Showing 258001 words to 261000 words out of 294767 words
Chapter 87 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
ba, so me sunan so wanda ya gunshi sadaukarwa abota da kyakkyawar fahimtar juna .....wannan ya sanya a tarihinsa bai taba budurwa ba a baya.....ba wanda ya isa yace ga budurrsa..... don kowacce mace ya kalla sal yaga kaman ba zata bashi abinda yake bugata ba ta hanyar haquri dashi ta kuma mallaka masa zuciyarta da rayuwarta dama gangar jikinta gaba daya...... auren dole yana daya daga cikin abinda ya yiwa mummunar tsana......ya kuma yiwa kansa algawarin bazai taba auren macen da babu soyayyarsa cikin zuciyarta ba
"Ki sake gayamin me kk bugata haidar zai kiyaye...."
"Idan nace kai nake bugata nayi daidai banyi kuskure ba?" Ta gwada fadi cikin zuciyarta, saidal a fili kuma idanunta ta lumshe. Batasan ya zatayi masa bayani ba.....batasan yadda zai fahimceta ba ba tare data furta komai ba.
Bell din da aka kada ita
ta katse komal a tsakaninsu, ya waiwaya a hankali yana duban qofar kafin ya dawo da dubansa kanta
"Wipe your tears please baby gurl.... kada na je su ama ne ki sanya suyimin dukan tsiya..... naga har yanzu basa yina kedin dai ke sukeyi" ya fada yana dan ranqwafawa kadan ta saman kanta kamar me rada mata bayason wani yaji abinda yake fada din.
Jikinta ya bata su batoul ne, don kamar tana dan din muryarsu kadan kadan, ta jawo tissue tana sake tsane idanunta tare da gyara zaman mayafin kanta tare da gyara zamanta.
Ihun da suka saki yaran
ya sanyata duban bakin qofar bata shirya ba, dukka sun saki kayan hannunsu sun dane uban, shi kuma ya dagasu dukka su biyun kamar bayajin nauyi da girman da suke sakeyi kullum. Ya diresu suna gaidashi, benazeer tadan bata fuska tana cewa
"Ina mummy?" Da yatsa ya nuna musu ita, sannan ya ranqwafa a tsakiyarsu gasa gasa yana cewa
"Kuyi magana a hankali mummyn batason hayaniya......kuzo mujeku tayani bata haquri, wai haushina takeji" ya furta shima kaman garamin yaro yana dan bata fuska.
Agaba ya sakasu har
suka isa gabanta, sun tsareta da idanu kamar yadda itama ta tsaresu da idanun, sai ta bude musu hannuwanta, da gudu kuwa suka fada kanta.
"fais-le soigneusement (yi a hankali), karku buge baby" ya fada yana janyesu daga saman gafafunta.
RA
Batoul sarkin magana ce ta
daga kai da hanzari ta kalleshi
"Daddy ina babyn?" Ta fadi tana zare idanu. Hannunsa ya dora daman cikinsa sannan ya nuna mata sultana. Tsalle ta buga tana rigeshi da kyau
"Baby zata siyo mana daddy, mu xama mu haka?" Ta fadi tana daga yatsunta guda hudu.
"In sha Allah" ya fada yana murmushi. Harara sultana ta jefawa benazeer sanda ta juyo da niyyar mata tata tambayar, hararar ta sanya benazeer ta tsuke bakinta tsaf, daidai nan goumar ya shigo da sallama.
Zuwan nasu shi ya sake debe mata damuwa me yawa, tayi yogarin sakin jiki dasu, yayin da goumar uban tsokana yaketa son kwasarta amma kuma idanun maina ya hanashi. Duk motsinta akan idanunsa yake, ya lura kuma tana sane tana basarwa ne, kaman batason kallon idanunshi ne bataso kuma shima ya kalli nata.
Tare sukayi sallar magariba cikin falon dukansu, yana kuma sane ya hanasu tafiya da wuri ya jasu har magaribar saboda ita.
Bayan sallar magaribar abincin da yayi musu order daga wani gidan abinci ya iso. Kowa da zabinsa, ta mige ta wuce kitchen yaran suka bita don dauko spoons da plates, sai ya bisu da kallo yanaji a ransa Inama wannan yanayin ya dore har abada?. Sanda ya dauke idanunsa sai suka hada ido da goumar, dariya ta tasowa goumar din amma ya toshe fuskarsa da wayarsa, sai ya zabga masa harara yana dauke kanshi.
