Showing 60001 words to 63000 words out of 294767 words

Chapter 21 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

gwiwoyinsu hadi da furta

"Astagfirullah....... astagfirullah" cikin wani irin tashin hankali. Abun ya bata tsoro ya kuma daure mata kai,bata da zabi illa itama tabi sahunsu ta zube a wajen. Sai da suka gama neman gafara sannan suka zarce wajen daura alwala. Tasha wahalar kafin ta samu kan famfo din da zata daura alwalar,abinda nan duniya bata taba saninsa ba baya ga abinda ya faru da ita ba wato wahala wajen samun wani abu na duniya. Tana alwalar tana tuna adadin yawan kan famfo dake gidansu,wanda hatta tsuntsayen dake gittawa ta cikin gidan sai a inda suka zaba suke shan ruwa ballantana su,su dinma ita sultana shalelen bibi da aba.

Ayarin ta sake bi suna nufar wani guri,bata karanci ina bane sai da suka qaraso,masallaci ne,shima anja gate din an rufe,dukkansu saida suka sake zaman yin istigfari sannan aka bude musu suka sanya kai ciki.

Cikin wani irin tsari da burgewa kowa yahau sahun sallah,aka kabbara sallah. Mintuna kusan takwas sannan aka idar,tana niyyar miqewa taga ba wanda ya motsa sai qur'anai da ake budewa,kowa kuma yana lalubar 'yan ajinsu. Idanu ta shiga budewa tana waige waige,ba inda ta sani,ba kuma wanda take ganewa a wajen. Cikin haka Allah ya taimaketa ta hango fatima tana daga mata hannu. A sanyaye ta isa kusa dasu,ta miqa mata qur'anin,tasa hannu biyu ta karba,ta samu waje kusa da ita ta zauna.

"Ki bude,recitation za'ayi,za'a yi mana qarin karatu kuma,sai qarfe bakwai sannan zamu koma hostel mu shirya shiga aji" kai ta jinjina qasan zuciyarta fal da mamaki,wacce irin makaranta ce ama ta kawota haka?.

Buda qur'anin kawai tayi ta zuba masa idanu,saboda inda ake musun ita sam batazo wajen ba,yo inama tayi jumurin zuwa makarantar ballantana ta kawo nan,ta sani dai,ta kuma tabbatar su aminata da suke aji daya tare a baya sun wuce haka yanzun,saboda makarantar islmiyyarsu badai karatu ba,ita dince dai da bata sanya aka ba.

Tana nan zaune aka gama biyawa aka soma karanta musu suna bi,duk sai taji ta muzanta,bata kuma ji dadi ba ganin kowa yana bi tar tar,ita kadai ke baza idanu. Kusan ita daya ce sabuwar daliba cikinsu,saboda dokan makarantar bata yarda da daukan dalibi daga kowanne mataki ba saidai matakin farko wato J.s one,ita dinma sa'a ta taka da kuma sanayya ya sanya suka kaita j.s3 din.

Har akayi aka gama bata iya kama komai ba a ciki. Hakanan taji jikinta yayi sanyi qwarai,irin sanyin da bata taba ji ba wai akan karatu,ko don wannan din wani littafi ne na daban?,na musamman da ya banbanta da dukka sauran litattafai a duniya.

Suna hanya ameena aleeyu da Fatima ahmad yusuf sunata hirarrakinsu,saidai abinda ta fuskanta a gurguje kowa ke yin tafiyar zuwa hostel. Tun tana binsu a hankali ta fuskanci zasu tsere mata don haka ta dan daga qafa ta taddosu.

Waiwayota ameena aleeyu tayi tana murmushi

"Saikin saba da dukka tsari da dokar makarantar nan sannan zaki zauna lafiya,yanzun zamu wuce hostel ne,ayi share share,sannan mu wuce kitchen yin breakfast" idanunta tadan fiddo,duk wannan wahalar da tayi,da kuma qoqarin da take ta koma ta wuce toilet ta sheqa wanka ake batun shara da cin abinci?.

