Showing 210001 words to 213000 words out of 294767 words

Chapter 71 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

ba,baya ga ama da ita kanta mamarsu bayajin anyi wata halitta da yakeso sama da yaran,bai sani ba ko a nan gaba zata haifa masa makwafinsu.

Iya wannan tunanin nasa na qarshe ya haifar da kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Ya lumshe idanu yana budewa,sai ya samu kansa da motsa jajayen labbansa yana fidda addu'a daga bakinsa

"Ya rabb.....kana amsa addu'ar matafiyi......ina roqonka yadda kayimin waccar kyauta cikin ba zata......wannan ma ina roqonka ka azurtani da wasu bayin naka a matsayin diyoyina kuma mallakina" ya qarashe addu'ar yana rataya qaraman jakarshi a kafada,ya kalli gabas ya karanta addu'o'insa ya shafa,haka kawai sai yaji abun ya darsu a ransa,idanunsa suka dinga nuna masa sultanan tashi a matsayin me juna biyu. Murmushi ya kuma saki,shi kansa baisan irin kulawar da zai bata ba,baisan wanne irin soyayya zai gwada mata ba,a karon farko zaiso suyi rainon ciki tare,su kuma raba wuya da dadinsa tare,ya tallafi rauninta,ya goge laifinsa ta hanyar bata kulawar da wata 'ya mace bata taba hasashen samu daga wajen mijinta ba.

Wannan tunanin ya haifar da sakin fuskarsa sosai,wannan daurewar da daskararren miskilancinnan yau kam babu shi. Ya samu suhail tsaye a bakin qofa yana faman duba agogo,da alama jiransa yakeyi. Sai ya bishi da kallo yana mamakin me ya sanya walwala me yawa haka a fuskarsa?.

Idanunsa akan gidan sanda motar ke tashi dasu zuwa airport,yanaso xai kuma so yayi sallama da yarannasa,so amma yana da plan da dole ya tafin ba tare da yayi sallamar dasu ba,dama baya ta sultanar,tunda dukka plan din nata ne dama.



****wunin ranar gaba daya sai ya zame mata tamkar jarrabawa,duk sanda ta zauna shuru na mintu biyu koda zummar tayi wani aikin sai tunaninsa ya addabeta. Kallo na qarshe data yima fuskarsa dake dauke da bacin rai wanda tun bayan dawowarsa bataga irinsa ba. Kalmar data gaya masa na qarshe

"Bana sonka,kuma bazan taba sonka ba" ta tsaye mata cak a zuciya,batasan dalili ba,daga bisani wani sashe na zuciyarta ya fara raya mata rashin dacewar fadin hakan da tayi,wani sashen kuma na nuna mata ba aibu bane,ya shiga rayuwarta da yawa,ya kuma matsa mata.

Wunin duka bata bari sun hada guri da ayana ba,sam taqi yarda su hada waje,yawan kallon da take binta dashi da kuma yadda take yawan sanya mata idanu a dukka motsinta ne bataso,da tunaninsa da matsalar ayana dukka tayi yunqurin zubda su,ta tarkata kayan aikinta da system dinta ta fita can backyard na gidan tayi zamanta,duk kuwa da cewa ba wajen zamanta bane.

Batasan dukka qoqarin da tayi na yakice tunaninsa a banza tayi ba sai da aka kirayi sallar magariba,batasan ya akayi ba ta samu kanta da jiran jin door bell,tun daga sallar magariba har zuwa sanda tayi isha'i. Harta sallame ba motsin wani baqo,ama ce da ayana da yaran a falo suketa sabgarsu. Wanka ta shiga tayi,ta kuma shirya cikin kayan bacci don tanaso tayi bacci da wuri kuma isashe,tana jin jikinta dukka a mace,amma kuma idanun basa jin bacci,ta yanke cewa tana kwanciya wala'alla baccin yazo.

