Showing 3001 words to 6000 words out of 294767 words

Chapter 2 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ta tashi da kanta,kuma koda ta tashi din bata buqatar hayaniya,saboda abinda ya faru da ita din zai zaman kaman dai dai yake da RÃPÉ ne a wajenta". Dukka idanunta ama ta sanya ta kalli dr chafa'atou kafin tayi qasa da kanta. Kalma mafi girma da muni da tunda take bata taba ganin kalmar da aliyyu ya tsana a duniya irinta ba,tayi fama dashi kan ya shiga harkar kasuwancinta,tafiye tafiyenta da dukkan wani sabgogi da suka shafeta,amma game da harkar qungiyarta ta yaqi da fyadewa qananun yara da mata.... Ko sau daya batayi wahalar gayyatarshi ba,shi da kansa ya shiga saboda mummunar tsana da gabar dake tsakaninsa da abun,sai gashi yau kalmar na shirin lanqwashewa cikin jikinshi.

Akwai kyakkyawar kula cikin asibitin da koda babu me jinyarka za'a kula da kai. Hakan ya sanya sukayi zaune kawai cikin farfajiyar da zata sadaka da dakin. Wani irin zama maras dadi da bakuna duka gaza furta abinda ke cikin zukata,sai saukar ajiyar zuciya lokaci lokaci daga zukatan al'ummar wajen. A yanzun basu da wani sauran zanceme amfani da suke ganin zasu tattaunashi,farfadowar sultana da dawowarta cikin hayyacinta shine abu guda daya filo mafi muhimmanci da kowa ke sanya idanu da ran ganinsa.

Har zuwa lokacin da lokaci ya cika na zaman ganin maras lafiya ya cika sultana bata motsa ba,wani irin baccin takeyi wanda ko juyawa batayi,abinda ya sake tasar hankalin bibi kenan,har ta fara fidda qwallar da a baya batayi ba

"Hamidou.....idan har yarinyar nan ta rasu gwara su gayamin kawai,ni din musulma ce,zan kuma iya daukar qaddarar rashinta,kamar yadda na dauki qaddarar rashin mahaifinta da ma mahaifiyarta gaba daya" kamar ana tsira mashi a qirjinta haka ama keji,duk sanda ta tuna cewa aliyyu shine sila na faruwar komai.....shine musabbabi na wanzuwar ahalin cikin wannan mummunar halin sai taji wani irin nauyi ya sake saukar mata,sai taji tamkar ta nutse a wajen. Kuka daga idanun mutum me shekaru ba abune da kowacce zuciya zata iya dauka ba,bibi bata danya dangana ba sanda suka buqaci tafiyarsu gida da alqawarin bata kulawa har sai da aka dangana da ita dakin sultana,ta kuma gani da idanunta yadda qirjinta ke dagawa da komawa tabbacin akwai numfashi a gangar jikinta

"Bazan barta ta kwana ita daya ba"

"Zan zauna da ita bibi,zan koma gida na shirya na dawo" ama ta fada tana jin cewa duk duniya itace ahaqqu da daukar wannan nauyin.

Bibi bata musanta ba,saboda ita din shaida ne na yadda hamdiyyan ke iya hidima ga kowanne yaro na gidan tamkar daga cikinta ya fito,sai ta juya tana fita a dakin, zuciyarta da bakinta fal da addu'ar samun sassauci wa sultana.

Daga ita sai tanja cikin mota,saboda aba ya dauke tsohuwarsa a tasa motar. Barinsu tayi,saboda ta tabbatar a barnar da yaronta ya tafka dole suna buqatar kebewa da tattauna abubuwa masu yawan da ta tabbatar ba lallai taso jin wasu abubuwa ba. Ta musu uzuri,kuma dukka wanda zai zargi aliyyu ko yaga laifinsa tana tunanin itace mutum na farko game da hakan.

