Showing 201001 words to 204000 words out of 294767 words
Chapter 68 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
bataga ma'anarsu ba illa kawai bata mata lokaci da sukeyi,so take ta wuce daki gaba daya kifin da taci ma kaman yazo mata wuya ya zauns ne,bugu da qari wani abu daban kuma yaja hana numfashinta fita yadda ya kamata
"Me na gaggawar tamabaya?,gaki a cikinta?,nan da sati daya ma qilan ke xaki bawa wasu labari" ta qarashe da wani murmushin. Idanu ta kada tana duban maina
"Allah yasa haka......amma ya maina saika kawo taimako......tunda dai bansan ko ina ba ka sani.......sultana ki sanya baki ki tayani roqarshi kada yace a'ah" ta qarashe fadi a shagwabe.
Har tsakiyar ranta taji abun,amma kuma har yanzun tana yaudarar kanta da ba wata alaqa tsakaninta da maina din
"Sultana bare ce fa......kunfi kusa gaki gashi,ina da abinyi a ciki,lokaci kinsan yanzun sauri yakeyi,ko kai ka yankeshi ko kuma shi ya yankeka,goodnight, enjoy ur new home" ta fadi tana juyawa tayi ciki abinta.
Da kallo ya bita ta qasan idanu har ta wuce ciki,qaramin boyayyen murmushin gefen baki ya saki,dole yau yayi rarrashi koda indirect ne,ya hangi abubuwa masu kaifi cikin idanunta da batasan tana fiddasu ba,uwa uba kuma fushi dake lasar zuciyarta. Ayana ba damuwarsa bace,shi yasan maganinta,hakama laila,amma zuwansu sai yake neman zame masa alkhairi,kaman sun pushing nata ne wajen matso abinda batasan yana ajjiye cikun zuciyarta ba,abinda taketa qoqarin yima kanta qaryar babu shi sam tattare da ita.
Ta kusa minti biyar tanason controlling kanta da zuciyarta,ta zuqi numfashi ta fesar har batasan adadi ba amma abinda takeji yaqi ya sauka,gaba daya abincin da taci a wuyanta take jinsa,daga qarshe ta gasgata tabbas idan ba amayar dashi tayi ba ba zata samu sassauci ba,don haka ta wuce toilet kai tsaye,ta sanya brush a bakinta,zunguri daya kuma ta soma kelayashi kaman zata fidda 'yan hanjinta gaba daya a waje.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 107
Ta dade dafe da sink tana maida numfashi kafin fa samu numfashin nata ya daidaita,ta daga idanu tana kallon fuskarta da tayi jazur a mudubi. Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata,tasa hannu ta share,ta ware famfon ta tara hannuwanta tana wanke fuskarta gami da daura alwala.
Gefan gadon ta zauna tana lumshe idanunta,tasa qaramin towel ta share fuskarta tana sauke ajiyar zuciya kaman jaririn da ya kwana yana kuka yake kuma buqatar lallashi.
Saman gadon ta koma ta kwanta rigingine,ta rungume pillow tsam a qirjinta,idanunta a rufe amma batasan me take tunawa ba,tun tana a matsayin fakare har bacci yayi awon gaba da ita cike da wata irin kasala.
Ficewarta daga falon sai yaji gaba daya zaman falon ya gundureshi,ya duba agogo a hankali sannan ya maida hankalinsa yana duban batoul da benazeer
"Daddy zai gudu.....kuxo muyi sallama" ya fada yana miqa musu hannu.
"Naga dare kaman baiyi ba ya haidar......tun yanzun?" Ayana ta fada tana kallon agogon hannunta itama
"Ina da busy gobe in sha Allah" ya bata amsa yana miqewa tsaye,ya saka wayarsa a aljihun wandonsa hannunsa guda daya cikin hannun batoul da benazeer.
Durqusawa yayi yayi kissing hannayensu,ya dago yana duban ama
"Ama zan wuce...." Ya fadi yana duban idanunta
"Allah ya bada sa'a ya kiyaye,Allah ya bamu alkhairi" ama din ta fada,daga tsakiyar idanunsa ta karanci addu'a yakeso,kawai yana mata kawaicin magana a kai ne.
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya fadi yana juyawa
"Bari na rakaka......ya haidar baka gayyaceni naga gidan ba" ta furta a shagwabe tana karya wuya
"No,na yafe dare yayi...... goodnight" ya fadi yana nufar waje.
Jikinta a mace ta koma ta zauna tana kallon hanyar da ya wuce din.
"Ya kamata ki kwanta ki huta ayana......goben sai kiji dadin shiga school da wuri ko?" Ama ta fadi tana tarkata kan su benazeer da suka zube sunason fara bacci a gurin.
