da takejin bata buqatar taimakon kowa sai nata ita d'ai,don haka itama bata tada masa zancan komai ba.

Cikin kwanakin gaba daya tare da Bibi ake rainon yaran,sam sam ta hana a basu madara sai nono. Sultanan tayi kuka tayi kuka har idanunta ya dinga motsawa me ciwon amma hakan baisa bibi ta janye ba,duk sanda za'a basu nonon bibi ke tsaiwa a kanta saita tabbatar sun sha sun qoshi. Gaba daya jin abun take banbarakwai,abubuwan da take boyansu,abubuwan da take adonsu yau sun zama abebaden shan wadansu.

Amma kuma abun mamakin da yaran sun kama sun fara sha sai taji zafin da takeji cikin zuciyarta yana sauka a hankali. Wadansu irin yara ne,masu tarin wayo da wani irin farinjini da kwarjini da Allah ya zuba musu. Idan kana kallon fuskarsu ba zakaso ka daina ba,sun iya kallon mutum kamar sun sanshi ,bibi takance

"Wannan wayon da abinku aka haifeku,so kuke ma kufi uwarku wayo".

Kwanansu uku kacal da dawowa saiga tawagar family din MAYAK'I sun iso. Kusan kaf kowa na gidan ba wanda aka bari acan. Duk wanda ya daga yaran sai yayi kamar bazai ajjiye ba. Sultana na daki kwance jikinta a mugun mace,ta kasa zama cikinsu,ta kuma kasa hada idanu da kowa,jinta take kamar bare a cikinsu,a dakin su aminata suka cimmata suna santin yaran

"Wallahi kaman ba kece mamarsu ba sultana,don Allah ki barmuna su kawai" kanta ta juyar wani sashen tana cewa

"Ku daukesu kawai na baku" dariya sosai yasmine ta saki

"Wallahi qarya kike,wai ke irin bakiso dinnan,wa zai samu yarannan yace baiso?,ko ke bakiso na tabbatar yaa maina yana son kayanshi" a wani irin fusace ta juyo da fuskar nata data kawar dazu tana kallon yasmine. Ambatar sunansa kawai dai dai yake da kira mata uwa uba da duk wani da take gani da kima a mazaunin mahaifi ka zageshi. Tashi tayi ta zauna sosai daga kwanciyar da tayi dazun tana duban yasmine

"Kada ki sake ki qara kiramin sunanshi a nan wajen yasmine,don ba wajen kiran sunansa bane nan din" tayi maganar kanta tsaye,idanunta na bayyana abinda ke danqare kai tsaye a zuciyarta. Sanyi jikin yasmine da aminata yayi,suka kalli juna,sai yasmine din ta koma ta zauna daga gefanta

"Kiyi haquri,mantawa nayi,amma sultana.....baki tunanin a tsahon wannan lokacin ma a ina yake?,kina da tabbacin kawo yanzu yana raye ko ya mutu?,kinsan yaa maina....."

"Yasmine ya isa da Allah....." Sultana ta fadi tana sanya yatsunta cikin kunnuwanta,da gaske take,batason jin komai da ya danganceshi,bata qaunar ambatar sunansa a gabanta.

Ama ce ta bude qofar dai dai maganar yasmine na qarshe data kirayi sunan maina. Taji komai ta kuma ga komai,sai ta saki qofar ta tako a hankali tana shigowa ciki

"Yasmine,kuje kuci abinci an kammala" miqewa sukayi dukansu,daya bayan daya suka fice a dakin,sai a sannan ama ta dawo da kallonta ga sultana.

Takawa tayi a hankali,ta sanya sannu ta zare hannuwan sultanar daga kunnenta. A nutse ta soma warware idanun nata ta saukesu a fuskar ama. Taga gaskiya muraran saman fuskar sultanar na iya girman tsanar data yiwa mainan,ta kuma tabbatar da gasken gaske take,don daga fuskarta har cikin idanunta sun canza launi zuwa ja.

