Showing 276001 words to 279000 words out of 294767 words

Chapter 93 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ya kirayeta da wani irin sound da ya sanyata ta gaza jurewa ta miqe zumbur,amma sai ya sanya hannu da zafin nama ya fincikota jikinsa yana qyalqyala dariyar kunyar da yaga ta dabaibayeta. Bai mata matsugunni ako ina ba sai a saman cinyarsa,ya riqota sosai yana cusa kansa tsakanin wuyanta da kunnuwanta,kiran wayar ama ya katse masa hanzarinsa.

Ganin sunan ama ya sanyashi dole ya saketa,yayi gyaran murya yana gyara throat dinshi da kyau don kada ama din taji wani abu,sannan ya daga kiran yana yin sallama.

"Barka da safiya ama"

"Aikai zan yiwa barka maina.....sannu da yin gaban kanka.....daka daukemin yarinya ka gayamin?" A handsfree take,sai ya waiwaya yana kallon sultana data zame ta zauna a qasa tunda taji ya kira sunan ama

"Am sorry ama.......na shiga daki na sameta ta kasa bacci.......kuma ma.....na gaya miki bata iya bacci ama......idan na barta ita daya ba zata samu bacci ba......kuma yana da hatsari ga lafiyarta da lafiyar juna biyunta....ki tambayeta she's fine ama......i promise zan kula da ita......zan kula da ita da duka iyawata,bazanyi hurting nata ba....." Ya bawa ama amsar takai tsaye,tunda ya rasa ta wacce hanya zai gaya mata yadda zata fahimceshi.

"Ya isa" ama ta fadi da sauri tana katseshi gudun kada ya fadi wani abun da zaifi qarfin kunnuwanta.

"Kasan me Dr Noor ta fada?" Kai ya girgiza da sauri

"Tana tunanin yara uku ne a cikinta,so dole a kula da ita sosai,bata buqatar takura tana son hutu sosai.......inda zai yiwu ayi keeping nata daban a gef......"

"Allah ama bazan iya ba" ya fada da sauri yana katse hanzarin ama

"Bazan iya yin nesa da ita ba......amma nayi alqawari bazan takurata ba ama har zuwa sanda kika iyakance....." Nauyi ta danji kadan,saboda akwai abinda takeson nusashshe dashi. Wayar taji an zare daga kunnenta,koda ta waiwayo sai taga aba ne

"Aliyyu" muryar aba yaji ta maye gurbin ta ama

"Barka da asuba aba" ya fadi yana dan rusunar da kanshi gami da sosa tsakiyar kan nasa,can qasan ransa yana jin zuciyarsa fal nadamar zuwa nijer,inama yayi zamanshi da ita a can,wannan damar datazo masa zatafi kyau a Paris,nan din da alama za'a matsanta musu ne a hanashi samun duk wani abu da yakeso,a hanamishi ginin da yakeso ya sake yiwa zuciyarta da rayuwarta.

"Alhamdulillah....... Kayi zamanka da matarka.......ka kula da ita,babu me rabaku.......amma tana buqatar hutu sosai,ka bata hutu,karka matsanta mata kada ka takura mata saboda kare lafiyar abinda yake cikinta,ka daga mata qafa please ka fahimci abinda nake magana akai ai ko?" Bai taba jin kunyar aba irin yau ba, abinda ama keta son fada masa kenan ashe taketa gewaye gewaye?,yau din muryarsa har wani dan nauyi tayi saboda kunya

"Na fahimta aba,Allah ya qara girma" aba din bai amsa masa ba ya kashe wayar,sai ya juyo yana kallon ama da tayi tsaye a tsakiyar kitchen din bayan kowa ya fice ya barsu da aman.

"Yanzu da kanka kayi masa bayanin aba?" Ama ta fadi tana qaramin murmushi,can qasan ranta kuma tana jin farincikinta yana dawo mata. Bata da tashin hankali kullum kwanan duniya idan ta kalli aba ta kalli maina taga babu cikakkiyar fahimtar juna jituwa da shaquwa shi da babban dansa,babban dan nasa da zai zama kamar magaji a wajensa.

