Showing 30001 words to 33000 words out of 294767 words

Chapter 11 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

cikin office dinta ta tambaya

"fièvre ne me zafi,dashi ta dawo daga école(school)"

"Subhanallahi,idan yayi zafi da yawa ki samu mouchoir(handkerchief) me kyau da ruwa a goge mata jikinta,gani nan na tashi gida zan wuce dama,zan qaraso na dubata"

"d'accord(okay),amma ina neman alfarma,zan saka motocin mayak'i yanzu suzo su taho dake,je ne veux pas de retard(banason jinkiri)"

"Hakan yayi ba damuwa" wayar dukka suka ajjiye.

Idanunta a lumshe,yadda jikinta ke zafi da quna haka zuciyarta,tana jin sanda ama ta iso da ruwan da qaramin towel ba tare data nema kowa ba

"Tashi a goge miki jikin sultana la fièvre est si élevée(zazzabin yayi yawa)" kai ta girgiza a hankali sannan tace

"A kiramin bibi,bibi nakeson gani"

"Za'a kirata,amma a ragewa jikin naki wannan zafin kada tazo ta gani hankalinta kuma ya tashi,ko kinaso hankalinta ya tashi kuma?" Kai ta girgiza a sanyaye,sannan ta yunqura ama na riqe da ita ta zaunar da ita sosai ta rage mata uniform din,ya zamana daga half vest din da ta soma kare martabar qirjinta da su,sai gajeran wando mahadin vest din. Sam ba wani kunya tsakaninta da ama,don ta zama tamkar uwar da babu shamaki a tsakaninsu. Tana goge mata din ta kirayi layin tanja donta kira bibi din bata sameta ba,tace ta shaida mata sultana ke rigimar son ganinta yau kuma,ta tashi da wani dan zazzabi. Tanja din ta amsa mata sannan ta kashe wayar ta maida saman drawer.

Tana gama goge matan akayi knocking qofar sannan aka turo. Bibi ce sanye da lallausan abaya cotton 'yar marocco ta mata me hade da mayafi.

Ama ce ta amsa mata tana miqewa hadi da tattare towel da roban ruwan,ta kuma jawa bibi kujera zuwa gaban gadon da sultana ke zaune.

Idanun bibi qur cikin na sultana bayan ta daidaita zamanta saman kujerar,sannan a hankali ta maida dubanta ga qirjin sultanan wanda ba baqonta bane.

Wata mummunar faduwar gaba ta samu kanta da ita

"La haula wala quwwata illa billa" ta fadi qasan zuciyarta,sannan ta janye idanunta ta juya zuwa ga ama dake qoqarin saqale towel din jikin qofar toilet

"Me ya sameta?"

"Zazzabi ama,daga tafiya makaranta"

"Zazzabi kawai?,kuma iya yau?" Ta tambayi ama cikin mamaki a sautin muryarta

"Wallahi bibi,kuma koda safen lafiya lau ta shiga ta miki sallama nima tayimin sallama,sun dawo nasa azo dubata su bilki suka samu qofanta a rufe,sai da na sauko dubata na sameta kwance" aman ta yiwa bibi bayani dalla dalla. Kai kawai bibi ta jinjina jikinta yana wani irin sanyi,dukka gwiwoyinta kamar an bubbugesu,wani irin fargaba ya cika mata zuciya,ta samu kanta tana furta addu'a can qasan zuciyarta......dai dai lokacin aka shaidawa ama isowar Dr chafa'atou wadda drivern mayak'i mansion ya daukota.

"Kiyi mata iso ta shigo" tace dame aikin nata tana komawa opposite bibi tana zama itama,jikinta yana sanyi da ganin sauyawar reaction na bibi cikin tambayoyin da tayi mata.

Har qasa Dr chafa'atou ta tsugunna ta gaida bibi. Sannan ta qarasa gaban sultana tana kallonta.

Kallo na kusan minti guda,kallon da ya sanya sultana janye nata idanun daga kan Dr chafa'atou,haushi yana cikata duk da ciwon da takeji a dukka gabobinta,don meye zata sakata gaba da kallo kaman taga wata dodo?.