Murmushi ama ta sake mata tana hadiye wani dunqulallen abu da ya tsaya mata a wuya. Habar sultanar ta dan riqe

"Karki sake damuwa,ba wanda zaya sake miki maganarsa,an rufe babinsa kinji?,tashi kiyi joining 'yanuwanki kici abinci kema,ki sake a cikinsu,mutum kike kamar kowa,idan kina ganin abinda ya farun kamar ya rage daraja ko martabarki sam sam ba haka bane,a yanzunne ma kima da darajarki ta dagu,saboda kowa na miki kallon me hankali ne a yanzun,kina da abinda kaf 'ya'yan jikoki babu me shi sai ke,tashi kije". Da irin wadannan kalaman ama ta samu ta dinga rage mata kaifin abinda takeji cikin zuciyarta,ta dan sake dasu aminata tamkar suna gida tsahon kwanaki ukun da sukayi.


*********Misalin bakwai da rabi na safiyar ranar lahadin,cikin gidan ama dake garin abuja,babban gid daya ginu ainun da wani irin tsari da kai tsaye idan ka kirashi da MANSION HOUSE bakayi kuskure ba.

Cikin faffadan dakin da ya zama masaukinsu najma aminata da yasmine,dukkansu a zaune suke kaman ba safiya ba,saboda shirin komawa nijer da sukeyi a yau din. Najma tayi wanka,aminata na zaune tana jiran yasmine ta fito ta shiga,sultana dake zaune saman sofa gab da aminata,sanye da wata rigar bacci me taushi me gajeran hannu da iyakar tsahonta gwiwa tana kallonsu kawai. Jifa jifa aminata na sanyata a hirartasu,gaba daya amsarta bata wuce daya zuwa biyu idan tayi nisa uku.

Sake kallonta aminata tayi,can qasan ranta tana mamakin sauyawar sultanar,a duniya duka idan akace mata wani lokaci zaizo da sultana zata zama miskila to tabbas zata musanta,musu kuma me tsanani,sai gashi dare daya sultanar ta tashi daga ainihin sultana ta zama wani abu daban. Sultana da a baya ko fada kakeyi da ita ta sanyaka kuka badai kai ka sakata kuka ba..... sultana da a baya idan ta fannin magana ne saidai ta cinyeka badai kai ka cinyeta ba.......saidai ka haqura kayi shuru ka barta......... saidai ka gaji kayi shuru badai ita ta gajiya ba.......yau sultana ce magana ke mata wuya,murmushi ya zama wani kayan gabas a wajenta

"Don Allah sultee......ki canza please,wannan sabon halin naki nikam baiyimin ba,kuma bayamin dadi" aminata ta fada tana bata fuska. Fararen idanunta kawai ta daga ta kalli aminata din sai ta maidasu ta lumshe. Aminatan ba zata taba ganewa ba,ba zata taba fahimtar what she goes through ba......a yanzun a cikin ruhinta itama jinta takeyi kaman ba sultana ba.

Kafin tace komai bibi ta shigo dakin,rungume take da wasu sabbin atamfofi wanda duk zuwa Nigeria sai an sayesu an tafi dasu,ayita ajiyarsu saboda tashin wata hidima ko kuma dinkin yaran gidan. Kusan al'ada ce da maina ya kafa saboda yadda ya tsani yawan ta'ammali da English wears da su sukeyi wanda ba komai bane kusan al'adarsu.

Ama ke biye da ita dauke da wasu kayan masu yawa itama data ware zata rabawa su najma,kayayyaki ne da tasan suna qanfarsu a can. Turus bibi tayi tana dan duban sultana

"Ya na ganki zaune kowa yana shiryawa?,bakisan tare zamu koma ba?,tunda shi hamidou komawarsu ba yanzun ba?" Idanu ta daga ta kalli bibi,sai kuma ta maida dubanta ga ama kafin ta janye duban nata idanun nata na cika da hawaye duk da basukai ga zubowa ba. Sam batajin zata iya komawa cikin qasar nijer taci gaba da rayuwa,a yanzun bata sha'awar hakan sam sam sam. Da wanne ido zata kalli jama'ar data sani a baya?,da wanne ido zata kalli mutane?,tace musu me?,batajin tana da rufin asirin da ya wuce mata rayuwa yanzu cikin Nigeria

"Zan zauna a nan ne,bazan biku ba" qarasawa bibi tayi ta zube kayan hannunta baki bude tana duban sultana

"Kamar yaya?,saboda me?" Hannu ta sanya ta dauke siririyar qwallar data ziraro mata

"Nafiso nan, nafison na zauna a nan kawai,ki barni a nan don Allah bibi" ta qarashe fadi muryarta tana rawa.