Murmushi aba ya saki,bai bata amsa ba sai daya matso kusa da ita,ya lalubi hannunta ya damqa mata wayar sannan yace

"A qyale aliyyu haka......ya cika d'a na halak.......yayi dukkan qoqari yayi kuma biyayya......ya dauki dukkan sharadi da qa'ida da doka dana sanya masa koda akan gaskiyarshi ne......for now aliyyu zai huta....... shima ya jishi magidanci kamar kowa...." Tsaiwa yayi ya maida numfashi sannan ya sake matsa hannun ama din

"A yanzu ne ya samu abinda yake da buqata,so nayi imanin bazaiji ba bazai gani ba,saidai ki masa dabara kaman yadda nayi masa,ki kumayi addu'ar Allah ya tsare abinda yake cikin nata.......she will be fine in sha Allah......amma aliyyunki dai saikinmasa uzuri......ba lallai ma su dawo gidan nan kwana kusa" ya qarasa fada yana sakin murmushi me sauti hadi da jan hancin ama.

Riqe hannuna ama tayi tana dariya dariya

"Wato like father like son ko?" Kai ya girgiza yana dariya

"No......wannan ba haka bane....." Qasa qasa yayi da murya kaman wani zaijishi

"Twins yake badawa wanann ga triples suna tafe.......abbanshi daya daya ya dinga bayarwa,da aka karbi uku ma sai akace an daina karba haka nan" kunya tadan kamata,ta masa hararar wasa tana cewa

"Basai ka kawo danya shakaf ta qaro maka wasu ba" dariya ya sake

"Inaaaaaa...... hamidou mijin mace daya ne in sha Allah....... Har yau bai manta wahalar da yasha kafin ya samu hamdiyya ba,am belongs to you forever" murmushin jin dadi ta saki,har jiya har yau har kuma gobe lafuzzan aba a kanta saika zaci yau din ya fara saninta.

Ido ya lumshe yana jin dadin maganar da suka gama da aba din. Yau din aba ya gama biyanshi dari bisa dari,ya bashi license ya sake sakar masa ragamar komai,ya bashi cikakken 'yanci. Ya saki murmushi sanda ya hangi sultana na juya kai cike da kunya. Tsam ya miqe ya isa gareta,ya sanya hannu ya sureta yana dariya

"Waike kunya ko?, zakiyi bayani ne.....donma bance masa ke kika dinga roqona Allah annabi nazo na daukeki mu gudu ba" kukan shagwaba ta fashe masa dashi tana dan dukan qirjinsa,sai kuma ta riqe wuyanshi da kyau takai masa cizo a lips dinsa. Qaramar qara ya saki shima yana sane ya fara murza lips din nasa yana fadin bazai yarda ba sai ya rama. Ta dinga qyalqyalewa da dariya tana boye kanta a jikinsa.

A fannin rayuwa raino da kuma nunawa juna zallar soyayya sultana din za'a iya cewa tsohuwar dalibarsa ce. Halayyarta da nashi kusan ba baqin juna bane. Raino da kulawarsa a gareta ba sabon abu bane,banda qaddara data gifta tayi kuma sanadin tarwatsewar komai tare da manta zallar sadaukarwa rayuwarsa da lokacinsa a kanta.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 148


Wata sabuwar rayuwa ya soma shimfidawa ruhinta. Wa ta rayuwa ya fara tsara musu,irin rayuwar da yakewa kanshi mafarki,irin rayuwar daya jima yana yiwa sultana sha'awa,irin rayuwar da a baya yakan zauna yana tsarawa bibi itace irin rayuwar da yakeso sultana tayi a gidan aurenta,irin rayuwar da itace mafarkinsa akan sultana.

