Showing 96001 words to 99000 words out of 294767 words
Chapter 33 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
A nutse nutsuwar dake bayyana a iya fuska takunsa da ayyukansa na zahiri kadai.....yake saukowa daga matakalar jirgin da yayi jigilarsu daga niamy zuwa nan marad'i bayan dogon zaman da yayi daga makka a jirgin Ethiopian airlines.
Dogon ba'abzinen,Giant me wani irin qawataccen tsaho da murjajjen jiki......fari tas ma'aboci sassalkar cikakkiyar sumar da kai tsaye za'a kirata da sumar gado,sanye cikin wata farar shadda qal.....da aka zamanantar da dinkinta ya zauna a jikinsa tamkar don saboda shi shi kadai aka qirqiri dinkin. Dogon wando ne da gajeriyar riga ta ciki me gajeran hannu,saidai kuma an qawata shigar tasa da babbar riga da kuma dakakkiyar hular da bata rufa dukkan asirin sassalkar sumarsa ba. Daga nesa idan ka hangi tsahonsa da yanayin jikin gami da shigar tasa zaka dauka jinin hambararren shugaban qasar nijer ne wato mohamed bazoum,saidai kana kallon fuskar zata tabbatar wannan jinin MAYAK'I da jajirtacciyar tsohuwar yar kasuwa NADEEYA ne.
Gujajjen D'a daga ainihin qasarsa ta haihuwa,daga ainihin gidansu abun alfaharinsu,daga ainihin garinsa ahalinsa da kowa nasa......yau gashi cikin qasar da ya barta ba tare da sanin zuwa wanne lokaci zai dawo ba?,yau gashi kan hanyar komawarsa gidan daya fita cikin fitar hayyaci da rashin sanin abinda zai biyo baya,yau gashi zai fuskanci ABA AMA BIBI DA D'ANSA DAMA MAHAIFIYAR YARON SULTANA.
"Bienvenue Monsieur" yaji an fadi daga gefanshi da harshen faransanci ana yunqurin karbar luggage dinsa da suhail ne ya samu nutsuwar hada masa kayan nasa. Kai kawai ya gyada ya sakar masan,don already yasan waye,uniform din jikinsa ya sake gaya masa waye din,kuma aikin sardauna ne duka ya sani.
Yana biye dashi har suka isa gaban wata Mercedes Benz baqa wul dake daukan idanu qirar wannan shekarar ce da suka siyeta su ukun,shi sardauna da kuma suhail. Kai tsaye yace a turo tasa nan,a ajjiye a kamfaninsu dake shirin fara aiki a qasar tasu.
Yau ya fara ganin motar ido da ido,amma a yanzun bashi da cikakkiyar nutsuwar qare mata kallo,don haka shigewa kawai yayi back seat din da ya bude masa,ya maida motar ya rufe,ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar suka dauki hanyar fita daga airport din.
Baisan wanne yanayi zuciyarsa take ciki ba,baisan kuma meye yakeji a dukka jikinsa ba,abu daya tak ya sani,zai fuskanci babban QALUBALE......zai gamu da komai,zai ga komai zai kuma ji komai,amma koma meye ya dawo da dukka qarfinsa,ya kuma dawo da shirin fuskantar KOMAI DA KOWA.
Unguwar tasu ya dinga bi da kallo,a tsahon shekarun akwai ci gaba sosai,komai ya sauya,ba wani abu da yaga yaci baya,har zuwa LOKACIN da ya driver din ya iso dab da gidansu.
Lumsassun idanunsa ya ware,ya miqa hannu ya taba kafadar driver din,da muryarsa dake can qasa yace
"arrêt(tsaya)" bai musa ba ya gangara gefe saboda ya bawa motoci biyun da suka biyo bayansa damar wucewa,ya tsaida motar daga gefe daya.
"Bani maqullin,tu peux y aller(zaka iya tafiya)"
"d'accord Monsieur(to yallabai)" ya fadi cikin girmamawa yana bude murfin ya fita kaman yadda ya buqata.
