Showing 273001 words to 276000 words out of 294767 words

Chapter 92 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ama ta daina yayinsu.

Yadda hankalinsa ke a kanta haka itama,ta gefan idanu take satar kallonshi tana tuna abinda ya faru dazun tana dan jin kunya kuma. Dama haka kishi yake da ciwo?,haka yake da radadi?,ash haka yake rufe maka idanu?. Batasan yaushe ta fara qaunar yaa maina ba har haka,amma maganar gaskiya bata jin zata iya rabashi sharing nasa da kowacce mace a duniya,tabbas a gaida matan dake da abokan zama,mazaje ne a ma'anar kalma.

A nan tasa balkissa ta sauke musu abincin dare. Tayi tayi su batoul su taso suci suka qiya,an samu abun kwadayi. Ita da maina din suka fara yin dinner din. Yana ci suna hira jifa jifa da ama din,amma dai still hankalin da tunanin yana ta wani waje.

Ganin goma ta gota ya sanyashi duba agogonsa. Ya saci kallon ama sannan ya saci kallon sultana. Wani tausayinta yaji yana saukar masa,ya tabbatar koda zatayi bacci ba irin baccin da takeso ba,yanason ya bata matsananciyar kulawa kamar 'yar tsanar roba.....yanzunne kuma dai dai wannan lokacin daya dace tunda ya mallaki dukka soyayyarta zuciyarta dama rayuwarta.

"Sultana ki tafi ki kwanta hakanan.....jikinki bashi da wani qwari naga alama tun dazun,kamar qarfin hali kawai kikeyi" ama ta fada cikin tausayawa da kulawa.

Murmushi kawai ta saki me kama da yaqe,ta yunqura ta miqe,sai ama din tace

"Akai miki yaran daki,saisu tayaki kwana"

"Baci gaba kenan?" Ta raya a ranta,don ba abinda take tunawa sai lokacin da maina yayi mata batan dabo a Paris,sanda take kwasarsu tayata kwana su debe mata kewar mahaifinsu da batasan tsumammiyar soyayyarshi ke walagigi da ita ba.

Tana shirin wucewa sai suka hada idanu,ya saci idanun ama ya narke mata,ya wani koma kalar tausayi sosai,tadan kauda kanta gudun kada suyi abun kunya gaba ama din.

Duk takunta daya zuwa daki sai yaji kamar ana gutsirar wani abu daga sashen zuciyarsa,duk takunta daya sai yaji kaman tana nesantar rayuwarsa ne,ya dinga qoqarin danne abinda yakeji din,amma sanda yaga sun gama shigewa dakin gaba daya sun yiwa idanunsa nisa sai ya gaza daurewa

"Ama......am......" Yadan tsaya yana sosa qeya bayan ya kira sunanta. Ido ta zuba masa da kyau*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 146


Tana kallonsa,ta riga ta fahimci inda ya dosa,amma tanason taji meye zaya ce

"Na'am ina jinka"

"Nace wai....sultanar a nan zata kwana ne?"

"Eh meye ya faru?" Ta sake jefa masa tambayar,kanshi yadan kawar gefe,yana matuqar kunyar ama,amma zuciyarsa na azalzalarsa,yayi imanin idan yayi kawaici daga shi har sultana din zasu cutu ne kawai matuqar cutuwa.

"Ba komai.....kawai ba kasafai take iya bacci ba......" Sai kuma ya kasa qarasawa. Kobai qarasa ba ta fahimta,daga yadda take faman narkewa cikin kujera tasan dawar garin,tasan akwai ciki me matuqar son jiki,ta tabbatar kuma abinda ya samu sultana din kenan.

"Wani ciwo ne da ita?" Kanshi ya shafa,yasan ama tana sane

"Babu ama.....lafiya take"

"To madalla......ni xan wuce ciki" ta fadi tana miqewa,don batason taci gaba da zama yaci galaba a kanta ko ya kashe mata zuciya ma.

