Showing 282001 words to 285000 words out of 294767 words

Chapter 95 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Ido ya zaro waje yana dubanta,sai kuma ya shiga girgiza kai

"Bazan iya ba,haba bibi kaman companyn buga jarirai nake da?" Yadda ya fadi maganar sai ya bata dariya sosai,har shima ya tayata suka dara.

Sati guda kacal da share biki suka tattara suka koma paris,saidai koda suka koma din kusan shirye shirye ya dinga yi gadan gadan na dawowarsa qasarsa a watanni bakwai masu zuwa adadin sanda ama zasu gama nasu wa'adin,bawai kuma da nufin yabar paris har abada ba,a'ah....zamansa zai koma nijer ko Nigeria ne guraren daya yanke kafa business dinsa da kuma inda ama ta aje nata business din,da inda plazas na BB MAYAK'I suke.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 151


Yayita zuba idanu yaga sanda sultana din zata koma aikinta,amma saboda yadda baya samun zama sosai tunda suka dawo sai hankalinsa ya dauke daga kan hakan. Yasan dai tabbas bata zuwa din,tunda ba zata taba fita ba tare da izininsa ba,bata kuma sake tayar masa da maganar ba.

A wani dare,yana zaune cikin falo sanye da abaya ta maza me gajeran hannu,yana zaune saman sofa dake falon,amma kuma qafafunsa suna miqe a qasa. System da tarin takardu ne a gabansa. Kusan kullum cikin wannan hidimar yake,yanason fidda duk wata dukiyar daddyn sardauna daga hannunsa yayi musu handing over,kama daga asibitinsu da suka damqawa ragamarsa zuwa sabon company dinsu dake aiki a niamy.

Dauke da varnish tray take takowa daga cikin kitchen din zuwa inda yake zaune. Tana iya hangen fuskar nan tashi me yawan kwarjini da cikar kamala musamman idan yana zaune irin haka yana aiwatar da wani abu me muhimmanci. Sumarsa ta sanyata sakin murmushi,dukka a cakude take,alamun da zai nuna maka lallai aiki yasha kansa sosai. Skirt da blouse ne a jikinta amma sakakku,duk da sakewarsu hakan bazai hanaka ganin cikin jikinta ba. Cikin wata biyar amma sai ka dauka yayi watanni takwas ko tara dinsa ma. Wani irin girma yakeyi,duk da Dr Camille tayi mata dukkan bincike,kuma bakinsu yazo daya da Dr Noor, triples suke sanya mata ran samu. Jikinta yayi sanyi tana tuna wahalar cikin twins ma ina ga wannan?,amma tsaiwar gwarzon namiji irin aliyyu a gefanta ya sanyata ta koma jin koda yara biyar ne ma zata iya haifewa.

Kulawarshi a kanta ya danne dukka tsoro da fargabarta,soyayyarsa a ranta kuma ya bata wata irin nutsuwa da qaunar koma meye zata haifa din.

Iya dososhi da tayi kadai yaji a jikinsa tana tahowa,da sauri ya sauke system din kan cinyarsa yana miqewa ya kuma nufota yana kama qugunsa

"Me ciki na'am.....gani nan tafe.....me ciki na'am gani nan tafe" yadda yakeyi din ya sanyata sheqewa da dariya da gaske,shima yana tayata,ya kuma matsa yana karbar tray din hannun nata,ya saka daya hannun ya riqo hannun nata. Zaunar da ita yayi ya ajjiye tray din,sannan ya zauna sosai a gabanta dirshan yana tanqwashe qafarsa

"Me yasa dole dole saikin wahal min da kanki?,ko nauyin abinda kike dauke dashi bakiji soulsis?" Murmushi ta saki,ta miqa hannu tana shafa tudun cikin nata. Iya nauyi tana jinsa,amma har yau taqi yarda ta nuna masa,ta sanshi da damuwa da yawa akan lamuranta,tasan kuma yawan ayyukan da sukayi masa rubdugu,yanzu yanzu sai ya kasa yin komai ya aza damuwarshi a kanta,bayan kuma lafiyarta qalau take jinta,nauyinne da sauran lalure lalure da ama kan gaya mata dama me ciki ba'a rabata dasu.

