Showing 15001 words to 18000 words out of 294767 words
Chapter 6 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
gwadata din. Ta tabbata sicklier dince kuwa, sicklier dinma irin chronic sicklier dinnan,don kuwa kwata kwata rayuwar nafessa kusan rabinta a ciwo take.
Allah ya mata halitta me sanyi,nafessa din yarinya ce me tsananin sanyin hali,shuru shuru,matuqar girmama duk wanda ya girme mata,ga tsananin son karatu kamar me?,saidai kuma karatun nata kusan rabi ne,rabin tana yinsa ne ga gadon asibiti. Duk da ana cewa sickle suna girma ciwonsu yana qara ja baya,ga nafessa abun ba haka yake ba,tana girma ciwon yana sake nuqurqusarta. Duk sanda ciwon nafessa ya tashi ba zaka iya banbance waye me ciwon ba tsakanin ita da maina. Ita kuka maina kuka,idan kaga walwalarsa to nafessa ta samu kanta. Koda bacci yakeyi muddin yaji murya ko nishin nafessa bacci ya qare masa. Abun ya sake dagawa ama hankali,tana ganin shaquwar kamar ta wuce hankali. Buqatun nafessa da hidimarta itace gaba data kowa cikin gidan,walwalarta itace tashi.
A haka shekaru suka dinga tafiya,shine komai na nafessa,shine gatan nafessa shine kuma mai tsaya mata,muddin yana wajen ba wanda ya isa ya tabata. Ya wuceta da aji daya,amma yasa aka maidashi baya ya koma ajinsu nafessa din,daga boko har islamiyya haka yayi ba tare da ama ta sani ba. Ranar data samu labari kuwa tashin hankali tayi sosai,har ta dinga ji a ranta anya wannan abun nashi na lafiya ne?. Tun nafessa nada shekara goma daga mohmoud har bintou raayinsu yazo daya na aurar da ita da wuri,saboda yanayin lalurarta suna ganin taci gaba da karatu ma kamar sun wahalar da lafiyar gangar jikinta ne.
FURUCIN da bibi tayi a wani lokaci kusan shi ya sake sanyata tsaiwa da qafafunta akan aliyyun nata. Ranar suna tasowa daga makaranta,sai ta rigashi tahowa,ashe wani ya biyota ya kuma tsaidata,maina din ya shigo gida yana cika yana batsewa, bibi tayi dariya tace
"To ko 'yar gida za'a yi?, irin wannan kishi haka maina?" A kunnuwan ama tayi zancan,saidai bata daga kai ta kallesu ba,saidai maganar ta sauka sosai cikin zuciyar ama din,ta kuma tsaye mata a rai,daga lokacin ta fara takatsantsan da fara janye maina din daga nafessa dama harkokin gidan gaba daya,makaranta ta sake samar masa wadda zai zamana sai kusan bayan isha'i zai samu sakewa cikin gidan. A lokaci shi da nafessa din duka suna ss.2, shekara daya kawai ya rage musu su zana jarrabawar kammala secondry school.
Rashin ganin maina din kwanakin da suka biyo baya ya sanya nafessa din zuwa har sassan wajen ama nemansa,abinda ba kasafai ta fiya yinsa ba idan ba mamanta ko bibi ta aiketa ba,duk da cewa ba wani abu ama ke nuna mata ba,hasalima tana mata komai na kyautatawa kaman kayan qyale qyalen rayuwa da sauransu saboda ita daya ce mace a gidan,don ko da su oncle bashar da ocle oumar sukayi aure yara mazan suma matansu dukka suka haifa,sannan ita dinma data sake samun ciki namijin dai ta sake haufa,duk da addu'ar data dinga yi da kuma qulafucin samu diya mace data dinga yi. Haka kawai dai ba sakewa tsakaninsu,ita ama zurfin alaqar dake tsakaninsu dinne bataso,da yadda dukka haidar ya tattare tsakaninsu da kuma bibi,ita din ta zama kamar ta haifa musu shine kawai.
