Showing 156001 words to 159000 words out of 294767 words

Chapter 53 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

yake zuwa

"Indai suhail ne kayi duk yadda kakeso dashi,hasalima ni zan tayaka" ya bawa maina amsa yana isa gaban babbar tv plasma dake maqale a bango ya tsugunna ya kunnata,sannan ya juya zuwa wajen fridge yana cewa

"Bari muga me zamu samu a office din likitan zuciya" cikin dan tsokana da jan wasa.

Sanda ya bude bakinsa zai bashi amsa,daidai lokacin muryarta ta karade dakin,cikin tattausar muryarta me dauke da tataccen harshen France,wanda daji kasan ba tsintarsa tayi a hanya ba,don ya kama bakinta radam.

Idanunsa nakan wayarsa a sannan yana duba saqonnin ayana da na laila da suka kusan yin gware wajen shigowa wayarsa,kowacce na tura masa saqon fatan alkhairi ne da fatan nasara.

Da sauri ya cira kansa daga screen din wayar zuwa screen din tv din,idanunsa sukayi kuwa kyakkyawan gani.

Beautiful sultana,farar ba'abziniya wadda dukka kamanninta sukafi karkata da jinin arab,fara sol me wata irin ni'imtacciyar fata me azabar sulbi da sheqi,sanye cikin ainihin kayansu na al'ada,kayan da aka san kowacce mace ba'abziniya da sakasu,kalar shuni da sukayi masifar fidda kyawunta suka dace da jikinta,hatta da kyawawan qwayoyin idanunta a yau sun fidda kyansu,brown din qwayar idanu me wani irin sheqi tamkar an diga mai a cikinsu,siraran labbanta sunsha nasu adon,kamar yadda zara zaran yatsunta da hannayenta suka sha adon banguls na azurfa da tagulla da wasu irin duwatsu irin nasu. Gashinta kawai bai fito ba,ta sayashi cikin daurin kallabin dake kanta.

Da qyar ya zuqo numfashinsa,da mugun wahala da kokawa da rai ya zaquloshi ya maidoshi cikin qirjinsa. Me yake shirin gani haka?

"Ba sultana bace" wani sashe na qwaqwalwarsa ya gaya masa

"No" ya furta a sarari wanda banda hankalin sardauna nakan wayar da yake amsawa fes zai jishi. Sultana ce,babu wani yanayi da zai hanashi gane sultana,babu shi a duniya!,tsanani wahala ko dadi.

"Ma sha Allah,wannan kamar shigar gargajiyarku ko haidar?,da alama presenter din expert ce......wannan program din zaija jama'a gaskiya" sardauna ya fadi bayan ya dauke idonsa daga saman tv din yana lalubar wajen zama.

Kasa hadiye abinda ya taso masa yayi,ya sanya remote ya kashe tv din gaba daya. Dago kai sardauna yayi da zummar tambayarsa me yasa ya kashe?,ya barshi suga gargajiyar nijer a paris mana?,sai maina din ya rigashi tambaya

"Wanne gidan tv ne wannan?,a ina kuma yake?"


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 page 82


"ga logo dinsu can a sama,kaman national TV ne ai ko?" Sardauna ya fadi yana kai cup din bakinsa.

Remote din ya ajjiye ya sake daukar wayarsa cikin karsashi,gefe guda yana jin ranshi yana sosuwa,yana hasaso dubban miliyoyin jama'ar dake kallonta yanzu haka live

"Ya salamu ya Allah" ya furta qasa qasa bayan dukka bayananta sun fito a page din gidan tv din a matsayin sabuwar ma'aikaciyarsu ta sashen al'adu.

Iska ya sake furzarwa,kusan ya gama samun komai,a yanzun samun adress nata ba shine a gabansa ba,don yasan bazai zama damuwarsa ba. Bai sauka ba sai daya gama bincika dukkan abinda yake da buqatar bincikawar,wanda ya daukeshi dogon lokaci,don har sai da sardauna ya tafi ya bashi cikin office din.

A nutse take driving cikin takatsantsan dabin dokokin qasar,gefe guda kuma ranta fes,nishadi takeji sosai a ranar,komai yayi successful,su kansu suna yabawa da yadda ta gabatar da program din cikin zaar qwarewa,babu wani abu da zai sanya kayi tunanin farin shiga ce ita din,ta samu yabo sosai,hakanan a iya ranar kawai gidan tv din ya sake samun qarin viewers da sukw bibiyarsa ta kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa.