"Ni bana jin komai,ko tsere ne zan iyayi dakai kuma na wuceka"

"A hakan?" Ya fadi yana dariya gami da kallon tulelen cikinta. Cikin qwarin gwiwa ta daga kai

"Sosai"

"Naga alama......ni na isa na wuceki daman?,Allah ya taimakeki" ya fadi yana dunqule hannunsa tamkar meyi mata jinjinar sarauta. Dariya suka saki gaba daya,ta soma zamowa da zummar sauka qasa tayi serving nashi. Sauri yayi ya matsar da tray din

"Dakata...... zauna kawai ke kin gama aikinki" ya fadi da sauri ya soma zuba musu abincin.

Idan yaci spoon daya sai ya bata daya,da haka da haka har suka kammala,ya ajjiye spoon din ya zuba mata idanu

"Ina mamakin wai yaushe baby sultana ta iya wadannan zaqaqan girkin?,kinsan kin batarmin da kowanne taste din abinci daga bakina idan ba naki ba?" Ya qarashe fadi yana dage mata dukka girarsa biyun, maganar kuma yana fadinta da gaske daga qasan zuciyarsa.

Murmushi ta saki tana jin qaunar ama me qarfi a ranta,ta koyar da ita komai na rayuwa,duk abinda ya kamata diya mace ta iya ta sani kota fahimta don zamowarta cikakkiyar mace ama tayi mata shi

"Aikin uwa ta gari ce.....ama" idonsa ya lumshe ya kuma bude lokaci guda. Mahaifiya daban take,dukka tayi wadannan abubuwan sabodashi,saboda yaji dadi,saboda ya samu abinda kowanne da namiji ke fatan samu daga wajen iyalinsa. Ta gefe guda kuma ta inganta duniya da lahirar marainiyar Allah.

*******Washegari yana shirin fita yaga itama tana shiryawa

"Aikin zaki koma?" Idanu ta fidda sai kuma ta saki murmushi

"Zuciyata ba zata taba nutsuwa da aikin da ina yinsa mijina yana cikin kishi da rashin nutsuwa ba......na ajjiye aiki a bangaren gabatar da kowanne shiri muddin za'a doramin camera" ta qarasa fada tana zama gefan gado saboda nauyi sai taji tsaiwar ta mata wahala. Hankalinsa dukka ya tattara a kanta yana dubanta da wata irin narkakkiyar qauna. Duk yadda takai ga qaunar wannana aikin?,duk yadda takai ga shan gwagwarmaya don cimma wannan burin?,anya ya yiwa kansa adalci idan ta aje aikinta dukka saboda shi?.

"Baki nema izini ba sultana?,me yasa?" Yayi tuhumar a sanyaye

"Yardar Allah nake nema da kuma yardarka bloodline" ta bashi amsa itama a sanyaye

"Sun roqi naci gaba da aiki dasu a bangaren culture din.......koda iya research ne da tsara program din nayi na tura musu,zasu samu sabuwar presenter.....nace su dan yimin haquri har na haihu.....koda na koma qasata zan iya wannan" ta bashi bayanin da ya sanyashi ajjiye comb din hannunsa ya dawo gefanta ya zauna. Idanu kawai ya zuba mata ya rasa abun cewa,saita saki murmushi tana waving hannunta saman fuskarshi

"Wake-up bloodline" murmushi ya saki kawai,ya kama dukka hannayenta ya saka cikin nasa ya damqe,yayi kissing dinsu a tausashe

"Allah yayi miki albarka" ya qarshe dashi.

