Showing 132001 words to 135000 words out of 294767 words
Chapter 45 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
yana duban yaron dake musu gugar
"Kwashe kayan gaba daya,kaje ka fidda duk wanda tace bataso a goge din a dawo dashi ciki"
"In sha Allah" matashin ma'aikacin ya fadi yana duqawa ya tattare kayan yana fita dasu,sai ta koma ta zauna idanunta akan suhail
"A ina ka sake samo mana bafullatani?" Maganar ta bawa suhail mamaki, baiyi zaton zata gano bafulatani bane shi nan da nan,lallai tsohuwar nada kula sosai
"Hala bai baki labarina ba?"
"Shin kaine suhail?" Ta jefa masa tambayar sai ya qarasa sakin murmushi
"Nine bibi,barka da warhaka" ya soma gaidata cikin girmamawa yana murmushi,qarasa sakin fuskarta tayi tana amsawa,sai tahau shelanta kiran masu aikinta
"Nayi baqo,a kawo masa abun tabawa". Tace da masu aikin nata.
Yadda suke gaisawar kamar sun jima da sanin juna ya bawa maina mamaki,daga dai yanayin yadda ta saki jiki da suhail har hira na gudana tsakaninsu ya tabbatarwa maina haduwar jini ta qullu tsakanin bibi da suhail,sai maina kawai ya sanya kunne abinsa yana jin yadda suhail ke kwasar bibi suna hira,da yake shima gwanin barkwanci ne idan taku tazo daya,itama kuma ama din tana da son barkwancin.
Har ta sanya key ta bude motar ta kuma zura jakarta a ciki sai ta tuna aminata tace tana da ajjiya wajen bibi. Murfin ta maida ta rufe,ta soma takawa zuwa cikin gidan tana gyara yafen mayafinta. Dab da zata shiga sasaan bilki data karbo maqullan sassan baqi a wajen bibin za'a gyara ta fito,ta bawa sultana hanya tana fadin
"Kece qarshen tafiya kuma kece wadda kadai bata taba zuwa ba" murmushi sultana ta saki
"Yanzun zan wuce in sha Allah,yauwa......don Allah ina samun daffafiyar madara idan na dawo?"
"In sha Allah za'a hadata"
"Na gode,bari na qarasa" ta fadi tana sanya kai falon.
"Shekar kusan hudu bibi wannan jikan naki gashinan,bai tab......." Maganar ta tsaye masa a maqoshi sanda sassanyan muryarta tayi sallama cikin falon.
Kusan a tare idanunsu suka sauka a kanta,suhail da maina,mabanbantan feelings kuma suka sauka saman zuciyar kowannensu.
Da kallo daya tak ya gama karance shigar dake a jikinta,don shi din mutum ne me kaifin basirar dauke komai hadi da ankara,sai ya maida idanunsa ya lumshe zuciyarsa tana bugawa,wani irin kishi yana mintsinarsa har kaman zai kasa controlling kansa.
Suhail kuwa gaba daya idanunsa ya zube mata,sam bata lura dasu ba dukka su biyun har sai data qaraso tsakiyar falon. Kasa haquri yayi yakai hannu yana tabo maina zuciyarsa tana bugawa. Fes ya bude idanun nasa,saidai basu sauka a ko ina ba sai akan sultanar. Sarqewa da tafiyarta ya fara yi ya tabbatar mata da idanu da yawa a kanta,tun shigowarta falon qamshinsa ya shaida mata akwai mutum ta wajen,inma yazo ya tafu ko yana zaune a wajen,ta watsa fararen idanunta cikin falon don batason tabi ta gefan da yake yayin da take cema bibi
"Bibi ta.....zan wuce duk sun tafi sun barni,saqon aminata". Kaiwa qarshen maganarta yayi daidai da tuntube da tayi hakanan
"Subhanallah......kula kada ki fadi" suhail ya fada da hanzari har yana dagowa daga saman kujerar da yake kai kaman zai tallafe ta. Maganar da yayin yasa ta lura da zamansa a wajen,ta juya fuskarta sashensa ta masa kallo daya tak sannan ta janye idanunta tana ji a jikinta kamar tasan fuskar,kamar sun taba haduwa a wani waje daban taci gaba da takawa gaban bibi. Dukka kaifafan idanunsa ya zubewa suhail,motsin da yayi kadai a yanzun ya harbawa maina kokwanto da shakka a kansa cikin zuciyarsa
"Why he was so bothered?,don tayi tuntube meye na nuna damuwa qarara haka?" Ya fadi a ransa yana duban tsakiyar qwayar idanun suhail din.
