Showing 102001 words to 105000 words out of 294767 words

Chapter 35 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

shirin yin dambe da qaddararta.

A yanzun ba bibi kadai ba, kusan duk wanda keda ruwa da tsaki da rayuwarsa yasan a tunzure yake dashi,bazaiyi wani abu kuma da zai sake tunzurata din ba don yanzun tamkar itace sitiyarin gidan gaba daya,samun kanta shine samun kan kowanne mutum dake cikin gidan,don haka yaci gana da takawa yana nufarta

"Au......ba zaka dakatamin a nan ba?,la'ilaha illallahu......da gaske dai aliyyu ne!, jama'a kuzo ku ganemin ikon ubangiji na" ta sake fada cikin daga murya tamkar tanasom tara masa jama'ar gidan gaba daya

"Bibi kibi a hankali,ba fatalwa bane na gaya miki maina ne" tanja ta furta adan daburce ganin yadda bibi ta dage lallai saita hada masa jama'ar gidan. Shikam ko gezau be fasa takawa zuwa wajenta ba,yayin da taci gaba da kwakwazo da jan salati iri daban daban.

Yana isa dab da ita baiyi wata wata ba ya sanya hannu ya riqeta da kyau

"Sakeni,sakeni nace" ta fadi yana qoqarin qwace hannunta daga nasa cikin fada da hargagi

"Kiyi a hankali,tunda dai baki samu damar hadamin jama'ar da kikayi niyya ba aisai ki haqura ki zubawa sarautar Allah ido ko?" Ya fadi yana qoqarin zaunar da ita. Dukka sauran qarfinta ta sanya ta tureshi cikin fusata tana cewa

"Gafara can ka bani waje,wato nice marainiyar wayonka,ka tsallake katanga.ka shigowa mutane cikin gida a sirrance zaka zo.ka cuceni,banga alamar akwai wanda yasan da shigowarka cikin gidan nan ba" qaramin murmushi ya saki yana sake yunqurin riqota

"Allah ya kiyaye.......da lalacewa ta sameni,na gudu daga gida......na tashi dawowa na biyo ta katanga?.....ai kuwa da nayi asarar suna,kuma da daga yau na ajjiye sunan Aliyyu na koma aliya"

"Ahaf.......lalacewa kuma ta nawa?,duk dan da zai tsallake albarkar iyayensa yabar gida shekara da shekaru ai lalacewa ta gama samunsa" ta fada tana sake qoqarin tureshi . Har cikin zuciyarsa maganar tata ta bashi dariya,saidai boren nata yayi imanin mataki ne na nasara,nasarar da ya tabbata tana da alaqa da addu'ar da ya tsananta yi tun kafin ya sanya qafafunsa cikin gidan.

"Kina batan lokaci ki zauna ki marabceni kawai" ya fadi yana sanya qarfinsa cikin tausasawa ya maidata ya zaunar saman kujera,sai ya waiwaya yana duban tanja

"Jeki abunki kija mana qofa miji zai gana da matarsa" dan qaramin murmushi me hade da hawaye ya qwacewa tanja,tayi missing maina qwarai,bama ita ba,kowa dake gidan idan zaiyi magana ta tsakani da Allah zai fadi haka. Duk da zamantowarsa me zafi fushi da kuma zuciya......amma kuma shi din mutum ne me dadin mu'amala qwarai da gaske.

Gadon bayansa ta kaiwa dundu da dukka qarfinta tana fadin

"Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe nayi miji da kai,mijina jarumi ne,bai tana ja da baya ba" ta fadi tana yarfa hannunta,don dukan data kai masan ba shine yaji zafin ba itace taji,ita dimma bata ankara da wautar da tayi ba na kai masa dukan sai daya zauna ya babbake a gabanta sannan ta qare masa kallo tsaf. Ya zama ingarma dake da wani irin ginanne kuma tsayyen jiki da nuna zallar qoshin lafiya da cikakken qarfi,ko ina a murde alamun daga qarfe sosai sun bayyana ga jikinsa,duk da cewa cikin sutura yake cikakkiya.