"Wajensu ama nakeso na yini yau"

"Kina da dama.....kwana ne kawai bazan iya bari ba soulsis" dariya ta tuntsire masa dashi. Yasha cewa taje din,to amma ita damuwarta tace idan taje ta tabbatar su batoul ba zasu barta tayi baccin ranarta ba,zasu cikata da tambayoyi ne kawai da labarai na school,sai kuma tambayar daddynsu.

Tun a bakin qofa suka dinga ihun ganinta,tambayoyi kam haka suka dinga jera mata su akan cikinta,har sai data kusa buge benazeer sannan ta nutsu.

Sunyi hira sosai da ama,tana ta nan nan da ita,duk inda suka gifta ita da yaran sai farinciki ya kama ama

"Alhamdulillah" da take maimaitawa cikin zuciyarta har batasan adadi ba. Hikimar ubangiji gaba daya yawa ne da ita,shi yasa kome ubangiji yayi ba'a son ka cika qyamarsa,me yiwuwa akwai hikimarsa a ciki.

Sultanar dai ashe ita aka haifawa?,ashe dai daga qarshe sultana tata ce,itace tushen zuri'arta da kafuwarta?.

Dafa wannan ajjiye wannan haka me aikin bibi ta dinga jerewa sultana. Duk yawan cin abincinta har sai data ture,kafin wani lokaci jikinta ya mutu bacci yazo. Ama tanata lura da ita, tausayinta ma gaba daya ita takeji. Tana qanqanuwarta amma Allah ya qaddara mata haihuwan yara bibbiyu uku uku,gadon dangin mahaifiyarta.

"Ku raka mummy daki ta kwanta ta huta hakanan" ama tace dasu benazeer.

Suna gaba tana biye dasu a baya har suka isa dakinsu,saita samu dakin turmus da kaya.

"Kayan qannenmu ne wai inji ama" benazeer ta fadi tana murna sosai harda juyawa kamar zata taka rawa. Dariya taso qwace sultanar,taja qaramin tsaki tana ture pillows din dake saman gadon batoul ta yada kanta idanunta akan kayan dake jibge. Sai yanzu take sake yarda,komai nata ba halayya benazeer ta dauko,batoul kuma maina ce a wasu abubuwan da dama.

"Ku fita ku bani waje bacci zanyi"

"Idan kin tashi zamuyi hirar?" Batoul dake tsaye a gabanta ta fada. Dole suka bata dariya,ta saka hannu ta riqe hannayensu tana murmushi

"Eh zamuyi" idanunta a kansu har suka fice,sai ta sake maida kallonta ga kayan. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci irin haukan siyayyar da ama ta yiwa su batoul shine zata yima wanann cikin,kaya har sunfi nasi batoul yawa,ta kuma san bawai ta gama siya bane.

Ko ba'a fadi ba tasan Allah ya zubawa ama son 'yaya,ko daga yadda ta dinga dauko riqon yayan yan uwa ana hanata,da yadda takema yaran gidan tun sultana na sultanarta,bare kuma yanzun data samu mallakinta halak malak.

Sallah kawai ama ke tashinta tayi ta koma,ba ita ta wartsake gaba daya ba sai da tayi magariba. Me aikin ama ta shirya dining,basukai ga fara ci ba maina din ya iso.

Sau daya ta dubi qwayar idanunsa ta fahimci yauma a gajiye yake tulus. Bataji kunya ko nauyi ba,ta yunqura duk nauyinta ta tarbeshi,ta kuma ajjiye masa ruwa da sauran abinda tasan yakan buqata idan ya shigo gidan.

Abun ya yiwa ama dadi sosai,idanunsa shima a kanta ta furta

"Allah yayi miki albarka" yanason kulawa,kuma ya sameta har fiye da yadda yakeso.

