Showing 93001 words to 96000 words out of 294767 words

Chapter 32 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

kawai ake cikin gidan babu kama hannaun yaro. Da fari ta soma halinnata na dararewa da kebe kanta akan komai,daga bisani su aminata suka mata bore kan basu yarsa ba

"Abinda yayiki shi ya yimu,kuma meye hujja ki dalilinki na tsame kanki daga cikinmu sultana?,bayan idan kin koma paris sai mun ganki fa" wannan dalilin ya sanya tayi qoqarin sakewa sosai a cikinsu. Duk wata hidima sai sun tsomata a ciki. A hankali saita fara warewa,wannan yanayin......wannnan yanayin......wannan lokacin da wancan zamanin dukka da ya dade da shudewa cikin rayuwa da mafarkanta sai ya dinga farfadowa. A hankali ta dinga samun nishadi cikin zuciyarta,wani nauyi dake qirjinta ya dinga raguwa kadan kadan. Son kadaicewa......jin kanta kamar ta banbanta dasu ya dinga raguwa sosai.

Mutum daya ke neman matsanta mata,babu daman ya gansu sun fito sai ya matso gaban motarsu,idan anci sa'a ita keda driving ranar kafin ya iso take maka baqin glasses wa idonta ta finciki motar su fice,najma tayita mitan ta bari mana ko wajenta zayazo amma bata bi kanta,idan kuwa najma cw driver dinsu na ranar to ya samu yadda yakeso. A fakaice yake gasa mata maganar

"Karki manta,tu es la femme de quelqu'un d'autre(ke matar wani ce)" Baisan iya adadin yadda kalmar ke motsa zuciyarta ba,sai ranar da abun ya qureta kawai taji hawaye ya tsinke mata. Cikin arashi kuwa a gaban idanun uncle bashar abbanshi,shi yayi masa tas yace su shige mota su tafi abinsu,Allah ya tsare. Daga ranar ta samu sauqinsa,saidai fa hausawa sunce me hali baya fasa halinsa,duk ko yaya ya samu dama sai ya sake fesa mata,duk hade ranta da dauke kanta bai dameshi ba.

Siyayya sosai ama tayi musu na biki a dan tsakanin,kayan gargajiya na hausa sosai,ready made na atamfa da laces,don su benazeer din basu da wani kayan gargajiya sosai saboda yanayin inda suka taso. Kafin wani lokaci ama ta kammala musu komai,don wasu abubuwan amma matar uncle bashar ta kammale musu dama.


**********Tun yammaci ta sanya driver ya dawo da ita gida ta baro su aminata suka wuce wajen booking musu lallen biki. Ba yadda batayi su cire sunanta ba amma najma tace

"Sai kiyita yi" najma ta fadi tana jan motar, driver modu ya jata ya dawo gida da ita.

Duka saurin da takeyi don ta amsarwa ama girkin aba. Tana sallar la'asar ta kammala komai,qarfe biyar aba ya aiko atta a fito musu da girkin wani kebataccen waje daga bayan gidan,da alama suna sa tattaunawa ne shi da uncle omar da oncle bashar.

Tun daga nesa ta fahimci zaman na musamman ne,akwai invitation na daurin aure da yawa a wajen da sauran takardu.

A nutse ta durqusa ta ajjiye musu komai akan tsari,sannu dukka suke mata. Iya 'yan kwanakin kawai kowanne mamakin sultanan yake,kamar ba sultanar data fita a gidan bace wata ce daban aka sauyota.

"Allah yayi albarka,ya shirya miki zuri'arki" aba ya fadi cikin qauna da kuma tausayi

"Ameen aba" ta amsa ranta yana mata fari sosai

"Bashar......ka rubuta cikin calendrier (schedule) na abinda zamu tattauna.....mu duba yadda zamu warewa marainiyar Allahn nan igiyar wannan yaron daga kanta don mu bata damar rayuwa cikin 'yanci kamar kowacce yarinya...".