"In zaka fita ka yiwa tanja magana a rage electronics dinnan kada a barsu su kwana a kunne" baice komai ba sai ya miqe kawai,kaman xai yiwa ama din kuka,ya tabbatar inda shi din mace ne da kuka zai fashe mata dashi ko zata fuskanceshi,laifin ita sultanan da bata nuna komai ba. Yana tsaye har ama tabar falon tana wucewa sassan aba,ya dauke kai yana ji har cikin jikinsa tabbas ana nuna masa 'yan ubanci ne kawai.

Zamanshi yayi a falon abinsa ya sauya tasha,tun tanja na leqowa za'a kashe wutar wajen har ta haqura,shima daga qarshe yace mata taje kawai zaiji dasu. Sai daya mula don kansa ya kashe komai,ya kuma saita komai ta yadda zayajin dadin shigowa a saquqe.

Parking lot na gidan ya wuce,ya zabi mota daya cikin motocinsa ya fita da ita waje yayi parking dinta.

A nutse ya jefa key dinsa da wayoyinsu aljihunsa sanda agogo ke nuna masa sha biyu daidai na dare. Ya tako a hankali yana barin sashen nasa bayan ya saka key ya rufe ko ina.

Kai tsaye ya ratsa falon da babu motsin komai a cikinsa,ya dinga tafiya cikin nutsuwa kuma hankalinsa kwance har ya isa qofar dakin nata. Murzawa yayi ya tura ya shige,idanunsa suka fara sauka akan tanja dake kwance saman rug din dakin ta lulluba da babban duvet. Daga saman gadon fuskokin batoul da benazeer ne cikin duvet.

Babu ita a gadon,amma qarar bude qofar toilet ya dauki hankalinsa yakai wajen. Itace sanye cikin wata tattausan rigar bacci off white data saukar mata har zuwa qaurinta amma basu qarasa rufe mata qafafunta ba. Kanta sanye da wata qaramar hula me kyau mahadin rigar wadda ta bawa sassalkan gashinta damar fitowa ta qasan wuyanta da gefan kunnuwanta. Sake zuba mata ido yayi kaman zai cinyeta danya,yayin da ita kuma ta narke masa hadi da shagwabe masa gaba daya tamkar benazeer ko batoul.

Bawai ado tayi ba,amna sosai ta sake tafiya da imaninshi,Idanunta sun sake wani haske me daukan hankali,da alama cikin zai matuqar qara mata kyau.

Hannuwansa dukka biyun ya bude mata,tamkar me jira ta tako da sassarfa ta fada qirjinsan nan da take matuqar kewa. Kyakkyawan masauki yayi mata,ya maida hannuwansa duka biyun ya lullubeta dasu,ta aza kanta sosai saman qirjin,sai ta sake masa wani irin shagwababben kuka

"Shshshsh.......ya isa,yanzu zamu wuce,bazan iya jure kewarki ba....."

"Tanja fa?"

"Koda zata tashi ko idanunta biyu a gaban idanunta zan wuce dake.....oya take your jilbab" ya fadi yana sakinta.

Tausayi taso bashi ganin yadda jikinta yake rawa wajen daukan hijabi,yayi imanin da lafiya lau take,sultanarshi me shegen dakiya da cinye abu bazatayi masa haka ba,duk da shi hakan ya masa,ya samu tabbacin yau zaya morewa amarcinsa yadda ya kamata.

"Wait.....wait" yace da ita yana zare hijabin daga hannunta,ya juyashi daidai yana sakin murmushi

"Babyn nan yana matuqar son daddynshi da yawa,kada fa yazo yafi su batoul son daddy" ta fahimci sarai me yake nufi,saita fada qirjinsa tana boye fuskarta

"Allah......Allah ka bari"

"Allah Allah dadi nakeji idan na tsokani baby sultana" ya maida mata amsa da irin muryarta da ta masa magana yanzun da ita.