A hankali ya fito daga bayan yana komawa seat din driver idanunsa bisa babban gate din mansion house din nasu,jikinsa yana bashi wani hidima akeyi cikin gidan don yaga alamun haka,zuciyarsa ta raya masa wani abu da tilas ya rufe idanunsa yana kiran sunan Allah sannan ya tayar da motar
"Bana fatan na mutu ban gurfana gaban aba da ama ba......bana fatan na mutu da hakkinsu" ya furta a fili saidai can qasa bayan zuciyarsa ta raya masa kodai wani daga cikinsu ne ya rasu.
Motoci biyun da suka wuce su yabi,dukkansu security suka budawa hanya suka wuce ciki,saidai kuma ana zuwa kanshi suka jaa qofan saboda kasancewar motar baquwa a idanunsu,sannan kuma basu tabbatar da motar waye ba,don haka ba zasu bata daman shiga ba har sai sunyi checking nata.
Cikin dakewa da sanin makamar aiki daya daga cikin security din ke matsowa,idanu maina ya zuba masa,houdu ne,daya daga cikin security na gidan tun kafin barinsa gidan. Ya tabbatar shine mutum na farko da zaya fara shaidashi,saboda yasan fuskar tasa tun babu saje babu gemu,ya sanshi tun a sanda saje ne kawai dashi,a yanzun da gashi ke kwance luf bisa tsari na samuwar shekaru a tattare dashi bazai gaza shaidashi ba.
Abu daya tak yayi,houdu na matsowa yana sake glass din motar,dai dai sanda ya iso dai dai sanda shima ya kammala saukewar,sai sukayi ido hudu da MAINA din.
Duk wani connection na jikinsa ya katse cak na wasu mintuna,sannan second kadai ya dawo bisa saitinsa,idanunsa fes cikin nashi,sai yasa hannu yana cire hulan kanshi,sai maina ya dora hannunsa saman lips nashi dole houdu ya maida maganarsa cikin cikinsa,ya kuma juya ciki da sassarfa yana bawa saura umarnin su bude,ba musu tunda shine shugaba suka bude din ba tare da sanin waye cikin motar ba,ya dage glass dinsa ya danna hancin motar zuwa farfajiyar gidan bangaren ajiyar motoci bayan shekaru biyar da barinsa gidan...........
*_WELCOME BACK MAINA_*😂😂😂
Sanda take wucewa falon aba dauke da saqon aba a hannunta kunnuwanta sukaji qarar shigowar wata motar. A ranta take dariyar mugunta,tana kyautata zaton goumar ne ya nemo najma data boye ya maidota gida,don ta barshi a can ranshi bace yana nemanta,yayi rantsuwa bazai barta a wajen ba. Ta rasa wanne irin kishi gareshi haka?,abun goumar yana daure mata kai,duk da migraine da take fama dashi amma itama sai data rama yau dubu cikin abinda yake mata
"Ta can baya na ganta da wani farin buzu me irin tamu fatar" tayi furucin ko a jikinta tana bude motar ta cilla kayanta ta shiga tabar wajen tana hangensa ta madubi. Gun data fada din yakeson zuwa,amma ya dake yaqi nufar wajen yana tsoron ko tsiyarta ne yasa ta gaya masa hakan saboda yasan hali sarai,barin hali kuma sai mutuwa,ta kuma karanceshin itama haka ta dinga dariya cikin mota ita kadai har ta fice a wajen.
Daga qafarta zata sanya a falon aba din yayi daidai da qarasa shigowar motar gidan,ba kasafai hankalinta ke kaiwa ga shigowar motoci gidan ba,amma wannan sai taji gabanta ya yanke ya fadi. Dan dafa saitin qirjinta kadan tayi tana cewa
"Hasbiyallahu lailah illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem"
"Waye a nan?" Muryar aba daga cikin falon ya isketa daga nan inda take
"Aba nice,saqon oncle sidi ne" ta amsashi tana qarasa shigowa ciki. Sai data shigo din taga bashi daya bane,kamar kusan kowacce rana,tunda aka fara hidimar bikin basa rabo da irin wannan zaman waje daya. Oncle bashar oncle umar da oncle issoufou,sai qani ga mahaifinsu da bai jima da dawowa nijer ba.
