Showing 105001 words to 108000 words out of 294767 words

Chapter 36 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Suna idar da sallar aba din yadan ja gaba ya fita a sahun,sannan ya zauna sosai ya fara azkar din daya zame masa.jiki duk safiya muddin yana da lafiya,idan kuma baya dan jin dadi yana komawa gida yayi cikin falonsa balcony ko bedroom dinsa.

Daidaikun mutane da sukasan maina sai suka dinga matsowa suna gaisawa dashi tare da tambayarsa yaushe ya dawo qasar,saidai ya danyi murmushi yace musu

"Jiya" yadda suka dinga masa barka ya alamta masa lallai sunyi zaton karatu ya tafi. A hankali a hankali yana gaisawa dasu har zuwa sanda suka kammala,ya dan juya idonsa kadan ya saci kallon aba. Yadda yake tun dazun har yanzu a haka yake a zaune,yaja numfashi sosai,sannan ya miqe cikin mazantaka ya taka izuwa garesa.

A gabansa ya zube gwiwoyinsa,muryarsa cike da girmamawa da kuma rusunawa ya furta

"Barka da asuba aba" idan carbin dake hannunsa ya amsa shi shima haka,sai yaci gaba da jan tasbaharsa baiko motsa ba bare maina ya sanya ran ya jishi. Sake maimaita gaisuwar yayi,wanda yana direta aba din ya yunqura ya miqe yana durfafar qofa,baiyi qasa a gwiwa ba ya take masa baya,saidai kafin ya cimmasa har ya sanya slippers dinsa masu tsananin taushi ya soma barin farfajiyar masallacin.

Dab da zai fita ya cimmasa,ya sake taresa karyar da wuya dama murya gaba daya

"Aba.......na roqeka don......"

"Bakaji abinda na gaya maka ba jiya?,kai wanne irin mahaukacin yaro ne?, meye alaqata da kai da zaka dinga bibiyata haka?,ni bani da wani d'a me kamanceceniya dakai,ka fita daga harkata tun kafin na saka hukuma su kamamin kai" yayi maganar a fusace yana nunashi da yatsa,sannan ya kewayeshi yana wuceshi bayan yaja dogon tsaki. Sosai jikin maina yayi sanyi,abinda yake gani a idanun aba din me girma ne,anya zaici gaba da tunkarar aba?,anya ba bibi bace kadai tsaninsa kaman yadda oncle issoufou ya gaya masa?.

Cikin qarfin hali yaci gaba da takawa cikin gidan. Koda yakai bai koma sassansa ba sai ya zarce sashen ama. Can dinma mutanen daya samu a sassanta wadanda suka tattashi sallah dukka basu koma ba binsa suka dinga yi da kallon yaushe gamo?,ya gaisa da wadanda zai iya gaisawa dasu,ya tambayi bilki me aikinta ta gaya masa yanzun ta shiga daki.

Sau uku yana knocking sannan ya murda qofar,bakinsa dauke da sallama,qasan zuciyarsa cike fal da addu'a. Da ita ya fara tozali,tana zaune saman tattausan abun sallarta dinnan,jikinta sanye da ustazah hijab da skirt dukkansu kala me haske. Tsananin tsafta da gayunta ya santa kusan komai nata me hasken kala ne,sai dai daiku masu duhun kala. A nutse ya qaraso cikin dakin,ya kuma yiwa kansa mazauni a qasan dandagaryar turkey carfet din dake malale a dakin wanda ya qarawa dakin kyau da kuma tsari.


Hannayenta a sama tana addu'a,sai shima ya buda nasa tafukan hannayen,sanda ta kammala suka shafa a tare,sannan ta waiwayo suka hada idanu.

Kwarjinin nan nata yana nan,gaba daya fuskarta ta cika da hasken ibada sanin kima da martabar kai. Wani lokaci su uncle abdulhakeem kan bata lokaci kan cecekucen kwarjinin da yayo gadonsa yayi,amma basusan tsakanin hamid da hamdiyya waye yafi wani kwarjini ba?.

