Showing 123001 words to 126000 words out of 294767 words
Chapter 42 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
na na karba......tunda da gumina......da kudina a matsayina na dan makaranta na biya sadaki.......zan iya yarda idan kikace nayi abun ne ta yarda ya dara shekarunki......but har a gurin Allah bani da laifi.......wannan kuma bazai zama hujjar da a yanzun zan dinga baki dama kina gayamin dukka maganganun da suka zo kanki ba,bazanyi tolerating rubbish ba.......dole dole kisan matsayin da Allah ya bani a kanki......ina buqatar zama muyi magana dake ta fahimtar juna.......zan nema afuwa a duk guraren da kike ganin na saba miki" batayi shirin zama ba amma sai data koma da baya ta zauna saman kujera,batayi tunanin yana da zarra da qarfin hali har haka ba,batayi tunanin akwai lokacin da zayazo ma ya tsaya a gabanta ba bare ya fadi mata ire iren wadannan maganganun,yanzun yana ganin laifinsa da qanqanta har haka?.
Kaman yasan me take saqawa a ranta sai ya maida hannayensa yana goyesu a bayansa,sannan ya fara takowa zuwa kujerar da take zaune a kai, tahowar tasa data sanya hanjinta kadawa,zuciyarta kuma na saqa mata tsaf zai iya maimaita aikata abinda ya aikata a baya. Wani irin hautsinawa tayi gefe,sai gata ta sauka a qasa,zata miqe ya cimmata,ya sulale shima a hankali ya tsugunna a gabanta,tsugunnon da ya basu kusanci qwarai
"Kar ka aikata" ta fadi kuka yana qwace mata sanda ya miqa hannu da nufin janye mata gashinta daya warwatsu har kusa da idonta
"Halalina ce fa" ya fada calmly
"Bani da wani miji.....ni ba matar kowa bace!" Ta fadi tana jin zafin kiranta da matarsa da sukeson gwada mata qarfa qarfa shi da goumar
"Am really sorry.......kowanne kalan ban haquri kikeso ki fadi zan miki shi SULTANA" Kaf gidan yafi kowa iya furta sunanta,kaman saboda shi aka halicci sunan,kaman sunan yasan shine wanda ya zaba mata shi.
"Bana buqatarka a rayuwata......ka fitamina a rayuwa"
"Am so sorry sultana.......ni benazeer da batoul muna da buqatarki......kiyi haquri ki yafemin,let build a home ni dake for our kids please" sosai ta bude fararen idanunta da suka koma kalan manja a kansa
"Which kids?,baka da wasu yara,yara yaranane......kaman yadda ni ba matar kowa bane.......zasu samu wani iban,nima zan rayu da duk mijin da na zabawa kaina wanda yasan darajar rayuwa da mutuwa" wani ciwo maganar take ji masa a zuciyarsa har yanajin kamar bazai iya ci gaba da dauka ba
"don't say that please 🙏" ya fada idanunsa a rufe gam
"Bazan daina fada ba!.....bazan daina ba,that's my truth!" Dole ya sake bude idon nasa a kanta a Karo kusan na uku
"Baki canza ba har yanzu sultana?,da gaske akwai sauran wani gyaran?" Tambayar da yayi mata kaman ya sanya sarqa ya kulleta ne,tanason ta fahimci abinda yakeson cewa ta kuma gaza fahimta din,sai kawai ta sanya hannayenta duka biyun ta dafe qasa taja da baya sannan ta miqe tana son dosar qofa
"Ba abinda zai canza a maganata hukuncina da kuma ra'ayina,you better to stay away from me........"
"How can I do that?,dukka rayuwata tana tattare da ke,'ya'yana gudan jinina......matata....."
"Baka da mata.......kalamanka ba zasu taba rusunar da zuciyata ba........ saboda kai din azzalumi ne.......me take......" Labbanta basukai ga qarasa cewa komai ba suka tsinci kansu tsakiyan tausasan nasa labban,kafin tayi kowanne yunquri ya hadeta da bango sosai ya kuma sakar mata qarfinsa,sannan ya sanya hannayensa ya riqe kanta da kyau yana sake kamo labbanta sosai cikin bakinsa.