Tun saman hanya ta gaza jure isarta gida ta taras dashi,zuwa lokacin ta tabbatar koda bai dawo gida ba to yana a kusa da gida din. Tasan cewa zaiyi wuya ya dawo a lokacin da ya saba saboda ya sani shi din me laifi ne,don haka ta soma lalubar number dinsa ta wayarta.

Tun bugun farko éteindre(a kashe take)haka computer ta gaya mata,amma tayi burus kaman bata fahimci yaren da computer din ke magana dashi ba ta shiga maimaita kiran nasa babu ji babu gani,saidai kuma amsa daya ce dai ake bata,dole ta maida wayar gefanta ta aje tana jan doguwar qwafa hadi da ajiyar zuciya. Wato yasan ta'adin da yayi shi ya sanyashi kashe dukka wayoyinsa?,batajin wannan lokaci zata daga masa qafa ko qanqani,kafin aba ya hukuntashi itace mutum ta farko da zata fara masa nata hukuncin.

Batasan inda bibi da aba suka tsaya ba amma dai ta rigasu isa gida,maimakon ta zarce sassanta sai kawai ta wuce sashen bibi din tana karbar key din dakin sultana data damqa ajiyarsa a hannun tanja.

A nutse ta bude dakin cikin sanyin jiki,ta sanya hannu ta kunna makunnin fitilar dakin. Tarwai haske ya gauraye dakin,yamutsatsen gadon da ta tabbatar akai sultana tasha dukkanw ata azaba daga hannun maina ya bayyana cikin idanunta. Takawa tayi a nutse din tana nufar gadon,har tsakiyar ranta tana jin abinda maina din ya yiwa sultana. Koba komai ita din diya macace,kuma tasan irin zafi da radadin da kowacce mace ke fuskanta a duk lokacin da zata rasa wannan abun me muhimmanci cikin rayuwarta koda kuwa an karbeshi ne cikin lallashi riritawa da kuma soyayya,ballantana uwa uba kuma karba ta fun qarfi,karba ta qarfa qarfa da nuna izza isa da iko.

Hannu ta sanya ta tattare dukkan abinda ke saman gadon,kama daga zanin gadon da ya gama baci da jini zuwa pillow din da tuni ya zame daga cikin gidansa, blanket dinta da shima jini ya taba,sai kayan sawarta da suka gama zama tsumma.

Sanda take rungume da zannuwan gadon zuwa toilet din sai taji zuciyarta tayi nauyi,data waresu cikin toilet din ta fara wankesu kuwa dukka qwalla da zafin da zuciyarta keyi wanda taketa riqewa sai ya gaza riquwa. Wata siriryar qwalla tabi ta gefan idanunta tana bin jinin da kallo,tausayin sultana ya tsargama zuciyarta irin wanda bata taba ji ba. Wannan zallar rashin imani aliyyu ya gwada mata,wanne laifi tayi masa da zafi haka daya zabi yiwa rayuwarta wannan ta'addancin?,ba zata qyale maina ba koda kowa kuwa zaice a daga masa qafa. Zaiyi wuya a yawan jinin data gani jikin zanin gadon yarinyar bata buqaci qarin jini ba. Cikin raurawar zuciya ta dinga wanke zanin gadon zuwa blanket din,abinda tsahon rayuwarta bata taba yi ba da hannuwanta.

Cikin mintuna arba'in ta kammala wankesu tas duk kuwa da nauyinsu,ta koma ta kintsa dakin shima tamkar ba hamdiyya abdu me kano ba. Tana kammalawa bibi na turo qofar dakin,sai ta saki siriryar boyayyar ajiyar zuciya da bibin bata isketa tana tsaka da wanke kayan da haidar din yayi aika aikarsa akai ba.