Bakinsa dauke da sunayen Allah ya ajjiye motar kan tsari kaman sauran motocin gidan,ya kasheta ya kuma zura qafafunsa yana furta
"Bismillah" ya taka dandagaryar qasan gidan. Sai daya kulleta sannan ya juyo,juyawar daya samu security na gidan tsaitsaye daga bayanshi suna kallonsa cikin tsantsar mamaki. Murmushi ya jefesu dashi,sannan ya juya yana fuskantar ainihin ginin gidan,zuciyarsa na shawarta masa INA YA DACE YA FARA NUFA?. sassa guda biyar din dukka sai sukayi masa kwarjini,daga qarshe zuciyarsa tayi masa ragama izuwa sassan AMA saboda tuna masa da tayi UWA CE,zata iya zame masa tsanin zuwan kowanne qalubale da sauqi.
Kasancewar kusan kowa bai dawo daga wajen dinner din ba sai daidaiku,sai ya dinga tafiyarsa ba tare da yaci karo da kowa ba. Daf da qofar sassan ama din yaja burki kaman yadda wanda ya fito da hanzari dauke da gorar babban lemo a hannunsa shima ya tsaya cak kamar an tsaida mashi.
Almu ne,wani irin kallon gigita da bazata yake bin maina dashi,sai gorar lemon hannun nasa ta sulale ta fadi qasa. A nutse maina din ya duqa ya dauko masa,ya bude tafukan hannayensa ya zura masa a ciki ya kuma damqe hannun cikin nasa,sannan cikin karyayyar muryarsa yace masa
"Kaini wajen ama" maganar tasa saita zamewa almu kamar wahayi,bai musa ba don dama tun dacan ba musu tsakaninsu,bai kuma iya tambayarsa komai ba saboda tsananin mamaki ya wuce gaba maina yana biye dashi.
Yasan inda ya baro ama din yanzun daya fito daga wajenta,tana falon farko wanda take da bedroom a wajen,ya barta suna hada shimfidun da za'a fitarma dakin baqi na gidan ita da tanja,don haka suna zuwa dai dai qofar dakin yaja ya tsaya yana bawa maina hanya,tamkar yana nufin
"Ya maina na gama nawa" idanun almu din ya kalla,sai ya sake kama hannunsa ya riqe sosai
"Ka jirani koda a nan ne,kada kaje ko ina" kamar mataccen qadangare almu dai ya gyada kai,yayin da maina ya sanya hannu ya murza handle din dakin ya sanya kai bakinsa dauke da cikakkiyar sallama........
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 52
Sallamar tasa ta iske kunnuwansu dai dai sanda ama ta miqawa tanja blanket din tana cewa
"Kowanne gado a canza don Allah kafin mutane sukai ga dawowa daga wajen dinne........." Cak sauran maganar ta tsaye mata a qasan maqoshinta,kowanne gaba na jikinta yayi wani irin mutuwa gami da yin sanyi kamar anabi ana zare mata laka.
