Showing 231001 words to 234000 words out of 294767 words
Chapter 78 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
bika,ni ba mara kunya bane" yadda tayi maganar da zallar quruciya dukka da yarinta a mode dinta yaso bashi dariya,amma a yanzun yana jin ba lokacin dariya ko wasa bane,lokaci ne da zai nuna mata qarfin qwanjinsa,ya kuma murda tashi mazantakar,aba da ama sune rauninsa,idanunsu ke masa gate suke kuma kawo masa tsaiko wajen maidata qarqashin umarni mulki da kuma ginin gidansa,a yanzun kuma ya samu cikakken izini koda da gatse aba ya fada,koda ba da son ranshi ba.
"Ni kuma ba kunya gareni ba......don aba kanshi yasan haka,yasan waye haidar......muddin yaci gaba da riqe masa mata yanzun ba juna biyu kika samu ba?,to idan ana daukan ciki kafin a haife wani zakiyita daukan ciki a gabansu........bana iya barin abinda nakeso.......zuciyata bata iya son abu da wasa ba kota fara so tayi sassauci a ciki......saboda idan ta fara son tana yin wannan soyayyar ne da gaske......batasan wasa ko ha'inci ba" ya gama kashe mata duk wani qwarin gwiwa da kafiya da takeji tana dashi,saqon kuma da idanunsa ke isar mata yafi wanda yake furta mata da bakinsa tsanani da kuma tarin kaifi,don haka ta juya da nufin ta isa dakinta ta kulle kanta da kanta,don duk tsanani ba zata iya binsa haka siddan don aba ya fadi wannan maganar ba,wala'alla ma yayi ne don ya gwadata,daga ya fadi magana sau daya sai ta tattara ta bishi kaman dama tana jira?.
Abinda ta manta shine maina din tamkar uba yake a wajenta?,haifanta ne kadai baiyi ba,amma dukka halayenta ya gama da saninsu daya bayan daya,don haka ya kausasa murya yana bata umarni nakai tsaye wanda ba wasa ko sassauci a cikinsa
"Kikayi kuskuren kulle qofa bayan kin shiga zaki gane baki da wayau kwata kwata......zaki fahimci kuma maina aliyyu ne,bashi da sassauci......ina fatan baki manta yadda ya dinga iskeki duk dare ba koda bayan kin rufe qofa ne....." Ya isar mata da saqon da ya sanya ta kasa maida qofar ta kulle kaman yadda ta niyyata,sai kawai ta buge da wucewa dakin da gudu gudu,ta kuma fada saman gado tana fashewa da kuka. Gaba daya ya sanyata a tsaka me wuya,jin laifi takeyi a kowanne sashe na jikinta,tasan koda zata hadiyi qur'ani ama da aba ba zasu taba gasgatata cewa ba ita ke kawo aliyyu ko kuma ita ta bashi fuska ba. Abun kamar almara?,wai ciki a jikinta?,cikin maina again?,bayan duk wahala da fadi tashin cikinsu benazeer da ba zata taba mantawa dashi ba?.
Idanunsa ya lumshe yana furzar da numfashi,sai kuma wani murmushin ya sake kubce masa. Wannan karon koda bori zata hau.....koda aljanu zata tayar sai ya tabbatar mata da cewa shi din likitane,zai banbance mata zaqin soyayya da kuma banbancin kulawarshi a kanta sama da kulawar kowacce halitta.......wannan soyayyar da yayi nasarar haukatata tayi bishiya me manyan jijiyoyi da rassa tsakiyar qwaryar zuciyarta cikin sati uku kaman yadda ya tsara kuma lissafinsa ya tafi dai dai.......zai finciko wannan qaunar.......zai tasheta daga dukkan wani bacci da tayi. Ya sake lumshe idanunsa yana budesu murmushi na sake fita akan fuskarsa kamar me aljannun murmushi. Iya abinda qwayar idanunta ya gaya masa a kanta,baiyi tsammanin aikinsa zaiyi wannan uban tarin nasarar a sati uku kacal ba,tanata wahal da kanta......tanata qaryata kanta akan abinda gaskiyarshi kenan,ita dole ba zata yarda ta kamu ba?,ba zata taba yarda ta fara mahaukacin son maina d'a ga hamid da hamdiyya ba?
