Showing 228001 words to 231000 words out of 294767 words
Chapter 77 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
dr?" Ama data kasa buda takardun ta tambayeta
"Votre fille est enceinte(yarku tana da juna biyu)" wani duka maganar tayi saman kunnuwan ama da wani dirar mikiya naban mamaki
"quoi ?(what?)" Bakinta yayi subutar fadi ba tare data shirya tambayar ba. Kai dr ke gyada mata har yanzu fuskarta da murmushi,don ta yarda da tarbiyyar mutanen dattako da nutsuwarsu harma da kamewar yarinyar,tayi imanin cikin da ta gani tattare da yarinyar zaiyi wahala ya biyo ta baragurbin hanya
"Eh madam". Tattaro dukka wani busashen yawu dake bakinta ama tayi,ta kuma aro murmushi ta jefi dr dashi
"Na gode sosai da wannan albishir dr"
"Ba komai.....sai a kula da ita da kyau,duk sanda akaji wani abu kuma da ba'a yarda dashi ba hanya a bude take kada ayi jinkiri a sanarmin koda bana gida"
"In sha Allah,na gode" ama ta sake jaddada godiyarta,tana bin dr kawai da kallo. Duk yadda taso yi mata tattaki koda zuwa bakin qofar falonne ta kasa,tana jin qafafunta sun mata nauyi da wani irin dan banzan mamaki mara adadi.
Saida dr ta fita sannan taji tana da muradin kiran sultana,amma sai taji kamar muryarta ba zata kai ba. Sai a yanzu ta samu kanta da wani matsanancin fargaba da wani mummunan tunani daya rikito mata
"Ciki?,na waye?, yarinyar data shekara shida rabonta da d'a namiji?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un..... Sultana ba zata taba aikata alfasha ba,amma kuma cikin waye a jikinta?,shin akwai boyayyar alaqa tsakaninta da maina?" Dukka wadannan tunaninkan suka dinga bugun kan ama har ta rasa hanyar da zata kira sultana din ma
"Ya Allah.....Allah kasa boyayyar alaqar ce" ama ta samu kanta da furtawa a sarari bakinta yana rawa,tsoro da fargaba kamar zasu dulmiyar da ita a wajen.
Sai sannan idanunta ya fada kan tanja,ta tabbatar zaiyi wuya ta fahimci duk maganar da sukayi da dr tunda kaf da harshen faransanci ne,wanda nata harshen baiyi nunar da zata fahimci duka komai ba
"Tanja kiramin sultana" ta fada tana fasa kiran nata datayi niyya,wayarma saita sulale daga hannunta. Da dan mamaki saman fuskar tanja din ta miqe tana nufar dakin sultana.
Ta gama salla kenan da hijabinta a jiki tanja ta isar mata da saqon,gabanta ya sake faduwa kaman dazu,sai ta miqe kawai ba tare da tsaiko ba tabi bayan tanja.
Tunda ta sanya qafafunta ta fito daga dakin ama ta soma qureta da wani irin asababben kallo da bata taba ganin tana mata irinsa ba,abinda ya sake qara yawan faduwar gabanta,ya kuma saka dukka gwiwoyinta sanyi,a haka ta isa gaban ama,sai ta samu kanta da sulalewa ta zauna sosai a gabanta. Kasa cewa sultanar komai tayi saici gaba da kallonta da tayi,don ta rasa da wanne harshe ma zatayi tambayar,da hausa koda turancin ko kuma da faransanci ko da yarensu na abzinanci?.
"Sultana" ama ta kirata sosai
"N....na'am" ta amsa mata tana dan daburcewa,don sosai takejin shigar kallonta
"Cikin waye a jikinki?,kuma wata nawa?" Kamar da wadda ta yiwa magana da yarbanci haka taji,don kwata kwata sai taji sautin ama kamar me koyon magana a yau din. Gefe guda kuma kamar an sharara mata ruwan zafi haka taji,wannan ya sanya ta dago a firgice tanason tabbatarwa ita ama kewa wannan tambayar?, don tana jin kamar bata da alaqa da tambayar,meye hadinta juna biyu kuma?.
