Showing 204001 words to 207000 words out of 294767 words
Chapter 69 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Idanu ta fidda sosai ganinsa kwance dai dai abinsa saman gadonta,da alama ma ya fara bacci ne abinsa. Tsoro sosai ya kamata,ta kalli agogo,uku saura na dare,ta yaya zaiyi mata bacci a daki?,bata tsoron asuba ta riskeshi suje suyi kacibus da wani cikin gidan?. Cikin sanda ta dinga takowa har ta iso gefan gadon ta zauna. Idanunta suka sauka saman kyakkyawar fuskar nan tasa dake da wani irin kwarjini,ta qura mishi idanu tana kallon fuskokin su benazeer cikin tashi,wani lokaci kuma sai ta dinga hangen tata fuskar kadan kadan. A baya sanda yake matsayin uncle mafi soyuwa a gareta tafi kowa jin dadi idan akace suna kama,amma daga baya sai ya zamana muddin zaka ce suna kama da yaa maina to ka tarowa kanka masifa,ranan babu me rabata da kai sai Allah,ta dingi mita har sai bibi tayi kaman ta bugeta,amma sai gashi a yau din da idanunta tana hangen gaskiyar maganar quru quru.
Idanun ta janye daga kallonsa,tayi masa kallon da bazata iya tuna lokaci na qarshe data yi masa shi ba,idanunsa na ganin kyawunsa zuciyarta nata avoiding,zuciyar kuma na karbar wani saqo da batasan daga wanne guri ya taso ba.......amma taurin kanta da jin cewa ba komai game da ita daya shafeshi ya hanata yarda da hakan.
Maida dubanta ta sakeyi,da gaske lokaci yana tafiya,kuma awanni kadan suka rage lokacin sallar asubahi yayi,tayi imani kuma muddin ama ta samu maina a dakinta a yau dai ba ita ba kwanan paris,tana kyautata zaton saidai ta kwana a nijer.
Hannu takai zata tasheshi sai kuma ta janye zuciyarta na gargadarta da kuskuren tabashi,ta dunqule hannun nata tana wassafa yadda zata tasheshin,bata da wata mafita don haka ta sake kai hannu,saidai yanzun ma kuma janye hannun nata tayi kamar me tsoron taba wuta. Sake kallon agogon tayi, tafiyarsa yakeyi bai fasa rage tsahon mitunan da suka rage musu ba,sai ta sakejin hankalinta ya kuma tashi.
Motsi ta jiyo daga bakin qofarta kaman ana shirin mata knocking,ai batasan sanda ta sake kai hannu da zummar tashin nasa ba. Tattausan hannunsa da yayi wani dumi ya miqa ya jawo hannun nata da sauri ya aza saman kuncinsa sannan ya lullube bayan hannun nata da tafukan hannayensa. Da sauri ta dauke kanta daga kallon qofa da ta tafi yi ta dawo dashi kansa,saita samu zagayayyun lion eyes dinshin nan fes saman fuskarta yana kallonta da narkakkun idanun nan nasa da a yanzun suke matuqar bata tsoro. Kallon kallo suka yiwa juna na wasu sakanni,yana lumshe idanunsa yana kuma budesu dukka lokaci guda,shi daya yasan me yakeji a kanta,bai taba tsammanin watarana zai jarabtu da soyayyar 'yarshi ba,koda kuwa a wasa ne.....wancan lokacin..... wancan ranar da komai ya afku ya zame masa alkhairi. Kalmar FYADE shikam zai iya cewa alkhairi ce a tattare dashi,banda furtatan da tayi yayi imani da tuni a yanzun ita din ta zama mallakin wani.
"Kinason kallona amma gulma ya hanaki ko?......am aliyyu maina,not yaa maina da kika sani shekarun baya.....ni naki ne yanzun.......ba maina yayanki kuma uncle dinki da kika sani ba" sosai kalamanshi suka sauka a zuciyarta,amma kuma tana cikin tsoron da bata da nutsuwa
"Don Allah...... please na roqeka,ka tashi ka tafi tunda ka gama abinda ya kawoka..... inajin motsi kada wani ya shigo ya sameka a nan" ta fada a mugun narke sannan kuma a karye tana daga hannunta guda daya da bai samu ya riqe ba alamun roqo.