"Bayan zazzabin kinajin wani abu dabanne?" Dr chafa'atou dake qoqarin bude dan akwatin aikinta ta fada. Da qyar ta motsa lallabanta ta bata amsa a gajarce

"Babu"

"Okay.....yaushe rabon da kiga period dinki na qarshe?" Tambayar da ta sake sanya razani me yawa a zuciyar bibi,ta kuma saka ama barin abinda takeyi tana duban Dr chafa'atou da batasan ma duka suna kallonta ba,don ita nata zargin yayi wani waje daban,don haka ta yankewa kanta yin abu guda daya da take da babban zato a kansa ba tare data batawa kanta lokaci ba.

"Bana tunanin zata iya riqewa,don kwata kwata al'adarta ma ina jin batayi yakai sau shida ba,niketa qoqarin tsara mata calendar dinta da sanar da ita lokaci donta dinga kiyayewa" bibi ta yiwa Dr chafa'atou bayani tana dubanta

"Okay ba matsala" ta amsawa bibi bayan ta gama fidda container dinta

"Kina Jin fitsari?" Ta tambayi sultana tana kallonta

"Kadanne"

"Yimin shi a nan koda dan kadan dinne" sai ta miqawa sultana container din.

Daga bibi har ama bin container din sukayi da.kallo,dukkansu sunsan gwaji akeyi da ita,kuma batun gwajin fitsari wani al'amari ne me zaman kanshi

"Amma ba fièvre du paludisme(zazzabin malaria) bane Médecin?(Dr)"

"Yanzun zamu gani in sha Allah hajiya" ba wanda ya iya sake cewa komai. Dr chafa'atou dince ta riqe hannun sultana har qofar toilet sannan ta dawo tana fidda kayan gwajinta. Duka duka bata wuce minti daya ba ta miqawa Dr din kwalbar ta koma saman gadon ta lafe tana rufe idanunta,don a yanzun babu abinda takeso da qauna irin ta ganta a kwance,cikin daki me qarancin hayaniya irin haka.

Duk motsin Dr chafa'atou suna biye da ita,har zuwa sanda ta kammala tsatsube tsatsubensu na likitoci,ta daga pt strip din da ya bayyana komai dara dara yana sake bata haske.

Saukeshi tayi tadan saci kallon ama da bibi,akaci sa'a dukkansu idanunsu yana kanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna,ita kanta tana jin fargabar bayyana sakamakon gwajin,amma kuma har kusan hada baki ama da bibi sukayi wajen tambayarta

"Ya dai?,an kammala?" Kai ta gyada musu,ta aro dukka jarumta da dauriya irin ta likitoci sannan tace

"JUNA BIYU GARETA!" Dif wutarsu ta dauke na dan wani wucin gadi,haka kunnuwansu suka tsaya da aiki na wucin gadin,kamar yadda kwanyarsu ta daina banbance saqon da aka aika mata dashi na wasu daqiqu. SULTANA dake a kwance kuwa taji dukka kalmomin Dr chafa'atou,amma abu daya zuciyarta da kwanyarta ta gaya mata

"Bafa dake take ba,magana take akan wata" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata zuciyar na wani irin mugun bugu kamar ta balle daga qirjinta

"Kin duba da kyau kuwa Dr?" Ama data tattaro dukka sauran maqalallen busashen yawun dake saman halshenta ta fadi

"Na tabbata,a yadda kuma ya nuna shi sosai bana tunanin ma yana qasa da wata daya ne"

"Mun gode kawai Dr,tattara kayanki kije,banda rainin wayo ta yaya zaki kalli kaman sultana kice tana da ciki?, shekara sha ukun?,lallai na yarda da akace wani lokaci qwqwalwarku tana tabuwa" bibi ta fada da wani irin yanayi da zai gaya maka lallai ba cikin hayyacinta sosai take magana ba.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 page 16


"iya abinda na gaya muku hajiya bana tunanin akwai son rai a ciki ko kuma ba dai dai ba.....dukkanmu munsan me ya faru,ina ganin ba abu bane na mamaki don ance ciki ne da sultana ba......" Ta qarashe fadi cikin tausasa harshe da kuma dukka yunqurinta nason ganar da bibi abinda ke wakana.