Idan ya lura,idan kuma idanunsa da gaske suke nuna masa to tabbas kallonsa nakan sultana,kuma idanunsa na manne da ita tana zama a gefen bibi
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 69
"Dama ni ke nake jira,ki shiga dakina daga cikin cupboards din kusa da bandaki ki bude zakiga baqin leda ki ciro,bansan meye ne a ciki ba aka qulleshi haka" murmushi ta saki wanda ya sake qarawa fuskarta ainihin kyau,murmushin da ya sanya suhail murmusawa shima yana jin tana qara burgeshi da duk wani motsinta,ya kuma sanya maina lumshe ido yana jin bugun zuciyarsa yana qaruwa musamman da ya maida kallonsa kan suhail yaga yadda ya maida hankali a kanta
"Ba fada meye ya kawo gaba?" Suhail ya kasa jurewa ya furta,maganar tashi a karo na biyu ta sakata waiwayowa tana kallonsa
"Sorry?" Ta furta da alamun rashin ganeshi qarara a fuskarta,saita juya zata wuce ciki amma idanunta sukayi kuskuren fadawa cikin na maina.
Janye idon nata tayi da sauri hadi da fadin
"Barka da rana,ina wuni" ta furta masa sabo tunawa da girman ama a wajenta,gaisuwar duk a hade lokaci guda tana wucewa ciki
"Alhamdulillah" yayi qarfin halin fada yana ci gaba da monitoring suhail har sanda ta wuce ciki.
Ajiyar zuciyar da suhail din ya saki dukka tsakanin bibi da maina saida suka dubeshi
"Lafiya ko?" Bibi ta wani abu ya darsu a ranta ta fada tan kallon suhail, murmushin qarfin hali ya saki yana shafa kansa
"Ba komai,kawai akwai wani abuna ne daya bata nake tunanin kamar na tuno inda yake"
"to alhamdulillah,ai haka akeso" bibi ta fadi tana kawar da maganar gami da jefa masa wata tambayar,ya nutsu kuwa yana bata amsa tare da sake qanqan da kanshi,don yana da tabbacin zaiyi wuya sultana ba jikar bibi bace,daga kuma yadda bibi din ta amsheshi o bibbiyu tabbas alamu sun nuna yana cikin nasara. Ya matsu ta sake fitowa daga dakin ya samu yabi bayanta,a yau basai gobe ba zai sake gabatar mata da kanshi. Yadda ta kalleshi dai ya nuna sam bata ganeshi ba,amma jikinsa bai bashi haka ba yana ganin kawai jan aji ne irin na isassun mata irinta.
Zafin da zuciyarsa ke masa ya sanyashi kasa ci gaba da zama a wajen,sai ya miqe tsam yana zube hannayensa a aljihun rigarshi
"Ina zuwa?" Bibi ta daga kai tana kallonsa qwayar idanunsa na nuna tasirin fushi kadan kadan daga zuciyarsa
"Zan samu ruwa nasha" ya bata amsa yana nufar hanyar kitchen. Taso ta dago wani abu,saboda indai ruwa ne gashinan a nan wajen gaban suhail,ta san maina din sosai,tasan kuma akwai abinda ya tadashi,uwa uba kuma ta karanci mugun kishin nan nasa kwance cikin idanunsa,taga kallon da suhail yabi sultana dashi,tayi imani wala'alla abinda take ganowa cikin idanun nasa yana da tasiri da wannan. Tasan halin 'yan kayanta sarai,tsoronta daya kada sanadin kallon ya sanya ya yiwa dan mutane diban karen mahaukaciya duk da matsayinsa na baqonsa.
Freezer din ya bude ya ciro ruwan gora me sanyi har yana tsatsafa,ya balle murfin ya kafa kai ya soma kwankwada. Duk kuwa da cewa shan ruwan sanyi sam baya cikin dabi'arsa amma sai daya shanye shi tasa sannan ya buga ribar ta daki kitchen cabinet din ta fado qasa,sanyin da yakeson ji a zuciyarsa bai sameshi ba kwata kwata,ya furzar da iska ya ciro handkerchief daga aljihunsa yana share zufan data tsatstsafo masa a goshinsa,sai ya juya kawai gadan gadan zuciya tana ingizashi yana fita a kitchen din.
Daga qofar kitchen din yana hango bibi da suhail suna ci gaba da hirarsu abinsu. Wani abu ya tsaya masa a wuya daga kallon fuskar suhail kawai,abinda bai taba ji ba tsahon zaman tarensu. Kanshi ya kawar sannan ya nufi sashen dakin bibi din kansa tsaye,babu tsoro ko shayin bibi ta ganshi ko wani cikin masu aikinta.
