Showing 246001 words to 249000 words out of 294767 words

Chapter 83 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

biki da birthday

"Tabbas likulli ajalin kitab" ya fadi a ransa sanda tazo dab da motar

"Wannan fa?" Ta fada tana turo baki,don batason saita shiga sannan y sake fiddota.

Sake binta da kallon qwaqwafi yayi from head to toe,a cikin jikinta har sai da taji kallon yayi yawa.

"La ba'as..... amma dai.....is okay" ya fada yana dage kafadunsa. Tanata tura baki ta bude gidan gaba ta shige,saita dauke kanta dukka gefe ta maida bangaren window.

Tanata jira taji ya tada mota shuru sammakal,har sai data gaji da sauraro ta waiwayo sashensa. Ashe kwantar da kujerar yayi abinsa ma yanata danne danne a waya. Ido duka hada ya matse fuskarsa don ya fahimci me takeson tambaya

"You know what?,......ba driver kika dauko ba da zaki zauna kina juyan qeya......if kin shirya tafiya ki gyara zamanki dai dai da yadda kowa yakeyi,Si vous n'êtes pas prêt à partir, cela ne me dérange pas de rester ici(idan baki shirya tafiya ba ni bazan damu muyita zama a nan ba)"

"Wai Allah na" ta fada qasan zuciyarta,mulkin mallakarshi yayi yawa,hatta da zama ma sai wanda ya aminta dashi zatayi?,ya Allah" ta sake fada tana fitar da numfashi. Dole ta motsa,ta gyara zaman nata tana bada attention dinta cikin motar.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 131



Boyayyen murmushi ya saki,yana tausaya mata ne kawai,saboda kowanne minti da second soyayyarshi yayi imani tana ninkuwa ne cikin ranta,kuma zatakai matakin da nan gaba sai ta yiwa kowanne sashe na jiki da zuciyarta illa,don ita soyayya ba'a hanata fidda kanta daga zuciya.

Wani slow music ya saka musu,daya daga cikin waqoqin wani shararren mawaqi dan qasar France. Cikin waqoqin da take mutuwar so a shekarun baya,waqan daya sanya saita dinga tuna mata quruciyarta,ta dinga tuna mata wani moment daya dade da shudewa,ta rufe idanunta kuma tana tuna abubuwa masu yawa da suka shude cikin rayuwarta.

Bata bude idonta ba har sai da taji ya kashe motar. Ta bude idanunta a hankali tana duban wajen. Asibitinsu ne ya kawota,daya daga cikin private hospital na musamman a garin.

Kamar kowanne lokaci shi ya bude mata qofar,yakuma bata hannunshi,dole ta aza nata akai,ya hadesu guri daya yana tallafe da hannun har ta fito ya rufe motar suka jera zuwa ciki.

Duk inda suka gifta sai sun dauki hankula,shi din sanannen likita ne cikin asibitin,don shine shugaban likitocin dukka asibitin gaba daya,amma ganinsa da kyakkyawar mace kaman sultana yaja masa wani kallon na daban.

Kowa ya sani turawa mutanene da basu iya munafurci ko boye abinda ya burgesu ba,cikin reception haka nurses ma'aikatan gurin suka dinga gaidashi suna kuma tambayar wacece?. Kai tsaye yake amsa musu matarsa ce,suka dinga kodasu suna sha'awar hadin,har zuwa sanda ya isa bakin wata qofa dake dauke da sunan mamallakiyar office din,har a lokacin kuma yana riqe da hannunta tsam kamar za'a qwaceta.

Knocking kawai yayi aka bashi izinin shiga,ya Murda handle din ya bawa sultanan dama ta fara shiga sannan yabi bayanta.

Babbar macace farar fata,wadda a qalla ta kusa shekara hamsin. Kamila ce sosai,kana kallonta kuma zakasan cewa musulma ce,don ta nannade kanta da scarf ba'a iya ganin gashinta.