"Wanka kuma fa?" Ta tambaya tana dubansu. Dariya kadan sukayi

"Ba batunsa,sai Allah ya kaimu biyu na rana idan an tashi class" cikin ranta takejin ba zata iya wannan rayuwar ba,itakam koma meye dole tayi wanka da safen kafin ta wuce aji,don ba haka ta saba ba.

Suna isa labour perfect na raba aiki,kusan kowanne class da suke hade a hostel guda sunsan area din da zasu share,suna da yawan da ba'a kula da baquwar fuska bace ita,don haka ta nufi bangaren da toilets dinsu yake don yin wankan. Kowanne toilet a kulle yake gam,taja baya ta tsaya tana duban qofofin,ta kuma kalli bucket din hannunta. Da gaske kenan saidai ta koma sai qarfe biyun kamar yadda ameena aleeyu ta gaya mata. Ranta a bace take takawa zuwa sassan dakinsu cikin babban compound na hostel din nasu da yakai girman babban parking space,bayan football field da suke dashi dake hade da table tennis.

"Ke!" Taji an kirata daga bayanta. Cak ta tsaya tana jin amsa kuwwar kiran cikin kunnenta,irin kiran data fi tsana duk duniya,kiran wulaqanci da yaa maina kadai keyi mata shi,a yanzun batasan kuma waye ya ara ya yafa ba. Waiwayawa tayi jin an sake ambatar

"Ba dake nake ba?" Kafin tayi komai taga daya daga cikin daliban dake daura dasu ta saki tsintsiyar hannunta,ta kuma qarasa da sauri ta zube bisa gwiwoyinta tana fadin

"Aunty gani". Mamaki sosai ya kama sultana,aunty kuma?,harda duqawa saman qafafu?,ita sam a wannan wajen bataga aunty ba,tunda duka duka ma autyn da ake kira dinma baifi ta bata tazarar shekara biyu ba

"Ba dake nake ba,da wannan 'yar iskar nake" ta fadi cikin dagawa da izza tana nuna sultana. Wani abune yazowa sultana wuya ya tsaya mata,ta tattara dukka miyan bakinta ta hadiye,ranta yana sosuwa da sunan 'yar iska data kirata dashi. Waishin ma ita din wace da zata kirata da wannan sunan?,ta buda baki zatayi magana muryar Fatima ahmad ya gauraye gurin

"Baquwa ce aunty,don Allah batasan tsarin komai ba,tana cikin sabbin daliban da aka kawo jiya"

"Tambayarki nayi?,ita batasan wacce makaranta ta shigo ba?,uban meye takeyi da botiki a hannunta lokacin tsafta da gyara waje?"

"Bata sani ba kiyi haquri aunty"

"Samomin bulala" prefect din ta fadi tana bawa yarinyar dake durqushe a gabanta umarni.

Tsaiwa cak sultana tayi tana jiran ganin ikon Allah,tanason ganin yau din wacece zata daketa?,wacce me tsautsayin ce?,batasan babu wani halitta da ya isa ya daketa ba bayan ruwan sama?. Cikin qasa da minti daya yarinyar ta iso,cikin ladabi irin nasu na makarantar daya zamewa kowanne dalibi tilas ya siffantu dashi ta duqa ta miqa mata

"Zo nan" ta yiwa sultana umarni cikin tsawa

"Kije don Allah,don Allah kije sultana" Fatima ke fadi cikin tsoro

"Har saikin roqeta ma?,idan batazo bama zan qaraso da kaina" perfect din ta furta tana takowa gurin sultana din cikin izza,zuciyarta na gaya mata duk yadda akayi 'yar gidan uban wani ne daga wata qasar,don sam batayi zubin qabilun nigeria ba

"Durqusa kikayi tsai kina qarewa mutane kallo!" Ta fadi cikin wata sabuwar tsawar*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 32


Ci gaba da duban tsakiyar idanunta sultana din tayi tana hadiye wani abu daya tsaya mata a maqoshi,wannan din ya sake tunzura prefect din,ta daga bulalar hannunta da nufin saukewa sultanan

"Lafiya?,me kukeyi a nan carko carko?" Muryar Metrom din dake kula da shiyyar ta gauraye wajen.