A nutse ya murda handle din qofar dakin sannan ya tura yana shiga. Tana duqe tana qoqarin jawo ledar tana mita qasa qasa yadda bakajin abinda take fada din sai dan sound na lallausar muryarta dake dan motsawa cikin dakin. Jingina yayi da qofa yana qare ma qugunta kallo wanda ya turo sosai saboda duqawar da tayi,gaba daya qamshinta ya cika dakin,wani irin lallausan qamshi me kwantar da zuciyan. Baisan ya akayi ba sai siriryar ajiyar zuciya data kubce masa,wani mahaukacin kishinta ya sake taso masa ya dinga ji kaman zuciyarsa zata zauce,wannan ya sakashi sakin hannayensa daya goye a qirjinsa ya soma takowa cikin dakin zuwa inda ta ajjiye handbag dinta da key din motar.
Shaqar iska ta gaba da zatayi saita gauraya da qamshinsa,abinda ya haddasa mata mummunar faduwar gaba,ba shiri ta saki ledar data jawo din,ta miqe tsaye sosai sannan ta waiwayo a nutse fuskarta a dinke tsaf.
Yana tsaye daga bayan nata,duka duka taku shida ne adadin tazarar dake tsakaninsu su. Idanunsu suka gauraya waje daya kaman yadda qamshin jikinsu ya cika dakin bibi din.
Yadda take kallonsa fuska a hade haka shima,asalin fuskar maina take gani yanzun a tattare dashi. Dakiyar nan da hadaddiyar girar nan da yakan cure guri guda duk sanda zai musu hukunci,bakinsa yakan tsuke kadan a wancan LOKACIN to yanzun ma haka,saidai wannan karon siraran labban nasa dake da wani irin launi me kyau zagaye suke da gyarraren saje daga qasan habarsa zuwa qasan hancinsa. Haka kawai taji bugun zuciyarta ya sauya,sai ta janye idanunta tana gargadar zuciyarta da kada ta kuskura taji shakka ko tsoronsa,don haka sai ta juya tana yunqurin ci gaba da jawo ledar ba tare data ce masa kanzil ba,duk da yadda tsoro ya mamayeta,kwarjininsa a yau yakeson mamayar dukka qarfinta yakai qafafunta qas,abinda bata jin zata bada damar ya faru
"Waye kika tambaya da kike shirin fita baki nemi izini na ba?" Har cikin kwanyarta taji tambayar ta mata banbarakwai,ta ciro ledar daidai lokacin,don haka ta miqe tsaye riqe da ledar tana fuskantarsa
"Izinin wa kika nema?,ko kina rayuwa ne on your own?" Ya maimaita mata tambayar a karo na biyu. Dara daran fararen idanunta da hasken qwayayen dakin bibi ya qara haskawa,suka kuma fidda ainihin oily eyes dinta ta zuba saman fuskarsa. Qaramin bakinta ta motsa da niyyar maida masa da dumi,sai kuma dukka kalmomin data tattara don yaba masa suka fara sulalewa sunayin nasu guri,saboda takowar da yakeyi zuwa gareta ya haifar mata da fargaba. Batason ya sake taba jikinta ko ya sake kusanto inda yake,to amma kuma tana jin asarar tsaiwa bashi amsa. Duk taku daya idan yayi fargabarta ce take daduwa,amma kuma kaman wadda aka kafe a wajen ko aka qullewa baki taqi cewa dashi kanzil.
Sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya miqa hannunsa,miqawar data sanyata qanqame jikinta a tsorace. Tsaiwa yayi da abinda yayi niyyar yi din yana qarewa fuskarta kallo. Baby face dake dawo masa da shekarun baya fes cikin kwanyarsa, fuskar sultana sosai ta bayyana,har baisan sanda wani siririn murmushi maras sauti ya qwace masa ba,ga tsoro ga ban tsoro,ga tsiwa ga kuma tsoron hukunci.
Tas ya zare mayafin daga jikinta,tana tsaye tana jin yadda kowanne sashe na mayafin ke fita a jikinta yana barinta gaya,sai daya gama zareshi duka sannan ya dunquleshi cikin hannunsa,yayi kaman zai cillar sai ya fasa,ya sanyashi saman kafadarsa, lallausan qamshinta kuwa yace salamu alaikum,yadan lumshe ido ya bude
"Wannan din ba mayafin yafawa bane,duk randa kuma na sake ganinki dashi na rantse da Allah sai na hukuntaki ko a gaban waye" daga haka ya juya yana takawa a hankali,sai a sannan ta samu nasarar bude idanunta da suka cika da hawayen takaici tana binsa da kallo,tana mamakin kuma me zaiyi ta qofar bayan sassan bibi?,bazai fita ta normal qofa yadda kowa ke fita ba?,salon ayi zaton suna tare a dakin?,to ta yaya ma zata iya iya fita a haka ba mayafi,wanne kallo bibi da baqonta zasuyi mata?,bayan kuma ta tabbatar sunga shigowarsa?.
