Showing 285001 words to 288000 words out of 294767 words

Chapter 96 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ama din kadai ne. Duk wani abu da sukeji yanzun a wancan lokacin ama ita daya ta shanyeshi,lallai ama ta cika jarumar mace,ta kuma cancanci dukkan yabawa. Macace me kamar maza,wadda tayi abinda kaf family din MAYAK'I ba zasu taba mantawa da ita ba.

Da taimakon aba komai ya daidaita,sai aka koma hira kadan kadan,amma duk da haka maina ya kasa zaune ya kasa tsaye. Kamar ma ya manta da kowa a cikin dakin,don duk bayan minti kadan ko second kadan sai ya tambayeta

"Ba wani abu?"

"Ba komai" take amsa masa,har ta fara jin Kunyar yadda yakeyi din,don kamar ya raina kulawar da kowa ke qoqarin bata ne.

Sanda nurse ta shigo tafiya da ita kasa tsaiwa yayi a wajen,don yana jin yadda idanunsa sukeson fidda hawaye,yanason fita amma qafafunsa sun riqeshi

"Muje daga waje ta qarasa shiryawa" aba daya lura da yanayinsa yace dasu,duk sai suka juya suna ficewa,dakin ya zamana daga shi sai ita sai nurse din da zata bata rigan da zata saka. A zafafe ya sanya hannu ya jawota jikinsa,zuciyarsa tana wani irin bugawa da qarfin gaske,hawayen nan da yake son riqewa suka biyo ta gefan idanunsa. Tsam ya riqeta cikin jikinsa,murya a tausashe ya soma mata magana can qasa

"You will be fine in sha Allah,you will make it in sha Allah.....ki yafemin please sultana....am sorry for my past....a irin wannan lokacin daya kamata na tsaya dake.....amma ya zamana bana kusa dake,bani da ikon bayyana kaina.....ina miki fatan alkhairi soulsis". Hannu bibbiyu tasa tana dauke masa hawayen,tata zuciyar tana son tayi rauni amma tana bawa kanta qwarin gwiwa.

Shi ya karba kayan,yayi dressing nata da kyau,ya tsaya ta bayanta ya cusa doguwar sassalkan sumarta cikin hular da suka bayar. Hannunta ya kama yana juyo da ita idanunsu cikin na juna. Murmushi ya sakar mata,kayan sun mata kyau kamar don kwalliya akayisu

"You look so gorgeous my baby sultana" dariya ta kufce mata

"Still baby ce?,duk da babies din da take bayarwa?"

"Yes.....baby ce,tu continueras toujours à être un bébé pour moi(zakici gaba da zama baby a wajena)".

Abun sai ya burge nurse din,ta saki murmushi sannan ta danyi gyaran murya ganin kamar sun manta da ita a wajen, dukansu suka juya suna kallonta don da gaske sun manta da ita din

"Yallabai ga kujera ko zata hau mu wuce?" Hannu sultana ta saka ta tura kujerar baya,sannan ta maqale a kafadar maina din sosai. Dariya ya saki yar qarama,ya gama fahimtar abinda take nufi,don haka ya waiwaya ya kalli nurse din

"Kije zan rakota yanzu"

"To yallabai" ta amsa masa tana dariya ta tura kujerar ta fice abinta.

Yana riqe da ita a kafadarsa hannunsu cikin na juna har suka is qofar theater room din,ya juyo da ita yayi kissing nata sai ya juya a hankali yana barin wajen. Bata iya taka qafafunta ba har sai data daina ganinsa,sannan ta juya ta wuce ciki tana karanto dukka addu'o'in data sani da wadanda ya gaya mata tayin a dazu.

Ji ya dinga yi kaman dunuyarsa ta tsaya cak,ya dinga ji kamar rayuwarsa ce take a tsaye guri guda,kowanne minti daya daidai yake da awa goma a wajensa,wani irin jira me cin rai wanda tsahon rayuwarsa bai taba jira me wahalar wannan ba.

Duk da qoqarin yakicewa da sukeyi dukkansu kowa hankalinsa nakan dakin theater din yana jiran jin sakamako. Dukkansu counter ne a hannunsu suna ja kadan kadan.

Sanda danjar dake saman dakin ta sauya zuwa launin kore sai dukkansu suka miqe. Duk yadda yaso riqe kanshi kada yayi azarbabi ya zama daga gaba ya kasa. Shine na farko daga bakin qofar,ya hade hannayensa waje daya yaba murzasu,labbansa suna haduwa suna kuma rabuwa yana kiran sunayen Allah duk wanda yazo bakinsa.

