Showing 135001 words to 138000 words out of 294767 words

Chapter 46 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

tana jin zuciyarta na sake samun rashin madafa game dashi,wanda muddin hakan yaci gaba da kasancewa tasan tabbas......indai tanason tsira da rayuwarta to takai batun gaba bro da daddy. Muryar tata ta fita tas ta kuma karade motar har kaman tana amsa kuwa.

"Am on the way laila......i will call you" ido ta runtse,wannan kalmar ta gama haddaceta tsaf a bakin maina,kuma ta fahimci dukka salo ne na koreta daga yin doguwar waya dashi.

"Alright" ta amsa masa a taqaice tana katse kiran.

Gaba daya ji take kaman ta sauke glass din ta fita ta window din motar,laila.....laila.....bashi da aiki sai zancanta?,shi ko kunya ma bayaji?,ya gama yawon duniyarsa ya dawo da abokiyar shashanci har ya bari ta dinga kiransa?.

"Mtseww" taja tsaki tana gyara yafen mayafinta. Sam sam bata dauka tsakin zaya fito ba,saidai ya fita din da sautinsa sosai. Ido ya runtse yana jin kaifin tsakin kamar an zura masa abu cikin kunnuwa.

A nutse ya rage gudun motar,sai ya koma tafiya slow kafin ya sanya signal ya fara sauka gefan titi. Mamaki ya cikata ganin yana qoqarin parking qasan wata bishiya cikin bishiyoyin da aka qawata gefan titin dasu. Bataga wani shop ko masu saida wani abu a wajen ba bare tayi tsammanin wani abu zai siya. Sanda ya tsaida motar cak ya kuma kasheta sai mamaki ya hanata sukuni,sai data juyo tana dubansa da fararen idanunta.

A lokacin ya nutsu ne gaba daya ya zuba mata lion eyes dinsa yana kallonta,dauke idanun nata tayi tana kauda kanta hadi da hadiye abinda takeson fada. Tana ganin bata bakinta da lokacinta ne ma ta tsaya yi masa magana,shuru shi yafi dacewa dashi.

"Waye kika yima tsaki?" Kasa bashi amsa tayi sai qeya data juya kasa,kwantankwacin abinda takeyi masa a shekarun quruciyarta sosai duk sanda yake mata fada

"Look!" Ya fada da kakkausar muryarsa

"Kinyi tsaki na farko a waya.....nayi warning dinki,kinyi na biyu yanzu a gabana......karkiyi kuskuren maimaita na uku......am not your mate..... uban 'ya'yanki ne....yayanki kuma mijinki,hope i made it clear to you?" Wani haushi ya sake saukar ma zuciyarta,yadda yaketa jero wadannan bayanan da matsayinsa mataki mataki tana jin kamar ta fasa motar ta fice,saidai tunda suka shiga taji qarar saka security a kulle take. Bai damu da amsarta ba don yasan tsiyar daya qulla mata a yau din,sai ya juya sosai ya soma kwantar da kujerar motar ya miqe qafarsa ya kuma yi relaxing bayansa abinsa bayan ya kunna sauti can qasa.

Shurun da taji yayi yawa ba motsinsa ba kuma alamun kunna motar shi ya sanya ta fara tambayar kanta da kanta ko lafiya?,banda sauti da AC din da ya bari a kunne ba abinda ke motsi cikin motar. Ta dinga qoqarin kallonsa ta gefan idanu,saboda batason ta juya ta kalleshi ta bada kanta,da qyar ta hangeshia a kwance abinsa sambal tamkar yana cikin dakinsa a kan gadonsa

"Wannan wanne irin mulkin mallaka ne?" Ta tambayi kanta da kanta bayan ta duba agogonta taqa a qalla sun share mintuna talatin a wajen shi bai motsa ba itama bata ce masa ta tafas ba. Ci gaba tayi da duba agogonta akai akai,taci alwashin ba zata masa magana ba har dai ya gaji da kansa ya tashi motar sun tafi,saidai kuma duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya kuma baci akan wancan bacin ran. Wanne irin mulkin mallaka ne wannan?,hankalinsa kwance yanata sauya tattausan busar guitar din dake tashi a motar xuwa nau'i daban daban?,ita ya barta zaune ya kuma tsareta?,bai barta ta tafi ba bayan bata gayyatoshi cikin rayuwarta ba?.

"Zaka iya bani key din motata ka sauka ni na wuce,ina da wajen zuwa" ta karya billenta daga qarshe ta furta murya a cunkushe kamar wadda aka yiwa cushen tsumma.