Banda wayarta bai bari ta dauki komai ba,ya riqe hannunta tsam cikin nasa suka fara takawa suna ficewa daga dakin.

Fetal farfajiyar gidan,ba kowa banda security na gidan mutum biyu dake on duty ranar.

"A sauka lafiya yallabai" shine abinda ya hadashi dasu,ya amsa musu suna ficewa,fitar data sakashi sakin murmushi,don ta tuna masa da wani abu,har ya kasa shuru,ya waiwaya yana kallonta sanda ta zauna sosai saman seat dinta shima ya miqa hannu zai tayar da motar

"Lokaci makamancin haka na fice a firgice ina tunanin makomar rayuwata,da makomar rayuwar baby sultana......na fice da dimbin qiyayyata dana bari a zuciyar sulthana ta....yau sai gashi cikin wani tsohon dare zan gudu da wannan baby sultanar......amma a yanzun maman twins ce maman unborn sannan kuma wannan zuciyar a yanzu cike take da soyayyar mijinta..... uncle dinta kuma yayanta" murmushi me sanyi wanda ke cakude da kunya ya kufce mata,saita aza kanta saman cinyoyinta tana sakinsa a hankali

"Ashe haka soyayya take da dadi?" Ta jefawa kanta tambayar

"Ni ban taba qin yaa maina na ba...... Kawai dai nasan inajin haushinsa......ina kuma qyamar halayensa a zatona baida halin qwarai .....ashe zallar wauta da qurucciya ce ta cikamin kaina a lokacin".

Wani irin murmushi ya kubce masa,kalamanta sai yakejin kamar sun qara masa qaimi da karsashi a dukka jiki zuwa zuciyarsa. Kasa jurewa yayi,ya miqa hannunsa a hankali ya lalubo tattausan hannunta ya maqale cikin nasa,yana driving da hannu daya,daya hannun kuma yana murza tafukan hannayensu guri guda,kadan kadan da wata irin lallausar murya yana farke mata dukkan wani sirri dake zuciyarsa game da ita.

Ta kasa komai kaman yadda ta kasa cewa komai,sai idanu kawai da take lumshewa,kunnuwanta na sauraren kalamai mafiya dadi ga kunnuwan nata cikin muryar da har yau bataji wani sauti da yakai sound na muryarsa dadi da kuma ratsa zuciya ba. Ji takeyi kaman zata narke sabida yadda yake qara aza mata nauyin soyayyarshi,wanda kafin sukai gidan ya cire mata kowacce laka dake jikinta,ya kuma zare mata komai daga zuciyarta face zallar son kasancewa dashi.

Daga qofar gidan kadai zakasan anyi gini na qasaita,gini na masu ilimi da ya cakuda da hankali,gidan ya tsaru da wata irin fikira......ba babba bane tangameme,amma a wadace yake irim wadatar da kai tsaye za'a iya a kirashi da babban gida.

Tun daga falo suka zube warwas,daga shi har ita ba wanda yake da ikon sarrafa kansa ko yiwa kansa waigi,dukkaninsu burinsu shine junansu,a nan suka baje kolin duk wata tsohuwar soyayyar da aka fara ginata akan tubalin quruciya,soyayyar da akayi tsammanin ta uba da 'ya ce kota kawu da diyarshi,ashe tsumammiyar soyayya ce da zata juye musu zuwa wannan fuskar.

A yau yarinyar da yakewa kallon yarinya ta gigitashi fiye da yadda duk wani hasashe nashi yake bashi. Ta kaishi wajen da tabbas yayi imanin inda abune wanda ubangiji bai hukuntashi a matsayin sirri ba ba shakka da yayi matuqar jin kunyar da baisan da wanne idanu zaici gaba da kallon kowa ba,sai Allah ya sanya suna cikin wata sirrintacciyar duniya ce,wadda daga ALIYYU MAINA sai SULTANA HAMANI.