A nutse aka bude qofar,nurses biyu suka bayyana fuskokinsu dauke da murmushi

"Le CS a-t-il été complété avec succès ?(an kammala CS din cikin nasara?)" Ama ta tambaya cikin son jin lafiyar sultana din. Kai ta gyada

"Oui madame, les bébés sont en sécurité, leur mère est également en sécurité.(eh madam,jarirai suna lafiya mahaifiyarsu ma tana lafiya)"

"Alhamdulillah" kusan dukkansu suka hada baki wajen fadi

"à quoi a-t-elle accouché ?(me ta haifa?)" Najma ta tambaya cikin zumudi.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 153



Yatsunta uku nurse din ta daga sannan tace

"triplés" Dan qaramin ihu najma ta saki,har cikin ranta tana jin wacce irin me sa'a ce sultana?. Goumar yadan jefa mata harara sanda wajen ya kaure da fadin

"Alhamdulillah"

"Bakiji abinda kowa yake fada ba zaki mana ihu?"

"Yaa goumar......don Allah kayi mana addu'a,Allah yasa kaima hakan take" idanu yadan fiddo yana kallonta,Allah ma yasa qasa qasa tayi magana

"Au daga yaa maina dinne ma?"

"Nidai haka nake gani" ta fadi a shagwabe,abunda ya sanyashi sakin dariyar da bai shirya mata ba.

Daya nabin daya suka shiga dakin bayan an fito da ita,tana daga kwance tana hutawa ruwan da ake qara mata yana shiga jikinta a hankali. Yaran suna kwance daga gefanta cikin gadajensu da aka killacesu da kyau. Kowanne nannade cikin fararen kaya masu matuqar haske da daukan idanu saqar qasar turkey na kamfanin firstcray.

Kiran sunan Allah ne kawai a bakunansu da tsarkake girmansa. Bibi kuka takeyi wiwi ana miqa mata yaran daya bayan daya tana dauka. Biyun cikin blue din kaya wanda ke nuna maza ne,dayan kuma cikin pink color wanda ke bayyanar da jinsin mace ne

"Ko yau na mutu na godewa Allah,sultana da diyoyi har biyar,wayyo Allah na,Allah na gode maka,inama yau ace mohmoud yana da rai?,yazo yaga jikokinsa bayan ya rasa nafessarsa,ko yau na mutu na godewa Allah"

"Haba bibi,ya da fadar haka kuma bayan nima nawa twins din suna tafe?,aisai kin gansu in sha Allah" goumar ya fada yana zolayarta. Fuskarta da hancinta ta goge da tissue din da maina ya warwaro mata,wanda dukka hankalinsa yana kan sultanarshi wadda take bin kowa da idanu,da alama bacci ne yakeson fusgarta

"Kayya goumar,kayya.......sai me yawan rai"

"To Allah ya ara mana" yayi saurin yin addu'ar,wanda duka dakin suka amsa da

"Ameen".

Sanda yaran suka iso hannun ama sai da ta goge hawaye sosai,yau itama dauriyarta ta qare,abun kamar a mafarki,abinda koda wasa bata taba kawoshi ba,wai sultana ce ta zama jini da tsoka kuma zuciyar kafuwar zuri'arta,yau diyar nafessa.....nafessan da aka haifa ita daya qwal......ta haifi sultana ita daya qwal itama yau itace taketa tara mata zuri'a haka. Allah al hakeem kenan......ba ruwansa,mulkinsa da ikonsa ne abun dubawa,d'a guda daya yana iya yara gari guda,duk cikin hikimarsa ce haka. Idonta ta maida ga sultana,sai taga bacci tuni ya dauketa,maina da har yanzu bai sanya yaran a idanunsa ba yana gefanta yana gyara mata rufa.

Sai da suka tabbatar komai yayi settle sannan suka bar asibitin,ama ce kawai ta rage,don bata jin zata iya tafiya. Goumar ya dauki bibi da najma suka wuce gida,amma zuwa anjima yace zai dawo ya kawo musu abinci,sai ya taho da benazeer da batoul dake wajen tanja suga qannensu.

Aikoda suka isa gidan shine ya fara musu albishir,wani irin tsalle da suka hadu suka daka suka daneshi tabbas banda namiji ne da sai sun kaishi qasa. Fafur suka dage sufa sai ya tashi kawai ya koma ga kaisu asibitin,da qyar da lallama najma da tanja suka lallabasu akan za'a dafa musua abinci sai suje akai musu.


"fatabarakallahu ahsanul khaliqeen........maina ya dinga maimaitawa yana juya yaran a hannunshi daya bayan daya.

Tun dazun da bibi ke sambatu akan yaran yana jinta,amma da yake dukka hankalin yana kan uwar yaran bai bada hankali ba. Da gaske ne,komai nashi yaran sun dauke,hatta da yatsun qafarsu irin nashi ne. Zama yayi dirshan yana qare musu kallo,hatta da safar qafafunsu sai daya cire, hakanan hulunan kansu, kasancewar dakin babu kowa saishi kadai da kuma Sultana dake bacci.