Wani irin gumi ne yake yanko musu su dukka. Yayin da sultana dake kwance taketa qoqarin fasa maganar Dr chafa'atou cikin kanta. Wanne irin ciki take nufi tana dashi?,shin mene ne ma cikin wai?. Wani muguwar razana tayi sanda tunaninta yakai inda ya kamata yakai din,ita kanta batasan yadda akayi ta isa gaban Dr chafa'atou ba bare bibi da ama dake zaune kowanne jinin dake jikinsa nason daskarewa.

Kyakkyawan riqo ta yiwa Dr chafa'atou, muryarta da wani irin galabaitaccen amo......fararen idanunta da suka sauya launi dukka sun fito waje tana duban Dr chafa'atou,hucin da jikinta ke fitarwa bai damunta ko kadan

"Ba Bibi tace ki tafi ba?,me yasa kikeson sake jefani cikin halaka?" Ta jefawa Dr chafa'atou tambayar

"Don Allah medicin kice ba haka bane.....kice kuskure kikayi......me nayi miki zaki jawomin wannan abun?,ta yaya zan iya haihuwa?,kinga cikina fa dan qarami ne amma kike cewa wai ciki ne dani?" Ta sake fada tana sakin Dr chafa'atou,sannan taja da baya da wani irin hanzari tana tattare rigar jikinta har saman qirjinta,plate tummy dinta wanda ke shafe hade da bayanta ya bayyana. Daga jajayen idanunta tayi tana maida dubanta ga Dr chafa'atou dake tsaye tana karantar yadda kwanyar sultana din ke shirim birkicewa

"Kinga cikina?,ko plate din abinci daya bazan iya cinyewa.....amma kikayi qarya kikace ciki......." Bata barta ta qarasa ba ta sanya dukka hannunta a tausashe ta jawo sultana cikin jikinta ta rungumeta tsam

"Kiyi haquri......wasa nake miki,kinyi qanqanta sultana,har yanzun ke yarinya ce" ta fada muryarta na rawa,tsananin tausayin sultana yana taba zuciyarta yana ratsa jikinta.

Daga bibi har ama gaza riqe hawayensu sukayi. Hawayen tausayin sultana,ta yaya zata iya karbar wannan qaddarar da qananun shekaru irin haka?,ta yaya zata iya fuskantar wannan qaddarar cikin rayuwarta?,ya rayuwarta zata zama?,ciki a shekarun da duka duka basufi sha uku zuwa sha hudu ba.

Sun jima a haka dakin tsit,bakajin komai sai sheshsheqar kukan sultana,wanda tun tanayi da ragowar qarfin da ya ragewa jikinta har ya zama bata iya koda motsi saboda wani mahaukacin zazzabi da yafi na baya daya sauko ya rafketa.

Cikin hanzari Dr chafa'atou ta fara bata taimakon gaggawa don kada zafin zazzabin ya kaita ga convulsion musamman da yake ba ita kadai bace,zazzabin zai iya zama illa ga abinda ke mahaifarta,duk da cewa ta lura har yanzu bibi ko kadan bata yarda da abinda ta gaya musu ba.

Kimanin awa daya kafin bacci ya dauketa,don Dr chafa'atou ta sanya ruwan allurar bacci cikin ruwan,saboda a yanayin da take ciki yanzu bacci ne kawai maslaha.

"Zan wuce,Allah ya bata lafiya,saidai koda baki yarda da abinda na fada ba yana da kyau a kula da lafiyarta,a sake gujewa sanyata damuwa" tayi musu taqaitaccen bayani dukansu da ama da bibi din.

