Showing 180001 words to 183000 words out of 294767 words

Chapter 61 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

me tsayawa a zuciyar wanda ake bawa saqo.

Idanunta dake da yalwar eyelash ta lumshe sannan kuma ta budesu,abinda yayi matuqar yi masa kyau,sai suka zama tamkar wani ado na musamman saman fuskarta,ya janye dubansa daga gareta yana sake hade rai,hade ran daya fidda ainihin miskilancinsa da ta sanshi dashi na asali. Juyawa tayi tana guna guni cikin ranta ta nufi dakinta. Saman bedside drawer ta dauko key din,har ta isa qofa ta fasa,ta dawo da baya saboda tuna wani abu da tayi,ta bude Wardrobe dinta ta fidda mayafi medium dake da kauri ta lulluba saman kanta. Sosai mayafin ya sake qara mata kwarjini,ya kuma cikasa kwalliyata,ta fita sosai da kamanninta.

Tana takowa waje tana wara maqullan tana laluba na motar,har yanzun mita takeyi qasan ranta. A saman idanunsa ta fito daga dakin,ya saki wata siririyar ajiyar zuciya,mayafin data sanya din ya masa dadi sosai,bai tsammaci zata saka din ba,sai gashi ta rufe jikinta yadda ya kamata.

Ratasu tayi a nutse har ta fice daga falon,ta maida qofar ta sakayata. Numfashi ya kuma ajewa,sai kuma yayi saurin daidaita kansa don ya tuna a inda yake,ya dan juya sashen ama,basu hada idanu ba amma kuma yaga sanda take maida dubanta wani guri na daban. Haka kawai jikinsa ya bashi duk abinda yakeyi din ta ganshi,sai ya danji nauyi ya kamashi,don haka ya miqe,idan ya fita waje tamkar ya bita ne,don haka kawai sau ya wuce kitchen yana cewa

"Bari na samo ruwa" batace masa komai ba don nunawa tayi ma kaman bata ganshi ba,ya miqe zuwa kitchen din yana dan shafa sumarsa kunya na tabashi.

Tana tsaka da mitarta sanda take bude motar taji muryarsa. Goumar ne,ta juya tana kallonsa,da alama a gurguje yake saboda yadda yake tafiyan da sassarfa

"Mommyn twins me za'a dauko mana ne?" Ya furta cikin tsokana. Harara ta watsa masa sannan ta juya tana jefa masa key

"Sarkin bin qwaqwqwafi......ka bude boot ka tayani mu kwashe kayan ciki"

"Angama matar babban yaaya" ya kirata da sunan daya jima bai kirata din ba. Tayi tsammanin zataji zafin nan da takeji cikin zuciyarta a baya idan ya kirata da wannan sunan,ta dauka zataji qunci a zuciyarta kaman yadda takeji a wancan lokacin,sabanin hakan bataji wannan ba,saidai taji kaman furucinsa ya taba zuciyarta,ta jefa masa harara tana cewa

"Wallahi yaa goumar ka bini a hankali,idan ba haka ba har najma ka shafa mata wallahi"

"Tuba mukeyi kar a hadamu da babban yaaya" ya fadi yana qyalqyalewa da dariya.

Shine ya taimaka mata tana fiddo kayan yana kwashewa har suka kammala tas. Kafin ta isa falon benazeer da batoul sun cikashi da karadin murna. Yau mummynsu ta basu gifts din da bata taba basu irinsu ba. Da gudu suka qaraso sanda take shigowa,suka rungumeta da kyau kaman yadda suka yiwa maina

"Mommy mun gode,thank you,thank you" yadda suka rungumeta din suna murna sai taji wani abu me sanyi yana sauka qasan zuciyarta,ta miqa hannunta ta dora a hankali saman sassalkan gashinsu da yasha gyara

"Allah yayi muku albarka" ta samu kanta da furtawa zuciyarta tana motsawa.

Ajiyar zuciya ama ta sauke tana jin wani alfahari da iyalan nata yana kamata,tayi qas da kanta tana yawaita addu'a cikin zuciyarta a kansu gaba daya

"Mummyn twins ina tunanin saidai ki fiddo abincin nan,idan nabar yaran nan a wajen nan barna zasuyi mana" ayeesha dake tsakiyar yaran ta fadi. Juyawa sultana tayi,sai tadan saki murmushi tana gyadawa ayeesha kai ta wuce zuwa kitchen din.