Wani numfashi ta zuqa me zurfi da nauyi tana jin kowanne gaba ta jikinta na rawa, zuciyarta ta motsa sosai da wani irin matsanancin bugu,qafafunta na hardewa ta qara sauri tana barin wajen ba tare da ta jiyo amsar dasu oncle bashar suka bawa aba ba......*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 50


Da dan sassarfa ta qarasa sassan bibi don shi yafi qarancin mutane. Dakin bibin ta wuce don rabonta da dakinta har ta manta,tun wancan ranar sam bata iya shiga dakin ta zauna,saidai idan wani abu zata dauka kota ajiye,tana shiga kuma take fitowa.

Sai datakai can quryar gadon sannan ta kwanta,rigingine tayi tana qoqarin ganin fitar numfashinta ya dai daita. Tsahon wasu mintuna sannan ta motsa bakinta a Hankali idanunta na runtse

"Ya Allah.....ya rabbussamawati ka bawa wannan bawan naka ikon rabani da wannan alaqaqai din igiyar" tayi addu'a tana fita daga tsakiyar zuciyarta.

Har cikin ranta taji addu'ar ta karbu da gaske,sai taji tadan samu nutsuwa,ta juya barin hannun damanta tana fadada tunaninta na yadda zata tafi da rayuwarta cikin 'yanci,tana sake fadada mafarkinta na zama fitacciyar 'yar jarida a duniya. Da wannan tunanin a hankali a hankali bacci yazo yayi awon gaba da ita.

Washegari me qunshi ta musamman dakewa ama qunshi tazo yi mata. Su benazeer tace a fara yiwa. Da farko batoul taqi yarda wai tsoron lallen takeji,tunda ba'a taba yi musu ba tunda sukazo duniya. Bibi kaman ta ari baki,ta dinga fada

"Haihuwar faransa rainon faransa.....ai dole,ba abinda kuka sani daya shafi al'adar africa.....don lalacewa atamfa nan murna wai yarannan suke zasu daura zani,laifin hamdiyya ne.......banga ta barinku ku tabbata a turai ba,gwara ku dawo nan kusan rayuwa" Dariya surukai da sauran 'yan uwa dai daiku da suke wajen suka dinga yi. Benazeer babu tsoro ita ta fara miqa hannunta akayi mata,sai da batoul taga benazeer din ta cire,lallen yayi matuqar kyau a fara tas din fatarta, benazeer din nata murna tana shafawa,abun yana bata sha'awa ita karan kanta sannan batoul ta yarda ayi mata.

Matsawa batoul din tayi kusa da sultana dake shirya duka kayan da zasu sanya cikin bikin a wasu madaidaitan akwatuna guda biyu,ta zura mata hannun saitin fuskarta

"Auty bakiga hannuna ba?,kaman ba nawa ba auty,kema ayi miki,zaiyi miki kyau aunty" tayi nisa a tunanin da ita kanta batasan na meye ba,haka kawai tun jiya gabanta ke yawaita faduwa,ta laluba kafff batasan dalili ba,saidai zuciyarta tafi raja'a akan kodai tana tunani akan wanne hukunci su aba suka yanke game da makomar igiyar auren dake kanta?,tayi winning ko batayi ba?.

Fararen idanunta masu yalwataccen gashi ta daga ta kalli fuskar yarinyar,sannan ta maida ga hannun da taketa zura mata. Ita kanta hannun yarinyar ya burgeta,jan lallen ya kwanta saman jar fatarta kamar jan lalle saman hannun balarabiya

"Ma sha Allah,tabarakar rahman......kinyi kyau sosai" farinciki sosai ya kamata,ta buga tsalle saman katifa tana kiran yaran da suke gurin sa'anni kamarta tana gaya musu

"Kunji ko?,ko aunty ma tace nayi kyau".