"Ka shirya Next week ko upper week zamu wuce Nigeria, ina tunanin adadin bukukuwan zasu dadu, so nake a hade bikin duka lokaci daya idan zai yiwu" maina ya fadi yana bude wayarsa da sago ya stigo, daidai sanda kuma take fitowa ita da yaran daga kitchen din
"Bukukuwa yaa maina.....bikin waye?"
"Ka fito da passport dinka kawai, ka gayama ama ta fiddo nasu benazeer zan duba mana ticket, idan munje zaka gani"….*_GUDUN KADDARA_*
*HUGUMA*
B00K 02 PAGE 138
Goumar daya ga isowarta
gurin ya daga kanshi ya kalleta, suka hada idanu saita kauda kai tana ajjiye abincin data dauko musu a hankali.
"Mun gode" goumar ya fadi cikin sanyin jiki. Dukka juriyarta da yogarinta ta tattaro ta aza saman fuskarta ta kuma fidda murmushi
"Aunty najma zata biya bagin buzu" duk da yana cikin yanayi na rashin
Jin dadin zuciyarsa amma sai daya maida mata murmushinta. A nutse kaman bataji komal ba ta juya, duk kuwa da cewa zuciyarta na wani irin rawa.
"Zan shiga daki zaku zauna wajen uncle goumar?"
"Zamu biki dakin" benazeer tayl saurin fada. Bata hanasu ba suka bita a baya, benazeer tana gaba batoul na binta a baya ita kuma tana bayansu.
Ko cikin dakin sun sake abinsu sunata dara, tana zaune kawai tana binsu da kallo, yayin da zuciyarta tayi nisa sosal da gangar jikinta. Tana jin wani rauni yana mamayarta, da gangar ya kasa fatimtar ta?, ko kuma da gaske yake bai fahimceta din ba?, zata kuwa iya jurewa wannan hukuncin da ya yanke musu me gaba daya ita dashi?.
Qarar wayarta ya dawo da ita hayyacinta, ta kalli wayar daga inda take zaune, abun mamaki sai taga goumar ne, ranta ya bata ko akwai wani abu me muhimmanci ne ya sanyashi kiranta.
Da sallama a bakinta cikin
raunanniyar muryarta, ya amsa sal kuma shuru ya biyo baya tsakaninsu
"Sultana" ya kirayeta da sunan data manta rabonshi da kiranta.
"Na'am" ta amsa masa a sanyaye.
"Kinsan waye maina kuwa?" Yayi mata tambayar da ta rasa abinda zata ce masa, sal shuru daya ratsa a tsakaninsu
"Why sultana?..... me yasa ba zaki yafe ba?, me yasa komal bazai wuce ba?, me yasa ba zaki bayyana masa soyyaya ba?.. kinsanadadin yadda yaa maina yake mutuwar sonki?, kinsan yadda ya daukeki a rayuwa?, kinsan adadin soyayyar da ya baki?, kinsan iya matsayinki da matakinki a rayuwarshi?.......
yana bugatar wata soyayya wadda bata uwa ba....yana bugatar wata soyayya wadda bata 'ya' yanshi ba..
...sultana pl......
Maganarsa
ta yanke sanda take jiyo muryar maina ta cikin wayar, da alama ya shigo gurin da goumar din yake zaune, alamu kuma sun nuna baya wajen sanda yayi kiranta
"Ki turo su batoul zamu fita" goumar ya rufe maganar tashi da wannan.
Sauke wayar tayi tana
jin idanunta suna mata zafi, kuka takeso tayi amma kuma batason ta karya farincikin da yaran suka samu ta sanadinta.
"Kowa ya sanya cap dinshi, uncle goumar yana kira" da saurinsu suka maida p_caps dinsu da suka cire garin tsalle tsallensu, suka kuma ruga suna rige rigen fita daga dakin.
Rub da ciki tayi qwalla na silalo mata, da gaske ne dukkan abinda goumar ya fadi mata?, da gaske ne komal goumar ya fadi a kanshi tattare da ita?, ta yaya ya kamata ta fuskanceshi?.