Cikin fushi perfect din ke maida jawabi,gurin yayi tsit har ta gama

"Shikenan ya isa,kowa ya koma kan aikinsa,ke kuma huda kiyi haquri,baquwa ce,amma zan mata bayanin komai" wani irin tsuka wadda aka kira da hudan taja,alamu dake nuna takaicin dake ranta fal,don taci buri sosai na ladabtar da sultana. Kyawunta wani abune da ya bugi zuciyarta qwarai ya kuma sanyata kishi.

Idanunta da suka dan jirkita ta lumshe sannan kuma ta budesu,ita kanta taso yarinyar da aka kira huda ta samu isowa gareta,ba shakka da ta barwa rayuwarta darasi. Don rayuwa ta cimmata hakan bai nufin komai da komai daga asalin sultana ya sauya ba,ba zata lamunci cin zarafi ko kuma qasqanci ba.

"Taho muje" taji muryar Metrom din na fadi tana kama bucket din hannunta. Bata musa ba tabi bayanta har zuwa wani kebantaccen waje da Metron din kan zauna ko tayi ajiye ajiyen kayanta

"Zauna,sultana mayak'i ko?" Ido ta daga ta dubeta tana mamakin yadda ta kama sunanta haka kai tsaye kuma lokaci guda.

"Zauna" ta sake maimaitawa,ba musu ta samu waje ta zauna,itama Metron din ta zauna tana duban idonta

"Sunana maama asabe,kina iya kira na maama ko asabe,da farko inason shaida miki,duk wani da kk da buqata ko menene shi kina iya shaidamin kai tsaye,za kuma ki sameshi in sha Allah" saita tsagaita tana kallonta. Mamakin sultana ya sake qaruwa,to meye hadi ko alaqarta da ita bayan yau ne ita karo na farko a rayuwarta ma data fara ganinta,ta yaya zata buqaci wani abu a wajen ma'aikaciyar da idan ita sultanan bata taimaketa ba ita din ba zata taimaketa ba

"Kada kiji shakkar nema ko tambayar komai daga hannuna tamkar kina gida,don komai zai fito daga hannuna da zaki buqata din daga gidan yake.....makarantar nan tana da dokoki da qa'idoji masu tarin yawa,duk dalibin da kika gani a makarantar nan yana rayuwa ne a kansu,kina da wata kariya da alfarmar da ba lallai ki fahimci abinda zan ce ba,kawaidai abinda zan gaya miki shine,don Allah ki koyi kiyaye kowacce doka da qa'ida,ta yadda babu wani hukunci da zaya dinga hawa kanki,ni kuma zanyi dukka qoqarina wajen tafi da komai" shuru tayi tana jujjuya maganganun maama asabe dake tafe da wani irin surkullen zance data kasa fahimta,to wai shin maama asabe ta santa ne ko kuwa?,akwai harshen damo cikin maganganunta da bata fahimci ina ta sanya gaba ba,daga qarshe kawai ta yanke ta gyada mata kanta

"Yauwa,yanzu lokacin tafiya kitchen yayi,kibi 'yan uwanki ku wuce" kai ta sake gyada mata,sannan ta miqe riqe da bucket dinta.

Cikin uniform ba tare da wanka ba ta sami su fatima,ta lura da tuni sun saba da wannan yanayin,don shirin tafiya kawai sukeyi kitchen. Ameena ce ta kama hannunta

"Don Allah ki kiyaye sultana,haka makarantar take,amma muddin kika kiyaye zaki fahimci rayuwa ce me dadi kike kai" bata ce da ameena komai ba,ta sunkuya qasan gadonta ta sauya takalminta. Wani irin takalmi ne me azabar tsada da kaf fadin makarantar.....duk kuwa da kasancewarta makarantar yaran masu hannu da shuni za'a samu me irinsa,ta dauki school bag dinta da tuntuni take dauke da litattafanta a tsare ta goya sannan tabi su fatima suka wuce kitchen.