Kamar ya samu sweet haka ya dinga sarrafasu daga lips nata har zuwa harshenta. Wata muguwar gigicewa tayi,saboda yadda abun yazo mata a bazata,ta sanya hannayenta ta dinga dukan qirjinsa da yunqurin qwacewa amma sam bai saurara ba bai kuma dakata ba,duk abinda tasan zatayi don ta dakatar dashi tayin amma hakan baiyi tasiri ba,sai kawai ta tattara dukka yawun bakinta ta tura masa bisa tsammanin zai janye. Zut taji ya zuqeshi gaba daya,ya kuma sake zura harshensa cikin bakin nata kaman ma me neman qarin yawun nata,abun sai ya zafafeta ta fashe da kuka gaba daya.
Sai daya tabbatar dukkan tsoro da mutuwar jiki sun mamayeta sannan ya zame bakinsa daga nata,tana zaton zata tureshi ta zille sai ya riqe qugunta sosai yana kallonta da lion eyes dinsa da sukayi matuqar yin laushi. Sosai qirjinsa ke bugawa fat fat har kana iya hangen hakan ta saman rigar kaftan din jikinsa,hawaye sun wanke mata fuska sosai,yayi mata riqon da ba abinda ke faruwa sai musayar numfashi da sukeyi shi da ita,ya fidda nasa ta zuqa ta fidda nata ya shanye,idan kuma ta kawar da fuskarta wani gefen ya sanya hannun ya tallafota,tanata bitar kalma guda da zata gaya masa da zata sanyashi jin haushi ta qona masa zuciya ya saketa ko bai shirya ba,tana kuma tunanin abinda zata fada din me zaya haifar mata
"Idan baka sakeni ba zan maka ihu na rantse da Allah" duk ya yadda idanunsa ke lullumshewa amma sai da maganar ta sanyashi fidda wani sassanyan murmushi me qaramin sauti,riqonta ya qarayi da kyau yana duban tsakiyar qwayar idanunta. A hankali yakai yatsansa gefen idonta guda dayan yana rayawa a ransa wataqila wannan shine tabon da ya kusa illata mata idanu. Idon nata ta runtse hawaye sabbi suna fita. Sosai yaji zuciyarsa ta matse,yaji zafin kansa da kansa sosai,shaidan tabbas yayi tasiri a lokacin,ya kuma iza masa wutar zafin kai data zuciya sosai a sannan,but......yayi alqawarin shafe wannan tabon dama lalurar gaba daya muddin yana numfashi
"Da kin kyautamin,kin kuma gajarcemin wahala......anyways......daga yau duk sanda kika taba lips dinki ko kika kalleshi a madubi zaki tuna cewa ke matar aure ce,kuma uban jarumin uban 'ya'yanki yana nan......na yarda ni din me laifi ne......duk wata tuhuma zan karbeta hannu bibbiyu......but tsiwa......da barranta kanki da yarana daga gareni wani abune da zuciyata ba zaya iya dauka ba" harara sosai take balla masa wannan karon,ta sake tattar qarfinta ta tureshi tana rushewa da kuka sai ya saketa wannan karon babu ja,ta nufi qofa yana yunqurin budewa
"Nop.....jirana zakiyi ai tare zamu shiga cikin gidan" ya bata amsa yana tattare hannun rigarsa sannan ya bude toilet din falon ya shige.
Sulalewa tayi ta koma gefe ta zauna tana sake sakin kukan,gaba daya abun nasa yazo mata da rainin hankali,ta yaya shike da babban laifi ko tace manyan laifuka irin wadannan dukka ya zauna yana qanqantar dasu a idanunta?,yana abu kaman baisan girman abinda yayi mata ba?.
Ya jima cikin toilet din yana ajiyar numfashi idanunsa kan fuskarsa daya bayyana tar gaban madubi,emotions da yawa yake gani saman fuskarsa
"Alhamdulillah" ya furta can qasa amma a fili,lallai addu'a ba abun banza bane,bare addu'a gaban dakin ka'aba?. Ya tsammaci bore fiye da wannan daga wajenta,sai gashi komai da alama zayazo masa da sauqi
(Nidai nace uhmmm malam aliyyu haidara,ba girin girin ba dai tayi Mai,kabi a hankali da sultana😂).