"Zakisha mamaki" ya fadi a fili siririyar dariya tana kubce masa.
Miqewa yayi a nutse daya tuna shigarta daki ba abinda zai sameta tanayi sai kuka tabbas kuwa,kukan kuma a matsayinsa na likita yasan baya haifar da d'a me ido ga mace me yaron ciki kamarta
"Tana buqatar kulawa da kwanciyar hankali......ina buqatar healthy baby" yayi wannan maganar shi da zuciyarsa
"Baby ko babies?" Ya tambayi kansa
"Ya rabbb......babies girls or boys.....ko mix dukka inaso" dukka shi kadai yake maganar can qasan ransa kamar wani zautacce,sai ya sake yima kanshi da kanshi murmushi. Bai taba sanin haka yake da son yara ba sai yanzu,koda yake d'an kanka daban yake da komai,zaka yita mamaki ace wannan wani yanki ne daga gareka?.
Qofar dakin ya maida ya kulle,sannan ya isa a hankali gabanta yana kallonta,sai ya zare hannuwansa daga aljihun wandonsa,ya zauna daga gefan gadon,ya sanya hannunsa dukka biyun yana qoqarin dagota zaune
"Tashi muyi magana......ki tsaida wannan kukan....." Yadda yayi maganar da sassaucin murya da kuma girman nan da tasan yana mata shi a baya yasa ta sassauta kukan. Dakin ya dan dauki shuru,sannan yayi gyaran murya ya jefa mata tambayar
"Me kike da buqata?" Muryarsa ta daki zuciyarta sosai,har wata yar shesheqa ta fita daga hunhu zuwa hancinta a sanyaye,tanason ko yaya ne shima yaji bacin ran data ji,rana tsaka ya jawo aba ya mata koran kare a gidansa?,ama kuma da alama itama bayi bayansa?.
"Bana sonka" ta furta zuciyarta na qaryatata amma labbanta sunason cewa gaskiyarta ta fadi.
Har qahon zuciyarsa yaji maganar,karo na biyu kenan data gaya masa kalmar gatse gatse,takuma sokeshi qwarai da gaske. Yadan cije lips dinsa,sannan ba tare daya dubeta ba yace
"I will slap you sultana......ni ba sa'anki bane,duk ranar da kika sake cewa you hate me ko?......" Sai kawai ya jinjina kai yana jin zuciyarsa tana motsawa
"Am just asking you me kikeso,saiki ce wani you hate me?.....ba rannan kin fada ba?,yanzun ma kin maimaita ko?,well.....karki maimaita na uku.......nima din na janye kalman i love you....i hate you..... shikenan?" Ya jefeta da tambayar yana dubanta.
Ko sau daya,koda wasa kuma bata taba kawowa a ranta zataji zafi idan ya gaya mata baya sonta ba,amma sai taji wani abu me tauri yazo ya tsaye mata a wuya kamar ma tana neman rasa numfashin shaqa
"So stop telling me......ina da wadanda suke sona,zanyi focusing a kansu.....now ki dauka kina tare da uncle dinki......nemi hijab ki saka muje,dole kibar musu gidansu yadda suka buqata" sai ya miqe kawai ya bude Wardrobe dinta.
Duk abinda yaga ya kamata ya dauka kawai yake dauka din,baima nuna yaji kukanta ba,har sai daya gama hada komai,yana daga tsaye ya fiddo waya ya kira goumar. Kamar me jiran kiran nasa ya dauka
"Qaraso ciki kazo ka fitarmin da kayan nan"
"Okay sir" goumar din ya fadi dadi yana cikashi. Wayar ya mayar aljihu ya waiwaya gefansa yana kallonta
"Idan kina zaton zan nema wani abu a wajenki ki daina wannan tunanin......zanje na kula da ajiyata.....idan kika sauke ya rage naki......yanzun na koma uncle dinki kamar baya,live your life.....banason na sake maimaicen magana dake,ki saka jilbab mu wuce" daidai nan goumar yayi knocking maina ya bashi daman shigowa.