Sanda taga ya motsa ta zaci tashi zaiyi ya tafi,sai taga ma ashe dogara gwiwar hannunsa yayi saman gadon,ya kuma tallafe kumatunsa yana sake qare mata kallo. Yadda tayi masa shagwabar nan ta sake tsumashi sosai,ta kuma sake tuna mashi da little sultanarshi,wani shauqinta yakeji kamar ya dauketa ya boyeta a inda idanuwa basu isa sukai wajen ba
"Pleeeeassseee ya mai......"
"Uhmmm.......say it.....i missed the way you are calling me YAA MAINA" Ya fada yana lumshe idanunsa dake kafe har yanzu a kanta yana fidda murmushi. Kanta ta kawar, calmly yake magananshi kaman baisan wanzuwarsa a wajen bai dace ba,ta fahimci abinda ma take hange shikam bashi yake hange ba
"Please" ta sake fada a mugun karye ba tare data kalleshi ba. Hannunta dake cikin nashi ya matsa
"I love it......inaso naji kina begging dina......but ba'a irin wannan yanayin ba,ba kuma a irin wannan muhallin ba.........inason wata rana tazo da zaki dinga begging dina kaman haka akan kinaso na kasance dake......,mu raye wani dare......." Wani zabura tayi a gigice kaman wadda aka watsawa kunama,abinda ya sanya zancansa yankewa ba tare daya shirya ba saboda dariyan da yaso kamashi,waishi baya jin nauyin fadin maganganu har haka?,yana mantawa ita din wacece?,qaramar sultanar nan daya raineta?,yana mantawa ne wai?.
"Already na gaya miki af first,idan baki saurareni ba a nan zan kwana ai ko, right?" Da sauri ta juyo a hargitse da firigitattun idanun nan nata tana dubansa
"Na saurareka,tell me please" tsareta yayi da idanu kafin ya saki wani tattausan murmushi
"It's too late madam sultana......baki saurareni ba saboda rad'in kanki,kin saurareni ne don tsoron kada azo a ganki da kwartonki ko me miki fyade kullum?" Ya furta da wani qaramin murmushin,saboda xuwa yanzun kalmar ta zame masa wani abu na daban cikin rayuwarsa.
"No....." Ta fadi cikin nuna karaya
"Oya.....zo muyi bacci.....bazan iya gaya miki komai ba yanzun don bacci nakeji,kin gajiyar dani" ya furta duka lokaci daya yana birkitota cikin jikinsa.
Wani kyakkyawan boyo yayi mata cikin qirjinsa,ya bata skin to skin contact me kyau wanda ya sanyaya mata kowacce gaba ta jikinta,tsoron kada ya zamana wani ne a bakin qofar dakinta ya sanya bata ko motsa ba tayi luf,saidai kuma qirjinta bai fasa bugawa ba da tunanin ta yaya zai kwana mata a daki kuma ya fice daga gidan salin alin ba tare da kowa ya ganshi ba?,ta sanshi shi din fada da cikawa ne,tunda ya dauki aniyar kwana tayi imanin bata isa ta sauya masa ra'ayi ba,sai kawai ta maida idanunta ta rufe tana ambaton
"Rabbi sallim sallim" cikin qasar zuciyarta,tana jinsa sanda ya saki wata wawiyar ajiyar zuciya yana furta
"Thanks" da tausasashen sauti,yana tsammanin tayi shuru ne don ta bashi hadin kan samun nutsuwa da bacci me kyau,baisan meke yawo cikin zuciyarta ba,hanyar da zai fita daga gidan ba tare da ya kunyatata ya tona musu asiri ba.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 109
Tun kafin a kira sallar asuba ta tashi,ta daura alwala ta zauna tana raba idanu,amma a zahiri ta nuna kaman tana jiran ayi kiran sallar assalatu ne,a qasan zuciyarta kuwa tana fata ya tashi ne yayi alwala ya fice,ita koda baiyi alwala bama din indai zaibar mata daki buqatarta ya biya.