*_wanda bai samu guri a HUGUMA CLOSET ba yayimin magana na sama masa 08187255862_**_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

*BOOK 02 PAGE 03*
_______________________________

*_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_*

*_SUTURA ABAR TUNQAHO_*

*_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_*

_Magana akeyi ta_

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

_GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_

*_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_*

*_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_*

*_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_*

*KYAU*

*QUALITY DA DAUKAN HANKALI*

*LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA*
*GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA*

*_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*

08135142610

*INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES

*FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA

*_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_*

*_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_*

*_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_*

*TASTED AND TRUSTED*👌👌👌
_______________________________



Ido suka hada da bibi,dukkansu sai aka rasa me cewa dan uwansa wani abu,duk kuwa da cewa alamu sun nuna kowanne bakinsa cike yake fal da maganganu.

Qarasowa bibi tayi ta zauna tana duban ama,ba tare data buqata ba ama ta sulale ta zauna aqasa tana duban bibi

"Har yanzu kunqi yimin cikakken bayanin meye maina ya yiwa sultana?"

"Ya karbi budurcinta ne bibi ta qarfin tsiya" ama ta amsa mata kai tsaye kanta a qasa tana me matuqar jin nauyin bibi din,don babu magana kwatankwacin hakan data taba ratsawa a tsakaninsu,uwa uba babu wani buqatar ci gaba da boyewa bibi din,don kuwa me afkuwa ta riga data afku.

Dif bibi tayi tana juya abun cikin ranta,duk da ta riga ta gama hasashen komai cikin ranta da zuciyarta

"Bansan da wanne baki zan fara neman gafararki ba bibi...." Katseta bibi din tayi ta hanyar daga mata hannu

"Daga haidar har sultana waye bare?,waye zan ware nace ba nawa bane hamdiyya?" Ta fada da wani irin tune na sarewa da sanyin gwiwa

"Ni babu abinda zancewa da ubangiji na saidai ALHAMDULILLAH har da ya haskamin,ya kuma hanani nutsuwa sai dana tabbatar na maida sultana halalinsa. Yau inda ace ita din ba halalinsa bace ya aikata mata hakan nayi imanin zuwa yanzu wala'alla ina kushewata......saidai duk da hakan......." Ta fadi daga qarshe muryarta na karyewa da wani irin yanayi

"Duk da hakan abinda yayin banbancinsu kadan da fyaden bibi......sultana nawa take bibi?,duka duka shekarunta nawa?,a musulunce ya kamata a nufeta a haka?,bibi....... kinsan dinki nawa aka......" kasa qarasa tayi saboda yadda zuciyarta ta karye hawaye ya sake tsargo mata a karo na biyu.

"Akul......kul kika sake bari hawayenki ya fita akan wannan batun,idan ba haka ba zamuyi mugun samun sabani ni dake,kin manta masifar hawayen uwa akan d'anta?" Bibi ta gada a hargitse kuma cikin gigicewa.

Ba aliyyu takewa kuka ba sam sam sam, a'ah tana tuna girma da masifar zafin stitches ne koda jikin babbar mace bare sultana da duka duka bata wuce raino ba.

Sau uku tana zirya sashen maina don ganewa idanunta ko ya shigo gidan kafin ta fita amma bataga alama ba,haka ta shirya duk wani abun buqata ta dauki daya cikin masu aikinta da driver dinta suka koma asibitin.

A hanyar komawar dai duk sammakal,tunda ta zauna cikin motar zuciyarta ta lula a tunani. Fuskar aba take hangowa kawai,har ta fito daga gidan babu wata magana data hadata da shi,ta tabbatar kuma abunne yake dukansa kamar yadda yake dukanta.

Cikin qanqanin lokaci moudu driver ya sauketa cikin asibitin. Shi ya fiddo komai da tazo dashi. Abinci ne tasa zunnira ta shirya cikin qananun warmer's masu kyau,saboda batasan sanda sultana zata farka ba,kada ta farka cikin dare ta kuma buqaci abinci,sai kuma kayan sanyawar sultana din da wasu qananun kayan buqatu nata.

