Showing 48001 words to 51000 words out of 294767 words
Chapter 17 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Wani irin mummunan baci ran ama yayi,bata tabajin haushin sultana ba irin yau,bata taba jin rayukanta sun baci dama ko meye takeyi ba irin yau.
"Ke sultana!" Ta kirayeta cikin tsawa,tsawar data kada zuciyar sultana din. Karo na farko a rayuwarta da tsawa ya taba hadasu da ama
"Ashe baki da hankali?,don baki sonsu sai akace ki kashesu?,yaran da kika haifa a cikin cikinki?,ke haka kika ga bibi tana miki?,haka kika ga aba yana miki?, oncle bashar oncle umar?,uwa uba mahaifin nasu da kikaqi jini?,shi ya goyeki a gadon bayanshi,ya baki abinci da hannunsa,yayi maka wanka,wankin kashi da na fitsari,shine yanzun zaki gangaro qananun yara da ko kwana daya basuyi ba duniya?,to ke kika haifesu duka 'ya'yanki ne,idan ke kika haliccesu ki maidasu inda suka fito" ta qarasa fada cikin bacin rai tana debe yaran.
Wani mugun mutuwa jikin sultanan yayi,dukka gabbanta sukayi sanyi,idanunta suka cicciko da sabbin hawaye,ranta ya dinga yi mata ba dadi da ganin bacin ran ama. A yau zuciyarta ke mata fadan da ya dace,bai kyautu ta yiwa ama haka ba,matar data tsaya da ita cikin wuya rintsi da dukka tsananin data fuskanta tsahon watanni goma,bata tana gajiya ba,bata taba sarewa ba,bata kuma taba ja da baya ba,bai kamata ta saka mata da wannan ba.
Tana jin sanda ama ta fita ta siyo madara tazo ta hada ta bawa yaran,babu jimawa sukayi luf,bacci yayi awon gaba dasu.
Ama bata sake saurarenta ba,iyakaci ta barta da tanja,tana ji tana gayawa tanja ita yanzun ta koma rainon jikokinta,ga diyarsu nan. Abun sai ya quntatawa sultana,a fakaice dai ama ta rabu da ita kenan?. Ko a washegari da mutane sukayita shigowa ganin twins duk wanda ya tambayi mamansu sai tace bacci takeyi,duk kuwa da idanunta biyu. Sosai turawan suka dinga shigowa ganin 'yan biyu,abinka da bature wanda baya raina abun kallo. Hotuna suka dinga yi da yaran,gif kuwa sai gashi sun cika wani sashe na dakin da gifts,har sai da ma'aikata suka kwashe aka kai musu ajiya dakin ajiya dake cikin asibitin. Wani irin kyau da murjewa yaran sukeyi,kusan kullum Allah ne da kullum amma indai rana zata fito ta fadi sai masu son ganin yaran sun shigo,kuma dukkansu turawa ne,duk wanda zai shigo kuma da gift dinsa,suna son yaran kamar su lashesu,akwai cikin ma'aikatansu da kullum a rana sai sun shigo kusan sau uku kawai saboda yaran,tamkar wadanda aka yiwa yayyafin farinjini,ita dai ama ta sani muddin suka dauko farinjinin iyayensu to lallai sai ta hada musu da addu'ar baki.
Kwana uku kacal suka sallamesu,har a ranar aman bata sake mata maganarsu ko tayin basu nono ba,hasalima ita da yaran saidai taji muryoyinsu daga nesa,suna qushin qushin din kuka ko wani abu daban.
Bata yarda ankai yaran ko ina na,cikin nan dakinsa tasa aka shirya musu gadajensu da komai da komai,komai nasu pink hot pink da baby pink,komai nasu designers ne,hatta da turaren jarirai na kamfanin Dior ta siya masu yawa ta ajjiye. Dukka kayan sawarsu kuwa cotton kaya ne masu kyau qwarai 'yan turkey,channel brand,h&m brand,zara brand,Lacoste fendi Balenciaga da sauran manyan brand. Tanason a san cewa tabbas daga tsatso da ahalin manyan iyali suka fito MAYAK'I FAMILY sannan jinin babbar 'yar kasuwar qasar nijer da kewayenta hamdiyya ABDU ME KANO ne.