Da wannan tunanin ta
dinga juyi saman gadon tana tuna abubuwa da yawa cikin kanta. Tun tana zuba ido tana lissafin sanda zataji motsin dawowarsu har taga
dadewar tayi yawa, tun tana kawaici har sai data daga waya ta kira goumar.
"Yanzun muka wuce gida, ama tace mu dawo dare yayi"
"Ku gaisheta" ta bawa goumar amsa
tana aje wayar.
Minti goma minti ashirin
minti arbain shuru bata ji motsin
dawowarsa ba, har ta share awa daya awa ta biyu ta wuce. A hankali wannan kasalar tayi mata rubdugu a jikinta, wani nannauyan bacci da bata shiryawa zuwansa ba ya ziyarceta, baccin da bata farka ba sai washegari daidal sallar asuba.
Ko da akayi sallar asuba
ma wani irin bacci ne ya sake surarta, saidai duka duka bata wuce awa biyu ba ta farka. Toilet ta shiga tayi wanka, ta tito ta tsaya gaban madubi tana duban lotion din da take amfani dashi. Ta budesti amma kuma ta kasa tabuka komal, qwagwalwarta tanata wassafa mata yadda zata fuskanceshi.
Handle din dakin ta ji an murza sannan aka tura gofar aka shigo. Aliyyu maina ne cikin wasu suit da suka karbeshi matuga da gaske.
Tsahonshi da mur jewar jikinsa dukka sun bayyana. Sumarnan baga sidik tanata shegi saboda gyaran da take samu a kowanne lokaci. Lion eyes dinnan nasa yau fes suke, sun sake wani haske da kuma girma kaman ya diga musu wani abun.
Sallama yayi yana motsa jajayen labbansan nan masu daukan hankali idanunsa tsaye car saman girjinta da ya zauna sosal, gefe guda kuma yana kokawar dauke idon nasa gudun kada ya kasa sauke abinda ya niyyata.
Muryarsa kawal ta saka
zuciyarta tayi rauni, amma duk da haka ta hana hakan bayyanuwa saman fuskarta. Ta jawo towel tana dorawa saman kanta ta yadda zai lullube mata kafadunta da girjinta da suka fito tana amsa sallamar.
Rarasawa yayi a nutse ya ajJiye complete kayan breakfast din daya shigo mata dasu kaman yadda ya saba "Ina kwana?" Ta gaidashi tana fatan samun damar yin wata maganar daban dashi bayan galsuwar
"Kin tashi lafiya?" Ya bata amsa cikin nuna kulawa, can yasan ransa kuma yana jin ba dadi kan yadda ta haramta masa ganin kyakkyawan fatarta dake gara wani sulbi da
"Athamdulillat"
"Zan fita.....
•zan zama busy sosal a
kwanannan.....idan kina da wata damuwa ko wata bugata kiyi magana akai" ya furta cikin salo na bada dama gareta. Bakinta ta motsa tanason tayi magana amma sai ta kasa furta komai din, ya motsa kadan yana cewa
"Abdulhamid zai kula da
abincinki in sha Allah, duk sanda kk da bugatar wani abu let me know... zaki iya serving abincinki da kankiko?, ina sauri zan iya makara" kai ta gyada masa, sai ya juya a hankali yana furta
"Fi amanillah" da idanu ta bishi har ya fice daga dakin, tana jin kamar ta dawo dashi ta zaunar dashi a waje daya.
*****Kamar yadda yace mata ne, cikin kwanakin duka busy din yayi. Amma hakan bai hanashi dubata da safe ba. Sau tari kuma Lokacin da zai dawo wani kasalallen bacci yayi awon gaba da ita, don haka bata sanin lokacin da yake dawowar.
Duk yadda takeson space takeso kuma ya bata sai wannan abun ya gundureta, ta dinga blaming kanta da kanta, me yasa?, wal me yasa?.
Duk da yanayin da take ciki me wahala amma hakan bal hanata hada program dinta ba. A ranar da ya zamana washegari ne ranar da zata shiga Tv station, takai har garfe goma na dare a zaune tana hada komai cikin laptop dinta. Ta kammala ta tattara komal ta aje gefe tana duba agogo, baccin da takeyi da wuri ne kenan ya sanya bata gane daren da yakey kafin ya dawo gidan ba?.
"To ina yake zuwa?, har yakeyin dare?" Ta yiwa kanta tambayar.