^^^^^Cikin farare qal din pyjamas yake takowa zuwa cikin dakin,hannayensa dukka biyun zube a aljihun wandonsa. Jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarensa.
A nutse ya maida qofar ya rufe yana jin wani shauqi yana ratsashi,yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Duk da dim light dakin yake dashi amma hakan bai hanashi hangota ba. Tana kwance miqe saman sofa da matsakaicin tsahon nan nata,ta rungume pillow tsam a qirjinta. Idanunshi fes a kanta har ya isa dab da ita,saitin kanta ya tsugunna yana kallon fuskarta,kallo daya yayi mata ya fahimci tunda ta shigo dakin a dazu bacci yayi awon gaba da ita. Gashinta dukka ya barbaxu saman pillow din kujerar da ta dora kanta. Dan qaramin bakin nan nata me labba masu sulbi ta turoshi gaba kadan,kana kallonta kasan cikin fushi tayi baccin.
Murmushi ya saki yana tuna quruciyarta,wannan kwanciyar irinta takeyi masa shi ko bibi idan tana fushi,ba kuma me shawo kanta sai shi ko bibi din ko madararta,madarar da baisan har yanzu me ya rabata da ita ba,tasha gaya masa
"Uncle......ko nayi aure ai zaka siyamin motar madara na tafi da ita ko?,kuma kaima tare xamu tafi ba zan tafi ni kadai ba kaman yadda aka yiwa su aunty chamsiyya" tayi tambayar ne a sannan cike da quruciya,tayi tambayar ne a lokacin ba tare da sanin me ma aure yake nufi ba,ashe shine mijin.......shine abokin rayuwarm.....Mallakinsa ce". Wannan tunanin da yayi ya haifar da raurawar zuciyarsa da kuma haihuwar wani abu me nauyi cikin qirjinsa da zuciyarsa,ya miqa hannu a hankali yana matsar mata da gashin da yake son rufe mata hancinta. Zama yayi sosai gabanta yana morewa kallonta,kallo irin me haifar da kusanci qwarai tsakanin zukata. Bayan wucewar kowacce daqiqa soyayyarta ke sake haukacewa cikin zuciyarsa,feeling sosai kallonta ke tayar masa,shi kansa yasan yayi mugun haqurin rashinta a kusa dashi, abinda bai taba kawowa zai iya ba.
Cikin baccinta ta dinga jin qamshin nan nasa yana isa har cikin kwanyarta,ta dinga motsa idanu a hankali,hankalinta da yayi nesa da gangar jikinta ya fara dawowa. Shuru tayi bata nuna ta farka din ba,ta nutsu sosai wai ko xataji wani motsi daya danganceshi?. Cikin ranta ta dinga fatan jin motsin ko yaya ne,duk da har yanxu batasan meye silar da yasa takeson taji motsin nasa ba
"Bs kowa,ke kadai ce dai" zuciyarta ta gaya mata. Qasan ranta taja tsaki,ta motsa tana son gyara kwanciyarta,saidai kuma batakai ga aikata hakan ba taji tattausan hannunsa ya lullube kafadunta.
Har cikin ranta taji saukar tafukan hannayen nasa,da mugun sauri ta ware fararen idanunta da suka sauya launi kadan saboda bacci ta watsasu a kanshi. Tabbas shine,farin qaqqarfan ba'abzinen nan daya qaurace mata tsahon kwanaki,qauracewar da tayi awon gaba da dukka nutsuwarta...... qauracewar da batasan dalilin da ya sanya ta dameta ba har ya wuce iyaka.
Da sauri tayi niyyar miqewa amma sai ya nuna mata mazantaka ya maidata kwancen,ya maye gurbin pillow din da take rungume dashi bayan ya zareshi ya aza mata nauyinsa.
Kallon tsakiyar idanu yakeyi mata wanda shi ya kassarata,ya kuma zare mata duk wata laka daga jikinta,bai daina duban tsakiyar qwayar idanunta ba kamar kuma yadda bai dagata ba,numfashinsa da nata sukaci gaba da gauraya waje daya,hakan ya haifar musu da wani irin yanayi me matuqar nauyi cikin gangar jiki da zukatansu.
Cikin qarfin hali ta soma yunqurin tureshi,amma sai yayi mata wani mahaukacin riqo,muryarsa da numfashinsa yana rarrabewa ya soma magana da ita cikin muryar can qasa
"ita yake sharewa amma shike amsar hukuncin fiye da ita.....Allah ne kadai yasan yadda ya wuce dararen nan.......awanni da sa'o'i masu tsaho da suka zame masa tamkar shekarun da suke wanzuwa rayuwar dan adam cikin tsanani.......kekam wai babu zuciya ne a qirjinki......ko sau daya mana ki gayamin cewa MAINA NAYI MISSING DINKA YADDA KAYI KEWATA NIMA" ya qarasa fada da wata iri murya yana kuma hade fuskokinsu guri guda,hancinsa yana gugar nata.