Wayarta kawai ta dauka,don a yadda ta shirya tana gama cin abinci xata dawo dakin ta qarasa aikinta a system dinta,ta jona system din a charge sannan ta fice a dakin. Fitar tata a yanxun ma dai kallon kallo ne. Ta dauke kanta tana jin wani iri da yadda damuwar ayana a kanta yake qara yawa,ama nata tsokanarta ta daki ta fito,ta qarasa dining ta zuba abinci ta fara ci. Batayi wani nisa da cin abincin ba taji ya fita a kanta,ta tureshi ta zuba lemon da aka matse strawberry aka samar dashi. Tanason lemon,ta kuma koya ne wajen ama,amma sai ya zamana har taso tafi ama din iyawa. Ama din irin matan nan ne da sukasan yadda ake sarrafa nau'ikan abinci iri iri,hakanan ba kasafai take shiri da lemukan roba kwali ko gwangwani ba,tafi ganewa tayi da kanta,don haka sultana din ta wannan bangaren ma ta qaru da ita qwarai.

Daki taso wucewa amma saita samu kanta da zaman falon,hankalinta ta raba gida uku,wani yana kan waya wani akan tv,wani akan motsin yaran da suke dan sanyota a rigimar su da basa rabo da ita. Agogo ta kalla,goma na dare a qasar Paris. Ba sabonta bane zaman falo har wannan lokacin,yau din batasan me ya zaunar da ita ba,me take jira?,itama bata sani ba,sai taja sirirj tsaki da ya sanya ayana daga kai ta kalleta,tana jin tsarguwa har ranta,tana jin kamar da ita take.

"Ama zan wuce ciki sai da safe" dan murmushi ama din ta saki

"Kinyi qoqari ma yau ai,Allah ya bamu alkhairi"

"Ameen" ta amsa tana wucewa ciki bayan ta amsa goodnight din da su benazeer sukeyi mata.

Ta kusa sha biyu na dare amma ba bacci a idanunta,a haka ta tattara komai ta kwanta.

Kamar jira kwanyarta takeyi ta kwanta din sai komai ya soma dawo mata,dukkan wata daqiqa da mintuna da suka taba shude musu a tare da juna. Ta bude idanunta ta kuma kulle yafi sau a qirga,taja tsaki har babu adadi,ta jawo pillow cikin jikinta tana qanqameshi da kyau,sallah takeso ta tashi tayi amma 'yar banzar kasalar da batasan dalilin samuwarta ba a jikinta ta hanata motsi,sai taji gaba daya dakin kamar ba nata ba,ta sake rufe idonta tana ambaton sunan Allah.

_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 112


Kadan kadan tana motsa bakinta cikin addu'a har wani bacci me dadi yazo ya saceta.

Tun baccin nata baici talata da laraba ba ta fada duniyarshi......duniyar mafarkinsa,duniyar ds bataga kowa a ciki ba daga ita saishi,saman wata tattausan shimfida ta wani lallausan carfet me gashi a jikinsa sosai,daga shimfidar har zuwa tufafin jikinsu dukka farare ne. Daga gefensu kuma yara ne qananu suketa wasa,a qalla sun kusa goma sha biyu,ba fuskan wanda ta gane a ciki,daga benazeer sai batoul kadai. Guje guje suketa yi a tsakaninsu,daga baya kuma suka samu waje suka zauna dukkansu suka zuba musu ido, benazeer da batoul kuma suna can ta bayansu a zaune. Shi ya maida dubansa kanta,sai ya sakar mata wannan murmushin nasa data sanshi dashi a zahiri,ya miqo mata hannu yana cewa

"Zo kiga......ke suke kalla,wai kaman kina fushi" ya fadi yana dage mata gira. Da farko harta noqe kafada,sai kuma ta waiwaya tana duban yaran. Har yanzu ita suke kalla,zuwa lokacin kuma fuskokinsu sun sake nuna damuwa da bacin rai sosai,sai ta miqa masa hannun ya miqa mata nasa ya jata zuwa cikin jikinsa,daidai nan kuma dukka yaran suka bace,daga ita saishi a wajen. Hannu ya zura cikin rigarta ya fara mata mata tafiyar tsutsa, abinda ya sanyata kasa jurewa ta riqe hannunsa suna dariya sosai,sai ya miqe yana dagata cak,yana daga qafafunsa sai kuma yayi tuntube,suka tafi luuu dukka zasu zube saman farin rairayin dake wajen......