"Yana makaranta" kawai ama tace da ita,sai ta miqe a sanyaye ta fice. A wannan tsakanin hamani ya dawo gidan sanadiyyar karatu da ya maidoshi nan garin,hamani d'a ne ga qanin mahaifinsu aba,hamani din kamar cousin yake a wajensu. Yana da matuqar kirki da son jama'a,uwa uba matashine me addini kamewa da sanin ya kamata.
Cikin lokaci qanqani ya fara sabawa da kowa na gidan,dukka yaran idan sukaji shuru na wasu awanni basujishi ba sun shiga cigiyarsa ina oncle hamani,harda nafessa kuwa,don kusan shike mata lesson din da yanzu maina baida cikakken lokacin yi mata shi yadda suka saba a baya.
A lokacin manema suka fara zuwanma nafessa din,duk wanda zayazo gurinta ko yace yana sonta sai maina ya sani,tare suke shawarar komai.
Kusan a kowacce qasa,kuma kowacce al'umma da yawanmu suna da qyamatar auren masu lalurar sicklier,to irin wannan qalubalen ne nafessa ta fara fuskanta. Tana da kyau ainun dake jan hankalin kowanne namiji,tana da nutsuwa da kamun kai dake bawa maza sha'awa,to amma kuma da zarar sunji irin lalurarta sai ka nema mutum ka rasa. Da yake auren bai kanta da farko bata wani damu ba har sai da tafiya ta fara nisa ta fahimci qalubalen dake a gabanta,ta kuma ga zallar damuwa tattare da mommanta. A hankali ta soma fahimtar komai,ya kuma soma damunta,maina dinne dai abokin shawara da fadawa damuwarta,sai kuma oncle hamani. Duk sanda wani yazo ya tafi da maina take tattauna damuwarta
"To sai meye?,yayita tafiya,Allah zai kawo miki wanda ya fishi" duk sanda ya fadi hakan hankalinta yana kwanciya sosai.
Ranar da zuciyarta ta karye sosai ranar da wani hafizzou ya shaida mata soyayyarsu ba zata iya ci gaba ba. Shigowar maina gidan kenan daga makarantar manya ta dare,yaga fitar hafizzou ya kuma ga shigewar nafessa ciki da sassarfa sassan bibi,sai kawai ya take mata baya yana addu'ar Allah yasa bame afkuwa bace ta auku.
Yana shiga ya sameta saman cinyar bibi din tana sharba kuka. Aba na falon haka haka ama,suna list na abubuwan da bibin keso ama zata taho mata dasu daga Nigeria,don saura kwana uku ta wuce can din,kasancewar bata rabo da zuwa don suna da tamfatsetsen gida a can da idan sunso suna iya share wata uku ciki kafin su dawo niger,ita da aba ko ita daya dinma.
"To sai meye?,a kansu kike zubda hawayenki nafessa?,suyita tafiya din,ni zan aureki,na yarda ni aliyyu zan aureki" ya fada cikin tsanani fushi da zafin zuciya. Ba ama kadai maganar ta yiwa luguden duka ba,har bibi da ita kanta nafessa din. Dif falon yayi abinda maina bai tsaya wani la'akari dashi ba yaci gaba da zazzaga masifa.
Sakale ama kawai tayi tana kallon ikon Allah kuma zatonta yana sake qarfafa lallai aliyyun wasu ta haifawa. Zuciyarta ta gaza daurewa ta daka masa tsawa me qarfi
"Yima mutane shuru dalla,shashasha!,fita ka bawa mutane guri" ta fadi a harzuqe. Har ya fitan suka gama abinda sukeyi ta fice itama babu wanda yace komai akan maganar.