Sirrintaccen murmushi daga can qasan zuciyarsa ne ya subuce masa,dama so yake gaya iya nata taurin kan da kafiyar,batasan yanzu aka soma ba

"Ni bani da abunyi.....don mun kwana a nan ma ba damuwata bane indai ba zaki koyi manner na magana dani ba" sake baci ranta yayi,me yake nufi?,ta qasqantar masa da kanta kenan ko.meye?,lallai tarin neman fitina ce kawai qasan ransa,banda haka na meye zai dinga shiga gonarta har haka?.

Sai daya mula don kansa sannan ya miqe ya zauna sosai,yasa zara zaran yatsunsa yana maida sumarsa baya,sannan kuma a nutse bakinsa yana ambatar

"Bismillah" ya tayar da motar,saidai a yanzun ya rage gudun da yakeyi sosai dukka hannuwansa dafe da sitiyarin motar.

Idanunta nakan hanya,tana kallon shimfidaddiyar kwaltar zuciyarta kuma cike fal da tunani iri daba daban. A hankali ta fara lura hanyar da yake bi din kamar ba hanyar gidan amaren bace,don ta riqe kwatancen da dunan street din nasu. Tsoro ya sake kamata,wannan karon kuma kai tsaye ta kasa shuru ta magantu

"Ina zaka kaini?,nan ba hanyar bace" juyowa yayi idanunsu suka hadu waje daya

"Nace miki fyade zanje nayi miki karo na biyu tunda wancan ya amsa sunansa" yayi maganar yana dauke kan motar suka shiga wani titi na daban da wani irin zafin nama.

Ido kawai ta zuba suna ci gaba da wuce wurare har suka iso babban ginin daya tsaya a gabanshi yana karbar binciken security kafin wucewarsa ciki.

Idanunta ta daga tana qarewa ginin kallo,sunan data gani daga qarshen sunan dake kafe a tsororuwar babban ginin ya sanya gabanta harbawa

"Hotel?,to me sukazo yi s hotel?" Ta tambayi kanta da kanta. Kafin ta lalubi amsa har ya gama da security ya wuce cikin babban harabar hotel din.

Ko ba'a gaya mata ba da ganin tsari da girman wajen tasan hotel ne na manyan mutane masu hannu da shuni,komai bisa tsari tun daga farfajiyar har tsarin ginin wajen

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 71


Bayan ya daidaita tsaiwar motar,ya zare seatbelt dinsa yana dubanta,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude side dinsa ya fice. D

Bata koda kalli sassan da yake ba har sai da taji ya maida murfin ya rufe, second biyu ta bayar ta waiwaya da kanta tana duban gefanta.

Cikin takun nan nasa me cike da ginshira da qasaita yake takawa zuwa main entrance na hotel din,hannunsa guda daya zube a aljihun wandonsa,daya hannun kuma wayarshi da key din motar ya riqe. Idanunta ta kawar tana tabe tana jan tsaki,tana mamakin irin qarfin halinsa,yanayin komai kamar baisan ya aikata komai ba,kamar kuma bame laifin komai ba,yanata maimaita kalmar fyade zaiyi mata kamar wata kyakkyawar kalma me dadin ji da sauraro?,baya ma ko kunyar idanunta bare abinda ya aikata a baya da ita har yanzun sunan fyade ta bashi?,duk da ta fahimci da gasken ba fyaden bane,sadakinsa na saifa daya bayar ya sauyawa abun suna a musulunce. Yanxun daya kawota nan din me zaiyi a ciki?, Tambayar data yiwa kanta kenan kuma bata da amsarta.

Tunaninta ya katse sanda kira ya shigo wayarta,ta bude handbag dinta ta zaro wayar tana gyara ajiyar cards dinta masu amfani dake ciki. Yasmin ce sarkin zaquwa da gaggawa

"Shuru.....shuru sultana lamarinki sam babu kara fa" yasmine ta fadi cikin zumudi

"Afwan yasmine...... kin ganni nan......" Da sauri ta katse abinda da farko tayi niyyar fadi,sam ta mance,tana shirin dabawa kanta da kanta wuqa

"Ina hanya bazan wuce awa daya ba in sha Allah"

"Shikenan,ina jira,aminata ma ke take tsumayi"

"In sha Allah" ta amsa mata tana lumshe ido saboda bacin rai daya taso.mata. gaba daya ya sauya mata akalar tafiya?,wai anya ma ba sassauci ya gani saman fuskarta yake neman rainata har haka ba?.