Sai data gama zuba masa dukka dafin kwarjinin idanunta sannan ta janye daga kallonsa. Zuciyarta na hira a kansa ita kadai. Mainan nata ya girma,ya zama cikakken mutum wanda ta tabbatar akwai maganganu masu yawa da labarai cikin tafiyarsa da kuma dawowarsa,saman kowacce fuska akwai labari......cikin kuma kowanne littafi nan ma tasan akwai labari,amma a yanzu bata jin zata bashi wannan qofar ko damar haka a kurkusa. Kaman yasan niyyan tashi ta bashi waje takeyi sai yayi caraf da dukka hannayenta ya kuma hanata miqewar,koda ta daga kai ta kalleshi sai ta tsinci hawaye fal idanunsa. Kuka a idanun aliyyu?,abinda zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba gani ba,tun yana qaraminsa kuka abune me wuya a wajensa bare kuma sanda ya mallaki hankalin kansa,yana da tsananin fushi kafiya da zuciya,wannan ya sanya ko yara sa'anninsa basu fiya takalar fada dashi ba,idan kuwa kayi gangancin yin hakan kaine zakasha qasa

"Don martabar fiyayyen halitta ama kada kiyimin haka,aba haka yakemin tun jiya,kema haka zakiyimin ama?,idan duk duniya sun gaza fahimtata ama na dauka ke zaki riga kowa fahimtata,ke zaki fara sauke fukafukan jin qanki a kaina ama?,ban tafi don wata manufa ba,banyi nesa daku saboda na rainaku ba.....hasalima nayi nesa daku ne saboda kunyar keta maganarku......saboda kunyar na aikata abinda ya kamata ace ya zama sirri ne tsakanina da ita saidai nayi ta yadda ya zai fita,na tafi ne saboda bansan da idanun da zan kalleku ba,bansan da bakin da zanyi muku bayani ba......ama....... wallahi wallahi wallahi ban tafi da nufin na tafi daga gareku kenan gaba daya ba.......na tafi ne da niyyar idan kun huce zan dawo......a raina ban taba sakawa zan tafi nayi koda wata guda ba.......sai kuma gashi komai ya sauya......ina biye daku ama......ina biye da duk wani motsinku ama.......ban yanke daga shiga rayuwar sultana tare da sanin hakinda take ciki ba ama......amma kuma saidai a cikin tarko nake......ina cikin wani dauri da muddin na bayyana a gareku rayuwata na cikin hadarin da bani da gatan da zai fiddani.... Lokacin kuma da nake tunanin na zama free......ina da 'yanci sai yayi dai dai da lokacin da zan cika BURIN ABA.....MAFARKIN ABA.....burin dana tabbata a duk sanda na bayyana a gabanki babu shi kema zaki qalubalanceni BABBAN LIKITAN ZUCIYA kuma DAN KASUWA CIKAKKE.....Na hadu da jarrabawar da na tabbatar barinku ne sila......na kuma hadu da lalurar da afuwarku da kuma yafiyarku ne kawai zai bani maganinta......" Hannu ta daga masa tana yin qasa da kanta,batason yaga zallar rauni da karaya daya zubawa zuciyarta,batason yaga tausayin daya lullube qirjinta,irin tausayin da dukka uwa keji akan d'anta komai girman laifi ko kuskurensa,saboda kasantuwar zuciyar mahaifiya ta banbanta da zukatan mutane gaba daya,koda kuwa ita wannan uwar wata halitta ce daban bata dan adam ba......

"Banason naji komai daya faru dakai,koda zanjin zanji ne a tare a kuma lokaci guda da mahaifinka,kaje ka nema yarda mutum ukunnan.......sannan ka dawo gareni" sai ta zame hannunta tana miqewa.