Cikin kwanakin ukun tanata shirin tafiya Nigeria amma ranta a matse yake,gaba daya ta rasa walwalarta,hatta aba da maina sunga canzawarta,tanata juya furucin maina a ranta,tana kuma hankalce da yadda suketa dan shige da fice a sassan bibin lokaci zuwa lokaci. Bataji koda d'ar ba,saboda ta riga ta sama ranta ko sama da qasa zasu hade ba zata yarda maina ya auri nafessa ba,abumma sam bai kama hankali ba,ko ita da mahaifinsa da sukayi aure duniya nada ragowar kwanciya ai dukkansu sai da suka mallaki hankalin kansu sannan sukayi,uwa uba ma kuma bataga dalilin da zai sanya ta bari maina din data dora buri a kansa ya auri sicklier ba,duk da nafessa bata da matsala ko makusa tako ta ina,amma abun ita sam bai kama zuciyarta bama bare hankalinta.
Haka ta tattara harda maina din suka wuce Nigeria,abinda yasa ta gane da wani abun a qasa,tun sanda zasu taho basuyi sallama da aba ba yadda suka saba,sannan a qa'ida tare suka tsara zasu tafin amma shi ya janye tashi tafiyar,bataji dadi ba amma ko a jikinta suka wuce din.
Sanda ta kammala kwanakin data diba zatayin sai taji kwata kwata bata sha'awar komawa nijer,tayi zamanta a nan din duk da lura da tayi maina ya takura su koma din. Suna hutu ne a sannan,kuma hutunsu yakan dauki dogon zango wani lokaci wata uku har hudu ma,ba guntun hutu irin namu ba,wannan ya sanya ta sake miqe qafa,tayi biris kamar bata karanci damuwarsa ba.
Sati guda ta qara akan ainihin kwanakinta aba yayi mata dirar mikiya. Hakanan kadaran kadaham babu wannan karsashin kamar yadda suka saba. Kwana daya kwana biyu shuru,a kwana na ukun suna breakfast da safe ya dubeta yana gaya mata labarin da ta jishi kamar saukar aradu
"Mun yanke shawarar daura auren maina da nafessa" a wani hargitse ta dago tana dubansa
"Wanne maina din?,kana nufin aliyyu haidar?,wanda ko qaramar secondry bai gama ba?dududu shekarar haidar din nawa?,,baya ga haka ka manta nafessa sa'arsa ce?,watanni sha biyu kacal ya bata?,ka manta matakin lafiyarta?"*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 08
"Dukka wadannan lissafinki ne,ba ruwana dasu" ya furta cikin halin ko in kula.
Wannan magana ita tayi silar kawo rikicewar familyn MAYAK'I a karon farko,ta nesanta zazzafar soyayyar dake tsakanin aba da ama me matuqar danqo,soyayyar da bibi bata taba sasanci ba a tsakaninsu,saboda ba qarya hamdiyya ta iya riqon miji qwarai da gaske.
Batayi qasa a gwiwa ba ta yanki tikitin komawa nijer saboda ta tabbatar ba shi daya yayi wannan shawarar ba. Ta dire gaban bibi takuma lissafa mata dukka hujjojinta na rashin amincewa da batun auren maina da nafessa. Bibi din jinjina kai kawai tayi, bata fidda matsayarta ba,don a duniya ba wanda zai kaita son ganin maina da nafessa qarqashin inuwa guda.
Ganin yadda abubuwa keta rikicewa cikin gidan ya sanya oncle mohmoud wanda tunda aka fara lamarin har sanda su bibi suka yanke hada auren bai taba magana ba sai yanzu ya gurfana gaban bibi yace yana roqon alfarmar abar wannan batun,ko don hamidou ya samu zaman lafiya da iyalansa,maina kuma ya samu albarkar mahaifiyarsa. Kai da fata aba yace shifa baisan zance ba,ya riga ya bawa maina nafessa,babu kuma fashi, saidai hamdiyya tabar aurensa.