Tana katse kiran tare da qoqarin sauka daga call logs dinta taji ya bude murfin motar a hankali. Sam batasan da isowarsa wajen ba don hankalinta baya kai. Idanunta ta daga a hankali ta sauke dubanta a kansa. Yana tsaye gabanta,cikin cikakkiyar tsaiwar nan tasa dake sake fidda diga da zatinsa. Cikakken tsayayyen ba'abzine dogo fari tas. Shima ita din yake kalla,hasken rana daya haska qwayar idanunta dake da sheqi kamar an diga zaiba sai ya bada wani irin haske me kyau,abinda ya masa kwarjini qwarai,mazantakarsa ta sanyashi shanyewa,ya sassauta kafin nasa qwayar idanun cikin nata kadan,sannan ya rusuna yana dauke handbag din take saman cinyarta,wanda kafin tayi kowanne yunquri ya soma takawa yana barin wajen

"Taso mu qarasa"

"ina?" Ta tambayi kanta tana fidda ido waje. Ganin bai waiwayo ba ci gaba yakeyi da shiga ciki,ga idanu da sukayi yawa a kanta dole ta zura qafafunta waje tabi bayansa. Tana biye dashi saidai ta cika tayi fam da bacin rai da baqinciki

"Wai me wannan yakeji dashi ne?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar. Yadda suka dinga wuce security ana checking nasu duk inda suka wuce ya sanya ta sake shiga nutsuwarta sosai amma kuma ranta cike yake fal da fargabar shigarta wajen,batasan me yazo yi ba,batasan me ya kawosu yi ba.

Elevator taga ya nufa,ya danna ta bude ta shige,sai a sannan ya waiwaya yana kallonta. Ja tayi ta tsaya,abun ya isheta haka,ya maidata kaman wata raqumi da akala?. Yana tsaye daga bakin qofar ta yadda bazai bata daman rufewa ba ya kuma tsareta da ido.

"Idan kika qara minti daya a nan wannan karon nine zan miki ihu na kuma tara miki mutane kaman yadda kika yimin wancan karon" hanjin cikinta taji ya dunqule guri daya,daga yadda taga wajen yadda yake cike da matakan tsaro idan ya aikata mata hakan ta kade daga ita har ganyenta

"Idan kin damqani a hannun police har na kwana ni a hannun da zan damqaki ko?......." Bai qarasa ba illa yatsansa daya nunata dashi wani shu'umin murmushi na mugunta na kubcewa daga saman labbansa.

Babu shiri tayi taku biyu xuwa gaba,sai yayi taku biyu baya har ta shiga elevator din ya rufe dasu suka fara wucewa zuwa floor din daya zabar musu.

Tana tsaye daga bakin qofar dakin take qarewa dakin kallo. Babban daki ne wanda aka wadatashi da komai na alatun rayuwa. Kana ganinsa kasan vip suit ne na isassun mutane. Idanunta ta dauke daga kallon dakin ta maida kansa sanda yake qarasawa ciki yana ajjiye key din motar saman bedside drawer din dake dauke da bed lamp. Wani abu ta sake hadiyewa me tauri daya tsaya mata a wuya tun dazun

"Amma dai kasan inda zanje ko?" Ta jefa masa tambayar muryarta na bayyanar da bacin ranta

"Na sani......ina da buqatar na huta tukunna kafin mu wuce"

"Bana buqatar wani hutu.. wannan abun da kakeyimin ya isheni haka,ka bani key dina na tafi,idan kaso ka bari sai wata shekarar sai ka taho wannan ba damuwar sultana bace" ta fada tana yarfa hannu cikin fusata. Sosai ya zauna saman sofan dake dakin,ya kuma dora qafanshi daya saman daya yana qare mata kallo tsaf har takai aya.

Murmushin gefen baki ya saki yana kada kai

"Taurin kai da rashin kunyar nan naga alama da sauranta har yanzu......yayi kyau......haka nakeson gani" ya fadi yana sauke qafafunsa qasa,sai ya miqe cak abinsa ya qarasa bakin window din dakin,ya zuge labulen yana hangen view me kyau daga nan cikin dakin. Abun sai ya fusata ta,wato ya maidata wata mahaukaciya ma,ta hasala sosai,kawai sai ta fara masifa idanu rufe. Yi yayi kaman baiji ba har minti kusan biyu. Ya saki labulen ya juyo a tsanake. Kallo days yayi mata sai yakau da kai,ya sanya hannunsa a nutse ya fara balle botiran rigarsa.

Da farko bata ankara ba har sai daya gama ballesu tas,fara qal din vest dinsa dake ciki ta bayyana kanta,ya saka hannunsa ya fara zare rigar a nutse,ya cireta tsaf ya ajjiyeta a gefe.

Kallo daya tayi ma qirar jikinsa wata shakkarsa me qarfin gaske ta shigeta. Murdadden jiki me cike da baqa sidik din gargasa. Ba tare da yace mata kanzil ba sai gashi dukka maganganun da take zubarwa tana musu muhalli tare da maidasu cikin cikinta ragowar da bata ida furtasu ba. Tsoro sosai ya shigeta sanda ya zare ragowar vest din data rage a jikinsa ya waiwayo kuma yana dubanta.