Babban hall ne da aka tsarashi da table da kuma kujerun cin abinci rukuni rukuni,kowanne rukunin table yana dauke da kujerun zama guda goma,kaman yadda yake a doka mutum goma ne ke zama kowanne table. Kafin isowarsu an shirya kowanne table da cooler din abinci, spoon cups da plates da kowanne dalibi zai buqata.

Yadda taga kowa ya zauna haka itama ta zauna,ta dinga nazarin wajen da.idanu tare da cika da mamaki,mamakin yadda duk yawansu kowanne dalibi na zaune bisa kujerarsa cikin tsari,kowanne table kuma cups da sauran tarkacen kai a qididdige suke dai dai da yawan masu zama a wajen.

Fatima ce ta miqe tayi saving nasu kamar yadda kowanne table mutum daya ke wakiltarsu. Tabi plate dinta da kallo sanda fatima ta gama ta koma ta zauna. Doya ce da qwai,sai kuma tea lafiyayye cikin kowanne cup,ta dauke idanunta ta fara bazashi a hall din sanda taji sun rude da addu'a duka lokaci guda.

Addu'ar cin abinci ne,sai da suka sauke sannan kowa ya fara kaima cikinsu,a sannan hayaniya ta rude a wajen. Ko hannu batakai ta taba abincin ba,bawai don baiyi.mata bane ba,aah tsabar rashin sabo da cin abinci cikin gamayya haka,uwa uba kuma a gida ta saba,baa taba ajjiye musu breakfast qwaya daya tsura haka,a qalla akwai kalolin breakfast uku ake ajewa ka zabi son ranka.

"Minti talatin kacal ake bayarwa,kiyi ki fara ci kafin a fara counting" ameena aleeyu ta fada tana kai cup din tea din bakinta.

Tun asali a dabi'arta bata iya sauri wajen cin abinci ba,don haka tana tsaka da soma ci din taji an fara irge kwatankwacin irgen da taji anyi dazu da asuba wanda ya sanyasu zubewa suna istigfari. Ture abincin tayi sanda fatima ke gaya mata lokaci ya kusa cika,gaba daya abincin ya taru ya dunqule mata a qirji,ta sunkuya ta dauki handbag dinta

"Baki dauki ruwanki ba" fatima tace da ita,kai ta girgiza alamun AA tana yin gaba,hakan bai hana Fatima daukan sassanyan ruwan ba tabi bayan sultana din dashi,tausayin sultanan yana kamata, saboda ta sani bata saba da irin rayuwar bane bisa dukkan alamu. Kaman hakan suma suka fara,sai gashi yau rayuwa ta fara koya musu yadda zasu rayu cikin dadi da kuma akasin hakan,hakan kuma ya zame musu jiki tamkar dama a haka rayuwar tasu ta taso.

Sai da taji qishirwa da gasken gaske,ta kuma tabbatar babu wani sauran bottle water a nan wanda ta saba sha a gida sannan ta amsa daga wajen fatima ta sha.

Kusan duk karatun da akayi cikin ajin shima nata idanu,bata fahimtar inda komai ya dosa,bata gane komai,tana jina rayuwarta kamar bata taba zama a aji ba. Haka kawai sai taji ta muzanta,ta kuma tsargu,kowa yana karsashi tare da qoqarin bada gwargwadon fahimtarsa cikin aji amma banda ita. A hankali ta dinga jin wani abu me kama da rashin jin dadi yana sauka a zuciyarta,ta dinga jin me ya hau kanta wancan lokacin?,me yasa bata tsaya tayi karatu ba?,tana gani yanzu a gaban idanunta tamkar ita daya ce bata gane komai cikin ajin. Koda kuwa akwai banbancij harshe da yare a tsakaninsu,amma tayi imanin inda ta tsaya tayi karatu a baya ayanzun batajin akwai abinda zaya gagareta,tunda ko a makarantar tasu ana koyar dasu harshen turanci sosai,kuma kaf gidan ba wanda ba zaya iya jefa maka turanci ba,bare larabci da ya zama yaren dukkan musulmin duniya.