"Laila......ayana" ta tuna
sunayensu, wani abu kuma ya darsu a zuciyarta, abinda ya sanyata taji kanta ya Sara kenan, ta saka hannunta daya tadan tallafi kan nata tana lumshe idanunta.
Tsation mintuna goma
sha biyar tana zaune a haka ta ji garar motarsa. Ta sauke hannunta a hankali tana kallon yadda hasken fitilun motar ke ratso labulayen dakin nata. Tana iya jin muryarsa gasa yasa da alamu waya yakeyi, ranta ta ji ya sosu, ta maida idanunta ta lumshe sai kuma ta mige tana wucewa toilet.
Fitsari tayi don a yanzun
ba wani rige fitsari takeyi sosai ba, sai kuma ta daura alwala kaman yadda ta saba duk sanda take da niyyar yin bacci, ta dauko garamin towel don tsane damshi sannan ta nufo waje.
Yana tsaye tsakiyar
dakin, hannunsa guda cikin al jihun wandonsa, dayan kuma dauke da wayarsa yana dannawa. Suit dinshi na saman yana rataye a kafadarsa. Haske wayar ya haske mata gajiyayyun qwayar idanunsa da suka rusuna saboda gajiya
"Sannu da zuwa" ta fadi a hankali tana sake takowa xuwa bakin gadon.
A jyar zuciya ya sauke yana saka wayar a aljihunsa
"Yauwa, fatan kin wuni lafiya"
"Alhamdulillah" ta bashi amsa
"Yau bakiyi bacci da wuri ba kenan?" Ya tambayeta yana duba abincin da abdulhamid ya dafa yau din.
Baki ta murguda tana harararshi gasa gasa. Bashi da aiki sai labta mata abinci?, ya temperature din jikinta yake?, yata wuni?, tasha maganinta ko a'ah, wannan duka suje abinda take da bugata? baisan yadda tayi missing gamshinsa ba?, baisan yadda tayi missing dumin fatarsa ba?, baisan yadda tayi missing air jinsa ba?, zazzafar rungumar dake bata peaceful sleep data jima bata sameshi ba?.
Bata wani ci abun kirki ba, sal ya dago wayar idanun nan nashi masu kwarjini yana dubanta sanda take amsa masa ciki ciki da cewa
"Eh
"Me yasa bakici abinci yadda ya kamata ba?, kinaso ki haifa baby garami?" Ya mata tambayar seriously. Yadda ya tambayetan da kaifafanidanunsa ya sanya ya mata kwar jini, ta kuma ji wani nauyi ya saukar mata, saita kauda kanta ba tare data amsa masa ba "Lafiya kike yau?"
"Eh" ta sake amsa masa a tagaice, shima sai ya jin jina kai
kawai
"Ba wani abu?"
"Eh" ta kuma ce masa wannan karon har sai daya tada kai ya kalleta sosai. Idanu ya zuba
mata, kamar zalyi magana sal kuma ya fasa, ya juya a hankali yana
cewa "Allah ya bamu alkhair...
well"
... sleep
"Ina da aiki gobe" ta fada tana rige gugunta da hannu daya, ta fadi kai tsaye ne da haushin ya kasa fahimtar ta, ta kuma fada kai tsaye da fatan haushi da bacin ran da takeji cikin zuciyarta shima ya ji irinsa. Ta dade da sanin ba abinda yakewa yiyayya irin aikinta, shine kadal kuma abinda zal bata ranshi.
Juyowa yayi kadan ya kalleta sai kuma yace
"Allah ya kaimu, Allah ya kiyaye hanya" ya taka a hankali yana ficewa daga dakin.GUDUN KDDARA
Chapter: B00K O2 PAGE 139
*_GUDUN KADDARA_*
*HUGUMA*
BOOK OZ PAGE 139
Da kallo yabi bayanshi
har ya fice, sai abun yayi mata banbarakwal. Bata taba zaton haka daga gareshi ba, bata taba zaton zaya ce mata ta je haka kai tsaye cikin saugi ba, saita zame tana zama daga gefan gadon tana hadiyar wani abu ranta yana sake baci.
** **Ita daya ta gama shirinta washegari cikin gidan, don ko abdultamid bai bari ba, yana gama ayyukanshi ya sanyashi a gaba, sai daya fita sannan shima ya fice. Tana dining area tana wassafa yadda zataci abincin, duka ranta a jagule yake kiran goumar ya shigo mata.