"Bafa mainan da kika sani a baya bane kike dukana haka bibi?"

"Na sani mana.....wannan wani shashashan maina ne,gudajje daga gidan iyayensa bayan yaso ya kashe 'yarsa kuma 'yaruwarsa sannan matarsa" ta fadi masa cikin fushin zuciya,tana jin takaicin yadda bata da cikakken qarfin tureshi ta tashi a wajen ta daina kallonsa. Wani qasaitaccen murmushi ya saki yana sadda kanshi qasa kafin ya dagoshi

"Kowa na gudu.....kowa guduwa nayi.......bien(da kyau),duk kuci gaba da fada,ba laifi tunda abinda idanu suka gani kenan,amma nan gaba kadan zan tabbatar muku da sabanin fahimtarku" ya qarashe maganar yana jan siririn hancinta me tudu kadan wanda kusan dukansu irinsa suka gado,wani irin hanci me kyau dake qarawa fuska kyawu.

Hannunta ta saka ta buge hannunsa tana cewa

"Ka fita ka bani waje tun banci mutuncinka ba,ko kuma na kira ubanka ya fiddamin da kai,tunda naga alama shi kake tsoro" idanu ya fiddo waje,sai ya sulale qasa yana riqe dukka qafafunta hadi da dora kansa saman qafafunta,yayi laushi qwarai da muryarsa cikin sigar tausayi

"Indai ba bindigeni kikeso aba yayi ba kiyi haquri kada ki kiramin shi,dazun nan ya gama kwakwadamin mari,bibi kaman zai tsinemin,ama taqi koda kallo na,kema nazo kin juyamin baya bayan ko meye ya faru ke kika dauremin qarqashin aikatawa......." Bakinsa ta kaiwa bugu da sauri,saidai kuma bata sameshi ba don ya kauce yana boye dariyar dake subucewa tun daga zuciyarsa,fiye da rabin tsoro razani da quncin da yake ciki a yanzun baya jinsa tunda gangar jikinsa ta gamsu da cewa yana cikin gida...... yana cikin family dinsa,yana cikin ahalinsa iyalinsa

"Ni nace kaje ka yiwa diyar mutane fyade?,ka kusa kasheta?,ka illata mata idanu maina?" Ta fadi adan rude. Maganarta ta qarshe ita ta dakeshi,har ta sanyashi daga idonsa yana kallonta,dan siririn murmushin da ya soma samu saboda tubura bibi da yakeyi ya bace bat daga saman fuskarsa

"Illata idanu bibi?, yaushe?,garin yaya?" Tambayar tasa ta sanyata daga hannuwanta dukka biyun ta zuba masa ranqwashi da qasusuwan yatsunta da dukka qarfinta,ta yadda tazan zafin zai ratsa tarin sumarsa ya kuma isa ga ainihin tsakiyar kansa. Idanunsa ya runtse gam,saboda da gaske zafin ya isa har fiye da inda taso yaje din

"Ni zaka yiwa tambayar yaushe ka illatata din?,sanda ka aikata aika aikarka wa kayi shawara dashi?,oh.....ni 'yar nan naga ta kaina......ban sake yarda lallai baka da kunya ba sai yau aliyyu......tashi ka bani waje,kada ka sake shigomin guri,ban gayyaceka ba,daka dawo bani ka dawowa ba,tashi nace" ta fada tana tureshi da gasken gaske. Yaga fushi da motsuwar bacin rai saman fuskarta,amma kuma ta wani sashen da batayi zato ba akwai farincikin ganinsa danqare qasan zuciyarta wanda batasan wannan hasken yana bayyana akan fuskarta ba.