Rayuwar ta dinga wanke da goge komai daya faru a rayuwarsu ta baya,rayuwar data dinga tuno da tsohuwar dangantakar nan dake tsakaninsu,dangantaka me matuqar danqo,wadda ta shimfidu cikin jini da jijiyarsu tun kafin zuwanta duniyar ma gaba daya. Irin kulawar da yake buri da fatan sakawa a tsakiyar tafin hannun 'yar nafessa. Duk wani sauran tausayi da jin qai da yakewa nafessa din ya juyewa sultana shi tasss.......duk wata riritawa da kulawa da yakewa sultana fata dukka ya juyeshi. Ba abinda yakeso ya tabata,bayason tayi motsin komai,bayason ta rasa komai koda na daqiqa daya ne.

Ta soma irin rainon cikin da yake cika mata baki akai,dukka wani kulawa da riritawa data samu daga wajen ama lokacin cikinsu benazeer saita zama lami.....ta kuma zama ba komai ba akan salon nashi kulawar.

Soyayyarsa wani irin abune dake ratsa jini da jijiyarta,ya dinga narka mata duk wata kafar jini da zuciyarta,ta dinga juya tsananin kulawa da tattalinsa a gareta. Tayi dukkan yunqurin ganin ta taka rawa itama don ta bashi kulawa amma ya hanata wannan,saita tattara dukka tunaninta da akalarta wajen bashi kyakkyawan kulawa a shimfidarsa. Kulawar tata saita zama abu mafi tasiri kaf cikin rayuwarsa,kulawar tata ta zama wani abu daya dinga hudashi yana gigita tunaninsa,ta kuma zama abu mafi soyuwa a gareshi,ta sake zama sila kuma sanadin sake liqe mata da kwadayin son kasancewa tare da ita ako yaushe,duk kuwa da warning din aba......amma aduk sanda ta kusanceshi da tarin soyayyar nan tasa me narka zuciya sai yaji ya manta da kowa da komai.

Hankalinsa ya fara dawowa jikinsa a wani dare bayan komai ya kammala,ta dafe mararta data fara mata ciwo,ya kula da hakan duk da basarwa data dinga yi amma sai da yabi ba'asi. Duk da ba wani tsanani yayin ba,qullewa ne amma hakan ya daga masa hankali,ya sanyata a jikinsa yana mata sannu kaman zaiyi kuka

"Idan wani abu ya sameki ko ya samu baby na bazan iya yafewa kaina ba" ya fada yana kallon qwayar idanunta. Paracetamol tasha cikin mintuna qalilan ta ware,ya dinga sakin ajiyar zuciya hankalinsa a kanta,da safe kuwa a asibiti suka dira.

An mata checkup sosai har ta dinga qorafi

"Am fine fa daddyn twins" ta fada a shagwabe sanda suka dawo cikin mota zasu wuce gida. Da lion eyes dinnan nashi masu kwarjini ya kafeta yana sauke ajiyar zuciya har sai data gaji da yadda yake kallonta. Takai hannu ta shafi fuskarshin nan da KO yaushe take cike da wani irin kwarjini

"Wadannan idanuwan.......suna kasheni......suna kasheni sosai" idanun ya lumshe mata yana murmushi

"Kinsan inda ace me yiwuwa ne,zan cire idanunkin nan masu kama da zaiba.......na sanyasu cikin aljihuna nayita kalla a duk sanda naji kewarki?" Murmushi ya subuce mata sosai,duk lokacin da maina zaiyi wata magana da ita,zaqin kalamansa sukan ratsata qwarai,har taji kaman ta zaro zuciyarta daga qirjinta gaba daya ta aza masa saman tafin hannunsa

"Idanuna basukai na wannan baby sultana din kyau ba.....ni da nake da lion eyes?,idanun lion suna da kyau?" Kunya ta kamata ta boye fuskarta cikin tafin hannunsa tana dariya

"Inason idanunka ya maina ko a baya.... Kwarjini sukeyimin kuma tsoro suke bani yaa maina......suna firgitani Ashe bansan ajiyayyar soyayya bace danqare qasan ruhina" bibbiyu ya riqe hannayenta yana sakin murmushi

"Ki daina haukatani haka sultana na roqeki.......banason na wuce gona da iri a kanki aba ya qwace license din daya bani" idanunta ta fiddo waje sai kuma ta shagwabe masa

"Ya maina......."