Sha daya aka fita break,masu sha'awar cin provision dinsu suka diba sukaci,ciki harda su fatima data fahimci ita da ameena aleeyu komai nasu a hade yake. Sukayi sukayi tazo suci abinci amma ta qiya,don bata sha'awar cin komai,hasalima dandanon bakinta ya dauke,ba abinda ke kai kawo a kwanyarta illa yadda zata tafiyar da baquwar rayuwar data fado mata rana tsaka ba tare data shirya ba.

Biyu na rana aka tashi da classes. Tana kallon yadda dalibai keta walwala zuwa masallaci,kowa na sabgar gabansa,sai ta dinga jin inama ace itama tana daya daga cikinsu. A yanzu kawai tana jin gangar jikinta da ruhinta ne a wata baquwar duniyar,bawai irin duniyar data saba rayuwa a ciki ba.

Sallah sukayi bisa jam'i a masallacin mata,abinda kaf rayuwarta zata iya cewa bata taba yi ba wato sallah cikin jam'i. Ta saba kammala sallarta a mintuna qalilan,yau sai gashi itace da tsaiwar sallah,sannan kuma bayan an idar sukayi zaman yi azkar na bayan kowacce sallar farilla,nan ma 'yar kallo ta zama,ta lumshe idanunta muryoyin daliban cikin NISHADI suna jeranta addu'o'in na shiga cikin kunnenta. A hankali ta dinga jin wani sanyi yana saukar mata,nutsuwa na zuwa ruhinta,qullin bacin ran dake danqare can wani kebantaccen saqo na zuciyarta yana neman hanyar fara kwaranyewa. Fuskokin benazeer da batoul suka gilma mata cikin idanunta,saita bude idanun da hanzari tana kiran sunan Allah. Daidai sanda suka kammala addu'an kowa ya soma miqewa domin kaiwa ga kitchen cin abincin rana.

Kaman dai da safe,komai da kowa kan tsari,sunyi lunch da lafiyayyar jallope din taliya da kuma soyayyen kifi. Wannan karon tadan cakula ta barshi kaman dai da safen,duk kuwa da cewa girki ne me kyau da bashi da makusa kwata kwata.

Sanda ta iske layin shiga wanka saita koma da baya kawai ta zauna,ta lumshe idanunta wani abu me kama da bacin rai nason sauko mata. Bakayi wanka ba tun safe,ka debo zafi da rana kazo da zummar ka wankesu kuma ka samu wannan layin da batasan ranar da zai ragu ba?.

Tana nan zaune bisa layi tana duba qaramin agogo dake hannunta,mintuna goma kacal suka rage lokacin yin wanka ya cika,a yadda kuma ameena aleeyu ta gaya mata indai hakan ta kasance kuma wanka saidai da dare,lokacin baccin rana ne. Abinda ya matuqar daure mata kai da ta gaya mata koda bakajin baccin dole nefa ka qirqiroshi

"Qangin bauta" hausar tazo mata a tsakiyar kai. Anya ama tayi mata dai dai kuwa?,wannan rayuwar da ama ta zabar mata tazo tayi da sunan makaranta irin rayuwar data dace da ita ne?,zata iya ci gaba kuwa?.

Dukkan tsammaninta ya yanke ganin mintuna biyar kacal sukayi saura,koda ta samu shiga a sannan tasan zaiyi wuya ta samu abinda takeso,tunda a qalla wankanta yakan dauki mintuna goma sha biyar kafin ta kammalashi

"Sultana mohmoud mayak'i" taji muryar Metrom asabe na kiranta. Waiwayawa tayi da fararen idanunta da suka fara laushi tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login