Tare kuma cikin kwano daya sukaci abinci da yaran,surutu har ya rasa na waye zai amsa,kusan benazeer ta fara koyawa batoul surutu,basu barshi ba har sai daya kusa qwarewa. Sulthana na gefe tana musu dariya,shine yake hanata hana benazeer yawan maganar nan tata

"Ki barsu,alamu ne na budewar qwaqwalwa wa yaro,duk yaro me yawan magana zai wahala ki sameshi baida basira......iya kanki kawai ni ya isheni misali na gani.... haquri ake dasu ayita amsa musu tambayoyin,inda sukayi mistake ko tambaya mara ma'ana kuma gyara musu akeyi". Abinda yake yawan gaya mata kenan.

Qwarewar da yayin sai duka suka nutsu,suka dinga jera masa sannu hankalinsu tashe,ya saki murmushi yana cewa

"Naji sauqi,mu qarasa cin abincinmu". Basu bar gidan ama ba sai kusan sha biyu saura,saboda aba ya sameshi, kuma sun tattauna dukka su ukun,wanda duka dai baya wuce kan dawowarsu qasa nijer.

*_akwai dinner in sha Allah,ku shirya_**_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 152



********A hankali take takawa tana fitowa daga toilet din tallafe da cikinta da yayi matuqar girma da tsini kamar zai fado qasa.

Jin alamun fitowarta ya sanyashi daga kansa daga akwatin da yake shiryawa,wanda ya gama shirya guda daya,dayanne a gabansa cike fal da kayan babies.

Dukka qarfin halinta ta tattaro ta sakar masa murmushi tana kallon qwayar idanunsa. Rauni zallah,kai tsaye ma zata iya cewa ita dake facing yanayin ta fishi qwarin gwiwa da kuma dakiya

"Bloodline saida tanja tace ka bari ta shirya kayan fa,wasu abubuwan na hidimarmu ya kamata ace kana hutawa,abun sai yayi maka yawa fa" ta fada a narke da shagwabarta wadda a yau ta motsa zuciyarsa da wani irin rauni. Duk tsanani duk kuma halin da take ciki qoqari take ta boye komai,qoqari takeyi ta nuna masa everything is fine koda kuwa can cikin jiki da zuciyarta ba haka bane. Shi daya yasan da yadda take bacci take kuma iya yini dauke da wannan qatoton cikin,ya gaji da gani shi yasa yayi deciding gwara a cireshi yana da sati talatin da biyar itama ta huta. Dama kuma ko can Dr Camille tace saidai Cs din,tunda haihuwan farko CS ne,yanzun kuma ba yaro daya bane a cikin,koda yaro daya ne a irin qasashen nan basa bari ka dauki wannan kasadar koda sau daya aka taba yankaka.

"Inda zai yiwu soulsis......koda numfashi ma yi miki zan dinga yi.....dani da yara na muna wahalar dake da yawa" ya furta yana kamo dogayen yatsunta da a yanzu suka ninka nauyinsu yana murzawa a hankali cikin tausasawa.

Murmushi ta saki sosai,ta tsugunna a hankali tana zama sosai a gabansa,ta saka hannu ta jawo wani set na bodysuit da kamfanin BB dinsu ya fidda sample dinsa

"Kowanne minti na guda daya cikin bautar ubangiji yake bloodline......ba wahalar banza nakeyi ba,duk macen data mutu ta wannan hanyar ka tuna tayi shahada?" Kalmar mutuwar data furta gaba daya saita kashe masa qwarin gwiwarsa,ya sanya daya hannun nasa ya riqe dukka hannayenta biyu cikin nasa,sai a sannan ta lura idanunsa har sun sauya kala

"Ki daina ambatar me raba masoya......me yanke jin dadi.....ba yanzh ba in sha Allah,na rantse miki da Allah sulthana bazan iya rayuwa cikin duniyar da babu ke ba,bazan iya qara cikakkiyar awa guda cikin duniyar da babu ke ba" murmushi ta saki tana son bashi qwarin gwiwa. Gaba daya ya koma macen,itace namijin,akan dukka abinda ya shafeta sam sam bashi da juriya batasan me yasa ba,rago ne ta wannan fannin na gaske kuwa.