Yana saman freezer dake daga bakin qofa,duk me shigowa babu lallai ya lura dashi, musamman idan hankalinsa bai wajen. Apple ce a hannunsa yake gutsira a hankali yana jefa qafafunsa tamkar qaramin yaro, nishadi yakeji sosai har cikin ransa. Fes ya ganta lokacin data shigo din,amma sai yayi biris ya kuma sake rage motsinsa don kada ta ankara dashi a wajen.

Idanunshi a kanta sanda ta zare mayafinta ta ajjiye, murmushi ya kufce masa jin tana qananun mitoci

"Yanzu zanyi maganinta" ya fadi cikin ransa yana ajjiye apple din a gefen freezer din sannan ya sauka daga saman nashi a hankali ba tare da sautin takun sawayensa ya fita ba saboda socks ne a qafarsa.

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 96


Cikin nutsuwa ya tsaya dab da bayanta,ya zura hannunsa saman ruwan cikinta ya jawota jikinsa sosai ya adanata tsakiyar qirjinsa,don dukka tsahonta bata wuce tsakiyar qirjin nasa ba,wannan ya bata damar samun kyakkyawan masauki cikin jikinsa.

A ba zata abun yazo mata,saidai kafin takai ga cewa komai ya Sanya hannu ya juyo da fuskarta gefensa yana fadin

"Yarinyar nan har yanzu na fahimci sai a hankali,akwai sauran ladabtarwata......."

"Wai baka da wani punishment sai ta haka?" Ta fadi da sauri tana katsar numfashinsa,muryarta na nuna zallar tsorota da tayi. Dole siririyar dariya ta kubce masa,a karon farko tsoro ya bayyana muraran cikin muryarta,wannan shine abinda yakeson gani,wannan shine abinda yakeson fahimta dama tattare da ita

"Ashe da gaske horo na yana isa inda ya kamata yaje kenan" ya furta hakan yana dora hannunsa saman dogon dokin wuyanta,sai ya fara neman hanya yana zarcewa qirjinta. Numfashinta yaso daukewa jin har ya fara isa samansu,tayi caraf ta saka hannu ta riqe hannayen nasa tana cewa

"Ni ba tsoron......"

"Ba tsoron abun kikeyi ba?" Ya qarashe mata yana sanya hannunsa ya juyo da ita gaba daya suka koma suna fuskantar juna.

Musayar numfashi suka shiga yi,idanunsu sarqe dana juna,ya sanya hannu yana jawota qugunta cikin jikinsa sosai yana cewa

"Tunda ke jaruma ce a sake gwadawa mana........" Kai ta fara girgizawa tana dunqule hannunta saman qirjinsa

"Ni......niwai......" Ta fara magana cikin in ina,don maganar Allah ta sani,shi din ba kanwar lasa bane,duk da zuwa yanzun tana jin wani irin sauyi itama,saidai ba zata iya bari ya fahimta komai daga gareta ba,don babu babban abun kunyar da yafi wannan.

Sanda hankalinta yake neman yin wani gefen yayi amfani da wannan damar ya zame hannun nasa,bata ankara ba ta tsinci lallausan tafin hannun nasa a tsakiyar dukiyar fulanin nata. Abun yazo mata a bazata don haka ta dan zabura,bata kuma shirya ba ta fada jikinsa gaba daya tana qanqameshi sosai wai ko zata samu ya saketa. Ajiyar zuciya ta kubce masa,shi hakan data masa ya masa dadi sosai,sai kawai ya tayata qanqamewa cikin faffadan qirjinnasa dake fidda sassanyan qamshin turare da wani irin dumi da nutsuwa ta musamman.

"Na maimaita miki ko mutuwa tana tsoron idon mahaifi......ki sassauta min ko don ama....ko kina zaton bata sona ne?" Ya jefa mata tambayar yana yamutsata da kyau. Ba tare data shirya ba ta saki wani zazzafan hucin da siririyar qara,abinda ya qara masa shauqi kenan,ya saki murmushi qasan ransa yana fadin

"Daya kenan"

"Ka sakeni please,kada wani ya shigo kasan dai gurine na jama'a"

"If not fa?"

"Zan kwarara maka ihu" ta fadi

"Ihu?,wow......abinda sai bada citta..... bismillah mana,kinga daga nan kin ragemin nauyin wahalar yiwa mutane bayanin ina qaunar matata......ina sha'awarta...... inason kasancewa da ita.......ina buqatar........"

"Enough please....." Ta fada da wani irin tune saboda bala'in da yake kunna mata cikin jikinta,ga kuma qarin kalamansa da suke matuqar mata nauyi.

"noooo please"shima ya fadi da narkakkiyar murya cikin salon kwaikwayon muryarta yana sake matsata da kyau sake da sanyata cikin jikinta kamar me tsoron wani zai qwaceta daga gareshi.