Idanunsa akan sultana gulma tana cinsa,maina yana ankare dashi don yasan halin mutanen nashi,ya jefa masa harara yana masa nuni da kayan,sai ya dauke kanshi yana qusnhe dariya ya daga luggage din ya soma janta,maina ya kira shi ya waiwayo ya jefa masa key din motarsa ya cafe sannan ya juya yana ficewa.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 124
Idanunta akan gidan,ta tsammanin can zataga ya wuce amma sai taga ya nufi motarsa. Goumar da ya jima da sanya luggage din a ciki yana tsaye jingine da motar. Zai bude mata maina ya daga masa hannu,yasa hannunsa ya bude mata gidan gaba ba tare da yace komai da ita ba. Kai ta daga ta kalleshi,sai kuma ta maida dubanta zuwa ga cikin motar, zuciyarta na karyewa ta saka kai tana shiga,rauni yana ziyartarta,tana ji a ranta zai nesantata da kowa nata,ta yaya zata iya tafiya tabar ama?,ta yaya zata iya nesa da benazeer da batoul yaran da kwanan da suka dinga yi tare dasu a dan tsakanin ya haifar da wata mahaukaciyar shaquwa a tsakaninsu.
"Banyi sallama da ama ba,banyi sallama da aba ba,benazeer da batoul" ta furta muryarta na rawa,sabon kuka yana so ya qwace mata sanda ya shiga motar seat din driver yana niyyar rufewa. Sai ya fasa tayar da motar,Iska ya furzar yana dan buga steering motar da yatsunsa dake samanshi. Tausayinta yaji ya kamashi,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fiddo jikinsa waje gaba daya yana nufar qofar gidan da zummar komawa ciki.
*_ABA_*
Abu uku ke turereniya a zuciyar ama sanda take barinsu a falo tana bin sahun aba zuwa nashi falon. Na farko mamaki dariya kunya da kuma tausayin sultana,dukka sauran abubuwan kuma wa aba takewa. Lallai gaskiyar hausawa da suke cewa ba'a shaidar d'an yau,ta godewa Allah da bata zafafa da yawa cikin lamarin maina da sultana ba lallai tabbas da yau taji kunya,ta sake godewa Allah da aba yabar batun raba auren,inda ya kafe akan hakan Allah ne kadai yasan me zai faru. Cikin biyu dai dole ayi daya,ko ayi cikin a waje wa'iyaxubillahi tunda dai rabo ya rantse,ko kuma aba din ya rasu kuma suci gaba da zaman aurensu.
Dariya ta kusa subuce mata sanda ta isa falon ta sameshi dirshan tsakiyar jikokinsa yana aikin bare musu sweet,abinda duk soyayyarsa da yara baya jurewa,zai dai siya,amma saidai ama goumar ko tanja suyi aikin budewa,yau sau gashi da bare leda ya kusa nawa,idan ya barewa batoul sai ya barewa benazeer. Ya amsa sallamarta yana daga idonsa a kanta,suna hada ido wata dariyar tazo mata saita kauda kai kaman tana neman wajen zama.
Jinjina kai kawai yayi qasan ransa murmushi yana subuce masa,ya sani,dariya take masa,kuma bama ita ba duk wanda yaji zancan shi da ya zaqe da yawa cikin lamarin zai fara yiwa dariya.
"Ku dauki ragowar kukai tanja ta boye muku.....ta saka muku house wear a cire wannan kayan" aba din ya fada yana tattara musu tarkacensu.
Sanda suka fice sai falon yayi shuru daga ita sai shi,sai aka koma satar kallo tsakaninta da shi. A karo na kusan ashirin da suke satar kallon juna daga qarshe suka kama juna,dole murmushin ama me sauti ya fita tana danne dariya kada ta biyo baya
"Aba....how far?" Tayi maganar tana kashe ido hadi da maqe murya. Dariya dole ta kamashi shima
"Hamdi ni kikewa dariya?"