Qwaqwwaran motsi aka rasa wanda zaiyi a cikinsu,ta tafi ta barsu da tarin tunane tunane qulle qulle da kuma kwancewa. Ita dai ama bata da abinda zata iya cewa bibi,maina ya tafi ya barta da dukkan wani nauyi da kuma kunya. Yayin da Bibi take juya maganar Dr chafa'atou wadda take jinta kamar a duniyar mafarki.

Shigowar aba dakin shi da goumar shi ya katse shurun da yake wanzuwa a dakin tsahon wani lokaci. Dukka suka daga kai suna amsa sallamar tasa yayin da nashi idanun suke kan ledar ruwan dake shiga jikin sultana.

"Dama bata da lafiya?" Yayi tambayar wa bibi. Da qyar ta iya buda fatar bakinta guda biyu tana gyara qafafunta da sukayi tsami

"Dazune kawai bayan fitarta makaranta"

"Subhanallah" aba ya furta bayan ya isa gaban gadon yana taba temperature na jikinta wadda ta fara sauka

"Allah ya sawwaqe ya taqaita gaba......amma ba damuwa bace har yanzu a ranta bibi?" Ya sake yin tambayar yana waiwayowa hadi da duban bibi.

Kai ta girgiza da qyar kamar me ciwon wuya alamun a'ah

"Wannan abinda ke damun nata a yanzun yafi qarfin damuwa muddin abinda Dr chafa'atou ta fadi gaskiya ne......muddin abinda tace yana damun nata da gaske ne dukkanmu muna cikin tashin hankalin da bamusan inda zamu ajeshi ba,bakuma musan da wanne ido mutane wadanda basusan sultana matar maina bane zasu kallemu" tamkar an doke masa gwiwa haka yaji,sai ya qaraso gaban bibi din ya zauna sosai saman qafarsa yana kallonta. Tun daga zuciya zuwa ruhinsa addu'a yakeyi, ubangiji yasa ko meye kunnuwansa zasu jiye masa yanzu su jiye masa sassauqar qaddara

"Ya salam.......wani mummunan ciwo ya shafa mata?" Tambayar da yayin sai data motsa ran ama. Tayi qasa da kanta tana jin babu dadi,yaronta kamammen mutum ne wanda tsahon zamanshi dasu ko sau daya basu taba gani ko jin labarin ya tsaida yarinyar kowa bama,amma me yasa tunanin aba koda yaushe ke zarga masa mummunan zato game da maina din?,dan cikinsa?,me matuqar masa biyayya?,don kawai Allah ya kawo tsausayin faruwar wannan abun?.

"Ba ciwo bane,juna biyu gareta wai" qas aba yayi da kansa zuciyarsa na cika da wasi wasi. Ko kusa ko alama baiyi tunani ko tsammanin jin haka ba. Maganar shima sai tayi masa nauyi,bakinsa kuma ya sarqafe ya kasa furta komai.

"Inaso gobe ni dakai da ita muje wani asibitin a sake gwadata,don inason sanin gaskiyar batun" ta fadi da alamun da gaske take maganar tun daga zuciyarta har harshenta

"In sha Allah".

Dukka sauran maganganun ama tana ji batace komai ba,nata tunanin yayi nisa ne kan yadda rayuwa zata kasance a garesu gaba daya. Batasan ME GOBE TA TANADAR MUSU BA.... BATASAN ME K'ADDARA TA AJIYE MA GOBENSU BA......yadai tabbata GUDUN K'ADDARA GUZURIN TADDATA CE.......


**********Dogon lallashi wayo da dabaru tayi kafin ta samu nasarar da sultana tayi wanka. Ta tabbatar a yadda jiya aba ya kwana da zancan cikin ranshi zaiyi wuya basuyi fitar safiya da ita yawon gwadata ba.

Breakfast me kyau kamar kullum ta shirya mata da kanta. Ta sameta zaune tsakiyar gadon. Gaba daya ta jeme ta lalace,tun daga wancan lokacin sultana bata sake kyawun gani ba,ta firje ta firgice,tsakanin jiya zuwa yau kuma gaba daya ta sake zama kamar wata susutacciya.