Idanun ne suka sauka kan takardar gwajin quru quru kafin takai ga kallon ama din,abinda yayi gaggawar fusgo tunaninta da hankalinta ya maido mata jikinta,maina ya fado mata a rai,dararensu dama sauran ranakunsu da BOYAYYAR ALAQARSU......
*_huguma ta gantale ko?,😂, afuwan,Allah kadai yasan nake squeezing nake muku rubutun nan,Allah ya saka muku da aljanna mutanen kirki da haqurinku gareni,in sha Allah muma mun kusa yin sauka,na gode_**_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 122
Kamar an kaba labbanta na sama da qasa an datse haka taji,gaba daya kowanne harafi da zatayi bayani dashi ji tayi yayi qaura daga bakinta. Wani mugun nauyin ama da bata taba jin makamancinsa ba ya saukar mata,taji koda wasa koda sau daya ba zata iya hada idanu da ama din ba,sai tayi qasa da qwayoyin idanunta da basa Gani da kyau saboda ruwan hawayen da ya cikasu.
Jinta takeyi tamkar ba zaune take cikin falon ba,kamar gangar jikinta ce kadai a zaune a wajen,amma ruhinta baya tare da gangar jiki nata gaba daya. Har yanzu idanun ama suna kan sultana,kaman yadda zuciyarta da qirjinta basu bar bugawa ba. Bata zargin sultana,amma kuma tana fatan taji wani abu daga bakin sultana da zai sake bata nutsuwar zuciya.
Jiki a sanyaye ama ta waiwaya bayanta jin takun mutum. Aba ne sanye da jallabiyya hannunsa dauke da key din motarsa,da alama yayi mantuwa ne a ciki zai fita ya dauko.
Yadda ama ta bishi da idanu haka shima ya bisu da kallo,fuskarsa na bayyanar da zallar mamaki a cikinta
"Ya dai?,me ya sameta hamdiyya?" Yayi tambayar yana duban fuskar ama da alamun tuhuma sosai a ciki. Kallon tuhumar da yake mata ya sanya ta kasa cewa komai,sai kawai ta zare takardun gwajin dake zube saman cinyarta ta miqa masa,ta hada hannayenta kawai ta rungume ba tare da tace komai ba.
Yana kaiwa qarshe ya zare glass din idanunsa,sannan kuma ya samu kujerar da tafi kusa dashi saboda wani iri da yaji jikinsa yayi masa. Sai daya zauna sosai sannan ya iya maida idanunsa akan fuskar sultanan
"Yi shuru,daina kuka hakanan......ki nutsu" muryar aba din sai ya zame mata kamar fami ga zuciyarta da kuma raunin dake ruhinta. Wai da gaske cikin ya maina ne a jikinta a karo na biyu?. Totally tayi disappointing dukkan wani qoqari na aba kenan?,da gaske ta bulawa aba qasa a idanu?,to wai da wanne bakin zatayi bayani?,da meye zata kare kanta?.
A qalla mintuna biyar aka sake sharewa cikin falon ba wanda ya iya cewa uffan,shidai aba ya bata space ne akan ta nutsu aji ta bakinta,gefe daya kuma zuciyarsa nata nanata masa sunan
"Maina ne....maina ne" to amma Ina maina din?,a ina ya ganta?,idan bai manta ba tun a Nigeria da suka rabu bai sake ganin alama ko samun information din yana qasar bama gaba daya bare ya sanya a ransa shine ya lallabo ya sake aikata wannan aika aikar a karo na biyu.