Yayi likimo kaman baisan meke faruwa ba amma yana sane din,ya danne dariyarshi kawai yana mamakin yadda tsabar rigimarta ta hana mishi barci itama kuma ta hana kanta,tanayin abune kamar wadda ta kawo kwarto. Yana sane ya sake miqewa sosai cikin duvet,bai kuma tashi ba sai da aka kira assalatu.
Hankalinshi kwance ya wuce toilet dinta,bai jima can can ba ya fito daure da alwala,ta bishi da kallo tana addu'ar ya fita amma sai taji yana bata umarnin ta shimfida musu darduma ya jasu jam'i. Da hanzarinta tayi komai tana zaton zai tafi idan sun idar,amma da suka idar din sai taga yayi zaman yin azkar din safiya. Nutsuwarta ta fara yin qaura daga gangar jikinta sanda taga alfijir yana neman ketowa,ta kasa azkar dinma gaba daya,sai idanu da take fama binsa dashi tana satar kallonshi.
"Ki nutsu kiyi azkar dinki,nima nan din gidanmu nefa,bawai baqo bane" ya bata amsa da dakiyar nan tasa yana kallon qibla ba tare daya dubeta ba. Duk yadda taso ta nutsu din ta kasa,saita soma sarewa sanda taji wucewar tanja har sau biyu zuwa kitchen. Dukka dauriyarta ta qare sanda taga ga kammala azkar din,ya miqe yana sake wucewa zuwa gadonta. Muryarta ta dauki rawa ta dubeshi
"Amma...... amma fa safiya yayi.....baka kalli agogo ba?" Girarsa ya dage mata dukka biyun sanda ya jingina da fuskar gadon
"Wannan ce gaisuwan barka da safiyan?" Nauyinsa kuma taji ya kamata,abinda ya kamata ace tayi ne batayi ba,sai tayi qasa da kanta don yadda ya tsareta da idanun ya mata nauyi
"Barka da safiya,ina kwana?" Murmushi ya sake kadan,yanajin inama zasu tabbata a haka ita dashi,sai ya miqa mata hannuwansa daga nan inda yake yana cewa
"Gaisuwan nesan nan bana sonta,zo kiji" ya furta yana lumshe idanunsa,feelings da yake samu a duk lokaci irin wannan yana motsa masa. Maslaha take nema,so take ta lallabashi ya fita tun aba da ama idanunsu baikai kai ba,don haka ta miqe a sanyaye tana takawa gareshi.
Da idanu yake bin kowanne taku nata,kowanne sashe na jikinta yana motsawa cikin wani salo kamar wanda ake bawa umarni,idanunsa suka qara qanqancewa,kishinta ya wani cikashi har ya dinga jin kamar zuciyarsa na matsewa. A hijab yaga dukka kyakkyawan surarta,ina ga sanda take cikin veil ko scarf?,ina ga sanda ta sanya abaya ko gown,anya kuwa zai iya ci gaba da xuba idanu?,xai kuwa iya tausa zuciyarsa yadda yaso yayi daga baya akan ya qyaleta ta mori karatunta?,aikin gidan tv fa?,abune da yake international ba iya state daya ba ba jaha daya ba na qasa baki daya.
Hannunsa ya sanya ya riqe dogayen siraran yatsunta yana kallonta,muryarsa tayi laushi sosai da wani irin duka da kishi yayi masa
"Please......ko menene,ko yaya ne sultana.....ki taimakeni,ki rufamin asiri ki killacemin kanki.....i swear bazan iya dauka ba,zuciyata me rauni ce a kanki,bazan iya jurewa ba naga wani ko wasu suna kallemin ke......" Bata yarda abinda yake fadi da gaske bane dai da yaja hannunta saitin qirjinsa,da gaske zuciyarsa bugawa takeyi,har abun ya bata tsoro ta janye hannunta da sauri tana kallon fuskarsa. Raunannen murmushi ya sakar mata yana kallon cikin idanunta
"Har yanzu maina shine nada,ba abinda yake sanyashi sauya magana.....so that kada ki damu da zamana dakinki don sai na qarasa hutawa.....karki damu ya waye zai ganni?,yaushe zan fita?,duk kada ki damu,ina da ragowar lokaci kafin na fita,zaki iya joining dina kafin lokacin walaha,karkiyi stressing kanki too much da tunani..... please" ya qarasa fada yana hade hannayensa waje guda alamun roqo.