Sosai maganar ta taba bibi,salin alin ta kwabeshi itama,tace kuma an janye maganar. Kamar jira hamani yakeyi yace shi zaya auri nafessa. Ba wanda ya qyamaci abun a cikinsu,saboda hamani din managarcin mutum ne,kuma dama can shi bame kule kule bane,hasalima babu wata yarinya da yake nema. Dai dai sanda ya kammala Phd dinsa daidai sanda nafessa ta kammala secondry school,babu jinkiri aka gabatar da komai,aba ya daure qarqashi akayi gagarumin biki, Wanda kamar ama tasan za'a yi hakan ta saka maina a gaba suka wuce Nigeria.
Tunda suka tafi din bai dawo nijer ba,hasalima sai ya fara neman gurbin karatu a can,don baijin zai dawo nijer kuma rayuwa taci gaba da gudanar masa kamar yadda yakeso. duk da yayi murna qwarai da nafessa ta samu mutum kamar hamani,yayi imani ba ita babu kuka saboda nagarta da kyan zuciyarsa.
Duka duka auren nafessa watanni shida,tana da ciki wata hudu bintou mahaifiyarta ta rasu. Mutuwar ta girgiza ta ta kuma jijjiga mohmoud,saboda shi kadai yasan irin macen da Allah ya bashi. Albarkacin samun nagartaccen miji dukan mutuwar yazo mata da sassauci,ya tsaya kai da fata ganin matarsa bata fuskanci raurawa ba.
Watanni uku da kwana goma nafessa ta haifi SULTANA, yarinyar da ta samu soyayyar da har ta dara wadda mahaifinta da kuma maina din ya samu,yarinyar data debo kamannin NADEEYA abinda ya qara adadin soyayyarta a zuciyar kowa da kowa. A sannan tuni dukiya ta fara yiwa aba ambaliya,ya fara shiga jerin sahun attajiran 'yan kasuwa masu cin gashin kansu,don bai jima da dukiyar ama a hannunsa ba ya damqa mata komai ya dorata akan turba ya kuma bata cikakken damar kula da dukiyarta kamar yadda kowanne namiji zaiyi shi kuma ya waiwayi tasa.
Iya bikin suna kawai kudade aba ya zuba masu ciwo yace ayi,duk da hamanin ma ba baya bane gurin samu,don tun yana lavel one a jami'a ya fara kasuwanci,kawo yanzu kuwa shima ya zama babban qwaro. Gata iya gata ta kowanne fanni. Ga hamma MAHMOUD jin sultana yake kamar wani yanki na jikinsa, soyayyarta bata taba boyuwa muddin zaka zauna dashi koda na minti talatinne. Ya zubawa sultana so wani irin so me tsayawa a zuciya tun tana zanin goyonta. A haka aka fara rainonta kafin me afkuwa ta afku,mutuwa ta rabata da mahaifiyarta nafessa.
Mutuwar ta daki maina matuqa ta kuma galabaitar dashi,sai kuma a lokacin mutuwar ne ya fara dora idanunsa akan sultana da a sannan take koyon zama watanni uku da kwanaki a duniya.
Wani irin masifaffen so ya azawa sultana,bama shi kadai ba kusan kowa na cikin gidan,yana ji a ransa kamar yanzun sultana responsibility nasa ce,kamar shike da alhakin komai nata. Rasuwar nafessa da samuwar sultana ya sanyashi ajjiye karatunsa ya dawo gida nijer. A hannunsa sultana ta taso,ya zama shine uwa kuma shine uba a gareta,tsarkin kashi wanka raino rashin lafiyarta dama walwalarta dukka na hannun maina. Maina ta budi idanu ta gani a matsayin uwarta kuma ubanta tun gabanin ma hamani da hamma mohmoud din suma subi bayan nafessa sanadiyyar hatsarin motar da suka samu shi da shi a hanyarsu ta dawowa daga ziyarar kabarin nafessa din. Wannan maraicin da sultana ta sake tsunduma ya sake ninka soyayyarta,ya kuma sanyashi sake ninka kulawarsa ninkim baninkin a kan sultana,ya ajjiye karatunsa gaba daya saboda ita,wasu abubuwan tun bai iya ba har ya qware sosai,hatta jakar goyon sultana yana da ita,yadda yarinyar ta taso tana qulafucinsa sai ya masa kamanceceniya da mahaifiyarta. Ta dabance sultana cikin gidan kamar yadda komai nata ya zama na daban,tana da farinjinin da kowa ya shigo sai ya dauketa ko ya tankata,tana da yawan surutu tun shekarunta suna qananu ainun,tana da kazar kazar irin ta masu cikakken lafiya.