"Idan ba damuwa kaje ka shirya ka dawo,ina da buqatar ka kwana cikin asibitin tare damu,don bansan meye zai iya tasowa ba na gaggawa" tace da moudu sanda ya gama kwashe kayan tsaf ya shigar mata dasu ciki,ta furta maganar tana fiddo kyawawan qafafunta dake sanye cikin wani rufaffen takalmi maras tudu

"To ba damuwa ma'am in sha Allahu" ya amsa mata a ladabce.

Akwai taqaitar zirga zirgar jama'a sosai cikin asibitin,abinda ke alamta maka cewa lallai dare ya soma tafiya. Cikin wani irin kasala mutuwar jiki da rashin jin dadi jiki da kuma na zuci take takawa har ta isa dakin.

Ta iske qwararrun nurses biyu zaune a dakin,suna hirarsu qasa qasa ta yadda ba zata damu mara lafiya ba bare ta tadashi.

Sunfi kowa sanin ita din wacece cikin qasar nijer,don haka girmamawa ta musamman suke bata. Sannu tayi musu cikin halin sauqin kanta idan taso,suka amsa mata,sannan suka sake duba komai,kama daga file din sultana,ruwan dake shiga jikinta da sauransu suka tabbatar komai yana kan order

"Zamu wuce ma'am,duk abinda kk da buqata akwai waya da zaki kira(ta fada tana nuna mata inda wayar take a girke)"

"merci(na gode)" ama ta furta idanunta akan sultana

"c'est bon" suma suka maida mata amsa sannan suka nufi qofa suna mata sallama.

A hankali ta matsa gaban gadon tana sake dora idanunta akan fuskar sultana. Kyakkyawar baby face dinnan,wadda bata rabo da tsiwa da rashin kunya gaba daya ta canza,qaramin bakinnan da baya rabo da murgude murgude yau din gaba daya a kumbure yake. Kyawawan idanunta masu wani irin maiqo kaman an diga ruwa a yau din ba sosai kake hangosu ba saboda kumburin da gefansu yayi. Wani abu taji ya motsa zuciyarta,karo na babu adadi taji abun ya sake taba zuciyarta sosai. Inda ace saddi mace ne kwance haka cikin wannan halin wani d'a namiji yayi masa haka ya zataji?. Tambayar data sanyata jawo kujera ta zauna sosai gaban gadon tana ci gaba da kallon fuskartq zuciyarta kuma na hakaito mata yadda abun ya gudana tsakaninsu,wani nauyi na sake sauka mata a qirji. Fuskar nafessa take hangowa

"Ya rabbbb.....kada ka kamani da laifin gudun qaddarar da nayi,ya ilaheee ASTAGFIRUKA" ta furta a fili saidai can qasa hawaye suna cika idanuwanta.

A hankali sai zuciyarta da kuma tunaninta suka fara komawa baya suna mata tunin wasu abubuwa da suka faru shekarun baya da suka shude.

*_WANNE QULLI NE ZARGE QARQASHIN WANNAN IYALI DAKE DADADADDEN TARIHI?,SANIN KOMAI DANGANE DA TARIHIN WANNAN AHALI SHINE TAMKAR MADUBI HASKE KUMA FITILA TA LABARIN GABA DAYA_*


*_WHO DIED? WHO LIVES?_*


*_MUHAMMAT MAYAK'I_*


Dattijon arziqi shine sunan da jama'a da yawa ke kiransa dashi cikin ainihin mahaifarsa dake qasar nijer garin AGADEZ. Garin da ya zama tushe kuma makafar buzayen dake qasar nijer din.