Koda komai ya daidaita sai ya rasa nau'in abinda zai zama sakayya ce a gareta,bakinsa ya gaza furta komai,sai qwalla data cika idanunsa har kuma damshinta ya taba gefa fuskar sultana. Sake lafewa tayi cikin jikinsa,me yasa aliyyun yake saurin yin kukan a kanta?,bai taba kuka akan kowacce diya mace ba,kuma ita din shaidace,amma yayi kuka a kanta karo na kusan hudu ko biyar a iya abinda zata iya riqewa kenan,kodai yana cikin nau'in mazan da tsananin soyayyar mace ke saka jarumtarsu guduwa?.

"Maina bashi da wata jarumta indai akan sultanar ne,zaki iya kiran maina ragon namiji indai akan sultana ne......kina mamaki idan kikaga hawaye na a kanki?" Ya jefa mata tambayar yana wasa da sumarta. Kasa amsa masa tayi tanason auna mizanin son da yake matan

"Soyayyarki cikin jinina take sultana tun ba'a haifeki ba......kin taba jin ka fara son abinda babu shi?......inajin daga kaina aka fara,tun ba'a haifeki ba na fara jin ina sonki sulthana......ya zuwa yanzu kuma mahaukacin so nake miki wanda bansan yanda zan fasalta miki ba......ki soni kawai ki kuma gwadamin a aikace wanna kadai shine qila zai gamsar dani" ya fadi yana sake riqeta ga jikinsa sosai. Kasa amsa masa tayi illa bugun zuciyoyinsu dake tafiya lokaci guda da ya dinga shiga kunnenta,sannu a hankali jikinsu dukka ya ida mutuwa, Allah yasa sun sauya masauki zuwa bedroom dinsa. Wani irin bedroom da ta dinga kallon tsarinsa da fasalinsa yana bata mamaki. Tana ji ya jawo duvet ya qarasa lullubesu gaba daya yana sauke ajiyar zuciya me nauyi tare da maida idanunsa ya rufe.


******Tun da asuba da tanja ta tashi sallar asuba taga bata ga sultana ba. Da fari ta tsammaci tana toilet dinta,ta zauna tayita jiranta shuru,ta dauka wani uzuri ne ya riqeta,don haka saita bar dakin ta shiga wani ta kama ruwa ta daura alwala ta dawo.

Har ta idar da salla ta kammala azkar dinta shuru ba ita ba motsinta,wannan yaja hankalinta ta duba bandakin wayam. Tunaninta sai ya karkata akan ta koma dakin ama acan ta kwana qila tunda ama tana sassan aba.

Bata damu ba ta tayar dasu batoul sukayi alwala sukayi sallah. Xuwa sanda gari yayi shaa tayi musu duk hidimar data saba,suka fice kitchen ta tarda su bilkissa suna hidimar hada breakfast. Haka sassan ama yake duk lokacin cin abinci. Girki akeyi sosai,saboda bata daukewa duk meson abincin sassanta ba zuwa ya diba yaci,wannan ya qara siya mata qauna da soyayya da kuma girmamawa ta yaran gidan,duk kuwa da cewa kowanne sassa na gidan wadace yake da abinci,kuma ba inda zaka shiga bakaci ka qoshi ba.

Ana kammala breakfast din ama ta shigo. Kaman kowacce safiya da kwalliyarta suke ganinta,ba zaka taba ganinta haka ba. Suka soma gaisawa cikin girmamawa ita kuma cikin mutuntawa.

"Yau kun kwana da mommy,Allah yasa kun barta ta samu bacci" ama ta fadi tana jan su batoul da wasa.

"Ai inajin sun matsa mata ne ma yasa ta gudu dakinki cikin dare" tanja ta fada tana dariya

"Dakina kuma?" Ama ta tambayi tanja cikin mamaki,don ta biya ta dakin ta shirya kafin ta iso nan,amma bataga alamar ma an shiga dakin ba

"Eh bata kwana dasu ba" mamaki yadan kama ama,saita juya tana duban zuwaira

"Dubamin wajen bibi sultana tana can?"