Ganin kamar ta daidaita kanta ya sanyashi gyara zamansa yana duban ama. Hada idanu sukayi,sai ama din tadan dauke kanta gefa,don tanajin kamar case din yana son ya fita daga hannunta,don gaba daya jikinta ya gama bata inda komai ya dosa,to amma kuma tanaso sultana tayi bayanin da dukansu zasu fita daga duhu,cikin saukar da murya da tausasa harshe ta sake maimaita
"Sultana.....ya akayi hakan ya faru?,juna biyun maina ne ko?" Ama ta bata tambayar me hade da amsa.
"Nawa ne ama......salamu alaikum warahmatullah" muryarsa ta bayyana tar a falon da bayyanannen amo daya wadaci dukkan falon.
Da aba da ama dukkansu suka waiwaya zuwa bakin qofar,yana shigowa ne riqe da hannun batoul da benazeer hagu da damansa,bayansa kuma goumar ne janye da luggage.
Sautinsa da amsarsa kusan lokaci guda suka daki zuciyarta dama kunnenta,ta daga jiqaqqun idanunta itama tayi duba zuwa qofar falon.
Aliyyu haidar MAYAK'I,jinin abzinawan nijer,mutumin da ta kwashe sati uku cif! Bata sakashi cikin qwayar idanunta ba,mutumin da duk yabi ya gallabi rayuwarta,yayi dashe a kowanne lungu da saqo na rayuwarta,ya maida kansa jinin dake gudana cikin jiki da jiyoyinta ta qarfi da yaji,ya dasa wani irin alaqa me matuqar qarfi tsakaninta dashi,irin alaqar da duk yadda taso ta kankareta kota gogeta HAR ABADA! Ba zata taba goguwa ba,ya maida dukkan rayuwarta tashi,fitar numfashinta da dukka motsinta.
Ama ce ta fara kauda kai tana jin kamar dariya ko murmushi zai kubce mata don nata mamakin gajere ne qwarai. Ita ta haifi abinta,tasan duk abinda zai aikata dama wanda bazai aikata ba,tayi shuru ne kawai ta sanyawa kowa idanu,amma jikinta ya jima yana bata,saidai kawai hausawa sunce dan yau ka haifeshi ne ba tare da ka haifi halinsa ba......sannan wayo da dabara ta yarda dukka ya nuna mata irin nasu na 'ya'yan zamani,amma ta jima tana suspecting haka,ta dade hasashenta yana bata,abubuwa da dama sun jima suna bata alamomi da sai yau haskensu ya fito tarwai.
Idanu aba ya bishi dashi kamar yaga wata sabuwar halitta,sai kuma ya janye kallon nasa daga kan maina din yana dawo dashi cikin falon kan sultana,ya zuba mata idanu kawai kamar me tunanin abinda zai gaya mata.
Tana jin idanun aba ainun a kanta,duk wata kunyar duniya da nauyi sun tarar mata. Tana tsammanin idan yazo zata samu sassauci da rangwamen kunyar data yi mata rubdugu,amma shigowar nasa bai rage mata komai ba saima nauyin daya qara mata da irin amsar da ya basu ta hanyar kai tsaye babu kwaskwarima.
Kwata kwata aba ya rasa me zaice?,ya rasa me zaya fada?,gaba daya kalmomin bakinsa sun dauke tsaf,ya rasa hukunci zaiyi ko meye?,idan hukunci yace zaiyi akan waye zaiyi?,kuma akan wanne dalili?,wanne kuma laifi aka aikata da za'a yi hukunci a kansa?.
Abu daya da yazo masa a rai shine,babu uwa kamar bibi,me hangen abinda zai wakana shekaru goma ma gaba.
Tun daga bakin qofa ya tsugunna yana zare takalman qafarsa,sai yara suka duqa suna tayashi cire guda dayan,ya daga kai ya kallesu ya sakar musu murmushi,kowacce ta dauki guda daya suka soma takawa zuwa gaban aba.