Ganin komai yakeyi kamar a mafarki,wai shine baban yaran?,mahaifinsu?,bayan su benazeer su biyu da Allah ya bashi?,me zai cewa Allah?. Zuciyarsa ta karye sosai,yau sultanarshi ita ta zama.uwar 'ya'yanshi,ashe kanshi ya yiwa rainon?,ashe shi yasa yakejin ciwo zafi da radadi a kanta idan tayi wani abu a baya fiye dana kowanne yaro cikin gidan?.

Ta jima da bude idanunta,idanun nata suna kanshi,yadda ya sanya yaran a gaba yana qare musu kallo ya dinga bata dariya. Ta dinga murmushi tana kallonshi tana kuma kallonsu,duk da cewa bata iya ganinsu amma tana jin wata soyayyarsu tana fusgarta har cikin jinin dake zagayawa dukka jikinta.

"Uncle maina" ta kirayeshi da jaririyar muryar nan tata data fusgi hankalinsa. Ya maida dubanshi gareta, kyakkyawan murmushin nan nasa na saman labba suka subuce masa,ya tsareta da idanu yana kallonta,sai kuma ya ajjiye yaran a hankali yana takowa dab da ita.

Hannunta ya riqe yana murzawa a hankali cikin nuna tsananin shauqi da kulawa

"Welcome back honey.......am glad to see you feeling better" ya furta yana ranqwafawa saman kanta a tausashe ya sakar mata lallausan kiss a goshinta. Idanunta ta lumshe hancinta yana shaqar mata tattausan qamshin nan nashi dake saukar mata da nutsuwa cikin kowanne irin yanayi take ciki

"Daddy of five" ta fadi tana kallon qwayar idanunsa da Murmushin tsokana. Qaramar dariya ya saki

"Ke kika maidani hakan matata abar alfaharina". Kafin ta sake cewa komai nurse ta shigo. Ta duba komai,ta tabbatar da komai lafiya sannan tace zata iya tashi ta zauna,a bata ruwan lipton me dumi. Rubuce rubuce tayi,daidai nan ama ta shigo hankalinta itama akan sultanan,ta matsa ta duba yaran sannan ta qaraso wajen nurse din suna magana da ita.

Dole ama ta sakar masa komai ta koma wajen jikokinta

"Wannan karon bai kamata kiyi wahala ba kwata kwata ama,ya kamata kema ki huta da wancan dawaniniyar ta farko da kikayi kadai ta isa,Allah shine zai biyaki" abinda ya dinga fadi kenan cikin ranshi. Sai daya tabbatar ta jita comfortable sannan ya koma ya fara dauko mata yaran yana miqa mata daya bayan daya yana tambayarta kowanne

"Da wa yayi kama?" Duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi take gani bata wani ba. Baby girl din ta qarshe data dauka ya gaza boye dariyarshi,cikin sautin dariya yace

"Ita dinma na dauka zatayi miki kara tayi kamanninki......Allah sarki sai gashi ta zabi daddynta itama" ya qarasa fada da sigar tausayi. Idanu ta zubawa yarinyar sosai saita daga kai fuskarta a narke ta maida kallonta fuskarsa,ta tabe baki kamar zata sakar masa kuka. Wayarta ama ta miqa hannu ta dauka kawai,ta samu tabi ta bayansu ta fice daga dakin tun ba'a saki layi ba tana zaune a wajen.

"Nifa ban yarda da wannan wayon ba,su BB ma duka ai kaine,haka akeyi tsakani da Allah?" Dariyarshi ce ta fito fili,ya hadasu gaba daya ya rungumesu yana dariya

"Karki damu,mu tara Next time,hudu zakiyo dukka masu kama dake" idanu ta waro waje tana fadin

"Kayi haquri uncle maina ban shirya ba" sosai ta sake bashi dariya

"Ba ruwan aliyyu daga Allah ne".

Shigowarsu batoul ya katse wannan ganawar,tunda duka shigo suka durfafi jariran,gaba daya suka hana kowa ya tabasu,akan baby girl din akaso ayi rigima. Batoul tace ita tafi son a bata ita haka benazeer,daga qarshe aka ce batoul taci girma ta barwa benazeer,ta saki kuka tace ita kuwa saidai a bata sauran guda biyun.

"An baki yaaya babba" goumar dake dariyar rigimar tasu ya fadi.