Tsaf ta shiryasu cikin wasu long sleeve body suit masu kyau da taushi na kamfanin channel,ta nade kowannensu cikin shawl me taushi sannan ta rungumosu kowacce ta kwantar da ita saman gadonta,ta daidaita qarfin AC din dakin,sannan ta fita zuwa kitchen don ta zuba ruwan zafi a flask dinsu ta hada musu madara.
NADEEYA ALIYYU MAYAK'I (BENAZEER)
FATIMA ALIYYU MAYAK'I (BATOUL)
_SAI MUCE BARKANKU DA ISOWA TSAKANIN CAKWAKIYAR DADDY MAINA DA MOMMY SULTANA_😂😂😄*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 02 page 25
Ta dade a tsaye gaban madubi daure da towel,ita bata shirya ba ita bata zauna ba,haka kawai takejin zuciyarta wani irin empty,sai tarin karaya da rashin confidence. Sake shafa fuskarta tayi a karo na babu adadi tanason tuna fuskokin yaran,batasan me takeji a kansu ba,soyayya ko qiyayya?,har yanzu bata tantance ba,abu daya ta sani har yanzu tana iya tuna wahalar da tasha a kansu,ko yanzu da take goge jikinta sai data kalli wajen da aka yanka cikin cikinta saboda yaran
"Mene makomata?" Tambayar da taketa yawaita yiwa kanta kenan,zata koma nijer ne taci gaba da fuskantar mutane?,taci gaba da fuskantar qawayenta a haka?,da wacce fuskar?,ita sultana me 'ya'ya har guda biyu?,duk da ama ta karbesu,duk da ama tace nata ne amma ta sani hakan bazai canzasu daga sunan 'ya'yanta ba tabbas!. Wanne bigire ta kama?,ina rayuwarta ta fuskanta?,bata sani ba!,bata sani ba sam sam sam......wannan itace amsar da take bawa kanta.
Qas tayi da kanta, hawayen da batasan ranar daina zubarsu ba suka fara tsiyaya daga idanunta suna diga saman madubin.
Sautin kukansu cikin muryar rigima sosai ita ta sanyata daga kan nata tana duban fuskarta ta cikin mudubin tamkar su din zata gani ta ciki. Idanunta ta maida ta lumshe kukan nasu na isketa har inda take,dukansu su biyun sun dage sai qyaqyata kuka sukeyi. Idanunta ta lumshe,batasan me yasa sam batason jin kukan ba,ta matsa daga gaban madubin,saita samu kanta da jawo babban mayafinta ta lullube dukkan jikinta,sannan ta taka a hankali ta murda qofarta ta fice.
Daga dakin ama ne kukan ke fita,ci gaba tayi da nufar dakin amma gabanta yana dukan tara tara,wata zuciyar kuma na hanata zuwan,sai ta kasa dakatawa,har ta isa qofar dakin ta tura ta bude.
Kanta ta fara zurawa tana leqensu,ba kowa cikin dakin sai su kadai,sun rude da kuka abinsu suna jejjefa qafa kamar zasu tashi sama
"Ya salam ya Allah" ta fada qasa qasa saboda yadda taji zuciyarta na motsuwa. Batayi tunanin komai ba ta sanya kanta cikin dakin,ta taka a hankali zuwa gaban gadajensu.
Fes kyawawan fuskokinsu suke,ba hawaye ko wani abu,harararsu tayi tana tura baki gaba,kamar an gaya musu wacece ita,kamar an sanar musu da matsayinta garesu sai kukan nasu yana baya sosai,da kadan da kadan yana ja baya,yayin da duk su biyun suka kafeta da idanunsu.