"Kece sultana......kece kike sake hauka maina.......bana iya sarrafa kaina a kanki sulthana.......am like crazy wollah" ya fadi yana sassauta muryarsa gami da sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa.

"ina sonka da dukka zuciyata" ta furta itama tana jin yadda nata bugun zuciyar yake motsawa

"Ina sonki da dukka rayuwata sulthana" ya furta yana maida idanunsa ya lumshesu. Waiwaya tayi a hankali tana kallonsa da kyau. Da gaske tako ina idan zai gwada mata yadda yake sonta......ko yaya zai ya fifita soyayyar da yake mata akan wadda take masa,da gaske ya fita sonta ko kuma ya fita iya bayyana soyyayyar ne.

"Kin qoshi da kallon nawa?,ko baki gamsu ba?,zan iya tsaiwa har adadin lokacin da kikeso kici gaba da kallon nawa" ya qarasa maganar yana ware mata manyan idanunsa. Kunya ta danji,sai ta dan kauda kanta tana boye murmushinta.

Murmushin shima ya saki sannan ya tayar da motar suka fara barin asibitin.

A hankali a hankali taga yana daukan hanyar gidansu,ta waiwayo ta kalleshi,sai shima ya kalleta yana kashe mata ido daya.

"Nayi missing ama......nayi missing BB"

"i missed them too....but" saita narke masa tana kallonsa

"Dauke idanun nan mommy twins kada na watsar damu a kwalta......menene buqatar?" Ya tambayeta kai tsaye. Murmushi ta sakeyi,wani mayen so yakewa idanunta ta sani tun tana qaramarta

"Kunya nakeji bloodline"

"Oh my god......da gaske kinaso na kasa driving dinnan soulsis......wait,mene ne abun kunya?" Idanu ta narke tana nuna cikinta da yatsanta.

Dariya ya kwashe da ita yana dan dukan steering

"Baby......ribar aure ne fa?" Sake marairaice masa tayi

"Amma fa bloodline......sanda zamu fita a gidan fa bamuyi musu sallama ba,sai yanzu bayan almost ten days muje?"

"Baby........gudu mukayi zuwa halinlinmu fa......ba saceki nayi ba don naje na miki fyade......" Dariya ya sake qyalqyalewa da ita,yayin da taci mur sosai

"Banason kalmar nan bloodline" ta qarashe fadi kaman zata saki kuka

"Duk yadda na tsaneta yanzun ina masifar sonta indai a kanki ne......saboda kinsan me?....." Bai jira amsarta ba ya dora

"Like play like play sai gashi ta zama silar mallakamin ke" ya bata amsa daidai sanda ya tsaya qofar tangamemen gate din MAYAK'I family house din.

Daya daga cikin security din da duke da duty a ranar ya taso,cikin girmamawa ya dage masa gate din,don plate number din family din MAYAK'I daban suke.

Tun kafin ya qarasa parking space na gidan ya sauke glass din motar yana gaisuwa da security din har ya isa,ya kashe motar ya waiwayo yana kallonta

"Kada kiji tsoro,am by your side" kai ta gyada sannan ya zagaya a nutse ya bude mata qofar,ya bata hannunsa saita noqe kafada

"What?" Ya tambayeta yana duban tsakiyar qwayar idanunta

"Zasu ganni ya maina.....Nidai Allah yasa kada naga su oncle bare aba" hannu ya sanya yana toshe bakinsa don kada taga dariyar da yakeyi mata. Ya tuna ranar data bayyana soyayyarsa gaban kowa,gaba kowanne ahali na gidan,irin bayyanawar dashi kansa baisan zata kai haka ba.