Fuskarta ta wadata da murmushi tana yiwa maina sannu da shigowa,da alama akwai fahimtar juna da sabo sosai tsakaninsu. Dr Camille tadan miqe tana dubansa,cikin tataccen faransancinta ta kasa shuru idanunta tsakanin fuskar maina dana sultana tace

"Yar uwarka ka kawomin ne Dr?" Tayi maganar cikin fara'a. Juyawa yayi kadan yana murmushi shima ya kali sultana,sai kuma ya dawo da dubansa kan Dr Camille

"Yata qanwata kuma matata" idanu sultana tadan rufe kadan tana bitar adadin sunayen da ya bata dukka ita kadai. Dr tadan saki dariya tana gyara ma sultana kujera

"Da gaske Dr?,ashe kai din me iyali ne?,amma kuna tsananin kama Dr.....tunda naji kace diyarka kuma qanwarka na tabbatar auren zumunci ne,haka ne?" Murmushi ya kuma saki,dr Camille ce kaf asibitin suke hira irin haka,itama yana mata kallo ne kaman na ama,saboda tana da tsananin kamun kai da kirki na gaske,sa'annan ita din ba yarinya bace

"Haka ne Dr"

"Duk family dinku masu kyau ne Dr da alama, za'a samu kuma kyawawan 'ya'ya sosai madam" ta qarasa maganar still tana murmushi tana kuma kallon sultana. Murmushi tayi qoqarin kawowa saman fuskarta,hakanan taji matar ta kwanta mata,bata da hayaniya tana kuma da tsananin kula da alama. Yadda ya tsareta da ido yanason yaji amsar da zata bawa Dr Camille ya sanyata jin nauyi,saita kauda kanta kawai ba tare data amsa din ba.

Sai daya zauna a kujerarsa sannan ya sake mata hannu,ta damqe hannun nata tana jin dumin jikinsa har yanzu yana ratsata, hakanan tafin hannun nata ya wadata da qamshinsa.

Hira kadan duka taba sanann ya maida nutsuwarsa yana yiwa Dr Camille bayani

"Na kawota ne a dubamin ita da kyau......Dr inason tayi register dake,ke kadai na yarda ki dinga dubamin lafiyarta......ina tsananin sonta.....ina kuma tsananin qaunar abinda yake jikinta......don Allah Dr ki basu dukkan kulawa da ya kamata.....su din rayuwata ne" ya qarashe maganar yana dan rusunar da idanunsa.

Wani murmushi Dr Camille ta saki,tana jin maina din yana burgeta,da gaske bata taba tsammanin mutanen Africa sun iya soyayya can can har haka ba,idanunsa kadai sun gaya mata gaskiyar abinda yake cikin zuciyarsa yake gaya mata.

"Na tayaka murna Dr da samun qaruwa,in sha Allah zan bata dukka kulawar data dace........madam" ta furta tana duban sultana

"Ina tayaki murna da samun miji kamar Dr maina.......shi din nagartaccen mutum ne da muke matuqar alfahari da shi" dan murmushi ta yiwa dr Camille tace

"Na gode".

A nan ya zauna cikin office din,ya kasa ya tsare yana kallon yadda Dr Camille ke gudanar da gwaje gwajenta.

Sultana kamar ta fasa ihu saboda yadda suka tsareta da bincike,duba wannan duba wancan,binciken qwaqwafi har sai data gaji kafin a kammala.

Tana jin sanda Dr Camille ke masa bayani filla filla cikin yanayin bayanansu na likitoci yadda zai fahimta. Shi kuma ya tattara dukka nutsuwarsa akan Dr Camille yana sauraronta.

"Wata nawa ne cikin?" Yayi ma Dr tambayar da yafi matsuwa yaji amsarta

"Sati goma......" Ajiyar zuciya ya saki yana fadin

"Kenan akwai sauran jira kafin na hadu da little angel dina?" Murmushi ya qwacewa Dr Camille,kulawarsa akan sultana da cikin yayi yawaa

"Amma fa bamu gama dubata ba,don akwai abinda na gani cikin scanning da nayi mata,inason cikin ya qara nisa kamar ya shiga sati takwas haka sai mu sake dubawa" idanu yadan fitar waje

"Da matsala ne?" Murmushi ta sakeyi

"Ba matsala sai alkhairi" ajiyar zuciya ya fitar

"Shikenan,godiya nakeyi'

"Ba wannan a tsakaninmu" ta amsa masa tana miqa masa folder din sultanar da aka bude da bayanan komai da komai a ciki,sannan ta juya ga sultana

"Duk idan kikaji wani abu,ko kina da wata matsala karki ji nauyin kirana ki sanar min,zan iskeki a duk inda nake in sha Allah"

"Na gode Dr" ta amsa mata,har cikin ranta taji dadin yadda tayi matan,ta karramata qwarai ta kuma nuna mata damuwarta a kanta.