Tsam ya miqe din yana dubanta na wasu sakanni ya qare mata kallo,sai ya zuba hannayensa a aljihun wandonsa yana magana a nutse,duk da qasan ransa akwai razanin jin cewa ya yiwa idanun sultana illa,saidai yana mamakin ta ina?,don baiga wani nakasu cikin fararen zagayayyun idanun nata data jefa masa kallo dasu a makka da kuma dazu dazu ba cikin falon aba

"Zan tafi bibi,amma bawai na tafi kenan ba,zan dawo koda zaki yayyanka ni ki sakani a tukunya.......kafin na karbi kowanne hukunci ya kamata a bani damar magana koda ta minti daya ne,zan bayyanar da kaina a gobe gaban kowa,zan kuma karba kowanne hukunci da kuke tunanin na cancanci ns karbeshi" daga wannan ya soma takawa don barin falon,amma kuma idanunsa manne da bakin qofar dakin,dakin da bazai taba mancewa dashi ba......dakin da yasha mafarkin gashi a cikinsa.....wancan din daya faru yana maimaita kansa har sau babu adadi.....cikin kowanne dare da zaizo ya shude. Cikin jikinsa ya dinga ji tana cikin dakin,amma koda wasa bibi na wajen bazaiyi gangancin shiga ba,a yadda take a fusace ya tabbatar tana iya tayar da boren da a yau aba da bibi ma basu isa sunyi bacci cikin gidan ba.

Dai dai lokacin daya fita din ta sulale qasa tana jingina bayanta da qofar dakin bayan ta gama kallon komai dake faruwa tsakaninsa da bibita qaramar hudar da akayi don hangen wanda ke waje. Tana ganinsun,amma kuma bata iya jin abinda duke fadi a tsakaninsu. Tun dazun hawaye ya gama wanke mata fuskarta gaba daya,saita qarasa zama dirshan qasan dakin tana rufe fuskarta da dukka tafukan hannayenta.

Duk da batajin me bibi ke gaya masa amma kuma sai tayi mamakin yadda bibin ta tsaya saurarensa koda kuwa kanainayetan yayi. Ta dauka zata sanya qafa tayi fatali dashi,ta zaci zata sanya madoki tayita dukansa har sai ya fice musu a daki da qafafunsa,duk wani action na bibi bai burgeta ba duk data fuskanci bore tayi masa,so tayi bibin ta masa irin tarbar da zaiji baya da sauran sha'awar sake zaman gidan.

"Ke sultana!.....,kukan meye kikeyi?,kin manta yanzun ke ba sultanar baya bace?,kin manta a yanzun ke wata sultana ce ta daban?,a baya min xubda masa hawaye,a yanzun bai cancanci kici gaba da xubda masa wannan hawayen ba,ki qarafafawa kanki gwiwa,ki gayawa kanki da kanki a yanzun damuwa bata cancanceki ba.......kiyi moving forward,kada ki bari ya sake maidoki inda kika riga kika wuce" kaifafan maganganun da suka dinga kai komo kenan a tsakiyar qwaqwalwarta.

Sosai taji ta gamsu,ta yadda yanzun shi din ba kowan kowa bane cikin rayuwarta,bashi da kaso ko misqala zarratin a rayuwarta,me yasa zata bari ya dameta?. Da wannan tunanin ta isa gaban madubi tana kallon kanta da kanta. Da gaske ta canza,da gaske ba sultana yarinya qanqanuwa bace wadda zai yiwa qarfa qarfa......wadda zai yiwa.kama.karya......wadda zai yiwa dukkan abinda yaga dama yakeso,a yanzun ta girma......ta kuma mallaki hanakalin kanta,koda jama'ar dake kewaye da ita wadanda zata rayu dasu sai wadanda taga damar zama dasu ta kuma zabesu.

"Dole ya sani ya kuma shaidawa kansa da kansa da da yanzu ba daya bane" ta furta a fili qasa qasa tana motsa jajayen labbanta. Bandaki ta shiga,ta raba kanta da kayan jikinta ta watsa ruwa hade da alwala. Sakakkun kayan bacci ta saka don tafi sakewa,duk wani motsi nata tana furta

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" saboda zuciyarta tayi sanyi. Hijab ta sanya har qasa,ta isa qofar dakin nata ta murza key don kada ma su dawo su dameta,tun dacan dama bata kwana da kowa dakinta don batason takura ko hayaniya,yanzun ma bata son kowa ya dameta shi yasa ta rufe dakin,ta shimfida abun sallah tahau ta kabbara salla shafai ds wuturi sannan ta dora da nafiloli.