Idanunta kawai ta mayar ta rufe saboda abubuwan daya aike ma jikinta ita kanta tasan bata isa ta kauce musu ba. Hakan yake nema dama daga gareta,ya kuma fahimci aikinsa na farko ya fara isar masa da saqon yadda yakeso,don haka ya zura hannunsa ta gefen kunnenta ya shafo wuyanta da wani irin salo da ya sanya ajiyar zuciyar da bata shirya fitarta ba kubce mata
"Ke bakya kewar mijinki?" Ya sake jefa mata tambayar yana lalubar bakinta. Batasan amsar da zata bashi ba,baima kuma bata daman yin hakan ba ya bame bakinta cikin nasa.
Wani irin zazzafan saqo ya shiga aike mata,wanda girmansa ya Sanya sofa din da suke kai ta gagara daukarsu shi da ita,suka zame a hankali zuwa qasan carfet din,jikinsa gaba daya rawa yakeyi,kaman yadda nata jikin ya dauki kakkarwa,tanata yunqurin janye hannunsa amma ina bai bata wannan damar ba,sake shigewa jikinta yakeyi yana kuma sake boye fuskarshi sosai cikin jikinta a duk inda yaga yayi masa,a kuma wajen da duk yake da muradin hakan.
Bata tayashi da komai ba,amma kuma ya samu cikakken hadin kan da bai taba samu daga gareta ba,ko a guri daya bata yi yunqurin hanashi ko dakatar dashi ba daga abinda ya nufa. Ita a karan kanta batajin zata iya hanashin,jikinta ya sauka daga dukkan wani tsari data dorashi akai,tahau wani bigire da ita kanta batasan yaushe ta soma hawa wannan layin ba,saqonsa ya isketa fiye da yadda ta saba jinsa.
Kuka ta sake masa tana juya baya bayan komai ya kammala. Dariya ce taso qwace masa,ya cusa kansa a tsakiyar bayanta tana fidda qaramin sauti gami da janye bargon data duqunqune a ciki.
"zo kiji mummy twins" ya furta yana qoqarin birkitota. Jikinta ta hade guri guda taqi bashi wannan damar,da gaske rigima takeyi masa,don ya gama sanyata ta kunyata iya kunyata,ita kanta tasan ta saki layi fiye da yadda ya dace,batasan da wanne ido zata kalleshi,ya sakata shallake iyakoki sosai. Har yanxu dariyar ke cinsa,ya sani shi da kansa yasan yau din baibi mata ta sauqi ba,ya sani duk dauriyarta......duk kafiyarta......koda wani irin mahaukacin qiyayya take masa a yau din layin da ya dorata akai dole tabi.
"Ba wani kunya mummyn twins......ba wanda yasan fa me ya faru.......daga ni saike fa.....kome kikayi lada za'a rubuta miki......kuma kome kika fada na miki uzuri nasan cikin yanayi kik......."
"Me kuma nace?" Ta tambayeshi da sauri,sai ya saki dariya har yana cusa kansa a pillow. Dariyar tasa ta sanyata ta tsargu,itakam yau ta shiga uku,ba zata iya tuna da meye da meye ta fada ba bare tayi gyara,Allah ne kadai yasan irin baran baramar da tayi kenan,sai kawai ta sake fashewa da kuka tana cusa kanta a qafafunta.
Har tsakiyar zuciyarsa yakejin sautin kukanta,ya lumshe idanu yana dakewa sosai
"Tashi muyi magana......"
"Banaso......ka barmin dakina" ta fadi tana kuka da gasken gaske
"Bazan fita ba indai baki tsaya munyi magana ba.....hasalima a nan din zan kwana kinji na rantse" yana kaiwa nan ya hantsilo daga gadon, cikin nishadi da kuma jin kansa da yakeyi fresh ya shige bandakinta.