Zubewa yayi a gaban aba din saman dukka gwiwoyinsa,ya zube kansa a qasa ya kuma hade hannayensa waje daya
"Indai faruwar hakan laifi ne aba.....gani a gabanka ka yanke dukka hukuncin daya dace dani......saidai don Allah ina roqonka,kowanne irin hukunci ne ya zama taqaitacce aba.....kada yayi yawan da zai sake ruguza kowanne irin gini da nake yunqurin ganin na aza..." Qafarsa yadan janye,gaba daya kunya ta masa wani irin dabaibayi,ya sake dan ja baya kadan sannan ya miqe yana dubansu benazeer
"Muje ciki ku tayani hira,tun dazu nake dakon dawowarku,na ajjiye muku abun dadi" Da murnarsu suka ajjiye takalmin suna bin bayansa,sai daya sanya yaran gaba suka wuce sannan aba din ya tsaya,ba tare da ya waiwayo ba ya furta cikin muryar bada umarni
"Ka dauki matarka ku tafi duk inda zakuje mara kunyar banza" daga haka ya taka zuwa gaba yana bin bayan yaran.
Dauke idanunta ama tayi daga kan aba din tana sake danne dariyar da a yanzun ta tabbatar idan batayi da gaske ba saita kufce mata. Sai kuma idanunta ya fada kan maina dake duqe a inda aba ya barshi.
Kunya ce ta kamata itama da nauyi,ga idanunshin nan daya tsareta dasu,saita sake tsuke fuska da kyau itama
"Meye kake kallona?,bakaji abinda yace dakai ba?"
"Naji ama" ya fada a mugun marairaice kamar marayan daya rasa danginsa gaba daya. Saidai kuma can qasan zuciyarsa wani irin mahaukacin farinciki ke ratsashi
"D great victory ✌️! Da sauri haka?,wannan d'a ko 'ya tabbas ba qaramin qaunarsa suke ba......yana da hope na samun cikin,amma kuma babu tabbaci sam sam sai addu'a". Kasa ce masa komai tayi sai kawai ta kwashe wayarta tabi bayan mijinta.
*_Allah sarki sultanarmu ta mutunci_*🥹😥😥*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 123
Tuni tanja tabar falon tun shigowar aba,don ita wannan gwaji ya biyata,ya kuma gama yi mata komai. Don haka a yanzu sai falon ya zamana ba kowa,daga shi sai ita,sai kuma ayana dake maqale bayan labulen dakin. Tun fara drama din ta farka daga baccin data kwanta tayi bayan ta dawo daga makaranta. Idanunta tamkar su fado haka takeji,kaman yadda zuciyarta ke wani irin bugu cike da mahaukacin kishi,kebewarsun yanzun ya sanyata sake lafewa da kyau tanason kunnuwanta su ida jin abinda zai sake gudana tsakaninsu.
Tsaye kawai tayi yana nade hannayensa a qirji yana qare mata kallo da zagayayyun lion eyes dinshi da a yau suke lumshewa da kansu suna budewa sau babu adadi,ya zuba mata dukka idanuwan yana kallonta,wani irin narkakken kallo dake cike da shauqin soyayya da tsumammiyar qauna irin wadda ta jima da narka zuciya gami da yi mata illa.
Yanajin sautin kukanta har cikin zuciyarsa da ruhinsa,saidai kuma bayason abinda zai katse kallonta da yakeyi. Yayi kewarta......yayi kewarta kamar hauka........yayi mutuwar kewarta har baisan iya adadi ba......yayi kewarta kamar ya karya tsari da lokutan daya diba kafin ta sake ganinsa,shi da ita baisan waye yafi wani gasuwa ba.