Aiki fa sai meshi inji bahaushe,da gaske raino sukazo yi,da gaske kuma sunyi qanne,don qiri qiri sukaqi matsawa daga jikin yaran,hakanan qiri qiri suka hana a daukesu,kowacce ta saka nata a gaba wai raino takeyi,abun ya dinga bawa kowa dariya. Koda za'a fara gwadawa yaran nono zama sukayi,saida sultana ta zare musu idanu sannan suka fice. Duk saita dirirce,na farko rashin sabo,don zata iya cewa su benazeer ba wani shayar dasu tayi na azo a gani ba,na biyu kuma ga master aliyyu ya tasata a gaba,a lallai sai yaga yadda sultanarshi zata bawa yaranshi nono.

Gaba daya ama taji zaman dakin yafi qarfinta,a ranta ta dinga shawarwarin wucewa ta barshi da matarsa,don da alama ya iya komai,hakanan bataga amfanin zamanta gaba daya cikin asibitin ba,don komai shike yi.

Ko wajen shayarwa dimma shi ya dinga tayata,gyara can tallafe mata can,a haka kowannensu ya dana shan,duk da ruwan bai wani zo sosai ba. Uwa uba dole a hada musu da Madara saboda yanayin aikin da akayi matan bazai bawa ruwan mama damar zuwa da wuri ba.

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 154



Da suka tashi tafiya saida goumar ya lallaba su benazeer ya tabbatar musu kuma gobe xai dawo dasu sannan suka yarda suka bishi. Sai da maina yakai zuciyarsa nesa sosai sannan ya iya tafiya yabar asibitin.

Ranar gidan ama ya kwana,ya kwashi su benazeer su suka tayashi kwana cikin dakin mamarsu. Washegari da wuri suka yiwa asibitin dirar mikiya suka dora daga inda suka aka tsaya.

Kwana uku kacal asibiti ya sallamesu,zuwa lokacin yaran sun sake washewa sosai,kyansu da kamanninsu da daddynsu ya fita sosai,ba macen ba ba mazan ba gaba dayansu MAINA NE.

Kanshi tsaye ya kusa tarewa a dakin,gaba daya sai ya zamana ama ke jin kunyar ma,ta tabbatar sunyi gangancin dauko masa mata da 'ya'ya kam,shi yasa take kaucewa zaman falon,ta tattara al'amarinsu ta damqawa tanja,idan ka ganta dakin sultana to bai iso gidan ba,daya iso komai nasu ya koma hannunshi har sai zai tafi.

A kwana na shida bayan sallar magariba ne,bayan ya gama riqe mata babban daketa rigima,ta goge jikinta sosai,ya tayata ta shirya cikin wani cotton material,ya tabbatar ta zauna taci abinci daidai yadda zai dace da lafiyarta,sai ya aza mata shi saman cinyarta. Tasan me yake nufi,tun tana kunyarsa da nauyin zaro maman a gabansa har ta soma sabawa. Tadan kauda kanta kadan gefe sannan ta ciro ta fara bashi ya soma sha.

Wata nannauyan ajiyar zuciya ya saki yana kallon yaron,ya miqa hannu ya shafa sumarsa me laushi da santsi irin ta jarirai,wadda kuma ta biyo gadon jinin ABZINAWA

"Ku taimaki daddynku ku rage masa shima......Allah bai gama qoshi ba kuka iso" yadda yayi maganar cikin karyar da kai da murya duk sai ya bata kunya ga dariya dake cinta. Zata iya rantsuwa wannan din ba uncle maina bane,ba aliyyu MAYAK'I bane,tana ganin aliyyu haidar kuma maina MAYAK'I ne kadai idan ya fita waje,amma duk sanda suka kebe irin haka wani mutum na daban yake zamar mata

"Zanje naga aba......ya kamata a basu suna,banji yace komai ba" ido ta zaro

"Bloodline......kada fa aga rashin kunya a abun,shi aba yasani ai,har yau bamuyi kwana bakwai ba" sumar kanshi ya shafa

"Allah na kasa controlling kaina,inajin kamar na hadiyeku na huta da azababben son da nakeji ina muku......bari naje dai......ina dawowa....." Har yayi gaba sai ya dawo,ya rusuna daidai kunnenta ya sassauta murya

"Yau dai please adan tanadin min wani abu da zan dan rage zafi kadan" yana kaiwa nan ya sakar mata kiss a wuya daya sanyata jin tsigar jikinta ta zuba. Ta bishi da kallon mamakin meye abun nema a wajenta a haka tana jego?,shi kuwa ko a jikinsa ya wuce abinsa ya fice.

Cikin sa'a ya samu aba a falon yana dinner,ya danji nauyin ganinsa da yayi ya fito daga dakin,sai yadan kauda kai yana sake shafa sassalkar sumarshi. Basarwa aba din yayi yana ci gaba da magana da ama kamar ma bai ganshi ba.

"Bismillah" aba din ya masa tayin abincin. Duk da a qoshe yake sunci abinci tare da sultanar amma borin kunya ya sanyashi zama dole yaja plate din.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login