Shima bai zauna din ba sai ya miqe yayi tsaye yana kallonta tana barin dakin

"Kiyimin alfarmar amsa gaisuwata ama.....koda iya ita kadai na roqeki" har ya fidda rai don takawa take tana barin dakin,kamar kuma ba zata amsa ba,dab da zata fita din tace masa

"Nayi maka" cikin dubunnan nauyikan dake qirjinsa yaji kaman an cire daya,ya fesar da iska me nauyin gaske da ya fusgota daga cikin cikinsa yana aza tafin hannunsa saman fuskarsa wani farinciki yana dan ratsashi,sa'annan yana jin qwarin gwiwarsa ya sake qaruwa. Sai daya ji ya nutsu sannan ya soma fita a dakin,cikin takunsa me cike da qasaita,saidai kuma a yau din a sanyaye yake takawar.

Bangaren bibi ya nufata kai tsaye,shikam a yau yakeson gamawa da bibi din,don dama bai azata a ma'aunin matsala ba,ya duba agogo dab da zai shiga sashen,ya kwasarwa drama dinta awa daya kacal,don yanason ya koma bangarensa ya sake runtsawa koda na awa daya ne sannan ya shirya ya fito,don yanason ayi daurin auren 'yan uwansa dashi.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 56


A falo ya sameta riqe da tasbaharta da masu aikin sassanta. Cikin girmamawa suka gaidashi sauran da jiya basu ganshi ba sai yanzu sunata satar kallonsa hadi da mamakin ganinsa da sauyawarsa lokaci guda. Da daya da daya suka zame a falon kamar yadda suka saba a baya,sai ya zamana daga shi sai ita a falon. Zamowa yayi ya zauna a gabanta yana dan matsa mata qafafunta daya tabbatar suna dan mata ciwo kadan kadan,ya kuma fahimci haka ne a rigimarsu ta jiya. Saurin janye qafafun nata tayi tana jifansa da harara,yayi amfani da wannan damar ya sakar mata murmushi sannan yace

"Barka da safiya da fatan kin tashi lafiya uwar gida ran gida" harara ta sake jefa masa tana hade rai da gaske

"Kaga ka fita a ido na,ni ba sa'ar wasanka bace,uwarka da ubanka ma duka basu isheni kallo ba bare kai mara kunya fitsararre" tana kaiwa qarshe ta fara yunqurin tashi,bai hanata ba,ta miqe tsam ta wuce bedroom dinta tana mita kaman zata ari baki. Biye yake da ita bata sani ba,sai data shiga dakin tana shirin maida qofa ya shigo

"Me ka shigo yimin daki?"

"Ba komai,nazo mu fahimci juna ni dake"

"Lallai aliyu raini ya shigo tsakaninmu,waishin me yasa baka tunkari uwarka da ubanka ba?,sai khadeeja marainiyar wayonka ko?,to na fika tijara" daga haka ta samu waje tayi zamanta. Qarasowa yayi gabanta ya zauna,duk wani yanayi da yasan zai bata ta tausaya masa amma taqi ma kulashi bare ya sanya ran samun wani ci gaba. Zuwa lokacin har maqoshinsa ya bushe kasancewarsa mutum bame yawan son dogon magana ba,yaja numfashi yana lumshe idonsa,qirjinsa wani zafi zafi yakeyi yi masa,ya kallo agogo yaga yana shirin cinye awa dayan da ya bawa bibi amma babu canji.

Tsam ya miqe yana tattare hannun rigarsa idonsa a kanta

"Allah ya gani nayi duk yadda zanyi na fahimtar dake kinqi fahimtata,shikenan zan tafi......kuma idan na tafin bawai zaki sake ganina bane,ba zaki sake ganina na ba har abada" yana fadin haka ya soma takawa. Da idanu ta bishi zuciyarta na rawa,tasan halinsa,aliyyu ne ba wani ba,komai ya fada yana aiwatar dashi,tsanani ko wahala basa sanyashi sauyawa,yana gab da fita taji bakinta ya fusgi kalmar

"Ina zaka?" Cak ya tsaya yana jin ranshi yana masa dadi,bai waiwayo ba yace da ita

"Zan koma inda na fito mana,tunda dukkanku kunqi bani dama na fadi abinda nakeson fada din"