Sake maimaita sallamar tasa yayi cikin karyewar murya da zuciya gaba daya,wata irin qaqqarfan qaunar mahaifiya tarin madama da jin cewa shi cikakken me laifi ne yana taso masa. Gabanta na faduwa ta kalli tanja,tun bata yiwa tanjar tambayar ba tasan amsar tambayar tata,amma saboda tabbatarwa sai tace mata
"Tanja?,muryar waye kunnuwa na sukeji?" Ta furta da wani irin sauti muryarta da mugun sanyi
"Shine...." Tanja ta fadi itama kamar me tsoron gayawa ama din. Wata qatuwar ajiyar zuciya ce ta kufcewa ama din,ta runtse idanunta sannan ta budesu,taja numfashi sosai cikin hunhunta sannna ta fesar,sai ta durqusa tadauki wani madaidaicin blanket din ta sake miqawa tanja tana ci gaba da yi mata bayani tamkar ba wata halitta baquwa data wanzu a wajen
"Ki ajjiyewa su bilkisu saiki dawo,akwai ragowar aiki a nan din" taci gaba da bayaninta.
Iya yadda tayi wannan motsin ya tabbatarwa maina akwai qototuwar matsala,ya taka zuwa bayanta jiki a mutuqar sanyaye,ya sulale a hankali ya zube bisa gwiwoyinsa kanshi a qasa ya kasa furta komai.
Cikin jikin nata taji alamun yana bayan nata,sannan satar kallon bayan nata da tanja takeyi yasa ta sake fahimtar a bayannata yake tsaye har yanzun. Wani nannauyan abu yana fusgar zuciyarta,dukka zuciyarta da kwanyarta na shirin shiga rudani,bataso ta waiwaya ta kalleshi......bataso ya saukar mata da rauni a a matsayinta na uwa,idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba tasan cewa kaf gidan gurinta ya fara dosowa kanshi tsaye.......ta tabbata ba wanda yasan da shigowarsa cikin gidan sai ita,akanme zata sassauta masa?,akan me zata bari zuciyarta tayi rauni cikin lokaci qalilan har haka?,tsugunnonsa da zamansa ba zata tana bari suyi mata tasiri ta kasa aiwatar da abinda ya kamata ace ta aiwatar din ba.
Dukka kayan tanja ta dauka sannan ta soma takawa tana barin dakin,duk taku daya sai ta waiwaya ta kalli maina har ta fice,yayin da ama kuma ta soma hada wasu kayan,duk da batasan ainihin me zatayi da kayan ba ita kanta. Cikin jikinta takejin wani irin yanayi,karyewar zuciya da mutuwar kowanne sashe na jikinta,yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya ta tabbatar akwai fushi me tsanani kwance a qasanta
"Assalamu alaikum.......don Allah ama koda ba zaki kulani ba ki amsa koda sallamata,ki amsa min da neman aminci da albarkar ubangiji da na rasa tsahon shekaru" maganar tasa sai ta zame mata kamar famin wani tsohon miki dake danqare qasan zuciyarta. Watsar da kayan hannun nata tayi sannan ta gewayeshi da hanzari zata fita a dakin.
Cikin wani irin zafi irin na namiji yasha gabanta,sai ya sake zubewa a gabanta yana riqe da dukka qafafunta da hannayensa
"Don Allah ama......na roqeki......ko sallamata kawai ama ki amsa min" janye qafafunta baya tayi da sauri,karon farko ta watsawa fuskarsa wani irin kallo .......wani rauni ya sake mamayarta. Mainan ta ne......ya zama cikakken mutum......mainanta ne.....ya zama babban mutum.....aliyyu ne da ya bar gabansu tsahon shekaru,yanzu gashi duqe gabanta cikin qoshin lafiya da dukkan alamu na nutsuwa da kwanciyar hankali tattare dashi
"Waye kai?,nace kai din waye?,don kaga na qyaleka a matsayinka na bare ka shigo har cikin dakina shine zaka zaqe da yawa haka?" Ta jefa masa tambayar da murya me cike da fushi. Sosai kalaman nata suka daki zuciyarta,suka kuma so tarwatsata zuwa piece's. Yau din shi ama ke barrantawa daga gareta?,shi ta maida bare?,wanda bata masan fuskarsa ba?. Ya hadiye wani qatoton abu daya tsaya masa a wuya,muddin ama tace zata qalubalanceshi ta haka bayajin zai iya dauka,ya shirya fuskantar kowanne irin fada da ladabtarwa,koda kuwa suka ne,amma bazai iya jurar shariyarsu da wofantar dashi haka ba.