Kunnuwansa ke sake dawo masa da furucin aba
"Ka dauki matarka ku tafi duk inda zakuje....." Sai wani tattausan murmushi ya kubuce ma kumatunsa. Zai iya cewa kawo zuwansa duniya zuwa yau bai taba jin wani umarni me gardin wannan ba.......qwaqwalwarsa ta lula wani irin tunani me zurfi,yana laluben wai a duniya a wanne shiyya zai ajjiyeta?,a wanne muhallin ne zaciyoyinsu zasu samu dukkan hutu da salama?,a wanne tsibiri tudu ko tsauni ne zaiyi shimfidar rayuwarsa da sultanarsa?, diyarshi?,rainonshi......matarshi?,uwar 'ya'yanshi?. Dukka wadannan tunanikan yana daga tsaye yake tsarasu cikin qwaqwalwarsa,kafin ya sauke hannuwan nasa yana takawa zuwa gareta. Yanaso ya dakatar da wannan kukan,sai ya dinga ji kaman abinda ke kwance qasan mararta ma tayata kukan yakeyi,ya gaji.......yanason tsaida wannan hawayen da sukayi shekara da shekaru suna zuba,ya kamata su tsaya hakanan.
Gabanta ya qarasa cikin nutsatstsen takunsa dinnan, baiyi qasa a gwiwa ba ya zauna sosai sannan ya tanqwashe qafarsa yana fuskantar ta har gwiwarsa tana taba tashi.
Taji isowarsa,ta kuma ji hucin dumin jikinsa,sai lallausan qamshin nan nasa da a yau takejin ya zama sabo cikin hancinta,har sai da qamshin ya tilasta mata fidda BOYAYYAR ajiyar zuciya,tana jin kaman ta shaqi wani abu me sanyi da ya dinga sauka har saman zuciyarta yana wanke mata zaciyarta.
"Sulthana" ya kirayeta a tausashe yana qoqarin leqa fuskarta ta qasan hijabinta.
Ta fahimci me yakeso,fuskarta yakeson gani,sai ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta da kyau saboda ta hanashi wannan damar. Wani qaramin murmushi ne ya subuce masa daga siraran labbansa,hakan da tayi sai ya tuna masa da little sultanarshi ta shekarun baya,ya sanya tafukan hannunsa cikin na juna yana mutstsukawa a hankali cikin wani salon nishadi,idanunshi kuma a kanta
"Am so sorry......ya maina bai kyauta ba.....don me zaiyita zura qwallo a raga ba tare da permission din goal ba?" Hakan da ya fada sai ya zama kamar tiri a gareta,ta kuwa sake sakin kuka mai qarfi tana jin takaicin sa. Ya sanyata abun kunya,irin abun kunyar da bazata taba mantawa dashi ba,ya goga mata kashin kaji,shi kuma nan ba ruwanshi gashi nan,da wanne baki zata kare kanta ne wai?,mutanen da suketa fadi tashi a kanta suke qoqarin ganin sun qwato mata 'yancinta?.
"Ki daina kuka please baby sultana(ya kirata da tsohon sunan da yake kiranta tun lokacin da batafi girmansu benazeer ba
".....nima duk kunya ta kamani,ashe ina tsallakesu ina tafiya dakin 'yarsu ina turmusheta" ya qarasa fadi yana kashe ido daya dariya nason taso masa.
Kalmarshi ta qarshe ta mata girma ta kuma sake tunzurata,ta rasa ma meye zatayi masa ta huce,saita fara shureshi da qafa. Kamo qafafun nata yayi ya aza saman cinyarsa yana cewa
"Indai wannan zai sanyaki ki huce sultana yita shureni har sai zuciyarki tayi sanyi......kiyi iya son ranki......eheenn" ya fadi yana sakin jikinsa da kyau. Ba haka takeso ba,tanason masa abinda zaiji zafi ne,amma it seems ma bai damu ba ko kadan?,muddin taci gaba da zama a wajen haukatata zaiyi,don haka ta miqe tsam taba kubce masa tayi hanyar daki.
"Ina zaki?,bayan aba ya bani damar tafiya da matata?" Ya jefa mata tambayar. Ji tayi ba zata iya jurewa ba wanann karon don haka ta waiwayo tana kallonshi da fararen idanun da suka jiqe sharkaf da hawaye
"Ba inda zan