Sai daya dage dukka gilasan motar ya kunna ac a madaidaicin sanyi sannan ya juyo gaba daya yana zube mata idanunshin nan dake mata nauyi yanxu

"Me dame kike buqata?,me kike son ci?,me kike sha'awa?" Ya jera mata dukka tambayar. A yanxun babban burinsa shine ya bata kulawar da ba kowacce 'ya mace ta samu gatanta ba,yana jin wani qaqqarfan abu a kanta,yana jin wata soyayya ta daban game da ita da abinda yake cikinta.

Shuru ta danyi,duk kuwa da cewa akwai abubuwan da taji tana sha'awa da yawa.


"Ba komai" ta fada qasa qasa tana lanqwasa yatsun hannunta. Idanunsa ya janye daga kanta yana dan lumshesu

"You are a liar" ya furta qasa qasa yana qoqarin tayar da motar.

Guri guri ya dinga kaita,guraren cin abinci da saida kayan maqulashe da kwadayi iri daban daban. Duk iya yawonta a Paris duk kuma iya qwarewar goumar a paris basu taba yawo irin hakan nan ba. Can qasan ranta ta dinga ji zuciyarta tana sakewa,amma kuma tana dakewa a saman fuskarta. Duk sanda ya kalli fuskarta sai dariya tazo masa,saboda yasan fake reaction ne,real one din yana danqare saman zuciyarta. Tana sane ta dinga wasa da hankalinsa,duk inda sukaje sai tace wajen ko abincin waje baiyi mata ba,dariya ta dinga bashi,ya sani tana sane,ta kuma shiryawa hakanne,saidai abinda ita bata sani ba shi ya fita shiryawa,don haka ya dinga canza mata guri,har suka iso daya daga cikin manyan guraren cin abinci dake anguwar.

A qalla an zube mata kalolin abinci da na kwadayi sun kusa guda ashirin. Yanayi na ciki ya taso mata,sai idanunta suka rufe,shaf tama wani manta da maina dake wajen,ta dinga jaye jayen bowl da plates. Ci wannan ci wancan har sai data ji komai yana neman fita a kanta sannan ta dawo hayyacinta.

Tana ajjiye spoon ta tuna ashe yana zaune opposite dinta. Wannan ya sanyata daga kai da sauri don taga shin ita yake kallo?. Motsinta qwaya tak ya gaya masa abinda zatayi kafin takai ga kallon nasa,don haka tun kafin idanunta ya sauka a kanshi ya daga magazine da ya sanya suka bashi ya rufe idanunsa.

Boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana jin dadi,ashe ma ba ita yake kalla ba,don haka saita goge bakinta da tissue ta kuma ja rai ta hade tsam tana kallonshi qasa qasa.

Ta sama yake kallonta ba tare data lura ba,sai ya maida magazine din ya ajiye ganin ta gama ya miqe yana fadin

"Let's go".

Ta zaci gida zaya kaita amma sai taga ya wuce wasu guraren da ita. Classes yaje ya mata register na rainon ciki,da kuma matan dake zuwa har gida su duba yadda lafiyarki da tsaftarki da kuma yanayin yadda kike rainon cikinki yake gudana. Ita kanta abun sai ya fara bata mamaki,damuwar da kulawar da yake bawa cikin kamar yaso ya wuce iyaka. Daga can kuma still sai suka koma yawon park,guda biyu kawai sukaje tace masa ta gaji. Gurare ne da suka qayatar da ita,suka kuma bata kyakkyawar iska da yanayi me kyau,suka dinga tayar da wasu matattun abubuwa dake zuciyarta,basu bar wajen ba sai ana dab da shigar loton sallar magariba.

Bashi kadai da yake driving din ba.....hatta ita dake zaune a gefe tana jin yadda jikinta ke amsawa da gajiyar yawon da sukayi idanunta yaga abinda ke tsaye qofar gidansu.

Full light ya saka,abinda ya sake nuna musu ita tarwai kaman da rana.

Ayana ce zaune saman wata concrete chair dake opposite da gidan nasu. Tana sanye da wasu English wears da warakin hijabin da iyakarsa kafadunta.

Daga qasa kuma a gefanta kwando ne me kyau lullube da wani farin yanki,hannunta riqe da wayarta tana dannawa,amma kuma motar data yi mata full light ya santa daga kanta da sauri tana kare fuskarta da hannunta.