"Ko na daukeki na goyaki?,ko kuma na daukeki na boyeki a qirjina don kada su ganki har na kaiki ciki?,ki zabi daya" ya tamabayeta yana duba agogonsa. Idanu ta fiddo waje,bata ma iya bashi amsa ba ta fito a gaggauce. Bai matsa mata ta bashi hannunta ba,sai yaja baya yana bata hanya,ya maida motar ya rufe suka wuce cikin gidan.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 149



Falon ama suka fara shiga,tana sanya qafafunta taji tamkar ta nutse. Ashe baqine a gidan da yawa,sam ta manta da wani lissafin a satin biki suke,don koda yasmine ta dameta da tsokana kasa bata amsa tayi. Tunda maina ya dauketa sukabar gidan ta wani manta da lissafin kwanakin biki da suka rage,da daya da daya suka dinga barin falon suna basu guri har sai daya zamana daga su sai ama sai batoul da benazeer da suka maqale daddynsu sunata bashi labarin irin kayan da ama ta dinka musu. Dukka labarinsu atamfa tafi birgesu,sultana ta dinga murmushi qasa qasa. Da gaske basu san wani atamfa can can ba,amma kuma suna mutuwar son atamfa,don ko yanzun kayan jikinsu kaftan ne na atamfar. Ta dinga tuna sanda maina yake yaqi da ita akan ta koyi sanya atamfa,a lokacin tana jin duk duniya bata maqiyi sama dashi,tana jin ba wanda ya tsani rayuwarta kamar shi din,tayi kuka har batasan adadi ba akan hanata fita da yakeyi don bata saka atamfa ba,har sai data tsaneta saboda haka,sai gashi yanzun Allah ya azurtashi da yara wadanda su kuma babu abinda suke matuqar so din sai ita.

Duk da ya hanata tuna wasu abubuwan da ta masa marasa dadi,bayason ma ta dauko zancan,amma ita a karan kanta idan ta tuna wasu abubuwan takanji nauyi. Kamar yanzun data tuna yadda yasha gwagwarmaya wajen ganin ta suturce al'aurarta,ta kame kanta daga mu'amala da maza da zuwa matattarar rawa ko party. Saita daga idanunta tana satar kallonshi sanda suke magana da ama. Har yanzu yana nan da nutsuwar nan tashi,soyayayarta ce kadai ke sauyashi a duk sanda suka kebe sai ya koma kamar ba ya haidar ba. Masoyi ne na gaske,masoyi ne na gani kasheni,a wannan qarnin da muke ciki bata zaton akwai masoyi irin nata.

Ta zuba masa ido sosai tana kallonshi amma a sace,wata qaunarsa na sake narka mata zuciya,batasan yadda zata fahimtar dashi tarin soyayyar da take masa ba,koda ta bude baki ta bayyana masa din,nashi kalaman guda uku rak sai taji ya rushe nata gaba daya.

Cikin jikinsa yaji ana kallon nasa,yadan waiwaya kaman zai sosai wuyansa sai suka hada ido. Ya sha'afa a gaban ama yake,da idanu ya soma mata alamar kota gaji ya taso su tafi?,saita sake masa murmushi kawai tana.kauda kanta. Gyaran murya ama tayi kadan abinda ya dawo da hankalinsa kanta kenan

"Komai dai lafiya ko?" Ta jefa musu tambayar

"Alhamdulillah ama,ba wani damuwa"

"Ma sha Allah,aba yace na gaya maka dama,yanaso ku zauna dashi,nima kuma inaso muyi magana dakai,amma......zuwaira!"ama ta qwala kiran sunan zuwairan,ba jimawa ta shigo.

"Kuje keda su batoul su nuna miki jakar kayan mamansu ki dauko" amsa mata tayi benazeer ta miqe ta rakata.

Ba dadewa suka dawo da.jakar,ta sanya zuwaira ta zauna ta bude komai a ciki ta zazzage mata

"Ga ankonki nan da sauran kayan da akayi yaran gida zasu saka" kunya ta kamata,ama suruka kuma uwa ta gari ce,hatta da kalar mayafin da duk wani dan MAYAK'I zai sanya ta tanadar mata a shirye a jakar. Ita tama manta da wani batun anko,cikin matuqar girmamawa ta soma yi mata godiya,ta kuma miqe zata basu guri jin tace zasuyi magana da maina din

"Yi zamanki,keda aliyyu ban taba ganin banbanci a idanuna bama bare zuciyata" komawa tayi ta zauna tana yin qasa da kanta, batoul da benazeer na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login