Alwala ya dauro sannan ya fito yana warware hannun rigarsa, idanunsa yakai kanta,sai baice komai ba ya fara takawa yana nufar qofar.
Key ya zura ya bude qofar sannan ya waiwaya a nutse ya dubeta
"êtes-vous prêt à aller?" Ya tambayeta yana tsareta da kallonsa hadi da miqa mata mayafinta. Kaman ba zata karba ba amma ta daure ta miqa hannu,sai ya gaza zare idanunsa daga dogayen hannun nata dake dauke da farar fatar da kamar ka wanke hannu kafin ka taba. Ganin kamar baida niyyan bata sai ta saka hannu tana zare shi daga hannunsa,dab da zata kammala zarewar yayi caraf ya riqe mayafin yana duban cikin idanunta
"Daga yau......kada ki sake fita bada izini na ba" haushi takaici,kaman tayita zunduma ihu haka taji,ta gaza jurewa sai data watsa masa wani kallo. Koda batayi magana ba yasan sarai meye a cikin ranta,shi ya raineta,duk wani motsi nata koda batayi magana ba yana fahimta,don haka ya sake riqe mayafin da kyau cikin hannunsa yana kuma sakar mata wani kallon da ya tabbatar sai ya isa har tsakiyar zuciyarta
"Idan da ba'asan inda nake ba,kuma ba laifi idan kinyi hakan,a yanzun ina nan,kuma ina shirye da sauke duk wani hakkina.....kema kuma dole ki sauke hakkinki"
"Dole?" Ta tambaya cikin salon mamaki tana kallonsa da rinannun idanunta,kai ya daga mata don son tabbatarwa
"Qwarai kuwa" so takeyi ta gaggaya masa maganganun da zasu yiwa zuciyarsa nauyi amma tata zuciyar sai ta kwabeta
"Kada ki fara,a nan din daga ke saishi.....karki maimaita kuskuren da kikayi a baya" wannan ya sanya ta tattaro dukka kalamanta ta hadiyesu,sannan ta sake zare mayafin sai ya sakar mata. Yana tsaye ya tsareta da kallonshi har ta lullube kanta saidai baiga ta motsa ba,ya fahimci me take buqata,don haka ya matsa daga bakin qofar yana cewa
"Bismillah" a nutse ta tako zuwa shiyyar ta kuma giftashi, iskar data kwaso din ta watsa masa lallausan qamshin jikinta wanda ya sanyashi sakin wata ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa tamkar yaron da yayi kukan neman mamarshi har ya gaji. Ko kafin ya bude idanunsa sai ya taras har ta fice ta kuma fara nisa da inda yake,sassarfa takeyi tamkar wadda ke gudun tserewa mayunwacin zaki. Murmushi ya qwace masa,kwata kwata sauri bai dace da tsarin halittarta ba,amma sai yayi tsaye,sai data qurewa saurinta,sai gashi a qididdigaggun taku ya cimmata.
Kamar ko yaushe,qamshinsa kadai ya sanya ta fahimci yana dab da ita,koda ta waiwaya ta ganshi saita fara qaramin gudu tana nufar sassan bibi,abinda ya bashi mamaki kenan,sai ya qara saurin tafiyarsa yana biye da ita......baisan me bibin zata dauka ba idan ta gansu a hakan sun shigo tare,koma meye a yanzun zatace ko zatayi bibin ko a kwalar rigarsa,kome dai meye she's his wife......kuma bazai taba bari damarshi ta kubce masa ba. A shirye yake ya fuskanci kowanne qalubale ta dalilin haka......komai tsanani,komai runtsi......
_maina fa da gaske yake_😂
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 65
Bibi na daga tsaye tana qoqarin karbar daffafiyar nonon raqumi me dumi da takansha daga hannun bilki taji sautin sheshsheqar sultana din,ko kafin ta waiwayo ta iske bibi din ta kuma rungumota ta baya tana sauke kanta a bayan bibin tana kuma sake fashewa da wani kukan.