Baki buden bibi ta waiwaya tana duban ama,sai aman ta dagawa bibi hannu sannan ta tako kusa dasu

"Tunda hakan takeso kiyi haquri bibi ki barta a nan din,in sha Allah zanci gaba da kula da ita,zan kuma riqe amanarki,duk lokacin da taji zata iya komawa can din,zan shiryata na maida miki ita har gida in sha Allah" zama bibi tayi tana duban ama

"Yo na tafi a cuci wadannan bayin Allahn?,kina gani da idona ma ba wani nonon arziqi suke samu ba?" Da sauri ta dago kai tana duban bibi. Kaji wani sharri irin na bibi(sultana ta fadi a ranta),tun bayan abunma ba'a taba takurawa rayuwarta ba yadda bibin ke takura mata. Cikin dare zataje ta debo yaran,ta tasheta a bacci,haka zasu kwana jikinta,wani lokacin haka zata kwana tashinta wai ta basu nono,wani lokacin idan abun ya isheta saidai kawai ta sake mata kuka,ta maidata kamar wata saniya,amma yanzun cewa take ba nonon arziqi suke samu ba?.

Murmushi ama ta saki me sanyi,makauniyar qaunar da taga bibi na yiwa yaran mamaki take bata,yadda yaran suke da saurin shiga zukatan mutane ta sani wani abune kawai daga Allah

"Duk hakan ba zata faru ba in sha Allah,na miki alqawarin zan kula"

"Idan naga sabanin haka,ko nazo naga yaran nan sun zube fa ba zanwa kowa ta dadi ba" bibin ta fadi cikin salon mita

"Ba za'a yi hakan ba in sha Allah" ama ta sake tabbatarwa bibi.

A ranar dukkansu suka tarkata suka wuce,sai gidan ya zamana daga ama sai tanja da Bibi tace ta barwa aman ta tayata kula da 'yan biyu duk da gidan akwai ma'aikata sosai,sai aba sai kuma sultanan.


*********** Watansu hudu amma sunyi kubul kubul dasu kamar ana hurasu,ga nauyi da suka sakeyi saboda isashen nono da suke samu,tun sultanan najin wani banbarakwai idan tana shayar dasu,har ya zame mata tamkar wata hanya guda daya da zata samu kusanci da yaran,ta kuma qare musu kallo yadda take buqata,don bata wani sakewa ko cikakken kallo tayi musu gaban mutane koda kuwa ama ce.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 29


*_BAYAN SHEKARA DAYA_*


K'awataccen falo ne da aka qawatashi da wasu irin resting chairs masu azabar kyau. Ba wani tarkace me yawa aka zubawa falon ba,kasancewar an yishi ne kawai domin hutawar baya buqatar tarin wasu tarkace masu yawa. Malale yake da carfet lallausa me kyau,sai wasu irin curtains da aka qawata bagunan gilasai manya na falon dasu.

Daga can sashe daya na falon take zaune,sultana ce sanye d wani yadi me taushi ruwan madara da aka yiwa qawataccen dinkin sakakkiyar doguwar riga. Ta nade kanta da mayafin kayan me sauqin nauyi,daurin da tayishi ta yishi ne simple saboda kada tabar kan nata haka,amma sai ya zamana kamar ado a kanta ya zaina daras ya kuma boye tarin sassalkar sumar kanta.

Game ce a hannunta take bugawa wadda ta zame mata abokiyar zama a duk lokacin da take da buqatar kadaici. . Tunda ama ta karanci hakan sai ya zamana bata da aiki sai siya mata games kala kala. wata guda baya ta cire benazeer da batoul daga nono. Ama bata hanata ba,saboda a shekara dayan da watanni yaran sun zama barden goyo,sun zama wasu dima diman da zakayi tsammanin sunyi shekara bibbiyu ne.

A hankali ta cira kanta tana kallon saitin qofa inda ta jiyo ihun benazeer daga farfajiyar gidan. Kamar ta maida kanta saboda tasan zallar rigima ce da suka saba yi ita da batoul amma kuma sai ta kasa saboda qara sautinta da benazeer din keyi.