Duk sai taji kunyar fita a hakan,ta koma ta bude wardrobe din bibi tana bincike ko zata samu wani abu da zata yafa itama tabi ta qofan bayan ta fice,don dai ba zata iya fita a haka ba. Allah ya taimaketa ta samu wani sabon mayafi a ledarsa,da alama cikin kyaututtukan da akewa bibi dinne cikin 'ya'yan 'yan uwa da kuma surukai saboda qarfafa zumunci. Sosai ya dace da kayan jikinta tamkar dama ta ajjiye ne saboda ita,ta farke ta yafa,sai taga yafi haskata ma akan wancan. Da sauri ta zari handbag dinta da ledar aminata ba tare data tsaya duba key din motar ba,burinta ta isa gidan ta kuma dawo da wuri,Allah Allah take kwanakin da zasu bar nijer ta cika ta fice daga qasar,ta gaji da ganinsa kwata kwata,ya soma shiga rayuwarta wanda ita kuma ba zata lamunta ba.
Da yake tabar qofofin a bude ne sai ta bude front seat,ta zura hannunta da zummar ajjiye ledan,wanne tudu wanne gangare ta tsinci kanta a ciki, kafin ta gama daidaita nutsuwarta ya miqo hanunsa har yana shafar qirjinta ya jawo qofar ya rufe,abinda ya sanya numfashinta daukewa na wucin gadi. Wutar jikinsa ce shima ta dauke tsaf!,sai wani irin shock da ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta yabi jininta,ya furzar da zazzafar iska daga bakinsa yana qoqarin dage dukka baqaqen glass din motar sama.
Tsaf ya dagesu ya miqa hannu a kasalance ya kunna ac din motar sannan ya fara yunqurin tayar da ita. Sai a sannan hankalinta ya dawo gangar jikinta,tsoro sosai ya mamayeta,qamshinsu da numfashinsu kawai ke karakaina cikin motar,sai bugun da zuciyarta keyi wanda take kyautata zaton shi dake zauna a seat dinsa tana iya jiyowa.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 70
Dukka dauriyarta ta tattaro cikin dakiya da son ragewa kanta tsoron dake damunta
"Ban fahimci abinda kike shirin yi ba?,ina zaka kaini?" Ta tambayeshi tana qoqarin duban tsakiyar idanunsa. Da idanunsa da sukayi laushi qwarai saboda yadda qamshinta ke kassarashi ya kalleta
"Shshshs......fyade zan miki" ya furta kalmar gatse gatse kansa tsaye. Karon farko ta janye idanunta daga kanshi tana jin wani nauyi yana ratsata. Karom farko da taji nauyi da girman kalmar har tsakiyar kanta,irin girma da nauyin da bata taba ji tayi mata ba,bugun zuciyarta ya sake daduwa har taji kaman iska tana mata wahalar shaqa.
Ya zaci zata ce wani abu amma sai yaji batace komai ba,duk da yana iya ganin yadda qirjinta yake dagawa ta saman mayafin jikinta.
Tana ji tana gani ya tayar da motar,maganganu ne fal cikin bakinta takeson furta masa su masu tsananin zafi,saidai duk sanda ta motsa labbanta da nufin tofar masa sai wancan ranar ta dawo mata,sai taji kaman abunda ya faru wancan karon shine zai sake maimaita kansa,haka ta runtsen ido kawai tana jin yadda motar ke gangarawa tana ficewa daga gidan zuciyarta na mata tsananin zafi.
Sanda yahau kwalta sosai sai ya figi motar kamar me tashi sama,irin dai tuqin nan nasa daya saba a baya,dama shi din bai iya yiwa abun hawa ta sauqi ba.
Shuru ne ya ratsa motar sosai,ba me cewa da dan uwansa wani abu. Ita din tayi shuru taga iyakar gudun ruwansa ne,yayin da shi kuma yake fatan taci gaba da zama a haka cikin laqwas din da tayi,wannan ce kadai damarsa da zai samu furta dukan abinda yakeso ya furta din ya kuma aiwatar
"Sulthana" ya kirayeta da wani irin sauti daya sanya jinin jikinta harbawa da gudu. Sake runtse idonta tayi tana jiyo yadda qasan zuciyarta ke zafi akansa,yana kuma tuna mata da abubuwa masu yawa da suka shude. Bakinsa ya bude zai kuma kiran nata saidai kuma kiran wayar laila ya dakatar dashi. Shuru yayi yana jin wayar tana ringing har ta katse,ta sake kira,dole ya danna accept ya kuma maida wayar a free.
"Hello dear....." Ta furta da salon karyar da murya tana langabe kai daga can barin da take