Da kanta ta zauna ta fara bata breakfast din bayan ta sha kanta. Saidai loma daya kacal ta fara kelayowa ama amai kamar me shirin amayar da dukka kayan cikinta. Hankalin ama din ya tashi qwarai ganin yadda take maida numfashi kamar wanda ke shirin qwace mata. Ita ta gyara wajen tas ta kuma gyara mata jikinta,sannan ta sauya mata wasu kayan.

Zaune tayi kawai gaban sultanar wadda keta rera kuka da galabaitacciyar muryarta. Abinda takeji din tunda aka haifeta bata taba jin makamancinsa ba,wani irin ciwo takeji da rashin dadi da sukuni,dukka duniyar takejin ta mata wani irin zafi kamar ma ta mutu ta huta,ba abinda takeso,babu kuma abinda yake burgeta.

Sau uku tana bude bakinta da zummar baiwa sultana haquri sai kuma taga na meye?,me zata cema sultana din?,babu wata kalma a yanzu da zata gayawa sultana da zata cire mata radadin da takeji yanzu a qirjinta. Laulayin cikin ba qaramar masifa bace ga duk macen da Allah ya jarabceta dashi. Inda idanun bibi a bude suke bata makance da son jin akasin gaskiya ba tana tunanin yaci ace ta fahimci da gaske ciki ne da sultana. Jiya bayan duk sun fice sun barta daga ita sai ita ta qarewa sultanar kallo. Komai nata ya canza,hatta qirjinta da suke matasa zuwa yanzu sun fara cikowa,abinda dukkansu suka makance idanuwansu basukai ga ganinsu ba. Dukkansu ubangiji ya kauda hankalinsu daga ganin wannan,sai a yanzu da yaga dama ya bayyana abinsa.

Saddi ne ya shigo a hankali idanunsa akan fuskar sultanan. Shi kansa mugun tausayinta yakeji,yakan kuma tambayi kansa kuma ME YA MAINA YAYI MATA NE WAI?,ME YASA YAYI MATA ABINDA YASAN BATASO?.

"Aba yace sultana ta fito" kai ta daga ta kalleshi

"Kace masa gata nan zuwa,zataci abinci ne" amsawa yayi ya juya ya fita. Shuru tayi tana tunanin me zata bata?,kaf tunaninta a yanzun bawai gudu yakeyi ba,batasan me zata bawa 'yar marainiyar Allahn da zai riqeta ba. Wani tunani ne ya fado mata,ta tuna abinda nafessa tafi yawanci sanda tana da cikinta,may be idan tayi gado itama ta iya ci din.

Cikin mintuna ta kammala ta dawo ta sameta,har yanxu kukan takeyi da wani irin rashin kuzari.

"Taso kiji sultana" ama ta fadi tana zama kusa da ita tare da dagota. Sanda takai spoon din kusa da bakinta kai ta girgiza tana kauda kai

"Don Allah ba don ni ba ki karba" karon farko da ama tayi mata magiya tsahon tarayyarsu,sai taji nauyinta ya kamata. Hidima take mata tsahon dare da wuni,duk da tarin 'yan aikin dake sassanta amma ta maida hidimarta saman wuyanta kamar yadda hidimar aba ta zame mata dole,batajin koda su saddi da suka fito daga tsatsonta sun samu nau'in kulawar da take samu cikin wata ukun daga wajen ama,wannan ya sanyata bude bakinta zuciyarta na mata nauyi.

Batayi tunanin ko Loma biyu zata karba ba,amma sai gashi har takai biyar,ata shida ta kauda kanta hawaye naci gaba da tsartuwa daga idanunta. Ko iya hakan da taci ya yiwa ama dadi,tasan dai aqalla dai ba za'a ce babu komai cikin cikinta ba.

Hijabi me kyau a tsaftace ta fiddawa sultana,ta sanya mata sannan ta bata takalmi ta saka ta sakata a gaba zuwa parking lot na gidan.

Acan ta samu oncle bashar oncle


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login