Ta cikin speaker din motar ta jona take sauraron VN din aminata da ta bibiyi shirin sanda ake gabatar dashi. Kalmomin yabo ne sosai da kuma alfahari da ita da family MAYAK'I keyi,ba aminata kadai ba,ta samu saqonnin cousins dinta da yawa da ayanzun take saurara yake kuma sake sanyata nishadi, kyakkyawan fuskarta tattausan murmushi kawai take fiddawa wanda yake qara mata wani irin kyau da kuma kwarjini.

A nutse ta isa qofan gidan,ta ajjiye motar a muhallin da gwamnati ta aminta da ajjiye ababen hawa,ta bude motar a nutse ta cire wayarta tana daukan hand bag dinta idanunta ya sauka akan pack na snacks da abokiyar aikinta 'yar qasar nijer ta bata dioura. Zuwan sultana ya yiwa dioura dadi sosai,don sai ta jita tamkar a gida nijer,ta samu 'yar uwa abokiyar aiki. Wunin ranar nan nan ta dinga yi da sultana,ganin farko dama Allah ya hada jininsu,gashi kuma suna qasa daya.

Daukan pack din tayi tana murmushi tana tuna kirkin dioura,a yau din tana jin duk wani baqinciki da bacin rai dake ranta ya goge fes,sai ta soma takawa cikin gidan riqe da Jakarta.

Sau daya tak ta danna bell aka bude kaman ana jiranta ne dama. Wani abu taji an watsa mata tadan kauda kai kafin ta bude idanunta tana duban benazeer da batoul dake tsalle a gabanta

"Happy happy mommy,first day a gidan tv" benazeer dake fama tsalle ta fada

"Mun ganki mommy Allah" batoul itama ta fada tana dariya. Murmushi ya qwace mata,abun nan da bahaushe ke cewa diyoyin sanyin idaniyar iyayensu shine ya saukar mata,tadan saci kallon ama dake tsaye tana murmushi,saita ajjiye kayan hannunta ta tsugunna ta rungumesu dukansu

"Thank you,na gode sosai" sai kuma ta miqe a kunyace ta qarasa gaban ama tana kallon dam decoration din da suka yiwa falon da rubutun congratulations

"Barka da warhaka ama,ya gida ya yara?"

"Barkanki dai ma fille('yata),tu as travaillé dur(kinyi aiki sosai),nayi alfahari sosai dake yau,ina fata Allah ya qara haska miki rayuwa,ya haska miki kuma dukkan kyakkyawan abu,ya haneki da fadawa hanyar da ba dai dai ba" ama tayi mata dukkan wadannan addu'o'in tana dafa kanta. Kunya ta sake kamata,ta rusuna tana sunkuyar da kanta qasa,sai ama din ta dan janye baya.

"Ki shiga ciki ki huta kafin aba dinku ya dawo ki bamu labarin yadda aikin ya kasance"

"To ama na gode" ta amsa mata. Da kallo ama din ta bita,dai dai da rana daya bakinta bai tana gajiya ba wajen roqon ubangiji ya daidata dukkan al'amuran rayuwarta,kai ta kada tana maida dubanta cikin falon,saita nufi benazeer da batoul da suka tasa cake din da ta sa aka kawowa sultana din a matsayin gift a gabansu suna lakata suna ci ta soma musu tsiya

"Tofa ga shazumamu me bakin shan zaqi"


*_Aliyyu maina_*


Sake juya fuskar system din masa yayi a karo na babu adadi wai ko arrow din dake masa nuni da direction din arean da phone number din yake aiki zai sauya akala,saidai fa ina,duka adress din da arrow din suna masa nuni ne da gidan dake kallon nasa gidan. Tsananin mamakinsa ya qaru,ya kashe system din ya sake kunnata,ya koma kan aikin nasa still abu daya yake nuna masa.

Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya sauke qafafunsa a hankali,ya zura takalmansa ya taka a nutse har ya isa gaban babban window din dake facing gidan da arrow din ke nuna masa.