Itama nata idanun ta zube musu, zuciyarta na ayyana mata abubuwa iri daban daban. Banda wahalar da ita daya tasan kalarta da tasha, tabbas da zatace ba yaranta bane. Dan mutum guda guda har guda biyu?. Murmushi ya subuce a saman fuskarta karon farko bayan shudewar watanni d'ai d'ai har kusan wata goma sha daya rabon da ya fita a fuskarta. Miqa musu yatsuntsa tayi d'ai d'ai kowanne ta cusa shi tsakiyar tattausan tafukan hannunsu. Mamaki ya kamata yadda taji caraf kowacce ta riqe suka sakeyin relaxing suna kallonta zaka rantse ba jariran kwanaki kadan bane.
"Batoul?, benazeer?" Ta furta qasa qasa tana nuna kowacce da yatsa daidai,tanason ganin ta banbance sunayen kowaccensu?. Kai ta girgiza tana ganin kamar bata fadi dai dai ba,amma ta tuna taji ama tana cewa gefan kunnen babbar akwai alama irinta aliyyu. Wani daci ya ratsa harshenta da tuna sunansa kawai da tayi, qirjinta na quntata ta sanya hannu ta duba gefan fuskokinsu. Taga alamar da ama din ke fada,kuma haka yake,sak irin nashi,tawadar Allah,tasha tambayarsa meye wannan tare da nacin sai ta kankare masa
"Nadeeya BENAZEER fatima BATOUL" ta sake maimaitawa kamar me gudun kada ta mance sunan. Sai taji sunan kuwa ya zauna daram a kwanya da zuciyarta.
A nutse ama ta maida qofar ta rufe bayan ta gama kallon duk abinda takeyi. Sautin rufe qofar ya sanyata waiwayowa a dan razane gabanta yana faduwa. Ya akayi ta shigo haka ta sakankance ba tare da tunanin ama ko tanja wani cikinsu zai shigo ya ganta ba?. Kauda kai ama tayi sam kamar bata ganta cikin dakin ba,ta fiddo kyawawan feeders dinsu guda biyu ta dora saman bedside table tana nufar gadon nasu tare da fadin
"Bansan kun qagu kusha ba,ashe yunwa kukeji my babies" ta fadi tana fara dauko benazeer da kukanta yafi na kowa,sannan ta dauko batoul ta iso dasu gaban gadon.
Dole saidai ta fara bawa mutum daya,don tanja ke tayata bawa dayan tanjan kuma yanxu ta fita,don haka ta fara bawa benazeer sai kuma batoul ta fara qushin qushin. Da idanu sultana dake qame take satar kallonsu,shan madarar takeyi yarinyar sosai kamar zata hada da feeder din,da alama me cice sosai
"Wai mutum mutumin sultana aka shigomin da shi ne?,zonan ki zauna ki taimakawa batoul idan zaki iya" ama ta fadi tana gyara zamanta. A kunyace a kuma mugun darare ta tako ta zauna. Sau biyu tana miqa hannu zata dauki batoul sai ta fasa
"Har yanzu baki sonsu dinne?" Ama ta jefa mata tambayar da ta sanya babu shiri ta dauki BATOUL din ta aza saman cinyarta. Dumin jikin yarinyar ya sauka a dukka cinyoyinta,yarinyar kuma ta sake zuba mata idanu sosai kaman dazu,tamkar tasan yau ne ranar farko da mahaifiyarta ta azata zaman cinyarta,zata kuma shayar da ita da madara bawai da nonon jikinta ba.
Dukka yadda taga ama tanayi haka tayi,har sai da ama din tace ta zare ya isa haka,ta basu ruwan zam zam da shine ya ruwam shansu,kuma shi zaici gaba da zama ruwan shansu cewar ama har sai sanda suka buda baki sukace sun gaji dashi muddin tana raye.