"Ki fito na saukeki, ina gofar gida" ya furta, mamaki yadan kamata, motarta na gidan ama, tayì zaton zatabi train ne kawai ko bus, tana kyautata zaton shine ya aiko goumar din. AjJiye yin breakfast din tayi ta dauki handbag dinta da sauran tarkacenta ta tito. Kaman basuyi kowacce magana ba jiya suka gaisa da goumar, saidai kuma ba wani
karsashi tsakanin shi da ita ko wani dogon hira ko tsokana kaman yadda suka saba ya dauki hanya da ita.
Har office sai daya tabbatar ya rakata, sannan ya karbi time da zata tashi ya fice yabar ma aikatar.
Ta tabbata ta kuma yarda
yau din a rude take, tarin kusakural ta dinga tafkawa wa jen alwatar da shirin, ta rasa nutsuwarta sam, wannan ya sanya dole aka haqura da sanya saka sabon shirin suka sanya malmalci na wancan satin.
Daidai lokacin daya dakatar da duk wani aiki da yakeyi cikin office din, ya kuma kunna tv zuciyarsa na wani irin zafin tururin kishi, yana wassafa wanne irin kyau ne yau zatayi?, mutum million nawa ne a fadin duniya zasu kalleta?, zasuji muryarta?, za kuma su kira suyi magana da ita.
Maimaicin da yaga an
sanya ya bashi mamaki tare da tambayar kansa me yake faruwa, ya dinga sauke a jiyar zuciya shi daya kaman yaron da yayi kuka ya ga ji.
Agalla ya samu relief tunda ba ita din bace live kamar yadda aka saba.
Banda kakkauran warning din aba gareshi ko duk duniya zasu taru baiga wanda zai sanyashi barinta yin wannan aikin ba.
Kasa kashe tv din yayi, yana kallonta kallon daya jima bai mata shi shi da ita ba. Ya fidda wayarsa ya fara kiran goumar.
Yau ko dioura kasa doguwar hira tayi da ita, tadai tabbatar musu bata da lafiya.
Hankalinsu duka ya tashi don basu taba ganin irin wannan yanayin tattare da ita ba. Ita daya ta wuce office din tana yogarin daidaita kanta. Ba jimawa kiran goumar ya shigo mata, ta bashi tabbacin ya shigo kawai su tati.
**** ***Kusan tafiya ce data shafi dukkansu, aba ama dashi kanshi maina din. Sati biyu kacal ya rage bikin goumar din da najma, goumar din kuma yafi garfin aike a wajen ama. Yana cikin mutane dake da muhimmancida daraja a wajenta, don haka ta yanke datse komal nata su kuma wuce nijer da wurwuri don a shirya komal tare da ita.
Sosal tayi mamaki da maina ya gaya mata zasu wuce ni jer tun a satin, sun tattauna sosal dashi,ya kuma shaida mata da benazeer da batoul da goumar din duka zasu wuce. Ganin kusan kamar cikin ayari ne tafiyar ya sanya ama tayi cancel din nata schedule din, ta siya nata ticket din, wanda tuni aba yayi gaba don akwai abubuwan da zai gabatar a Nigeria cikin abuja.
Ita dinma an samu banbacin lokacin tashinsu da kwana daya, ama zata riga tashi, su kuma washegari nasu jirgin zai tashi.
*** ** **A hankali take takowa cikin shigar bagar abaya me sulbi da tayi mata wani irin mahaukacin kyau, kyau irin na yaron ciki da kuma kyau irin na asalin halitta ga wanda Allah ya bawa. Duk jikinta bata jin dadinsa wannan ya sake sabbaba yaugi a yanga a komal nata wanda zaka zaci tana sane takeyi. Har yanzun jikinta yana bata tabbas tafiyarsu Niger ba haka siddan bane. Uwa uba yawan wayar da suketa yi da suhail da kuma sardauna abun ya wuce yadda suka saba. Dukkansu haushinsu takeji, tana danne zuciyarta ne kawai suna galsawa dasuidan har sun hadu bisa dole. Tayita zuba kunnuwa da ido ko zataji wani abu daga wajen ama amma shuru... hakanan tayita kasa kunne kozataji aba ya kirata shima bataji komai daga gareshi ba. Gefe bibi da take