Eh tabbas yaa maina na baya shine yanzun,wasu dalilai yasa take gani kamar ya canza amma bai canza ba din da gaske,ta saki baki tana kallonsa sanda ya shige duvet yana sake qudunduna da kyau,muryarsa can qasa ya sake cewa
"Join me please mummy twins" ji tayi kaman da gayya ma yake roqonta, saita dauke kai tana zamewa a wajen ta zauna sosai kaman me gadinsa,itadai tasan ya gama da ita,lallai yau da alama ranar shan kunyar su ne daga ita har shi ya kama,to amma zata iya cewa ita daya din,tunda shi koma meye zai faru shi ya jawo,kuma tunda yayi hakan tasan akwai abinsa ya taka.
Duk wucewar mituna tana irge dashi,rana na sake fitowa fargabarta yana qaruwa,ta dora kanta saman gadon a hankali tana kiran sunan Allah,fatanta daya ya tashi ya fice salin alin.
Knocking akayi wanda ya sanya 'yan hanjinta hautsinewa,tayi qoqari da qyar ta gyara muryarta qasa qasa,ta kalli inda yake kwance baima san anyi knocking din ba,ta sake maida dubanta ga qofar sanda ake qwanqwasawa Karo na biyu
"Waye?" Ta tambaya adan tsorace
"Mummy mune.....BB"
"Get out ko CC ne,da safen nan?,to ban tashi ba"
"Mummy ki bude mana don Allah,yau Halloween party ki duba mana kayan nan"
"Benazeer.......sa'arki ce ni?,zaku bacen a wajen ko sai na fito na bubbugeku?" Ta fadi a harzuqe tamkar su suka sanya daddynsu yayi kwance kwance a dakinta😂.
Tana jinsu suka juya jiki a sanyaye,ta zuqi iskar ta fesar tana ware idanunta,cikin ranta tana addu'ar Allah yasa kada yaran su matsa da yawa,kuma kada Allah ya kawo wani. Sau biyu taji sun sake wucewa da tanja zuwa kitchen,saidai ko motsi me qarfi taqiyi bare suyi tunanin idanunta biyu.
Awa guda ba kadan aka sake buga qofan,yanzunma dai a hasale ta soma magana
"Batoul ku fita a ido na fa?"
" Da sukayi me?" Taji muryar ama tana tambayarta daga bakin qofar. Wani gumi taji ya karyo mata
"Innalillahi" ta fadi da muryar rad'a tana ware idanu
"Tashina sukeson yi ama.... Kuma....."
"..... Kuma me?,yau baki da aiki ne?"
"Na dauki hutu ama sai next week ana gobe zan sake program" ta fada tana hadiye wani yawu me kauri a maqoshinta
"To yayi,kizo aba dinku yana kiranki......but kada ki wuce minti talatin don fita zaiyi"
"Gani nan ama" ta fada da sauri. Yadda take amsawar ya bawa ama mamaki,tadan tsaya jim
"Are you okay?" Ta tambayeta tana kallon qofar dakin
"Yes am....ama"
"Budemin qofar dai" ta fada tana jin bata gamsu da yadda muryarta ke fita ba kaman a tsorace.
Maida dubanta tayi ga maina a tsorace,hankalinsa kwance,hasken safiyar ya haske fuskarshi ta wani sake fresh.
"Sultana" ama ta sake kiran sunanta
"Gani nan ama ina saukowa daga gado ne....."
"Alright.....daga baccin kika tashi ashe.....karki zauna kizo kiran aba dinku" sai taji ama din ta juya tana barin wajen.