"Sakata a kafada har sai tayi gyatsa" cikin tsoro ta dagatan ta sakatan,suka shiga shafa bayansu ita da ama din,sai a sannan ama ta magantu
"A qalla idan baki sosu ba ko kulawa ki nuna musu,mafi qaranci dai zasu tashi da ganin kallon rahama daga idanun uwarsu.......maraici bashi da dadi,ke baki sanshi bane saboda an baki cikakken kulawa da gata,to kiyi qoqari su dinma koda sun rasa uba susan cewa suna da uwa a raye". Kasa cewa komai sultana tayi sai qas da tayi da kanta,wani abu yana dawainiya da zuciyarta.
Sanda ama ta lura batoul din tayi bacci tace ta kwantar da ita,lokacin da zata kwantar da itan kusa da 'yaruwarta ji tayi kamar kada ta kwantar da ita din
"zo ki zauna" ama ta sake fada kanta tsaye da daure fuska,daure fuskar da take sanya ma sultana shakkarta da kuma d'ari d'ari. A dararen ta zauna
"Ki saki jikinki sosai mana,ki manta ni momynki ce?" Maganar tayi mata dadi sosai,amma sai taji zuciyarta ta raunana,inda ace uwa mahaifiya a gareta tana raye wala'alla zatafi fahimtar duk wani rauni da quncinta ko?.
Kamar ama tasan abinda take tunani sai tace
"Zuwa yanzu banajin akwai wanda ya fahimceki kamar ni,akwai wanda zaisan ciwonki da zaqinki kamar ni......daga yau inaso sultana ta fara sauyawa,inason na daina ganin wannan sultanar,me musu da taurin kai,inason sassauqar sultana me cewa "eh to" a dukka lamuranta,inaso ki canza zan tallafa miki duk wani ciwo na zuciyarki ya gushe idan kin shirya" kai ta gyadawa ama tana share hawayenta
"Na shirya,kiyi haquri ama" ta fadi kuka yana tsinke mata. Cikin jikinta ta rungume sultana din tana rarrashinta. Sai takejin inama komai yazo ne a LOKACIN da ya dace,inama ace aliyyu baiyi gaggawa ba?,saidai idan ta tuns cewa rabonsu batoul......lokacin wanzuwarsu a duniya ne yayi shi yasa komai yazo a gaggauce irin haka,sai taji ta sake sallamawa lamarin ubangiji.
Hamdiyya abdu kano,jajirtacciya uwa kuma tsayayya. Itace ta shimfida dukkanin tafukan hannayenta......ta sadaukar da dukkanin dukiyarta........ta bada lokacinta da rayuwarta ma rayuwar SULTANA BATOUL DA BENAZEER.....ta sadaukar musu da dukka komai nata,ta kula da yaran ta kuma kula da uwarsu.
Dukkaninsu babu wanda ya samu naqasun kulawarta. Sau tari tanja kan zauna tayi shuruuu..... Eh lallai baka taba gama sanin halin mutum sai ka zauna dashi. Ashe wannan itace hamdiyya wato ama da sukewa kallon me izza,miskila saboda ganin ta mallaki maqudan kudade,wadda bata shiga shirgi ko sharafin kowa,ashe ita din me sadaukarwa ce,ashe ita din me sassauqar zuciya ce?.
Kulawa da sultana kusan itace ta kwashe mafi yawancin lokutanta. Fitness center ta kaita me kyau da suke bawa jikin sultana kulawa cikin kula da CS dinta ba tare da ya samu matsala ba,tanason sultanan ta koma sultana dinta,harma tafi da,tunda zuwa yanzun idan ka ganta zaka tsammaci ta shiga shekara ta sha bakwai ne bawai sha hudu ba. A gida kuwa lafiyayyun abinci da dukka nau'in ganye da tasan zai maida sultana mutum,ya murje mata jiki kullum cikin research da hade hadensu take,ruwan ganyen gwanda daya zamewa ama aboki a baya yanzun ta tilastawa sultana shanshi sau biyu a rana(yana hada nuna tsufa,yana maintaining jiki,kiyi looking younger akan shekarunki)daya daga cikin sirrikanta da take taqama dasu.