Kansa ya soma qoqarin cusawa a tsakanin dukiyar fulanin nata,ba shiri ta riqe kanshi da kyau,tanason roqonsa amma labbanta dake rawa sunqi bata wannan hadin kan.

Motsin tahowar da akeyi zuwa cikin kitchen din shine ya ceceta,ya saketa da hanzari yayi taku biyu baya yana qoqarin daidaita mode dinsa,yayin da itama ta taka gaban sink tana qoqarin daidaita numfashinta gami da gyara zaman rigar jikinta.

Dai dai sannnan ama ta qarasa shigowa kitchen din tana fadin

"Anya sultana?,meye ya tsaidaki haka?" Tayi maganar idanunta akan sultana dake qoqarin bude famfo jikin sink din. Dan tsaiwa ama tayi tana kallonta,yadda hannayenta suke rawa sai abun ya bata mamaki. A hankali kuma ta waiwaya bangaren hannun damanta saboda qamshin turarensa data shaqa. Suna hada idanu sai ya juya yana yana shafa sumar kanshi a hankali,sai kuma ya taka a hankali yabi ta gefen ama din yana fita daga kitchen din. Batace komai ba ko bayan ya fita din,saita dubi Sultanan

"Kiyi qoqari ki fiddo abincin don lokacin tashi ya kusa"

"Tohm" ta amsa muryarta a shaqe ba tare data yarda ta juya sun hada ido da ama din ba,itama saita dauki ruwa kawai tana fita daga kitchen din ba tare da tabi ba'asin komai, jikinta dai ya bata akwai wata a qasa.

Da qyar ta samu ta saita kanta ta fara fita da abincin,saidai duk fitar da zatayi bata taba yadda su hada ido da ama,hasalima ko maina rin taqi duban sashen da yake,tasan dai kawai zai ja Mata zargine a zuciyar aman,duk abubuwa da yakeyi din a waje basu isheshi ba,a cikin gida ma sai ya biyota yayi?. Qwafa taja kadan, cikin ranta tana raya cewa zata yiwa tufkar hanci.

A matuqar gajiye ta isa dakinta don fiye da rabin gift da suka samu sai da suka budesu,don qememe suka hanata tafiya ta kwanta abinda taso tayi kenan,don tana sanya ran tashi da wuri ta fece wajen aiki kafin yakai ga iskota. Tun ba'a tashi daga party din ba ta nemeshi ta rasa shi da goumar, batasan Ina sukaje ba,hakanan sai tayi dabarar qin xama a falon a bude gifts din gudun kada yaje ya dawo ya taras da ita,so batasan ya dawo ba ko bai dawo ba.

Ruwa me zafi ta hada tayi wanka kawai,ta hada kayan da zata fita dasu goben waje daya sannan ta isa bakin qofa,key din jikin qofar da tunda tazo gidan bata taba amfani dashi ba ta murza ta rufe qofan,wannan shi daya zai bata nutsuwa,tunda dai batasan ta yadda yake shigowa dakin ba,to ta tabbatar kodai aljanine shi bazai iya buda qofan ba,hankalinta kwance ta kashe wutar dakin tabi lafiyar gado tana karanto addu'o'in bacci.

A nutse ta gama ta hura saman tafin hannunta tabi kowanne sashe na jikinta da ita,taja duvet ta shige ciki tana lumshe fararen idanunta.

A hankali komai da ya faru wunin yau ya soma dawo mata kwanya,duk kuwa da cewa muradin bacci take dashi amma sai taji idanunta suna neman qeqashewa. A hankali komai komai daya wakana cikin office din ya fara dawo mata sabo,ta qanqame jikinta duk a yunqurin hanawa kanta jin abinda take ji din.

"Wai meye hakan?" Ta tambayi kanta da kanta,bata taba sanin wannan abun zai taba dadata da qasa ko da sau daya ba a duniya,duba da irin wahalar data gamu da ita a karo na farko na faruwar abun cikin rayuwarta.

Bude idanunta tayi da sauri waiko zata daina ganin abinda take gani din cikin duhuwar idanunta,nan ma dai baby wani sauqi sai a wajen Allah,ta kira sunan Allah zuciyarta tana karyewa,kada dai ace ya goga mata cutar addiction da abinda tasan temporary ne,tana dan da daukan mataki akan hakan?.

Daidai lokacin da yake tsaye cikin balcony din gidan nasa dake facing gidan ama. Idanunsa tar akan gidan,yana tuna tunda yazo qasar bai bari aba yasan da zamansa a cikinta ba bare maqotakar dake tsakaninsu,kuma ya tabbatar zaiyi wuya ace ama ya gaya masa.