"Ina fata har jikokinsu batoul sai mun gani in sha Allah......" Don kauda maganar sai ta sake daga bodysuit din

"Bloodline......har yanzun baka gayamin me zan haifa ba?" Dan qaramin Murmushi ya saki bayan ga ambato sunayen Allah gaba daya,ambaton da ya saukar masa da nutsuwa

"Kinsan wani ikon Allah?" Kai ta girgiza

"A'ah"

"Har yanxu babu wanda Allah ya bawa ikon fadin jinsin da zamu samu" dan sama ta kalla kadan alamun nazari,sannan ta gyada kai. Ita kanta sai yanzu ta tuna,tabbas babu wanda kam a cikinsu daya fadin musu sex na yaran.

Habarta ta kama ta riqe tana kallonsa,sai yadda tayi din ya bashi dariya,yasa hannu ya tungule hannun yana dariya,tayashi tayi itama,yadan jawota kafadarta ya rabata yana cewa

"Qiri qiri wadannan yara sun hanani rungumar matata yadda ya kamata" yayi maganar da sigar qorafi shima yana narke mata yadda take masa hadi da nuna dogon cikinta da yatsansa. Dariya tadan saki,ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Ban taba sha'awar naji abinda zaki haifamin ba sulthana soulsis.......duk abinda kika haifamin inaso......idan ana haifar rabin d'a idan kika haifamin inaso sulthana" kanta ta kwantar saman kafadarta,hawaye yanason balle mata amma kuma ta hanashi fita din,don tasan yanzun zata daga masa hankali. Itadai tayi imanin ta samu miji wanda ba irinsa a wannan zamanin sai anyi dogon nazari da kuma bincike.

Rana ce da Dr Camille ta sanya musu don yiwa sulthana din Cs,amma yayi qoqarin maidata rana me muhimmanci a garesu gaba daya. Ya hanata zaman damuwa ko tunani kamar yadda itama taketa qoqarin hanashi wannan.

Hudu na yamma suka tsara barin gida,amma ama tace su jirayeta ita da kanta zata shigo ta daukesu. Ta tabbatar a ranar aliyyu bashi da sauran nutsuwar da zai iya wani abun kirki. Ta sanshi sarai,tasan halinsa,ko itace bata da lafiya ba wani iya kuzari yake ba a ranar.

Kafin ama din ta iso sun kammala komai,don haka tana isowar suka wuce asibitin.

Tun daga bakin gate din asibitin har ciki haba haba kowa yakeyi da ita,kasancewarta matar babban likita a asibitin kuma likitan da suke matuqar so,wanda duka duka wata uku ya rage masa yabar asibitin nasu. Kulawa ta musamman suka bata,sukayi mata dukan abinda kuma ya dace.

Batasan goumar da najma suna gurin ba sai data baro dakin likita

"Baqin buzu da amaryarsa" ta fadi cikin sigar tsokanar nan tasa. A yau din yadda goumar ke mata magana sai taga shima jikinsa gaba daya a sanyaye yake,najma ce me qarfin halin. Murmushi kawai itama tayi,tana mamakin rauninsu haka a kanta. Tana zaune cikin dakin har aka sanya mata cannula da komai,tsakanin mintuna goma sha biyar sai shigowar bibi sukaji.

Bataji zuciyarta ta raunata ba sai da taga bibi afujajan,ta rungume bibi din sai dukansu kuka ya kubce musu.

"Kuyi mata a hankali kada jininta ya hau" Dr Camille ta fadi maina ya yiwa bibi bayani,wannan shi ya kawo nutsuwar. Dukkansu abun ya zame musu tamkar sabo,kasancewar sanda akayi nasu benazeer daga ita sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login