Sannu a hankali saiga sultana ta fara dawowa SULTANAN BIBI DA ABA,fatarta ta fara ninka kyanta,duk wata rama tata tana yin nata waje,komai yana komawa kan saitinsa. Tun usul dama damammen ciki gareta,don haka ko yanzunma ba zace ta taba daukan ciki a cikinta ba, stretch marks ne yaso fito mata dan kadan a fatar cikinta ama tace bataga ta zama ba. Kudi ta zuba sosai ta siya mata mayuka masu kyau da dan Karen tsadar da ko a can dimma saika ciza sannan zaka siya,sai gashi sun bace bat,babu su babu alamunsu,tunda dama bana halitt bane na ciki ne.
Gyaran kai, manicure da pedicure akai akai,so take ta koma sultana cikakkiyar 'yar gayu,cikin kwana talatin da biyar cif da haihuwar sai gata ta canza,ba zakace itace me jego ba.
Wani irin girma yaran sukeyi tamkar ba madara suke sha ba,wani irin wayo kai zaka ce sun doshi watanni uku ma. Bul bul dasu kamar ana hurasu, weather din Austria tamkar don saboda su aka halicceta. Wayo na masifa a cikinsu,sunsan idanun ama sunsan na tanja,don na sultana bai fiya ganuwa a garesu ba. Bata kyararsu,amma ba kasafai take shiga shirginsu ba,idan suna kuka dai takan daukesu idan ama bata wajen,amma indai tana wajen saidai ita ta dauka ko tanja.
Cikin kwanakin talatin da biyar din taji dukka hankalinta ya fara komawa gida. Ta yita duba saqonninta na layinta da email ko zata ga saqon sakinta daga hamid(aba) duk da tasan abune me wuya amma bata gani ba,sai saqon roqon ta dawo ta email dinta har babu adadi daga aba,saddi atta harma da almu.
Visa kawai ta shiga nema musu,tana ganin zuwa yanzu lokaci yayi da zasu koma. A yanzun zata koma da dukka qarfinta ne,zata sanya auduga ta toshe kunnuwanta,ta sanya duk wani effort nata ta nema inda maina yake,tana da buqatar danta,ba don komai ba kodon yaran da ya dasa baisan da wanzuwarsu ba,ya kamata su tashi da dumin ubansu. Ba zata sanya kowa neman maina ba,ita daya zata fuskanci komai,ita daya zatayi fadi tashinta,yadda suka dauki zafi dashi saidai suga dawowarsa gida......amma kuma hakan ba yana nufin itama ba zata hukuntashi ba bisa laifinsa,amma hukunci ta hanyar da ya dace.
Sultana batace komai ba bayan ama ta miqa mata passport dinta dake dauke da visa din Nigeria. Ta danji sassaucin ganin qasar nigeria zasu fara shiga,kwata kwata nijer ta fita a kanta, batasan ma ta yaya zata fuskanci rayuwa ba a can. Zaman gida zatayi tayi rainon yara?,ko makaranta zata koma cikin qawayenta da a yanzu ita kanta tasan tabbas ta banbanta dasu?,dukka dai bata sani ba.
********Sun baro Austria cikin matuqar kewa, Vienna garin da suka shuka tarihi a ciki suka kuma binne,sun fito da benazeer da batoul da a yanzun suke da shaidar zama cikakkun 'yan qasar Austria halak malak,wanda sanadin haihuwarsu qasar ya basu wannan damar.
Transit ne na kwana guda a Egypt cairo,sun sauke luggage dinsu a gajiye,amma ama tace su shirya su fita su zagaya,akwai guraren tarihi me kyau da yake da kyau suje din. Tanja na murna ta gama shirinta,ta kamawa ama shirya su benazeer daketa wutsil wutsil abinsu,kamar sunsan suna kan hanyar komawa qasarsu ne.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 26
Sanda ama ta fito sultana na zaune ta saka tv a gaba tana kallon news,wanda ama tayi imani ba wani fahimtar me akeyi takeyi ba,kawai tsabar zama