"Danki ne ama,ba wani bane daban,aliyyu ne ama......maina ne......danki bijirarre gujajje.....me tarin laifuka a gareku.......don martabar manzon Allah S A W ama kada kice ta wannan hanyar zaki horani" girman roqon da yayi mata yayi matuqar tasirin wajen rauna mata zuciya,amma hakan bai sanya ta kasa sake janyewa baya ba ta kuma nufi qofa da sauri tana jin kamar hawayen da take riqewa zasu balle kansu da kansu saboda girma da nauyin dake danqare cikin qirjinta.......ta jima da sarewa.....ta dade da fidda rai daga samun rayuwarsa,tana raye ne kawai tabarwa kanta abinda zuciya ke yawan raya mata a kanshi.....amma sam bata taba hasashen rayuwar aliyyu na nan tabbace saman doron qasa ba.
"Indai kazo ne na goya maka baya......na tayaka binne laifinka ba zaka samu haka ba aliyyu......nice mutum ta qarshe da zaka fuskanta,hukunci na shine hukuncinna qarshe da zaka karbanan din ba shine mihallin da zaka fara fuskanta ba" abinda ta gaya masa kenan a gaggauce ta fice a dakin,wani irin abu yana zagayawa cikin jini da zuciyarta,tunaninta yana rarrabuwa. Tasan tabbas!,Allah ne ya amsa addu'arta......amma me dawowarsa ke nufi?,meye kuma zai faru a nan gaba?,wannan dukka bata da masaniya. Taja numfashi da kyau ta kuma fiddoshi waje,ga mamakinta sai taji dunqulallen abunnan daya tsaye mata a maqoshi tsahon shekaru......wanda ta gaza gane meye shi tsahon wancan lokacin yana narkewa a hankali yana sauka.
A lokacin yana jin dukka jikinsa ya masa nauyi,yana jin kamar bazai iya motsawa daga wajen ba......yana jin kamar kwanyarsa ta daina tunani dai dai,saidai kuma a hankali ya kama sunan Allah,ya fusgeshi da matuqar qarfi
"Alhayyu alqayyumu" ya fara maimaitawa,a hankali sai dukka qwarin gwiwarsa yaji yana dawowa,ya kuma sake kiran
"Allah!" Da qarfin zuciya yana miqewa,ya nufi qofar dakin ya bude ya fice.
Inda ya tsayar da almu a nan ya sameshi,suna hada ido almu din ya sunkuyar da kai
"Ina zan samu su aba?" Da hannu almu ya masa nuni da hanya tamkar wani kurma,maina din ya karanci me yake nufi,sai shima ya masa nuni da hannu akan suje din,almu yayi gaba,shi kuma yaci gaba da bibiyar sahun almu din dake masa jagora zuwa falon.
Gaban aba ta qarasa ta durqusa kamar kullum tana musu barka da warhaka. Dukkansu suka amsa cikin kulawa,ta sanya hannu ta dauki ledar tana miqawa aba fuskarta fadade da murmushi
"yauwa ma sha Allah,ya cika alqawari,ungo wannan" aba ya fadi sanda yake warware kilishin da sultana ta kawo masa. Murmushi tayi ta sanya hannu biyu ta karba tana cewa
"To na gode aba sosai"
"Madalla" ya amsa mata,sannan ta yunqura tana miqewa
"Kinga sultana.......ki shiga ki gayawa mariya su duba abinda yayi ragowa a kayan amfanin gobe" oncle umar ya fada
"To uncle" ta amsashi tana nufar qofar tana ji aba yana tsokanarsu kan cewa boye kilishinsa zaiyi,diyarsa kadai zai iya bawa. Murmushi ta saki qasan zuciyarta,ba abinda zata ce ma Allah sai godiya,itakam batasan maraicin uwa da uba ba.