"Yo kaje mana,me jiya tayi ballantana yau......" Bai bari ta qarasa ba ya sanya qafarsa daya waje,sai kalaman nata suka sauya da

"Amma dai kasan hukuncin me bijirewa iyayensa ko?,kasan hukuncin gudajjen bawa ma bare gudajjen d'a ga iyayensa" idonsa ya lumshe hawaye na taruwar masa,ya godewa Allah.......tabbas ya samu baiwar soyayya daga iyaye da 'yan uwansa,wannan reaction din kawai na bibi ya bashi qwarin gwiwa matuqa fiye da kowacce sa'a da daqiqa,yasan a yanzun ya cimma kaso hamsin cikin dari,hamsin kadai ya rage masa,shima kuma yasan ta yadda zaya biyo masa. Dawowa yayi da baya cikin wani irin sanyi da ita kanta bibi ta lura dashi,tsugunnawa yayi a gabanta ya sanya fuskarsa tsakiyar hannayenta daya kama

"Ku yafemin bibi,ku yafemin.....na tafi na barku tsahon shekaru bayan nidin me laifi ne a wajenku" sanyi jikinta yayi sosai da taji damshin hawayen aliyyu,ganin fitar hawaye a idonsa ba qanqanin lamarj bane,sai dai ita dinma tanaji a zuciyarta bai kamata tanuna masa goyon baya ko.karaya tun yanzu yanzu ba,don haka ta janye hannayenta tana cewa

"Ka tashi kaje kaci gaba da neman afuwar wadanda sukafi cancanta,zamu qarasa magana ko zuwa anjima" bayan hannunta kawai ya juya ya sumbanta ya miqe a nutse yana ficewa batare da sake cewa komai ba,don zuciyarsa tayi nauyi,bata yadda zai iya sake cewa wani abu.

Tunda sukaga dinkin dogayen rigunan atamfar da akayi musu da zasu sanya ranar daurin auren suketa tsalle da murna,hakanan suka dami ama da cewa ranar yaushe za'a saka wannan kayan?. Tana sane take tambayarsu sunan kayan don bakinsu bai iya fadin ATAMFA da kyau ba,saboda bawai saninta sukayi sosai ba,saidai suyita qoqarin pronouncing dinta da suna kala kala,ama kuma tayita dariya. Suna daya daga cikin ababen dake sanyata nishadi da debe mata kewa da damuwa qwarai,a yanzun cikun rayuwarta bata jin akwai wani abu na biyunsu me daraja a gurinta,ko almu atta da saddi dai kawai ta haifesu ne,amma soyayyar benazeer da batoul daban take a ranta,bama ita daya ba,duk wanda ya kalli yaran haka kawai sai Allah ya jarabceshi da sonsu,suna da matuqar maqurar shiga rai.

Tun takwas na safe suke zaune a dakinta suna jiran ta shiryasu cikin kayansu da qananun mayafai masu tsada data musu order tun daga dubai,hakanan qananun hand bags nasu hade sukazo da takalmansu na musamman data zabi wanda za'a yi musun,kuma dukka samples ne na kayan da take zubawa a qatoton boutique dinta dake dauke da kaya designers a garuruwa daban daban.

Dole ta ajjiye kudin da take sanyawa yaran da zasu yi mata clearance din kayanta ta dauki waya ta kira tanja tace ta shiryasu. Nan ma wajen wanda za'a fara yiwa wanka suka gama fadace fadace,anayi ana rigima a haka tanja ta gama shiryasu. Ita kanta tanja baya taja tana kallan yaran tare da tsarkake girma da buwayar ubangiji daya samar da yaran cikin taqaitaccen lokaci cikin mahaifar mahaifiyarsu,ya kuma basu tsaro da kariya,sannan aka haifesu da wani irin kwarjini farinjini da kyau. Dariyar yadda suketa kallon kansu kayan na burgesu ta dinga yi,kana ganin yadda sukeyi kasan sanya atamfar ba sabonsu bane.