"Meye haka?,lafiyarki?" Ta jefa mata tambayar dai dai sanda maina ke shigowa falon. Idanunshi a kansu kaman yadda bibi itama take kallonsa,saita rasa bakin magana,ta dubi bilki
"Ajjiyemin madarar ki tafi abinki" ta amsa mata cikin girmamawa,ta qarasa kan daya daga cikin tables na glass dake tsakanin kowacce kusurwa ta kujerun falon ta aza akai sannan ta wuce.
A nutse abinsa ya qaraso cikin falon,ya samu daya daga cikin kujerun ya zauna ya kuma miqa hannu ya dauki daffafiyar madarar ya kurba. Sosai yayi missing al'adunsu,sosai yayi missing komai da ya shafi abzinawa,sai yanzu yakejin komai din yana dawowa cikin jikinsa
"Me kayi mata?" Bibi ta tambayi maina tana dubansa ganin yadda kukan sultana ke qara yawa. Sauke cup din da yakai bakinsa yayi yana dan juyashi a hannu sannan yace
"Ki tambayeta mana bibi.....nidai bansan wani abu da nayi mata ba......"
"Aliyyu" bibi ta kira sunansa na aihini kai tsaye
"Banason a samu matsala ko maimaicen kuskure"
"Ba za'a zamu ba bibi......ba wani abu nayi mata ba,kawai nasan na ja mata kunne ne kadan,tana yimin tsaki tana kuma gayan magana ba ta hanyar data kamata ba,ina cewa kun koya mana girmama babba ko?......to don Allah bibi ki sake karanta mata kafin ta fara zaman aure cikin gidanta ta gyara dukka wadannan dabi'un" maganar tasa saita zama kamar turin wuta,da sauri ya daga fuskarta daga kafadar bibi zuciyarta tana zugi cikin kuma muryar kuka tace
"Kinji ko?,kinji ko bibi?,ki gaya masa ya fita sabgata ya fita rayuwata,don ba abinda ya hadani dashi,bani da wata alaqa dashi,kuma ni ba matarsa bace na gaya masa,yaje ya nema matarsa,ki gaya masa yayi nesa da lamurana,tunda nidai ban shiga nasa hurumin ba" tana kaiwa nan ta saki bibin ta wuce ciki da sassarfa tana ci gaba da sakin kukanta.
Da kallo dukkansu suka bita,saidai sanda bibi ke dawowa daga nata kallon shi ya dauke idanu ya fuske din baiso ma bibin ta gani. Rai ta hade tsam tana dubansa
"Waikai din wanne irin yaro ne?,ka dawo da wannan manya manyan laifukan kuma kake tunanin kawai kai tsaye zamu baka ita?" Idanu ya zubewa bibin ga mamakinta sai taga ya saki murmushi
"To bibi idan baku bani ita ba dafata zakuyi ku cinye?,ni kadaine zan iya da ita bibi,sannan bugu da qari ma ai nasan kuna buqatar ganin wasu twins din ko?" Turqashi!,bibi ta fadi a ranta,yaushe aliyu ya soma komawa haka?. Bai taba gwada magana irin wannan ba don haka duk furucin sai ya sanyata ta daburce
"Qaniyarka.....ni kake gayawa irin wannan maganar aliyyu?,zaka maimaitata ne a gaban hamidou kuwa,kaga shi sai ya dauketa ya bakan" siriryar dariya ya saki,yasan a nan wajen bibi din nasararsa take
"To kece bibi mana,kun dameni da cewa na tafka laifi,laifina daya na rashin bayyana kaina ga kowa na karbi laifina a bayyane,amma duka sauran abinda ake tuhumata akai ban karba ba ban kuma yarda ba,ke kika sanya su aba da oncle bashar suka bani lasisin aikata komai fa,sannan a yanzun ki dawo kina min qorafi bayan abinda kikeson ji da gani kenan,gashi kinji kin gani harda result ma"
"La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam" bibi ta jawo dogon salati kai kace mutuwa ce akayi mata
"To da alama wannan shari'ar nema takeyi tafi qarfina,bari ka gani" ta fadi adan diririce tana juyawa kaman zata bar falon. Cikin zafin nama ya miqe ya tareta,ya kuma riqeta da kyau yana cewa
"Haba bibita......zo kiji,ai ba za'a yi haka ba" ya qarashe maganar yana zaunar da ita saman kujera,shi kuma ya koma saitin qafafunta ya zauna yana dan tausa mata qafar a tausashe.