Washegari wuni sur basu zauna ba suna wajen lalle,qin yarda tayi ayi mata daga farko don batason me yawa,tafiso sai an yiwa kowa me lallen ta gaji sannan ayi mata. Dan kadan din akayi mata,janne itama har bayan hannu sai na cikin tafin hannu,na qafa ma duka kadan akayi mata,ikon Allah sai ta zamana kamae zabarta me lallen tayi,gashi dai yafi na kowa qaranci amma kuma yafi na kowa yin kyau,ai kuwa suka yiwa me lalle caaa,itadai dariya ta dinga yi matar tana cewa

"Ba daga ni bane,daga me hannun ne......ina cewa kuna gani dai,fatarta tafi ta kowa kyau da haske" maganar matar dole ya sanya sultana murmusawa duk da jikinta da takeji wani iri babu dadi.

Ranar laraba aka fara biki sosai,komai nasu bisa tsari da kuma tarbiyya suka shiryashi,ba wani abu da ya wucewa tsari.

Duk wata shiga idan sultana din tayi sai ta fita daban,kallo kam ta shasu,ta tabbatar banda tana da yawan azkar tsaf baki zai kamata,komai nata me aji sanyi ds kuma nutsuwa. Wadanda suka jima basu ganta ba kuwa mamaki kowa yakeyi

"Wai wannan sultana ce da gaske?,wadannan diyoyinta ne?" Abinda kusan dukka suke tambaya kenan,wasu riqe da baki wasu kima fuskokinsu cike fal da mamaki. Itakam saidai tayi dariya ta wuce. Benazeer abun nema ya samu,ba zama wai an saci dan barawo,idan ta fice cikin jama'a sau tari sai ama tasa an nemota,bata nan bata can,kusan ita din akafi sani akan batoul,saboda kwata kwata ita din bame hayaniya da surutu bane. Duk da kamannin da suke dashi yana rikita mutane,amma kuma dabi'unsu ya sanya ake saurin banbancesu. Yawan qawayen da benazeer din tayi cikin dangi sai abun ya baka dariya ds mamaki,duk wani team na yara idan kaga sun hadu sai kaga itace shugaba. Sak SULTANA saidai wasi banbance banbance a tsakaninsu. Benazeer ta samu kulawar ama qwarai,data fuskanci yanayin dabi'u da halayenta sai take tarbiyyantar da ita daidai da halin nata,wannan ya sanya duk surutu da rawan kanta take da matuqar ladabi,tana da kirki tana da kyauta tana kuma da tausayi,bata iya rashin kunya ba sam, kusan duk wanda zata gaisar sai takai har qasa,saidai fa za'a cikaka da surutu da kuma labari. Randa aka soma bikin goumar baya nan,sai dare ya dawo washegari kuwa me daure musu qarqashi ya dawo?,ai har batoul itama saita bazama,basa zama sam,wani lokaci ma sai sunyi bacci da dare za'a shigowa ama dasu,sai kuma wata safiyar idan rai ya kaimu. Duk inda za'a suna gaban motar goumar din,kowa yasan nan ne mazauninsu ma bame zama wajen,haka aka dinga gudanar da event din daya bayan daya,komai ya qawatar ya kuma bada sha'awa.

Ranar juma'a itace ranar dinner. Qawatacciyar dinner da aka shiryata ga dukkan amaren da danginsu dana angwayen aminata da yasmine,ga dangin uwayensu mata,wannan ya sanya aka kama babban waje da zai dauki kowa da kowa a sake kuma akan tsari.

Tun asubar juma'a din ta tashi da wani dan qaramin zazzabi,har cikin qashinta take jinsa,hakanan kanta bangare daya yana sara mata lokaci lokaci. Idanunta ta lumshe tana mamakin abinda ya saukar mata da wannan zazzabin hade da bacin rai. Tasan dai lafiya lau ta kwanta bayan sun dawo daga kamun amare da akayi alhamis,sannan ba wani zirga zirga tayi ba,don ama ta bata daya daga cikin motocinta tace tayi hidimarta da ita,ko a canma tana zaune waje daya,saboda yadda idanu ke mata yawa suna binta da kallo duk inda ta motsa ne bata so,abinda kuma ya sake bata mata rai ta samu waje ta zauna,daya daga cikin abokan ango da tazo wucewa ta gefansu zata bude motarta ta daukowa wasu friends din su aminata sevenniours. Ya jima yana binta da kallo duk inda ta gifta,shine mutumin da ya sanyata ta dinga zabga tsaki har babu adadi,a yanzun kuma da zata wuce ta shiyyarsu sai yace da ita murya can qasa