"A'ah,aba ai dole nayi dariya,kaga aikin 'yan zamani ko?"
"Na gani hamdiyya,me na isa yanzu nace?,shi yasa nace ya tattara matarsa su tafi,bansan kuma da wanne ido zan sake muzurai da cika baki akan 'yar marainiyar da naketa haqilo ba"
"You learn a lesson aba......tsakanin miji da mata fa sai Allah,ma'auratan da dukka sun balaga harda 'ya'ya a tsakaninsu,haka kawai sai a turke kowannensu kamar dutse?" Murmushi yakeyi yana girgiza kai
"A'ah......ni na tabbatar daga yadda diyata ke kuka fin qarfi yayi mata..."
"Rape still?,wallahi aba wannan karon bazan yarda a jefawa dana kalman fyade ba,wancan karon nayi kawaici......amma dis time around nima murje idona zanyi......ahaaan......sanda suka daidaita kansu da inda suke jonewa ma baka sani ba aba,amma kazo kana yabonta.....saifa bango ya tsage qadangare yake samun wajen fakewa" ta fadi tana shan mur kamar da gaske.
Dariya sosai ta bawa aba,abun dukka sai ya juye masa nishadi musamman idan ya tuna wai BB nada qani ko qanwa a hanya.
"Maida wannan dogon hancin naki kada ya tashi sama.....wait......ashe dama baki da kara har haka hamdiyya?"
"A nan dai bani da aba.....,yarinya ta kawo maka result.... Ina laifin ma a yabawa d'ana shima?" Dariyar da tafi ta dazu ama ta bawa aba
"Fitinannen dankin nan ba,shekaru shidan da suka wuce da suna tare na tabbata for now mun gani da daukan jikoki ko?" Sai a nan kunya tadan kama ama,ta kauda kai tana dariya qasa qasa gami da cewa
"Oho.....koma dai meye,Allah dai ya sakawa Bibi da alkhairi"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu "aba din ya fadi yana jinjina abun qasan ranshi. Wato wani irin rabo ne me zafi a tsakaninsu wanda duk idan ya tashi zuwa baya zuwa da sauqi,ya godewa Allah da rabon baiyi ajalinsa ba. Ama na zolayarsa yasan amsar da zai bawa mutane batoul ta dawo.
"Ama wai kizo" kaman zata tambaya waye sai kuma ta fasa,ta miqe tsam tana bin bayan batoul suka fito.
Yana tsaye tsakiyar falon hannayensa goye a bayansa. Suka hada idanu da ama,yau din shima sai yaji kunya ta dabaibayeshi,yadan yi qasa da kansa,ama din ta gyara tsaiwarta tana hade rai
"Meye kuma?" Kanshi ya sake dagawa a karo na biyu,saidai kuma ya gaza hada idanu da ita,ya karyar da murya yana cewa
"Ama.....kuka take,tace ba zata tafi ba bakuyi sallama ba" tausayin sultana din ya saukar mata,tasan halin d'a namiji,bata kuma cire har d'an cikinta ba,sun qware wajen iya yaudarar diya mace da kalamai,sun muma qware wajen karyo dake su samu biyan buqatunsu idan suka so komai kafiya zafin kai da jajircewarki,ballantana sultana......sultanar da take tashi......sultanar da jinin jikinta ya gaurayu da nashi,sultanar da tayi amanna koda wanin maina ta aura a rayuwarta zai wuya yayi controlling nata yadda maina zaiyi,ta zama shi ya zama ita......kominsu daya ne.....girma da sauyin dabi'unta ya kawo jirkicewar komai a tsakaninsu.
Hijab dinta dake aje saman kujera ta dauka ta zura tayi gaba ba tare data ko kalleshi ba,sai yaji dadi ya saukar masa ganin tayi accepting abinda yakeson gaya mata tun kafin ma ya gabatar mata dashi. Bai bita ba,sai ya doje daga bakin qofar gidan,yana kallon ama sanda ta isa gaban motar ta sanya hannu ta bude murfin motar ta shige.