"To" zuwaira ta fadi tana sakin suyar chips da takeyi ta fita a kitchen din.

Ba dadewa ta dawo ta gaya mata tun jiya bibi bata ganta ba,tace ma ta turo mata ita idan ta tashi a bacci. Kai ta jinjina kawai tana sallamar zuwaira,tana juyawa suka hada ido da tanja. Dariya tanja keson saki amma ta cinye,saidai duk da haka ama ta ganota

"Kin gane abinda yaron nan yayi kenan ko?" Dole dariyar tanja ta kubce

"Kiyi haquri ama,yaran zamani?" Kai ama ta gyada

"Zaici qaniyarsa.....baisan shi akewa ba?,ni dashi ne" ta fadi tana ciro wayarta daga aljihun doguwar rigar jikinta.

_to ama dai da kinyi haquri cikin wanga sha'ani_

_na fara jin qamshin gama littafi,wata tace wai na yiwa Allah kada na yanke,alqur'an saidai kuyi haquri na rubutu jama'a 😂_*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 147


Kiran wayar ama ta shigo wayarsa daidai sanda yake bare mata kwalin madara ta biyu ya miqa mata. Da hannu biyu ya tallabe kumatunsa yana kallonta,kowanne motsi da zatayi a yanzun ba abinda yake tuna masa sai wannan little sultanar tashi daya raineta da hannunsa.

Yadda takecin abinci na daya daga cikin abinda yake bashi mamaki,don ya sani,ita din ba gwanar abinci bace,shine daya tilo dake tursasata cin abinci a yawancin lokuta. Amma yanzun zaka rantse bata taba cin abinci a rayuwarta ba sai yanzu.

"Ki ragemin don Allah mana" ya fadi yana langwabe kai sanda ta dauki ragowar apple din da yayi saura guda daya

"Wannan din?", Ta fada tana daga masa shi sama. Kai ya gyada yana dubanta

"Ka gyara zamanka ma idan na cinye ban qoshi ba dakai zan hada" gefe ya janye qafafunsa yana dariya

"Ai na sani,zaki iya aikatawa,wannan cin abincin naki kamar keda wasu kike ci?"

"Nida wasu ne mana" ta fadi tana dariya qasa qasa gami da dora yatsanta saman cikinta. Idanu ya fidda yana murmushi

"Kema kinason sake haifan twins?" Kai ta gyada tana murmushi.

"Ban taba so ko sha'awar ba duk da gidansu kakan ummana gadon hakan sukayi..... Ina ganin haifan 'yan biyu a wani abu me ban tsoro da wahala......basa ban sha'awa......kwatsam sai ga batoul da benazeer da sukazo a lokacin da ban shirya zuwan nasu ba......na gigice akan hakan ashe su din sanyin idaniya zasu zamemin....." Murmushi ya saki yana lumshe idanu. Tun baya tun asali can yana mutuwar son wannan muryar tata,ko sanda take magana din idanunsa nakan jajayen lips dinta dake motsawa da wani irin yanayi, yanayin da ya tuna masa da daren jiya. Daren jiyan kuma ya shiga cikin tarihin manyan darare masu daraja a wajensa da bazai taba iya mantawa dashi ba.

Hannunsa ya miqa yana riqo zara zaran yatsunta yana dubansu,sai kuma ya maida kallonshi kanta

"Kinsan irin kyautar da kika bani kuwa daren jiya?" Ya jefa mata tambayar muryarsa da wani irin laushi kamar ba aliyyu maina ba. Kunya ta sauko mata,don ita kanta a karan kanta batason tunawa,ita kanta tasan ta taka rawar gani ba kadan ba,saita kauda fuskarta gefe

"Sulthana"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login