Ana tsaka da fadan sanya turare wanda ama ta riga ta saba musu da sanyashi goumar yayi sallama yana murda qofar,yazo kuwa a dai dai,duk sai suka watsar da turarukan suka ruga wajensa suna masa oyoyo

"Maaa shaaaa Allahhhhhh BB na.......wai,wai wai" ya fadi saboda yadda kwalliyar tayima yaran kyau qwarai yana bude musu hannayensa. A tare suka isa suka fada,ya hadasu ya rungume. Benazeer ce ta fara mitan ya tafi ya barsu yau kwana wajen biyu,yadan saki dariya kadan yana lakuce bakinta data turo,shima sultana yake gani a yawancin lokuta,amma kuma lokaci bayan lokaci idan tayi wani abun dan uwansa MAINA take tuna masa

"Yanzun ai gashi na dawo ko?,am back"

"Ayi mana hoto,dama ama tace sai ka dawo"

"Tom an gama,kwana biyu nayi checking account dinku banga ama ta saka mana update na african twins BB ba" .

A gaba ya sanyasu,yau kowacce taqi yarda ya dauketa wai kada ya bata mata kwalliya,su a dole ga 'yammata. Ta baya can ya fita dasu,don ya tabbatar idan yabi dasu ta gaban gidan yadda sukayi kyau haka za'a bata musu loakcine,kuma ba za'a barshi ya musu hoton da kyau ba.

Cikin rumfar da aba ya sanya aka yiwa bibi saboda zama lokacin zafi suka tsaya. Guri ne da aka qawatashi sosai da zubin ginin gargajiyar qasar nijer,ya tabbata wajen zai bada background me kyau.

A nutse suka fara hotunan,kowanne idan ya dauka sai yaga yafi dayan kyau,suka gama tsaf,sai ya samu kujera daya a wajen ya zauna yana duba duka hotunan zai turama ama ta watsapp.

Hannayensa dukka zube cikin aljihun rigarshi yake takawa a nutse,sassalkan gashinsa dinnan me santsi da duhu yadan cakude kadan saboda baiyi combing nasa ba bayan yayi alwala. Yanayin da zuciyarsa ke ciki ya sanya fuskarsa ta danyi ja kadan,hakanan idanunsa daketa qoqarin saye abinda ke yawo a qirjinsa. Duk yana jin ba dadi cikin jikinsa,saboda ya saba kowanne lokaci kusan warhaka ya dawo daga gym ne yana shaqar daddadar iskar balcony din dake gaban dakinsa,a yanzu duk sai kasala da yanayin da zuciyarsa ke ciki suke son kashe masa jiki.

Kamar a iska yake jiyo muryoyinsu,yana ci gaba da takawa yana kasa kunnensa don yanason tabbatarwa muryar yaranne ko ba nasu ba?,yana tsoron kada tsananin damuwa da yaran da ba nashi ba,baisan me yaran waye ba ya sanya su fara shiga rayuwarsa har haka?,kada ya soma halin da ba nashi ba wato damuwa da abinda bai shafeshi ba.

Yana sake kusanto wajen yana sake jin tashin muryarsu,a hankali a hankali kamar almara sai ya fara hangensu yana kuma dab da isa inda suke.

Suna tsaye su biyun suna gwada yin selfie, benazeer ta matse batoul da yawa, batoul din na mita tana qoqarin banbare hannun benazeer daga wuyanta. Ta samu sa'a kuwa ta cire din,sai taja da baya tana tura baki gaba hadi da hararta

"Kina gani kina shaqemin wuyana?....bazanyi hoton ba ai uncle........." Bata iya qarasawa ba saboda dan juyawar da tayin idanunta ya fada kan maina. Dukka idanunta ta fiddo waje kamar zasu fado,ba wani jiran komai ta qwala kiran sunansa

"Uncle haidar!!!!....... benazeer kinga......zo kiga uncle haidar a gidanmu......" Da wani mugun sauri benazeer din ta juyo kuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login