Wani abune daya tsaya mata a wuya a tsahon xaman jiran dawowarsun da takeyi ya sauka xuwa cikin cikinta sanda ta fahimci motarshi ke shigowa layin. Ta miqe a hankali tana goye hannuwanta a qirji tana jiran isowarsa,wani zazzafan kishi yana tafasa zuciyarta don ta tabbatar duk tsahon awannin da tayi tana jiransu yana tare da ita ne........tunaninta guda daya.....yadda zata karya wannan katangar me danqo ta rugurguzata ta kuma kafa tata gwamnatin.........


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 132



Ci gaba tayi da bibiyarsu da idanu har zuwa sanda ya isa cikin gargajiyar gidan da motar,ya kasheta yana cire seatbelts din jikinsa. Juyawa yayi yana qoqarin kallon fuskarta don yayi imani taga abinda ya gani shima,saidai taqi juyowa bare su hada idanu,ya miqa hannu yana qoqarin cire mata seatbelt din,sai ta rigashi,ta sanya hannu ta zareta,ta kuma bude murfin motar ta zura qafafunta tana fita daga motar adan gaggauce.

Daidai sanda ayana ke shigowa dauke da kwandon,akan idanunta sultanan ta fito,ta kuma tsaya gaban qofar mashigar gidan tana rungume da hannayenta ta kuma basu baya. Shu'umin murmushi murmushi ta saki tana kallon bayan sultana din,tanaso ko sau daya ko iya yau kawai ta cusa mata haushin da zata kasa cikakken bacci,kaman yadda takejin zuciyarta cikin qunci duk sanda ta tuna maina yana tare da wata,aliyyun da take matuqar so yana tare da wata mace.

"Yayaaa" ta furta tana dan daga muryarta a shagwabe kamar qaramar yarinya harda karya wuya. Bai barta ta qaraso ba ya rufe motar yana dauke kanshi daga kanta,idanunsa akan key din da ya sanya yana kulle motar sannan ya fito daga wajen.

Kallo daya yayi mata duk wani rawar kai da karsashinta ya zagwanye. A yau fuskarsa tana tuna mata ainihin fuskar aliyyun da tasha jin daddy dinta yana fada lokaci bayan lokaci. Fuskar da bai taba gwada mata ita ba saboda darajar ama da kuma uncle tahir da suke dashi a idanunsa,kuma baya ganin ta tsallake limit,amma zuwa yanzun ya karanci abun kamar gaba gaba yakeyi.

"Me kikeyi a nan din da daren nan?,waye ya baki adress?" Ya jefa mata tambayar yana zura hannayensa a aljihun wandonsa. Tambayar daya tsaya ma ayana din sai sultanar taji kaman ta muzanta,tana tsaye ne tana jiransa ya bude mata qofa,amma saboda bayason ranta ya baci kenan shine ya tsaya ya fara ji da ita?.

Dan siririn murmushi ta saki tana kallon kwandon hannunta

"Banda abun yaa maina.....jini wasa ne?, goumar ya kawoni,naxo kawo maka abincin dare ne wanda muka dafa ni da ama" tsaiwarsa ya gyara,ya fahimci abubuwa da yawa cikin idanunta

"Ama din ce tace ki kawo ko kuma ra'ayin kanki?"

"Ra'ayin mu nida ama" ta fada tana kuma sakin murmushi,don bataso a yadda ta juya bayan ta zaci ba maganar lumana yake mata ba

"Yayi,kawo ki wuce gida dare yana qara yi"

"Goumar yace zai dawo ya daukeni" ta amsa masa da sauri,don tana burin shiga cikin gidan taga meye da meye a ciki. Tabbas ita shaida ce maina ya hadu,tayi imanin komai daya shafeshi din zai kasance na musamman,ta yaya zata bari wannan damar ta kubce mata?. Bayason tsawaita magana da ita,ga sultana da yake da tabbacin ta gaji,don haka ya taka zuwa gaban gidan,wannan ya bata daman binsa tana karadin yabon gidan.

Gefe ta matsa masa wajen da zai sanya key din tana kauda kanta gefe. Yadan dubeta shima saiya kauda kanshi don yadda yaga fuskarta yasan ta qulu ne. Ya bude qofar yana tura mata ita yadda zata shiga,saita waiwayo dukanta tana duban bayanta.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login