Halasci da sadaukarwar mohmoud ba abune qanqani ba da zaiyi saurin bacewa zukatansu ba,ba qaramin abu bane da zaiyi saurin shafewa a rayuwarsu ba,a wajen aba hamma mohmoud din uba ne wanda yayi masa komai a rayuwa,bashi da abinda zai saka masa dashi face ya bawa jininsa qwaya daya tal da ya bari a duniya dukkan soyayya qauna da kulawa,wannan ta sanya ya fifita sultana akan kowa cikin gidan,buqatarta ta zama gaba akan buqatar kowa.
Ya koma makaranta a nan maradi amma saboda hankalinsa nakan rainon sultana sai karatun nasa ya zamana asha ruwan tsuntsaye ne,yaqi ya maida hankalinsa duk da karatunsa karatu ne me tsada da wahalar samu,yake kuma da buqatar maida hankali akai. Aba da kansa da ya fahimci muddin yana tare dasu ba karatun zaiyi ba,sai ya maidashi niamy,ya tafi kuma da sharadin sai yayi shekara cur aba yaga kamun ludayin karatunsa sannan zai barshi ya fara zuwa gida weekend. Itadai ama bata tanka ba,don zuwa sannan ta zama 'yar don't care game da komai na cikin gidan,ba komai take sanya baki ba duk da dama ba halinta bane shishshigi,sa'annan har kawo yau aba zafinta yakeji akan hana auren maina da nafessa. Dukka tulin soyayya da suke nunawa sultana bataga aibu ba,don sultana din jinin mohmoud ce, MAHMOUD kuma abun asoshi ne,ko ita yana daya daga cikin mutane masu muhimmanci cikin rayuwarta,abu daya ne ta dinga jiye musu wanda a yanzun ya riskesu,sangarcewa da lalacewar tarbiyyar da maina keta fadi tashin ganin tafi kowanne yaro cikin gidan,abinda ta dinga gane musu kenan,amma taja bakinta tayi shuru don tasan ba muhallin da zatayi magana bane,don ba lallai su fahimceta ba. Kaf yaran gidan ita kanta sultana din tafi shiga ranta,tana tausayinta saboda maraicin da take ciki ta kowacce fuska,amma hakanan ta barma ranta hakan saboda a qalla dai a samu wanda koda da kallo zaya nuna mata kuskure idan ta aiwatar cikin gidan,sannan ba lallai su gamsu da ita ba wai don ta nuna tana qaunarta,duk da cewa tasan kusan komai ya riga ya wuce,family ne da basa da riqo sam sam sam,daya daga cikin halayensu dake burgeta.
Sanda ya cika shekara ya fara zuwa gidan bai fahimta wani sauyi sosai daga gareta ba. Saidai bahaushe yace sannu sannu hata hana zuwa saidai a dade ba'a je ba, shekara guda da fara zuwan nasa ya karanci komai,hankalinsa ya dagu sosai,yayi iya bakin dukka qoqarinsa wajen saita komai amma inaaaa......wannan shine ya zama SILA kuma SANADIN KADDARAR data samesu a yanzu.........KADDARAR da zata budewa SULTANA da MAINA qofofi masu tarin yawa.....
_Barkanmu da sauka😄,muje zuwa guwa ga tsakiyar labarin_🤩
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar