Showing 45001 words to 48000 words out of 294767 words
Chapter 16 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
yayi.
Dukka qarfi da basirarta ta sanya don tabbatar da farincikin sultanan. Ta sake qirqirar abubuwan da tasan zasu dauke mata hankali. Tilas ta dinga siyan ticket na zuwa qasashen da suke maqwaftaka da Austria duk don ta faranta ranta,ta kuma sake don a samu a cimma nasara.
********Misalin qarfe tara na dare ta fito daga toilet din. Daure da babban towel take amma sam ya kasa ratsata saboda girman uban cikin dake gabanta. Da qyar take daga qafafunta,duk ta qarasa zama wata babba ta kuma kumbure har fuskarta. Dazu daxu kafin ta shiga wankan ta gama cikin kukanta,abinda ya ruruta idanunta kenan,ya kuma sanya fuskarta ta sake yin jazur.
Kai tsaye ta isa gaban mudubin ta tsaya tana kallon kanta da kanta,wani zazzafan hawayen ya zake silmiyo mata,ganin kanta takeyi kamar ba ita ba,sau tari idan ta kalli fuskarta takanji kamar ba itace sultana ba,itakam a rayuwa tana jin hatta da shaidan saidai maina ya biyo bayan qiyayyarsa a zuciyarta. Batajin har abada zata iya yafe masa,batajin akwai wani wahala ko Azaba da zata ganshi a ciki da zai karya zuciyarta taji zata yafe masa. Kullum kwanan duniya fadi take fili da zuci
"Allah ka sakamin". Hannu ta saka ta yaye towel din,tulelen cikinta dake rinjayarta ya bayyana,yayi girma qwarai ya kuma yi tsini sosai,ta dafe qasan mararta da nauyin da takeji yafi yawa a nan akan ko ina,Allah Allah takeyi kwanan watan da ama tace mata zata karbi babyn yayi,Allah Allah take a cire mata shi,ta hanci ne?,ta baki ne?,ta kunne ne oho itadai ba matsalarta bane. Matsalarta daya ta wayi gari ta jita wayau,ta jita ta tashi babu wadannan lalure laluren da uban nauyin da yake damunta.
Turo qofar da akayi ya sanyata saurin sakin towel din. Ama ce ta kuma ga abinda ta tsaya din tana kalla amma sai tayi kamar bata gani ba,ta dauke kanta ta shigo dakin tana fadin
"Bakijin sanyi sanyin garin nan daya fara busawa?"
"Yanzu zan shirya" ta fadi da dakusashiyar muryar da har yau bata bude qwarai ba don ba maganar ma ta fiya yi ba bare ta bude yadda ya kamata.
Tana kallon ama ta gefen ido ta jawo akwatin da kusan kullum sai taga tazo ta shiryashi,ta kuma sake zuba kaya,ita kadai cikin ranta take mamakin kayan da ama din keta narkawa akwatin,bayan tace mata dashi zasu tafi asibitin,to tabbata zasuyi cikin asibitin da aketa loda ma akwati kaya?,oho bata da wannan amsar,sai kawai ta jawo lotion ta fara shafawa a jikinta.
*********Sanye da kayan theatre Dr abdur'razaq mansoor ke fitowa daga office dinsa. Gefansa wani gajeran likita ne baturen qasar Austria din,yana riqe da files a hannunsa suna magana da Dr abdur'razaq din cikin harshen German.
Ama dake zaune saman kujerun dake daura da theatre room din ta miqe tsaye tana jiran qarasowarsa. Dab da zasu iso din ya sallami likitan ya shige dakin theatre din shi kuma ya amshi file din hannunsa yana qarasowa.
Yaga fargaba,sarewa da kuma tsoro a tattare da ita,abinda bai tana gani ba kenan daga gareta tsahon watannin da sukayi suna zuwa gurin nasa. Tsayyayyar macace da ba komai ke firgitata ko kuma ya bata tsoro ba. Ya sani a irin situation din sultana dole ta fuskanci fargaba da tsoro,don haka ya sakar mata murmushin dake bada qwarin gwiwa,ya miqa mata file din yana kallon agogon hannunsa
"Ki kiranta a nutse ki sanya hannu,sanya hannun shi zai bamu damar fiddo miki jikokinki nan da mintuna talatin kacal in sha Allah". Hannu tasa ta amsa,ta koma ta zauna kusa da tanja gwiwa a matuqar sanyaye,ta buda page din ta fara karantawar tana sanya hannu,saidai a duk inda ta sanya hannun,sai zuciyarta ta jaddada mata.....muddin aka samu akasi la shakka itace ta kashe sultana
"Hasbunallahu wani'imal wakil" take bin mummunan tunanin da shi,har ta kammala ta rufe ta miqawa Dr abdur'razaq. Amsa yayi yana sake murmushi
"Compte à rebours les minutes(ki irga mintunan)" ya fadi yana bata qwarin gwiwa cikin idanunsa,sannan ya taka zuwa qofar dakin theater din ya sanya kai bakinsa dauke da bismillah.
Ragwaf ta koma ta zauna,ta dunqule dukka hannayenta cikin na juna tana jin jikinta yana mata wani yaarr,ta dinga maimaita kiran sunan Allah data samu bakinta ya fuzgo sanda tanja dake riqe da carbi take maimaitawa a fili don ta samu ama din ta kama kuma nutsuwarta ta dawo.
Mintina biyar kacal ambaton sunan Allah ya saukar mata da nutsuwa,saita zaro wayarta as usual ta turawa maina tex akan current situation din da ake ciki,ta maida wayar tsakanin cinyoyinta kawai tana ci gaba da kiran Allah.
Da ita da bibi batasan waye ya riga wani miqewa ba sanda qofar theater din ya bude ba,saboda mintunan da Dr abdur'razaq mansoor ya basu sun cika harma sun gota da wajen qarin mintuna wasu talatin din akai.
Dr dinne da kansa,iya fara'ar saman fuskarsa kawai ta bayyana musu labarin me dadi ne,ya qaraso gabansu yana cire facemask din fuskarshi
"Alhamdulillah,anyi nasara,an ciro mata tagwaye dukka YARA MATA" ya fadi yana duban tanja da ta qame cikin zallar farinciki.
Batasan yaushe bane,ba kuma tasan ya akayi ba,itadai taji dukka gwiwoyinta sun zube izuwa qasa,kafin daga bisani fuskarta da goshinta su kafu a qasa
"ALLAH kaine Allah,Allah ina me tuba izuwa gareka,Allah na tuba bisa dukka laifukana,Allah na tuba bisa dukka zunubaina,Allah na tuba bisa karan tsaye da nake yiwa al'amuranka, ubangiji a yau ka tabbatar min da qarfin ikonka,Allah ina godiya a gareka,Allah na gode mahaliccina na gode,ya hayyu ya qayyumu kasa yarannan rayayyu ne,duk wani dake boye da wanda ke a zahiri Allah ya daidaitashi cikin izza hikima da buwayarka,Allah ka bawa mahaifiyarsu dangana,ka bata haquri,ka taushi zuciyarta,ya hayyu ya qayyumu ka karkato da hankalin mahaifinsu gida,Allah kaine mafi sani,kafi kowa sanin hikimar data sanya ka wanzar da wannan al'amari,ya arhamar rahimeen ka sanya qarshen komai ya zamana da kyakkyawar cikawa" sannan ta cikashe da maimaita alhamdulillah har sau babu adadi.
Itama tanjan sumbatun addu'a kawai ta dinga yi,hawaye ne itama cikin idanunta,yau 'yar lelen bibi ta zama uwa,yau 'yar lelen bibi da yara har biyu?,tabbas wannan haihuwa inda cikin gida nijer akayita batasan wanne irin cika yau asibitin nan zaiyi ba,batasan adadin farincikin da fuskokin mutane zasu nuna ba.
Da suka buqaci ganinta ba'a hanasu ba,wata nurse ta musu jagora zuwa dakin hutun da aka bata wanda suna ciki ita da yaran da aka dawo dasu daga sashen yara yanzu yanzu bayan anyi musu gwaje gwaje da bin qwaqwafi irin na bature. Sakamakon da suka gani ya basu mamaki kodon qarancin shekarun uwar yaran. Sun jima basuga lafiyayyun yara irin yaran ba,ga wani irin girma kai baka ce daga cikin qaramar yarinya under 14yrs suka fito ba.(ai addu'a ba wasa bace,duk wanda ya gaza ganin tasirin addu'ar da yakeyi to baiyi addu'ar da kyau bane,ko bai cika sharuddanta ba,ko kuma baiyi addu'ar yana bawa Allah dukkan yaqininsa ba da yardarsa ba).
Duk yadda taso taje ta fara ganin fuskar sultana dake bacci daga ita har tanja sun kasa,gaba dayansu gadon babies din suka nufa,hannun kowa yana rawa yana saurin isa garesu.
"Ma sha Allahu la quwwata illa billa,ma sha Allah....tabarakallahu ahsanul khaliqeen....." Ama ta dinga maimaitawa bakinta yana rawa.
Wasu irin fararen yara masu cikar zati da kyau,wasu irin jarirai masu tsananin kama da juna,kyawawan jariran da batasan ma kamannin waye zatace sun dauko ba. Farare tasssss tamkar iyayensu haifaffun Vienna ne ba nijer ba,nannade cikin fararen kaya masu tsananin taushi da daukan idanu.
Yadda hannunta ke rawa ta tabbatar muddin ta daukesu tana iya yada su,hasalima bata iya gani sosai saboda uban hawayen dake narke cikin idanunta,saita sanya dogayen yatsunta ta riqe siraran yatsun yaran dake nannade cikin safar hannu. Duk yadda taso riqe kanta sai ta kasa,kuka ya balle mata,tayi qas da kanta tana kokawa,tanja tana bata baki.
Ina maina ya tafi?,ina aliyyu yaje?,yazo ya gani a yau shima ya zama uba,a yau yabar yabanya,a yau ubangiji ya cika masa burinsa,mafarkinsa,kuma fatansa,burin da a sansa yake furtawar yana fada ne kawai ba tare da samun tabbacin fatansa zai cika ba
_"duk randa nayi aure,matata ta haifami 'ya mace haihuwar fari ama ke zan bawa,in sha Allah sai na share miki kukan rashin haihuwar 'ya'ya mata,sai na dauke miki takaicin da ake sakaki na hanaki riqon 'ya'yan wasu"_ wasu daga cikin kalaman maina kenan a duk sanda yaga tana neman 'yar budurwar da zata riqe,ko kuma taje ta daukota akazo aka karbeta,ko kuma ta fara riqon taje hutu taqi dawowa. Yau gashi burin maina ya cika,bama yarinya daya ba,yara biyu reras a lokaci guda,itakam batasan me zata cewa Allah ba.
Ko sau daya ama ta kasa motsawa daga gindin gadon,ta kasa dauke idanunta daga kan yaran,duk wani motsi da zasuyi saman idanunta ne,kamannin yaran sun baci ainun. Wata irin mahaukaciyar soyayyarsu ce ke ratsata tun sanda ta dora idanunta saman fuskarsu,sai takejin kamar a duniya bata taba son wata halitta ba tunda Allah ya halicceta sai a kansu.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 page 24
A hankali ta zare hannunta daga nasu bayan sunsha hoto,sun sha videos har batasan adadinsu ba,ta matsa kusa da sultana karo na biyu taga kota farka a baccin?. Har yanxu dai baccin takeyi lakadan,fuskarnan ta fada tayi kuyas,hakanan duk girman jikinnan ksmaryan zugeshi tare yaran,ta ragu sosai,qanqantarta ta soma dawowa.
Sai data fuskanci lokacin sallar azahar yayi sannan ta tashi a wajen,ta shiga bandaki ta daura alwala tabar tanja a wajen.
Sanda take idar da sallar sultana ta motsa,ta shafa addu'ar da sauri ta miqe ta nufi sultanan.
Tun daga idanunta zuwa jikinta take jinsu wani iri,batayi yunqurin miqewa ba saboda nauyin da jikinta yayi mata,kanta ta mirgina gefe guda tana kiran Allah can qasan zuciyarta,zuciyar tana bata zaiyi wuya idan ba mutuwa tayi ba,don ba abinda zata iya tunawa,tadai jita daga qarshe kamar tana yawo cikin iska.
Ama data hango tana tahowa ta tsurawa idanu. Da murmushi a fuskarta ta taqaraso,ta jawo doguwar stool dab da gadon nata ta zauna. Idanunsu cikin na juna
Hannunta ta miqa ta riqe hannun sultana wanda babu qarin ruwa a jiki
"Kin tashi?" Kai gyada mata tana ci gaba da duban ama din
"Sannu" yauwa tace da ama,amma sautin baya fita sosai.
"Me yake miki ciwo yanzu?" Kai ta girgiza alamun ba komai,hakan ya yiwa ama dadi,sai taci gaba da zama a nan din bata sake cewa komai ba kaman yadda sultana din itama bata sake magana ba,sai idanunta data mayar ta lumshe. Tana jin alamun cikinta empty babu komai,duk uban nauyin dake jibge tana jin ba komai a cikinsa,tasan dai kenan tabbas an cire baby din kamar yadda ama tace mata,to amma yana ina?, Ta yiwa kanta tambayar
"Oho" ta sake baiwa kanta amsa
"Kome meye na cika umarnin ama,nima ama ta cikamin alqawarina,ban mutu ba gani ina raye,baby dama nasu ne,na gama nawa aikin" ta gayawa kanta da kanta,don haka tayi relax daga kwancen,duk da tanajin ta soma gajiya da kwanciyar.
Qushin qushin din qananun kukan jariri shi ya sanyata bude idanunta a hankali,saidai kuma bata yarda ta juyar da kanta sashen da take jiyo kukan ba
"Hajja yaran nan fa da alama maciya ne,tun dazu sun kasa nutsuwa sai mutsu mutsu sukeyi,ya kamata a nema wani abun a basu,tunda naji kince likita yace idan sun nema din a basu" tanja dake rungume da daya daga cikinsu ta fada
"Eh,ai bari nazo nayi musu addu'a cikin kunnensu" ta fada tana zame hannunta daga na sultana.
"Har su nawa ne?" Sultana ta yiwa kanta tambayar can qasan zuciyarta,duk takun ama zuwa wajen yana qididdige a kunnenta
"Wacece babba ne?" Tanja ta tambayi ama tana duban fuskokin yaran
"Akwai alama da suka sanya a qafafunsu"aman ta fada tana duban qafafun yaran.
"Ga hassana ga usaina" ama ta furta tana murmushi hadi da duban fuskansu.
"Anya wannan nan gaba za'a dinga banbancesu?" Fuskokinsu ama ta duba sosai
"Subhanallah subhanallah" aman ta fadi da sauri tare da yiwa tanja nuni da hannu. Daidai gefen kunnen hassana,wani digon baqi sak irin na maina
"Tanja kin gane wannan?" Ama ta fadi muryarta tana dan rawa,abinda ya sanya sultana bude idanunta da sauri,ta kuma juyar da kanta sassan da su ama ke tsaye tana ware idanunta cikin fargaba
"Allah hakimu,Allah me iko,irin digon baqin dake kunnen maina" da sauri sultana ta runtse idanunta saboda kiran sunan maina din, tsakiyar qahon zuciyarta taji kamar an caketa da wani qarfe. Tanason saka hannuwanta ta toshe kunnenta don kada ta sakeyin kuskuren jin sunansa ko wani abu da yayi kamanceceniya da shi,saidai a daidai lokacin ama ta yiwa tanja alama da idanu na kuskuren kiran sunan nasa da tayi,don haka tanja din bata sake cewa komai ba,sai ama data miqa hannu ta karbi yaran ta sanyasu cikin jikinta sosai,dumin jikinsu yana haduwa,wani irin qauna ta jini tana ratsata.
Dukka addu'o'in da musulunci ya tanada tayi musu,ta kuma yi musu huduba cikin kunnuwansu,sannan ta basu suna kanta tsaye ba tare da shawara da kowa ba FATIMA BINTOU DA NADEEYA (mahaifiyar sultana da kakarsu aba). Hadasu tayi dukka ta sake rungumesu a jikinta tana sauke ajiyar zuciya. Ko yau ta mutu burinta ya cika,babu kuma abinda zata cewa ubangiji face godiya mara qarewa.
"FATIMA BATOUL da NADEEYA BENAZEER" Ama ta fadi idanunta akan fuskarsu. Masu cikakken gata irin gata da ba kowanne bawa Allah ke tsagawa da rabonshi ba,amma sai gashi sunxo tsakiyar wata irin cudewa rikita rikita da kuma cakwakiya,saidai koma meye ita din ba zata bari komai ya shafi rayuwarsu ba,zata basu cikakken gatan da suka cancanci dashi,zata basu dukkan wata rayuwa da duk wani me tutiya da tunqahon gata zai sameta.
Har likita ya bada umarnin sultana zata iya zama zata kuma iya miqewa,sannan ya bada umarnin duka a ranar za'a iya goge mata jikinta,za'a kuma iya nema mata wani abu me ruwa ruwa tasha bata tambayi yaran ba ko sau daya. Duk ama na ankara da ita,ko sashen da suke bata kalla,sai tayi mata shuru batace da ita komai ba,har sai data gama goge mata jikin,ta zaunar da ita tana bata abu me dumi. Dab da sultana din take zaune,ta miqa mata spoon bakinta sannan tace
"Baki tambaya baby ba sultana uhmmmm" shuru ta danyi,sannan ta bude bakinta a hankali
"Naki ne ama,dama kince ke zan bawa,na bakin ai" kai ama din ta jinjina tana jin ba dadi,kada dai ya zamana su rasa soyayyarta kamar yadda taketa tunani tun dazu.
Rabuwa tayi da ita har sai data gama batan sannan ta maida bowl din. Ta qarasa inda yaran suke ta dauki batoul sannan tanja ta aza mata benazeer ta rungumosu a kafadanta.
Da idanu sultana ta bita sanda take aza mata yaran saman cinyoyinta,bata budesu ba ta kalleta tana murmushi
"Budesu ki gansu" cewar ama. Idanu biyu dukka sultana ta fiddo,sai kuma ga hawayen nan nata da bata gajiya da xubdashi
"Har biyu ama?,ni ba guda daya kikacemin bane?,har guda biyu?, gaskiya ni guda daya ne.....guda daya ne Allah" mamakin tarin quruciya irin ta sultana da bata rabuwa da ita ya kama ama
"To biyu Allah ya baki,yanzu a ciki wanne ne bake kika haifa ba?,wace bakyaso?,bude ki kalla ki zaba na zaba a bada dayan,dayar kuma saiki bata nono kinji kinga duk yunwa sukeji" kuka ne ya qwace mata
"Ni banaso duka,banaso ama,kuma ba Wanda zan bawa......." Sai ta kasa qarasa fadin nonon ta sanya hannunta mara qarin ruwan tana janye zaninta,abinda ya sanya batoul ta gangaro sosai jikin benazeer,nauyinta kuma ya sanya benazeer ta gaza riqeta suka fara gangarowa.
A gigice ama ta sanya hannayenta ta fada tallafe yaran zuciyarta na bugawa da tsananin tsoro,saboda ba qaramin shammatarta tayi ba,dukkansu yaran suka tsanyare da kuka a lokaci guda,da alama suma din sun tsorata dinne.