Hannu biyu ya saka ya yaye labulen yana sauke idanunsa akan gidan. Kamar kowanne gida dake qasarma gaba daya zai iya cewa,a rufe yake ruf baya iya hangen komai da zai bashi satar amsar tambayarsa. Dukkanin idanunsa ya zubawa gidan kamar yana fatan ganin gilmawar wani,saidai shuru ba motsi ko gilmin komai. A qalla ya kusa kashe awa biyu kenan daga aikin zuwa tsaiwarsa a wajen yana neman hujja,tunda ya dawo daga office bai bar gurin ba,ko abinci bai nema ba daga wajensu Ahmad,ruwan lemo kawai yake dirkawa cikinsa. Sakin labulen yayi da zummar komawa ya sake bincikawa,amma sai kuma yaji zuciyarsa ta kasa yarda da qaryata binciken da takeyi. Sake juyawa yayi ya kalli gidan,sai ya taka a hankali ya koma mazauninsa ya dauki wayarsa ya fara laluben number ahmad.

Bugu biyu kacal ya dauka,komawa yayi ya zauna yana amsa gaisuwarsa da harshen faransanci

"Ina da aike da zanyi maqota,akwai dan aike da zan samu?"

"Eh akwai,nan da mintuna biyar zai iso yallabai"

"Da kyau,na gode"

"Ba godiya yallabai" ahmad din ya fada yana murmushi. Shi daya yasan zallar karamci irin na maina,ya jima bai hadu da mutum me karamcinsa ba,amma kuma da sardauna yake gaya masa halin dattako irin nasa sai gaba daya ya qara sallamawa lamarinsa.

A nutse ya miqe yana binciken me zai aika dashi gidan a mazaunin saqo?,me zaya bada wanda zai bashi damar fahimtar su waye mazauna gidan?.

Tunawa da yayi da su benazeer ya sakashi bude fridge yana laluben chocolate din da ahmad ya zuba tun randa yazo gidan,shi din ba gwanin shan zaqi bane,wannan ya sanya ya manta da lamarinsu gaba daya. Dukka kwalayen ya debo ya shiryasu saman table,dai dai sanda yaji ana danna bell sai ya taka ya bude qofan. Matashin saurayin bature ne dogo siriri,ya gaidashi cikin girmamawa,ya amsa masa yana masa nuni da kwalayen,sannan cikin yaran faransanci ya nuna masa gidan da zai miqa din.

Bakin window din ya koma ya sake budewa yana dafe window din da hannayensa,yana biye da takun matashin har ya isa qofar gidan ya kuma soma danna qaraurawa.

Tana zaune tsakiyar benazeer din da batoul tana musu adon gashinsu. Dole suka sakata gaba akan ita zata gyara musu kansu saboda goben sunsan zata fita aiki ne tun da safe. Ama na zaune a gefe tana duba wani littafi daya shafi hikayoyin gargajiya da aka rubutashi da yaren faransanci,sultana ta yunqura zata miqe saboda qarar door bell din,sai ama ta ajjiye littafin tana cewa

"Yi zamanki" ta jawo wani madaidaicin farin hijab ta sanya ta miqe tana nufar qofar,a nutse ta murza key din sannan ta Murda handle din ta bude.

Tarwai fuskar ama dinsa ta bayyana a gaban qofar,ya lumshe lion eyes dinsa yana jin wani abu yana tsarga masa,ya sake budesu da sauri dai dai sanda ta waiwaya bayanta tana magana,da alama da sultana take magana,yadda kuma take kallon saqon bayan ya miqo mata ya bashi tabbacin ta dago haske ne,ko kuma ranta ya darsa mata wani abu.

"Merci" ta furta da yaran faransanci bayan ta karbi kwalin dake da sanyi alamun daga gidan sanyi aka cirosu.

Tunda ta karbi kwalin jiki da zuciyarta ke raya mata wani abu,alamu da motsin aliyyunta takeji all over her heart......tana jin kamar yana kusa dasu ne,tana da yaqini kaso tamanin cikin dari cewa daga hannunsa wannan ya fito.

"To idan bashi ba waye?" Ta tambayi kanta sanda zuciyarta ta soma mata wasi wasi. Daga ita har sultana ba wanda yayi ordering wani abu daga waje,hasalima sun gama siyan komai na birthday din yaran,goumar baya nan bare tace shine, after all shi daya yake wannan gift din ma yaran,tun sanda ma yake mutumin boye.

"Indai kuwa shine tabbas d'ana ya cika sadauki......ya kuma cika namiji sannan ya nuna mazantaka daya lalubo family dinsa da kansa" ta furta qasan ranta murmushi yana qwace mata a sirrance,don tana da yaqinin bai samu goumar ba kwata kwata ko a waya ballantana tace shine ya bashi haske.