Idanunsa ya sake kaiwa kan wayarsa daketa burari kira wani yana bin wani,sai ya dauke kansa daga kan wayar yana maidawa kan mug din hannunsa ya zuqe ragowar madarar dake ciki yana shimfide idanunsa akan window din dakinta.

Yanayin rashin wadataccen haske daga window din dake da alaqa da dakin ya tabbatar masa ta kwanta koma ta jima da yin bacci,cikin kowanne gaba na jikinsa yakejin kewarta,yana jin shauqi izuwa gareta, xayaso yaje yayi mata kyakkyawan good night,amma koda ya duba agogo sai yaga ya kamata ya barta ta huta,ya tabbatar yau din ta sha zirga zirga,dole ya danne zuciyarsa,ya saki ajiyar zuciya ya sanya hannunsa yana debe wayoyinsa tare da kashesu gaba daya,don ya gaji da jarabar kiran yaran su biyun,kowacce cikinsu akwai albarkacin da take ci yake dage mata qafa.


*********Da qyar ta tashi tayi sallar asuba saboda yadda takejin gajiya a sassan jikinta da kuma rashin samun wadataccen baccin da batayi ba a daren jiya,a daddafe tayi sallar asuba,bacci yanason dibanta amma ta gana hakan faruwa saboda plan din d atake dashi na kubce masa da kuma hanashi yi mata karantsaye a aikinta,ta hada ruwa me dumi sosai ta deba kayan wankanta ta wuce toilet.

Karfe bakwai ta gama shiryawa cikin dubai abaya dake da zip yun daga samanta har qasa,da iya mayafin abayar kawai amfani tayi rolling bayan ta nade gashinta dukka ta cikin dankwalin da ribbon me fadi,da hand bag dinta da takalminta me dan tsinin dunduniya dukka na kamfanin gucci ne masu asalin tsada da tsari,yau kam tayi amfani da sun glasses daya sake maidata balarabiya sak,bata tsaya saka tarkacen kayan qawa da yawa ba banda dan earrings me wani irin dutse mai daukan idanu da kuma agogon data daurawa tsintsiyar hannunta na kamfanin Rolex.

Dimple dressing tayi amma kuma yayi matuqar karbarta,ta fito da wani irin sassanyan kyau. A nutse take taku har ta fito falon,ga mamakinta sai ta samu benazeer da batoul da kuma tanja suna ci gaba da qarasa aikin jiya

"Tanja biye musu kikayi?,ke din da kika sha hanya ba zasu barki ki kwanta ki huta ba?" Murmushi tanja ta saki

"Aikinsu ai shine nawa,har kin fito haka yau da wirwuri?,gashi ko karin safe ban gama ba"

"Ba komai tanja,idan ama ta farka kice mata na wuce,zanyi break a office" ta bawa tanja sallahu tana amsa gaisuwar yaran sannan kai tsaye ta wuce zuwa waje

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 97


Akan qofar gidan idanunta suka fara sauka,saita dauke kai tana dan tabe baki,yau kam taga ta yadda zaiyi mata karan tsaye,ta riga ta kufce masa,zuwa aiki kam babu fashi.

Sanda motar ta saitu saman hanya saita saki ajiyar zuciya,tana jin cewa lallai tayi escaping. Hannu ta miqa ta kunna gidan radion qasa dake paris,tana da sha'awar sauran labaran duniya sosai,wannan yana daya daga cikin abinda ya motsa mata sha'awar aikin jarida a baya.

Cikin qwarewa sa tataccen harshen faransanci aka soma watso labaran,tana biye dasu yayin data raba hankalinta akan titi,har zuwa sanda ta sanya signal ta fada saman doguwar hanyar.

Tana sake nisa cikin hanyar tana tuna abinda ya faru jiyan. Murmushi ys qwace mata sanda tazo dai dai inda abun ya faru. Can wani saqo na zuciyarta yana cika da mamaki,duk sanda yayi wani abu saita dinga jin kamar ba ya maina ba,ya maina dai wanda ko dariyarsa ke musu wahalar gani,me azabar bada punishment dinnan wanda bashi da sasaauci ko sauqi ko kadan,wacce KADDARA CE ta gauraya rayuwarsu haka waje daya?. A yau din karon farko kawai taji tana yiwa kanta wannan tambayar.

Kawar da zancan tayi daga ranta,tana sake maida hankalinta ga titi sanda take dab da fadawa Street


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login