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 55



Idanunsa suna kan kowanne sashe na sassan nasa,yana nan kaman yadda yake,ba abinda aka sauya ba kuma wani abu daya lalace kamar bai dauki wadannan shekarun baya nan ba.

Duk inda ya gifta ba abinda ke dawo masa sai shekarun samartakarsa, abubuwa da yawa ya dinga tunawa har ya ratsa falonsa yakai ainihin bedroom dinsa.

Yana shiga almu yana ajjiye mop stick din daya gama goge masa tiles din wajen,suka hada idanu da maina din,sai yadan sadda kansa kadan. Abun almu din yana dan bawa maina mamaki,duk ya maidashi wani baqo qarfi da yaji,duk da ko a baya ba sakewa tsakaninsu sai desipline,amma kuma yana tunanin kaman a baqon almu yake kallonsa.

"Ina goumar?" Ya tambayeshi, tambayar data sanyashi daga kai ya kalleshi,don a nasa lissafin maina din bai wani san goumar can can ba

"Sunje niamy.....amma gobe da sassafe jirginsu zai iso da angon yaaya aminata" kai ya jinjina,shuru na wasu 'yan mintuna ya biyo baya,sai ya gyada kai

"Shikenan jeka,sai da safe"

"Akwai wani abu da kake buqata?" Almu din ya tambayi maina,har qasan zuciyarsa yana jin tausayinsa,duk da baikai wayon haka ba sanda yabar gida amma kuma yana iya tuna kulawa da yake basu,sa'annan a yanzun ya san cewa gagarumin qalubalen dake gaban yaa aliyyun,duk wata kulawa bazai sameta daga iyayensu ba

"Babu" ya amsa masa a taqaice

"Merci" ya sake fadi yana jin dadin yadda almu din ya nuna masa kulawa. A yadda yakeji din baya jin zai buqaci wani abu,nutsuwa kawai yake da buqata da kuma kebe kansa har zuwa safiya. Don haka almun yana fita ya soma zagayawa cikin dakin,yayi 'yan dube dubensa. Komai yana nan hatta da suturunsa ba abinda aka taba,ya maidasu waje daya ya killace,don a yanzun bazai iya amfani da ko daya daga cikinsu ba.

Kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya wuce bandaki. Ya jima yana dumama jikinsa sosai, tunani cunkushe a kwanyarsa. Baisan yaya safiyar gobe zata waye masa ba,baisan da wanne ido da kuma wanne hannu zasuci gaba da tarbarsa,saidai koma meye yana bawa kansa tabbacin juriya da dagewa hadi da jajircewa.

Kayansa da yazo da su ya bude,ya fidda pajamas marasa nauyi ya saka,kwanciya yakesonyi amma bayajin zai iya kwanciyar,don haka ya shimfida abun sallah shima ya kabbara sallah da tarin buqatu dake cikin ransa.


*********Tun asuba hayaniyar cikin gidan ta qaru saboda yawan jama'a da kuma hada hadar daurin aure da aka fara yi,wanda duka daurin auren su biyun zai gudana ne a babban masallacin alhj Mohammed mayak'i dake farkon street din nasu.

Tana idar da sallah ko hijabin jikinta bata fidda ba ta koma saman gado,idanunta fal da bacci don a jiya bata samu cikakken bacci ba.

Batasan adadin awannin data shafe tana bacci ba,ta daiji anata knocking sama sama amma bata ko motsa ba,don tasan mutane ne kawai zasu dameta,saidai a yanzun bugun da ake mata yasha banban da wadancan,don yanzun kamar za'a tsinke qofar a shigo,dole ta miqe tana lalubar dankwalinta da ya zame ta sanyawa kanta,sannan ta sauko daga saman gadon ta nufi qofar.