Dukka idanun yaran yana kan kwalin saboda ganin masoyiyarsu wato kayan zaqi

"Ama namu ne?" Benazeer ta tambayi ama. Rasa amsar da zata basu tayi,batason tayi wata magana da zata razana sultana ko ta sanyata dasa zargi a ranta kamar yadda zargin ya dasu a nata ruhin

"Naku ne,ku diba kadan ku sanya raguwar a fridge karku sha ya muku yawa" cikin murna suka amsa din suka baje suna zaba. Ama na zaune tana binsu da kallo tare da hasaso ta ina maina zai bullo indai shine?. Yayin da sultana ma sam bata kawo komai cikin ranta ba,saboda tayi imani dari bisa darin cewa bai isa ya cimmata ba. Tattare kayan kitson ta farayi,don tanason ta shiga daki ta qarasa abubuwan dake gabanta ta kwanta da wuri,don tanason fita aiki da cikakken energy da kuma nutsuwa.

"Nikam na gaji,tunda kun samu abunyi sai da safenku"

"Goodnight mommy" suka amsa mata a kusan tare ba damuwa tunda sun samu abun maqulashe.

Da baya da baya ya koma ya zauna a hankali yana furta

"Alhamdulillah" murmushi ya qwace masa saman fuskarsa,dukkansu yayi missing dinsu,yayi kewarsu kaman hauka,shi kadai kuma yasan me yakeji. Agogo ya kalla,dare ya fara yi,amma kuma yana da muradi,yanason ya isketa a wannan daren,idan da hali idan kuma zai yiwu,yana sha'awar raba dare da ita,ya kamata a karon farko ya bata wani lesson me wuyar mantawa,ya bata wani babban karatu da kowanne motsinta zai dinga tuna mata

"She's belong to him"

Hannunsa ya damqe qam qam guri guda tsigar jikinsa na zubawa saboda tunawa da yayi da komai nata,lallausar fatarta me qamshin nan,lips dinta dake da wani irin sulbi da sanyi,sassalkar sumarta dake da wani irin sulbi,uwa uba dumin jikinta dake da wani irin tasiri cikin qasusuwansa tun tana mitsitsiyarta.

Sake duba lokaci yayi,sai ya miqe a nutse yana komawa bakin window din,zuwa yanzu babu haske kwata kwata da yake iya hangowa,tabbacin sun wuce zuwa ga kwanciya,uwa uba qarin mota guda daya daya gani ya bashi tabbaci aba ya riga da ya dawo.

Juyawa yayi cikin nishadi ya wuce bedroom dinsa. Wayoyinsa ya kashe dukka gaba daya,ya jawo drawer din madubin ya zubasu,sannan ya soma zare kayan jikinsa ya wuce zuwa toilet ya hada ruwa me yawa da dumi. Kwanciya sosai yayi cikin bathtub,yana shirya komai cikin kwanyarsa,dole yau ta tsaya ta fuskancesa ko kuma yayi forcing nataa ta fuskanceshi ta dolen dole.....zabi ne guda biyu.✌🏽


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂.

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 83



Sai data dan sake bata lokaci gefen gado tana duba aikinta na yau,tare da dan qaramin research kan program dinta na wani satin da zata fara practicing dinsa tun daga gobe. Ta kusa awa daya sannan ta kashe system din ta mayar ta ajjiye,ta miqe tana miqa saboda gajiyar dake bin sassan jikinta. Tunda ta tashi yau din bata huta ba,yawan mutanen da yau tayi magana dasu da murmushinta a yau ya zarta na kullum. Mutane ne su masu son mutumin da yake da talent,wannan ya sanya suka yita zuwa ganinta tare da yabawa program din a iya yau kawai,dole kuma ta sakarwa kusan kowa a fuska kaman yadda ama tayi mata fadan haka sosai.

Kayan jikinta dukka ta zare ta daura babban towel,ta bude jakarta ta ciro sabbin bath set dinta daya hada da shower gel bath mist da sauransu,ta zare ribbon dinta ta azashi saman madubi,ta dauki qaramin towel ta dora saman kanta don tasan wankan tsarki zatayi,don kafin ta fita dinner ta duba taga al'adarta ya dauke. Ta zura slippers dinta na wanka ta wuce toilet bayan ta daidaita sanyin dakin.

Tun tana wankan takejin idanunta suna mata nauyi kaman zasu rufe saboda bacci da kuma gajiya,wata irin kasala takeji tana bin duka sassan jikinta,wannan ya sanya ta jima sosai a toilet din fiye da yadda ta saba dadewa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login