Ido ta lumshe tana yada kanta gefe hadi da sakin ajiyar zuciya
"Matsoraciya" taji ya fada da muryar bacci. Da sauri ta daga kai cikin mamakin dama duk abinda akeyi yana jinsu?. Tun bugun dasu benazeer sukayi suka katse masa baccinsa,sai baccin ya zama ba wani me nauyi ba,yanajin komai amma kwanciyar ta masa dadi shi yasa yaqi tashi. Idanunsa ya bude sai idanunta cikin nasa,ya ture duvet din ya miqe yana zama sosai saman gadon.
"Am starving......me zan samu?" Ya fadi yana lumshe idanunsa. Gaba daya zuciyarta ta karye,ya qarasa gigitata,sai kawai ta sakar masa hawaye. Ta yaya zaice zaici wani abu?,salon ta fita dauko masa wani ya shigo?.
Tsaiwa yayi yana kallonta,kaman bazaiyi magana ba sai ya rusunar da idanunsa yana cewa
"Banason kuka.......tashi ki shirya kije kiran aba"
"Ni a shirye nake" ta tari numfashinsa,sai kuma hankalinta ya dawo jikinta sanda taga yana bin jikinta da kallo. Tabbas yamutsewarta da yamutsewar jikinta kadai zai sanya ka saka mata ayar tambaya. Baice komai ba ya sauko ya a nutse daga gadon yana wucewa toilet,sai tayi amfani da wannan damar ta wuce wardrobe dinta tana laluba abinda zata sauya din.
Allah ya taimaketa ta shirya cikin sauri, doguwar riga ta saka daga ciki sannan ta dora babban hijab har qasa. Tana gyara madaurin fuskar hijab din ya fito daga toilet din,ta gefan ido ta saci kallonsa sai akaci sa'a shima ita yake kalla din,ta masa kyau qwarai,hijab din ya wani qara mata kwarjini sosai,ta dauke idonta tana qoqarin gyara igiyar,sai yayi taku hudu ya qaraso gareta. Hannunsa ya sanya saman nata,dumin hannunsa ya ratsata,sai ta zame hannunta da sauri,hakan ya bashi daman gyara igiyar ya daura mata ita saman tulin gashinta data nannade ya zamana kamar ribbon ta sanya.
Ta saman kafadunta ya zura kanshi yana kallon kyawawan idanunta ta cikin madubi
"Zaki tafi baki sake tambaya na me nakeson gaya miki ba.......well,na cinye abuna nima......yanzun ace aba ya tambayeki idan kinje......me ya kawo aliyyu dakinki yake kwana wanne amsa zaki bashi?" Ji tayi kaman a gaske aba dinne yayi mata tambayar,saita juyo a rude suka hada idanu,ta dauke kanta kuma da sauri tana jin tana dirircewa.
Murmushin gefan baki ya saki, yayi taku biyu da baya da baya
"If kuma ya tambayeki kinason maina?,zaki koma dakin mijinki?,wanne amsa zaki bashi?" Ya jefa mata tambayar yana kallon reaction nata ta cikin madubi. Qin daga idanunta tayi bare ya samu damar kallon qwayar idanunta,abu daya taji har cikin jininta ya jefeta da wata magana me girma. Ta qarasa ta zira slippers dinta ta soma takawa a hankali shi kuma idanunsa yana biye da ita,ta tsaya cak sanda ta isa bakin qofa,ba kuma tare data waiwayo ta dubeshi ba tace
"Zan gaya masa bana sonshi......ban kuma taba sonshi ba,bazan kuma koma ba.....idan zaka fita daga dakinnan kayi qoqari kada wani ya ganka please" daga hakan kamar wadda ke tsoron za'a kamata ta taka da sauri tana fita a dakin.
Qas yayi da kansa yana jin maganarta na shiga ranshi,baiga fuskarta ba bare ya karanceta ta cikin idanunta,saboda haka bashi da tabbas din abinnan da take gaya masa gaskiya ce ko qarya tsagwaronta,koma meye take fada yaji saukar furucinta sosai,wani qaramin murmushi da baisan a wanne gida ya ajeshi ba ya qwace masa
"Saina sanyaki kin qaryata kanki da kanki