Idanu ta zuba masa,sai yayi mata shuru ya qyaleta har sai da tayi hararar me isarta sannan ya sake matsowa kadan murya a tausashe
"Duk ki gama hararata bibi..... Allah dai ya rufa miki asiri kawai da baki zubda min cikin yara ba,da wataqila yanzun ina nan ina shari'a dake" baki ta bude galala,kunya kuma tana dabibayeta,saita watsa masa daquwa
"Ungo nan.....qaniyarka,wanne shaidanin ne ya gaya maka wannan maganar......nasan ba aikin kowa bane wannan saina wancan dan banzan goumar baqin buzu" yadda a yau din tayi amfani da sunan da sultana tafi kiransa dashi ya sanyashi sakin murmushi me sauti
"Kinyi zaton bana bibiye da rayuwar sultana?,kin dauka na watsar da ku da ita ne gaba daya?" Tambayar da ya jefa mata ta sanyata tsaiwa kawai tana dubansa
"To bari na baki labari" sai ya sauke qafafunta qasa,ya kuma fara gaya mata abubuwan da tayi imanin da gasken yana tare dasu,da gasken yana bibiye da motsin sultana lokutta da yawa. Haihuwarta tafiyarta Hassan gwarzo,metron asabe da ya bawa kwangilar kula da sultana da duk abinda takeso tsahon shekarun da zatayi ta kammala,wanda daga nan ne sadarwashi da ita ta yanke,ya tafi karatun da ya dauki alqawarin ma daddy daya kubutar dashi daga hannun mutanen da suka so tilastashi shiga aikin S.S.....ya kuma zo ya rasa number goumar tun ranar da shima yaje visiting hassan gwarzo
"Kowa bai ganni ba amma goumar ya ganni,har yayi wata magana a sannan da na tsammaci zaki dauki haske(inama kina iya ganin abinda nake gani)" fes maganar ta dawowa bibi,ta kuma tuna sanda goumar ya fadi hakan yana kallon wani guri daban,duka ta zaci iya shegensa ne kawai,ashe magana yake mata me harshen damo.
Hirarsu dashi din a yanzun ta sanyayawa bibi jiki,ta kuma fahimci a kame yake a hannun wasu da sukayi masa dauri me kamar sake don su sakashi cikin aikin da baiso qarfi da yaji.
Ajiyar zuciya ta saki tana lanqwasa yatsunta sannan a nutse tace
"Duk na fahimceka,kuma ka sani bana goyon bayan raba aurenka da sultana....... saidai ko kadan bazan tilastata zama da kai ba,bazan kuma baka izinin takurata ba,kabi hanyar data kamata ka shawo kanta ka amintar da ita,sannan kuma uwa uba ka sanya soyayyarka a zuciyarta".
********Tun daga wancan ranar da abun ya faru ta yima kanta alqawari ya daina ganin koda gilmawarta bare ya samu qwarin gwiwar tsareta da wasu kalamanta da sam basu da tasiri a gareta. Ta gwammace ta kwanana a daki sannan tayi wuninta gaba daya a dakin. A yanzun hatta da gilmawar benazeer da batoul ya ragu sosai cikin gidan,saboda bini bini suna tare da maina din,tana sane da komai,amma ta barsu ne ta zuba masa idanu taga iya gudun ruwansa. Abinda yafi komai yi mata dadi shine,kwanakin da zasuyi cikin gidan ba masu yawa bane,tasan komai ya kusa zuwa qarshe,da zarar ta wuce Paris ina zaya ganta bare ya gallabeta?. Bataga wani sakewa tsakaninsa da ama ba bare ta sanya ran zata zauna tayi dogon zancan da ya shafeta dashi,su benazeer kuwa ko kadan bata taba bari sun san lokacin komawarsun ba,don tasan su kadaine hope dinsa da zaiji komai daga garesu,musamman benazeer da bakinta bayaniya shuru,rawan kanta akan daddynta kuma ya fara bawa suktanan tsoro,ko shigowa sukayi gaidata in sha Allah kafin su fita a dakin sai ta mata zancansa,saidai ta koreta