Yasime ne a tsaye,tayi kyau cikin shigar wani arnen farin lace da ya wadatu da ado da duwatsu masu qyalli,kana kallonta basai an gaya maka ba amarya ce, fuskarta ta dauki makeup sosai wadda ta sake bayyana ainihin kyan nan nasu da sukayi gado. Houda na tsaye a gefanta cikin army green shadda da sukayi anko dukkansu 'yammatan amare suka tsara zasu sanya a yau din. Wata harara ta jefa mata

"Wai bacci ma kikey?" Hannu ta sanya tadan dafe kanta

"Da ciwon kai na kwana Yasmin,don Allah karkiyi qorafi" ta fadi tana karya murya. Dariya ta bawa Yasmin din

"Kiyi ki shirya don Allah,kada azo daukan hoto bake a ciki"

"In sha Allah" ta amsa mata,wanda ita kanta tasan ta amsa mata ne kawai,amma sam yau bata sha'awar fita ko nan da can. Harabar gidan gaba daya bata burgeta,ta tabbatar a yau din kusan labarin da zaiyi trending cikin gidan shine labarin dawowar maina. Suna juyawa tana shirin maida qofar ta rufe tanja ta qaraso

"Ama tace na dubaki kin tashi?"

"Na tashi tanja......don Allah tea nakeso me dumi sosai,madara da sugar kadan"

"Tea kawai?" Kanta ta gyada mata tana lumshe fararen idanunta,bakinta babu test kwata kwata,shima tea din zata sha ne kawai maganin yunwa.

Tanja tana fita ta juya ciki ta soma zare kayanta ta fada wanka. Koda ta fito tanja ta aje mata tea din,sai ta zauna ta fara kurba a hankali tana dumama cikinta. A hankali sai tunaninta ya koma daren jiya,wata siririyar faduwar gaba ta ratsa qirjinta,ta maida idanunta ta lumshe tana son kauda surar fuskarsa dake gilma idanunta. Benazeer da batoul ta tuna,wannan ya sanyata ajiye cup din a hankali,ta jawo hijab ta zura ta nufi qofa. Tana gab da fita a dakin wata murya daga can qasan zuciyarta ta jefa mata tambaya

"Idan kinje gurinsun me zakiyi?,zaki hanasu yawo ne bayan gidan cike yake da yara?,kada kiyi abinda mutane ko shi kansa zaiyi tsammanin kin damu da sha'aninsa ne,bake daya ba,akwai dakaru a gabanki da bai isa yace zaya dauki yaran ko ya aiwatar da wani abu ba" ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dawo da baya jiki a salube,daga tsaye ta dauki tea din ta kurbe,saita koma wajen drawer dinta ta soma duba kayan da zata saka, zuciyarta da tunaninta haka kawai ya raja'a akan yaran.

Tun asuba yayi alwala ya kuma fita sallar asuba kamar yadda kowanne namiji dake gidan yakeyi tun gabanin barinsa gida,har kuma yanzun babu abinda ya sauya. Yana qoqarin fita daga makeken gate din gidan sukayi kacibus da aba adan hanzarce,da alama shima yaso ya makara ne. Idanu suka hada da aba din,sai ya janye idonsa tamkar ma baisan mainan ba,ya kuma qara taku ya wuceshi a sanda maina ke yunqurin yi masa magana. Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke yana lumshe ido hadi da budeshi,wannan abun idan aba yana masa shi yana sanyashi jin tamkar zai mutu. Ba haka ya saba masa ba,a shekarun baya kafin komai ya faru idan sukayi kacibus irin hakan da hannu yake masa nuni da ya matso,idan ya matso din kuma sukan wuce masallaci tare da aba din kafada da kafada,a yanzu da yake ganin akasin hakan sai yakejin kamar zuciyarsa zata tsinke daga qirjinsa,bazai iya jurar wannan halin ko in kula na aba ba. A baya yaci gaba da bibiyarsa har suka isa masallacin,sanda aba ke qoqarin kafa sahu cikin zafin nama ya tsaya daga gefansa,ya kuma daidaita sahunsa dana aba din. Yayi zaton zaiyi wani motsi amma sai yaga ko daga kai ya dubeshi baiyi ba,tamkar ma baisan dashi suka hada sahu tare ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login