Guri daya idanunsu suka sarqe,ya lumshe idanun nasa yana mata nuni da dogon wandon jikinsa yana riqe hannunsa a qugunsa. Ba qaramar yarinya bace ita,hakanan tun ba yau ba yayi mata sabo da body language,don haka sarai ta fahimci me yake nufi. Cikin dakiya ta aje masa wani kallo zuciyarta na tsananta gudu kaman zata fasa qirjinta ta fito

"Muqulli na kawai nake da buqata......kada ka yarda kaci gaba da shiga hurumin........" Bata qarasa ba ta tsinceshi gabanta,yayi mata katanga da faffadan qirjinsa. Dukka tsahonta ya shanyeshi,bata kuma tsaya ko ina ba sai daidai qirjinsa dake a waje cikin ni'imatacciyar lallausar suma.

Baya tayi niyyar ja da sauri,saidai kuma kafin takai ga aiwatar da hakan ya sanya hannu daya ya fusgota. Batayi masauki ko ina ba sai saman qirjinsa,fuskarta ta samu kyakkyawar tarba tsakiyar kwantacciyar sumar qirjinsa. Wani dogon matsoracin numfashi taja wanda ke cakude da sassanyan qamshin dake fita daga cikin gargasar tasar. Kafin tayi tunani na biyu ya sanya dukka hannuwansa biyu ya warware mayafinta tas.....bai barta ta gama nutsuwa ko tattara hankalinta waje daya ba ya sauke mata dankwalinta,wanda cikin sa'a ya hada harda ribbon dinta,abinda ya bawa doguwar sumarta daman bajewa gaban fuskarta zuwa gadon bayanta.

Tana cikin qoqarin tattara sumar nata cikin tashin hankali da tunanin me yake shirin aikatawa,fit......taji ya sauke zip din gaban rigarta gaba daya tun daga sama har qasa,abinda ya sakata sakin gashin nata kenan a muqar gigicewa da kuma razanin yadda ya iya aikata hakan kamar qiftawar idanu

"Mm......meyeh.....haka?,wanne abunne wannan?" Ta tambayeshi a gigice tana qoqarin tattaro gaban rigar tata don hana bayyanuwar jikinta muraran

"Ladabi zan sakeyi miki,don na fahimci yara biyun ma da kika haifa basu sanya kin sauya hali ba...... karatu kawai kikayi ba ilimi ba, yanzun zan baki cikakken ilimi,and yanzun yara uku nakeso na baki ajiya!"

"Maina!...... don't......" taja sunansa da wani irin amon sauti me dauke da tashin hankali......Sai ta kasa qarasa fadin abinda takeson fada din saboda tsintar tausasan tafukan hannayensa da tayi cikin ainihin fatar jikinta yana yawo dasu daga saman cikinta ya zagaya har zuwa gadon bayanta sannan ya zarce yana neman maballin bra dinta

"Don't what?.......ehhh?,ba zaki daina bani warning akan abinda yake halali na ba?,karki damu wannan karon nayi hankali nima,na sake girma.......you will enjoy it......babbabn ALBISHIR dinma tare zamuyi rainon cikin,tare kuma zamu shiga labour room din".

Rawa dukka jikinta ya dauka cikin matsanancin tashin hankali,bakinta ya kulle gam,sai kawai ta sakar masa muka sanda taji d'as! Ya balle bra din. Jikinta ta cukuikuye waje guda tana girgiza masa kai sanda taji yana qoqarin zare rigar da bra din duka daga jikinta,yana nufin ya ganta a tsurarta kenan?,abinda bata taba yi ba gaban wani d'a namiji

"Please......don Allah,i beg you.....kayi haquri" ta jefa masa roqon ba tare data shiryawa hakan ba tana girgiza kai kaman ba gobe.

Cak ya dakata daga abinda yake shirin yi,yayi komai ne akan plan da son cimma wani abu na sanyata ta sakeyin laushi,amma kuma sai abun ke neman zame masa na gaske,don ba wata kafa a jikinsa da bata mutu ba,gaurayuwar jikinsu waje daya da kuma yadda fatarta keda tsananin taushi sulbi da wani irin qamshi na musamman sun masa wata irin mummunar illar da basuyi masa a baya ba cikin qasa da minti daya.

Sake mata komai yayi sannan ya juya a nutse abinsa yana wucewa toilet. Da gudu gudu sauri sauri ta dinga maida komai muhallinsa,ta mayar din amma kuma komai a hargitse ta maidashi,ta lullube jikinta da mayafinta,saita sulale a wajen tana sakin qaqqarfan kukan da take ta riqewa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login