Kasaqe tayi tana sauraren saukar ruwansa a bayi. Abinda bai taba yi ba kenan,ga qoshi ga kwanan yunwa,tasanshi farin sani,kuma ita zata fada bada labari a kansa,baya rantsuwa bai cika ba,da gasken idan bata saurareshi din ba xai kwana a dakin nata?,baya tsoron ama ko aba su ganshi?,baya tsoro ko kunyar idanun kowa?. Wadannan tambayoyin suka tsaye mata a rai,ta rasa wanne zata zaba,ta murje kunyarta ta saurari abinda zaice ko kuma ta barshi taga iya gudun ruwanshin,da gaske zai iya kwana din?,to meye ma wai zaya gaya mata bayan ya gama sanyata ta barar da mutuncinta?.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 108
Tana jin motsin fitowarsa ta maida idanunta ta kulle,ita batajin zata iya sake hada idanu dashi. Ta cure waje daya tana neman gurin cusa kanta taji anyi cak da ita
"Leave me please......ka sakeni......banaso" birkitota yayi ya lullubeta tsakiyar qirjinsa yana cewa
"Da alama baki biya bashin nan da kyau ba,shi yasa bakinki yake iya magana har haka" ya qarasa maganar yana laluben bakinta. Bam ta bameshi ta cusa dukka labbanta cikin bakinta. Qaramar dariya ya saki,yayi maganin mitarta hankali kwance.
Duk ta firgice kada yace shi zaya wanketa yadda yakeyi mata,itakam yanxun ma gaba daya lamuransa tsoro suke bata,nema yake ita kanta ya sauyata,so yakeyi yayi mata dole ya kuma shiga rayuwarta ta qarfin gaske. Sai daya gama hada mata komai,hatta towel da zata buqata idan ta gama sannan ya soma ficewa daga toilet din da baya da baya yana cewa
"Karki dade a ciki.....idan ki gama ki kirani" ya hada hannayensa biyu ya mata sign na heart sannan ya juya yana ficewa.
Wata doguwar ajiyar zuciya taja tamkar zata tsinke jijiyoyin zuciyar dake jikinta,ta sauke numfashi tana bude idanunta taba duban hanyar daya fice din. Batasan me yakeson sauyata ba kwata kwata,da gaske yake rikita mata tunani bayan ita a yanzun bata shirya faruwar hakan ba.
Tana wankan qwaqwalwarta ta dawo mata da komai daya faru tsakaninta dashi mintunan da suka shude,ita daya a toilet din ta dinga jin wani mugun nauyi da kunyar kanta da kanta,komai na jikinta a yanzun ta tabbatar babu abinda baisan gwajin yawansa tudunsa zurfinsa da kuma fadinsa ba.
"Innalillahi" ta fadi tana tara ruwan hawaye,me yasa ta barshi tun sanda ya fara abun batakaj qararsa ba?.
"Wajen wa?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta
"Ama ko aba?" Ta sake tambayar kanta. Kai ta girgiza,abunma sam baiyi ma'ana ba,takai qararsa tace me?,yana shigowa gidan?,yana kuma shigowa dakinta?,idan ya shiga to meye yayi mata daya cancanci takai qarar?.
"Tace gana k....."
"Subhanallahi" ta fadi a ranta da sauri,ba zata iya gayawa ama da aba wannan maganar ba,kenan koda zatakai qarar ma yana da hujjar musa mata?,yana da kuma hujjar kare kanshi tunda ita din dai bata da wata qwaqwqwarar hujja.
Wankan ta farayi amma har a sannan bata haqura ba,so takeyi lallai ta samo hanyar da zata yakiceshi,tana tunanin kamar zata iya din,kaman yin nesa dashi din ba komai bane a wajenta,batasan ya riga yayi mata dashen da rayuwarta ma ta soma dogara da fitar numfashinsa ba.
Tana yi tana zancan zuci ita kadai,tana wassafa yadda zata fita daga toilet din
"Wai ta yaya ma zaki iya kai qararshi wajen ama?.....shin kin manta cewa ita din uwa ce?" Tambayar data sanyata tsaiwa cak daga goge sumarta da takeyi da towel. Gabanta ya fadi tana maimaita kalmar uwa,saita koma da baya ta zauna kawai a toilet seat. Dukka zamannan sam sam ta manta da batun ama ba ita ta haifa ba MAINA ta haifa. Ta manta da zancan cewa ba zata taba qin maina ba saboda ita,wannan yana nufin duk abinda takewa maina kenan ama tana jun haushin hakan?,to amma me yasa?,me yasa ama din bata taba nuna mata ba ko a fuska?,wacce irin jarumar uwa ce ita dake iya shanye qiyayyar da ake nunawa dan cikinta?. Ta dade xaune a haka tana son tuno wanne iri da wanne irin rashin kyautawa ta yiwa maina a gaban ama tsahon zamansu,to amma abun da yawa, lokacin da tsaho ba zata iya riqewa gaba daya ba,dole ta gaji ta miqe tana daure bathrobe din jikinta sosai da nufin idan ta koma daki ta sauya kaya.