"quelle douce odeur(qamshi me dadi)" har cikin ranta maganar da ya fada din taji ta soketa. Eh tabbas,ita kanta ta sani,tana amfani da wani irin mayen turare ne me masifar kama jiki da sanyin qamshi,qamshin da hatta su aminata sai da suka magantu akai,tana maitar son turaren wannan ya sanya ya gama kama jikinta,amma aiba huruminsa bane yayi magana akai ko?. Bata kulashi ba ko waiwayo batayi ba ta wuce abinta,saboda kulawa ma ai yabawa ne. Sanda ta sake dawowa bai haqura ba sai daya sake magana

"Banyi mamaki ba don baki tanka ba.....ko makaho kukayi gaba da gaba dashi zaisan ke ta musamman ce......tu es une femme chic(macace ke me aji)" juyawa tayi tana dubansa,kamar zata tanka saita tuna hala dama tankawar nata yake da buqata,don haka saita sake masa wani siririn tsaki ta wuce abinta,abun haushin sai ta jishi cikin murmushi yana cewa

"Merci bébé(na gode baby)" maganar data qular da ita kenan ta samu guri tayi zamanta.

K'ofar aka taba alamun knocking,daga jin knocking din tasan bazai wuce benazeer ko batoul ba,sassanyan muryar nan tata can qasa tace

"Entrez(shigo)" batoul ce sanye da wasu cotton sleeping dress. Tabi yarinyar da kallo,kullum da kalan kayan baccin da zata gani jikin yaran,itadai batasan adadin guda nawa suke dashi ba,ita kanta wasu abunuwan nasu batasan adadinsu ba,saboda ko yaushe ama cikin kashe musu kudi take,cikin musu siyaya take,bata kuma iya musu siyayyan abu me araha ba,komai sai ta zuba me daraja da tsada. Kullum sake girma sukeyi suna wani wayau,halittar da Allah ya musu kyautarta na sake bayyana,yadda taji ana zancan har kamar ma sunason juyewa kamanninta.

"tante......ki fito inji ama kiyi breakfast,taji kaman su Yasmin suna cewa zaku fita" idanu tadan fidda tana dubanta

"Yau kuma na koma tante,aunty din in English bai isa ba?" Dariya ta saki sosai irin me cike da quruciyar nan

"Tante yafi dadi aunty......duka su aminata haka ake kiransu,kema a nan sunanki tante,saimun koma nigeria ko Paris zaki koma autyn" kai kawai sultana din ta gyada,ta fuskanci yau da surutu itama BATOUL ta tashi,don tanajin tanja tanata fama dasu daga cikin kitchen

"Ganinan zuwa"

"d'accord" ta amsa mata da farshen faransanci tana ficewa a dakin da dan tsallenta. Janye idanunta sultana tayi daga qofar tana jin wani yanayi yana shigarta,haka kawai takejin tausayin yaran yana shiga zuciyarta,dukka tayi qoqarin danne wannan,ta jawo qafafunta ta sauka ta wuce bandaki.

Wanka ta sakeyi hade da brush don ta hada gumi saboda maganin saukar da zazzabin da tasha,kuma alhamdulillah sai taji ya sauka din,saidai kuma rashin qwarin jiki. Simple gown ta saka na wata cotton atamfa maras nauyi,don ita ta tsammaci ma material ne da farko da ama tasa aka dinka musu,ta lullube kanta da dankwali sannan ta dauki wayarta ta fito.