Babban family garesu wanda yayi tambari sannan yayi suna ta fannin ilimi siyasa da kuma arziqin kansa. NADEEYA na daya daga cikin mutanen da suka sake sanya sunan family din MAYAK'I yayi shuhura. Qasaitacciyar 'yar boko 'yar kasuwa,wadda Allah ya huwacewa baiwar kwanya basira da iya sarrafa rayuwa. Gefe guda kuma tana daya daga cikin matan da koda cikin buzaye kyawunsu na dabanne. Wani irin kyau da akayi ittifaqin har xuwa yanzu shike bibiyar jininta,'ya'ya da kuma jikokinta. NADEEYA din ta fita daban,saidai a yanzun za'a iya cewa HAMDIYYA ABDU ME KANO wato AMA ita ke biye da sawayen NADEEYA da dukka tarin wadannan abubuwan da nadeeya din ta mallaka tamkar dama can ama ta fito daga tsatson nadeeya dinne. Saidai Sam,ita kanta ama batasan nadeeya da idanu ba wadda su aba ke kira da granny saboda ita din kaka ce a wajensu.

Ko cikin mata nadeeya ta dabance,wanann ya sanya ake tunanin ya zame mata kambun data riqa wanda ta zauna gaban Bobbi wato kakansu aba ita daya tal!,har zuwa lokacin da bobbi din ya rasu ya barta. Ita daya taci gaba da kula da 'ya'yanta cinsu shansu karatunsu har zuwa tarbiyyarsu. Allah ya albarkaceta da yara maza ne gaba daya su biyu,tayi mata sau biyu suna rasuwa,duk yadda takeson ta ganta da 'yar budurwa haka ta haqura. Allah ya raya mata yaranta rayuwa me kyau. ABDALLAH shine babban d'anta da ya zame mata gishiqi kuma madogara,wanda ta dora bisa dukkan wasu hanyoyi nata saboda halin rayuwa. Ya kama kuwa fiye da yadda ma takeso,wannan ya kwantar mata da hankali,saidai duk da haka bata nutsu ba har sai data tabbatar ta aurar dashi shi da me binsa wato ABDURRA'UF.

ABDALLAH ya auri bibi nana halimatou asalin bafulatana kuma buzuwa 'yar asalin garin AGADEZ. Kafin ya samu daukar halimatou bibi yasha fama a lokacin saboda wani irin farinjini Allah yayi mata,hakan kuma itama baya rasa nasaba da zallar kyau da Allah ya huwace mata,uwa uba tana da wata irin nutsuwa kamun kai da cikakkiyar tarbiyyar da takai duk yammatan unguwarsu idan an tashi kwatance da ita akeyi musu.

Gida guda nadeeya ta gina musu ita da yaranta,saboda tana da sha'awar su rayu tare. Wani irin gini tayi musu mahadi ka ture,ginin da saidai gidan sarakuna da manya manyan attajirai irinta.

Rayuwarsu na tafiya kaman yadda nadeeya ke buri,tsufa yana dada kamata,amma kulawar da take samu ya sanya take da cikakkiyar lafiyar da ciwo dai saidai irin wanda me dattijan da shekaru suka soma musu rubdugu basa rabuwa dasu.

A hankali bibi ta soma hayyafa,saidai faccalarta aseeya har zuwa lokacin shuru. Ba wanda ya daga mata hankali ko ya daga nasa hankalin,saboda dukkansu masu aiki da ilimi ne.

Dukkan me rai mamaci ne,sanda bibi keda yaranta maza har guda shida a lokacin ajali ya saukarwa granny nadeeya,lafiya lau akayi sallama da ita da dare ta tafi ta kwanta aka wayi gari babu ita. Sunyi kuka,sun kuma shiga tashin hankali sosai,saboda tsanani sabo da shaquwa da kulawar da suke samu daga yaran nata har jikokinta. Tayi masifar dasa musu wata irin qaunar juna a tsakaninsu,bawa juna kulawa da damuwa da damuwar juna, dabi'ar data bi jininsu qwarai da gaske,ta kuma zarce cikin jikin jikokinta har zuwa sanda suka zama cikakkun samari.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login