Zame game din tayi ta ajjiye,ta sauke qafafunta qasa tana gyara daurin scarf dinta da santsin sumarta ya sanyashi sauka,ta tako a da dan hanzarinta zuwa wajen.

Tana sako qafafunta wajen ama na fitowa a gaggauce ta qofar kitchen ta baya,hannunta dauke da ludayin miya. A duniya koda bacci takeyi taji wannan kukan nasu to sai katseshi.

Ta gefan idanu ama ta hangi kamar inuwar sultana din. Murmushi ta saki qasan zuciyarta tana jin dadin yadda ta yunquro don duba kukan me sukeyi?,ba kaman kwanakin baya da idan suna kuka irin wannan ko motsawa batayi bare ta lalubi abinda yake faruwar har sai ama ko tanja wani a cikinsu yazo.

Gilmawar ama data gani ya sanyata ja da baya ta boye bayan labule,saidai kuma daga nan inda take tsaye din tana hangen yaran da kuma hangen abinda yake faruwa.

Su uku ne, benazeer batoul da kuma goumar dake dauke da wasu kyawawan kwalaye guda biyu da dukkansu kalolin baby pink ne

"Dama kana wajen amma suke irin wannan kukan goumar?" Ama ta fada tana tsayawa turus hadi da duban hannun goumar din

"Ama kin sani dai,kinsan halinsu,abu kadan ita wannan lutiyar qaramar saita bude baki tayita zabgawa mutum ihu kamar an saceta" ya amsa yana qoqarin bude kyakkyawar takardar da aka lullube akwatin farko da shi,yaran kuma na tsaye kyam a gabansa riqe da rigarsa,kowa yana hanqoro a bude abinda ke ciki a bashi

"Shi wannan din daga ina?" Ama ta tambaya

"Ban sani ba,muna nan ina sakasu cikin keke me delivery yayi sallama,wai aikoshi akayi ya kawo,tun last week ma wai bashi da cikakkiyar lafiya bai samu fita aiki ba" ya fadi yana qarasa yage ledar, kyakkyawar akwatin ta bayyana

"Wata uku,wata shida,wata tara, shekara daya duka ina qidaye da kawo wannan saqon,wai me security na gidannan sukeyi da basu taba banbance wanda ke aikoma yarana gift ba?,a wannan yanayun na rashin tsaro da Nigeria ke dashi?" Ama ta furta cikin damuwa tana duban goumar,saidai shi goumar din baice komai ba yanata kici kicin bude akwatin.

Gift ne tsadaddu masu matuqar daukan hankali da tsari. Wasu irin abun hannu guda uku uku na wani irin duwatsu masu tsada da daraja,komai na jiki sak da sak iri daya,an rubuta sunansu a tsakiyar kowanne dutse,tarin chocolate,sai wasu qananun jirage masu kyau,qaramin turare sai card na gaisuwa dake dauke da haruffan Happy birthday.

Miqawa ama duka kayan goumar yayi bayan ya raba rigimar benazeer da batoul ya basu chocolates a cikin kayan. Hannu tasa ta amsa tana juyasu

"Kada a sake amsar wadannan kayan goumar,ba'a san waye ke kawosu ba"

"Nifa in kyautata zaton cikin masu ganin pics dinsu a Instagram ne ama"

"Kawai kuma sai a lalubi address dinsu?"

"Eh to da wannan kuma" goumar din ya fada yana shafa kansa.

A nutse ta koma da baya ta zauna,sannan ta dauki game dinta taci gaba dayi. Daga nan inda take zaune din tana iya jiro darar goumar da su benazeer,wani irin sabo da shaquwa ne sosai a tsakaninsu,wanda har takai goumar din ba kasafai ya fiya zaman NIJER ba,yanzun haka kusan a gidan ama yake,karatunsa ma ya dawo cancakat university of ibadan,weekends yana abuja wajen ama,idan ya samu dama kuma yaje NIJER din ya dawo.

Daidai sanda akayi mata game over taji hayaniyarsu batoul har saman kanta,ta daga kanta a nutse tana duban qofar sanda suke shigowa goumar na dauke dasu su duka. Idanu ta kawar tana qoqarin kashe game din ta sanya kata caji. Hakanan batason kallon goumar din sam,bata kuma son hada hanya dashi,dawowarsa gidanma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login