Fuskarta tayi fayau,ba komai saman fuskar sai dan alamun rashin jin dadin jiki. Akwai baqi a falon,ta bisu ta gaidasu har qasa cikin girmamawa. Wannan dabi'ar tabi jikinta durqusawa yayin gaida manya,tana daya daga cikin dabi'un da aka horesu dashi a hassan gwarzo. A nutse har ta qarasa dining,ta taras da houda salamatu dukka cousins dinta ne,suka gaisa ta samu kujera ta zauna tana duba abinda zata iya ci.

Tana ci suna hira a haka aminata ta fara shigowa

"Kun gama shiryawa?" Houda ta fara amsawa

"Mayafi na kawai zan dauko,Je pense salamatu est prêt(ins tunanin salamatu ma ta shirya)" ta fadi tana duban salma din,kai ta gyada alamun hakanne,aminata ta dubi sultana cikin kokwanto

"Kefa?" Dan motsawa kadan tayi sannan tace

"Ina ji fa sai dare zamu hadu gurin dinner din kawai"

"Baki isa ba" aminta ta fada tafa hannuwa cikin bala'i. Cikin sa'a yasmine ta shigo dai dai lokacin,suka hadu duka dinga mata. Ba wanda ta tankawa,don maganarsu ma so take ta daga mata ciwon kanta,ta barsu sukayi iya yinsu,amma yadda suka tarar mata tasan bata da mafita,salin alin ta koma daki ta dauko mayafinta kayan da zatayi amfani dasu da key din motar ta fito suka wuce. Mutun bibbiyu sukayi, yasmine da salma a motar salma din,sultana da aminata a motar sultana.

Katafaren beauty lounge ne da yayi suna cikin marad'i da kewayenta. Wajene da idan kinsan baki isa bama baki kai kanki wajen,service sukeyi na manyan mata tamkar a cikin gidanki. Tarba za'a miki da drinks lemo harda kalan abincin da kike buqata,itakam sultana dukka batabi takan wannan ba,sai ta wuce qurya salle de repos(resting room) nasu dake dauke da manyan sofas masu taushi tayi kwanciyarta. Tana jiyo duk wani karakainar su tana kuma hango motsinsu ta cikin babban glass da ya rabasu.

Idonta ta lumshe haka kawai yau takejin ta rasa gane kanta da kanta,hannunta ta zura cikin jaka cikin sa'a taci karo da tasbaharta,saita maqalata a yatsa ta soma hailala don mugun faduwar da gabanta keyi yana bata tsoro.

Awa biyu tsakani taji ta kasa nutsuwa,saita dauki wayarta ta soma kiran tanja. Har ta katse bata daga ba,da alama bata kusa,kasa jurewa tayi ta sake kiranta,bugu biyu ta dauka. Hayaniya ya fara cika kunnenta kafin muryar tanja

"Benazeer da batoul fa?" Ts tambayi tanja kai tsaye,tambayar data bata dan mamaki,shigen tambayar data taba ma ama a makka,amma saita share mamakin tace

"Suna lafiya.....suna tare da goumar"

"Yayi......shikenan" ta fadi tana katse wayar,ajeta tayi saman kanta tana furzar da numfashi,duk sanda akace mata suna tare da goumar nutsuwar zuciya da ruhi take samu,duk da irin yadda shi goumar din baya gajiya da cakar da ita da kuma tsokanarta,tasan wannan a jininsa yake,kuma akanta kawai cikin yaran gidan yake haka,duk da ita ta fara sanadin sanya masa sunan BAQIN BUZU da tayi.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 51


Kaman kowanne event sai sun tsokaneta bayan kowa ya gama shiryawa,yanzunma sun buwayeta da ya akayi komai lite tayi amma yafi na kowa kintsuwa da yin kyau. Ta gaji da wannan zolayar tasi,ciwon kai kawai sukeson qara mata,don haka ta fita daga wajen ta koma mota ta zauna tana jiran isowar angwayen da zasu dauki amarensu su wuce gurin dinner gaba daya. Har a lokacin jinta kawai takeyi sama sama,basu jima ba kaman sunsan a qage take suka iso,dukka motocin suka tashi a tare suka wuce.



*_MAINA_*


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login