Sanda taji an bude motar ta dauka shine,don haka tayi banza da ranta tana ci gaba da rera kukanta. Zama sosai ama tayi a seat din driver din tana kallonta. Qamshin turaren ama ya fallasata,saita daga kai da sauri,suna hada ido da aman ta gaza ci gaba da kallonta saboda kayan kunyar da takeji ta debo
"Au.....kuka kika zauna kinayi?,cikin shege kikayi ne sultana?" Maganar ta sanyata maido dubanta kan ama,tanason ta tabbatar da gaske ama bata dauki wani abu ba?,da gaske ba komai bane wajen ama din.
"Ko bashi da uba yana da kaka,auren sunna ne har abada tsakaninki da haidar haka ne?" Wani sanyi ya soma sauka mata cikin zuciya,ta shiga gyada kai hawaye na sake yawa cikin idanunta.
"Ki goge hawayen muyi magana ko na fita na barku" da sauri taja gefan hijabinta tana goge idanun nata tare da tattarawa ama hankalinta.
Tun maina da suka shanya a waje yana kallon motar har ya koma kallon agogon hannunsa yana irga lokaci.
"Wannan maganan yayi tsaho" ya sake fadi a karo na kusan biyar. Goumar yana gefe dariya kaman ya kasheshi,wai dama haka ya mainan yake mutuwar son sultanarshi?,da gaske irinsa dama soyayya haukatasu takeyi a mafi yawancin lokuta?.
"Goumar....ko zaka......" Sai kuma abinda zai gayawa goumar din ya yanke ganin ama na fitowa daga motar.
Tun kafin ta qaraso ya miqe yana jiran isowarta,gaba daya ama din ta zame masa wata boss. Tana isowa goumar ya matsa ya basu waje
"She's pregnant ka sani,akwai wasu canje canjen halaye wajen me ciki.....saurin fushi yawan kuka duk zata iya fuskantarsu,cin abincinta ya qaru,kowanne lokaci tana iya buqatar abinci......gata nan kaman ajiya ce.....kada kaga ance ka tafi da ita ziqau ka dauka ruwa tasha ko kaci bulus.....da sauran gatanta,kuma komai na 'yar gata zamuyi mata kaman kowacce mace.....cikin jikinta ne kawai zai kawo tsaikon wasu abubuwan....."
"Na shiga uku ni maina" ya fadi qasa qasa
"Baka shiga uku ba saika kasa kula da ita" ama ta bashi amsa idanunta cikin nasa
"Bamu hanaka saitata ba......da qin biyema kuskurenta ko son zuciya,tsawatarwa duk yana da kyau......amma ta yanda ya dace....ka cika mata zuciya da soyayyarka......banason na haifi d'an da mace zata kasa mutuwa a soyayyarshi" ama din ta fada kanta tsaye. Mutum ce me matuqar son soyayya,tana martaba soyayya saboda tasan dadinta. Yana daya daga cikin dalilan da yasa ko mutuwa take fata ta fara daukanta ko ta daukesu tare da aba..... namiji da tasan an jima ba'a yi kama tasa ba cikin duniyar iya nunawa matarsa soyayya.....girma shekaru ko tsufa basu sanya ya wofantar da hakan ba......ba wasu shekaru da suka dakushe salon nuna mata kulawa da yakeyi ko kuma soyayya,wannan ya sanya kullum kwanan duniya aba yake na daban a zuciyarta dama rayuwarta gaba daya
(Zuciyar mace 'yar son soyayya ce,komai tsufa da shekarunki kinaso kiga mijinki ya mato a kanki,yana tattalin farinciki da baki lokacinsa da dukka kulawarshi,ba abinda yakai wanann morewa a rayuwar mace).
Yana murmushi yana dosar motar,indai ta fannin winning zuciyar mace ne yayi winning zukatan matan da ba soyayya ne ya hadasu bama ina ga sultana......a nan koda sakewa sultana yayi yace tayi rayuwarta,yayi imanin ba zata taba kubuta daga sharrin tsumammiyar soyayyar daya dasa mata ba.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 125
A nutse ya shiga motar,yayi bismillah