Firgigit ta farka,ta miqe zaune da hanzarinta tana dube dube cikin dimlight na dakin,hannu ta miqa ta kunna fitila,haske ya wadaci dakin. Ba kowa a ciki,daga ita sai ita kaman yadda ta kwanta,sai taja wani irin dogon numfashi tana fesarwa,sannan ta sanya dukka tafukan hannunta tana lullube fuskarta tana kuma jin damshin dake goshinta da alama gumi takeyi.

Ta jima zaune a haka tana kiran

"Ya hakeem" qasa qasa sannan numfashi da bugun zuciyarta ya daidaita,ta daga kai tana duban agogo, lokacin sallar asuba ya kusa saura kadan,hannunta ta saka tana ture duvet dinta tasoma yunqurin sauka,lallai ba abinda ya sanyata yin mafarkinsa sai kwanciya da tayi da tunaninsa cikin ranta,to amma wai meye damuwarta dashi?,me yasa cikin lokuttan komai yake son sauyawa?,kwanyarta ke qoqarin damuwa da mummunan dabi'ar yawan tunashi?,bayan bataga wani dalili da zai sanyata hakan ba?.

Alwala ta daura tazo ta gabatar da nafilfilu,tayi shuru saman abun sallar tana jiran lokacin assalatu ya qarasa shiga,amma kuma mayyar zuciyarta da mayyar qwaqwalwarta shi din suke sake tuno mata

"Why?" Ta tambayi kanta, yanzun nan fa ta gama addu'ar yayewar hakan daga gareta amma kaman bata roqi komai akan hakan ba?,kaman qari ta roqa ayi mata?.

Idanunta da suka rusuna saboda rashin samun wadataccen bacci ta daga a hankali tana kallon window dinta, window din dake duban fuskar gidan nashi,tayi tsai da idanunta ata wajen,kamar wadda ke fatan ganin gilmawa ko motsinsa

"Rabbi yassir wala ta'asir,wa tammim bilkhair" ta furta a hankali tana maida idanunta ta lumshesu,daidai lokacin wayarta ta kada alarm na kiran sallah,saita miqe kawai tana wasu addu'o'i cikin zuciyarta.


*_BAYAN AWANNI_*


Tsaye take gaban madubi tana duban fuskarta kamar wadda aka bawa contract na kallon kanta da kanta,yadda fuskarta take qara glowing yake bata mamaki,itadai tasan products din da take amfani dasu sune dai,bawai ta canza wasu bane,paris kuma zamanta a cikinta wancan karon ai batayi kyan da tayi wannan karon ba,meye banbacin wancan lokacin da yanxu?. Ajiyar zuciya ta saki,ta kasa gano komai,kawai dai taji dadin dogon baccin data samu,don badon Allah ya taimaketa ta samu baccin ba tabbas da yau din tasan akwai matsala. Qarar wayarta ya sanyata barin gaban madubin,ta dauki wayar tana duba me kiran,sai ta samu waje ta zauna tana amsa wayar.

Kafin ta kammala kiran tanja ta shigo dubata inji ama,saita yanke kiran tana bin bayan tanja.

Ba kowa gidan, benazeer sun tafi school,ayana itama ta tafi nasu school din ta qarasa abubuwan da batayi ba.

Tun abincinta na safe tanja ta dumama mata ta dawo mata dashi,ta jawo gabanta ta fara ci,to amma kuma abincin kwata kwata bai mata dadi ba,ba taste haka take jinsa,dole ta haqura dashi tana maida tray din gefe.

"Yadai?" Ama da take ganin sultana din wani iri iri haka ta tambayeta

"Ba komai,na qoshi kawai ama" ta fadi tana dubanta

"Ai an kusa gama lunch,saikici,dumame breakfast dama ya zaiyi miki dadi?"

"Okay" kawai tace. A maimakon komawa daki da takeyi kamar yadda ta saba,saita samu kanta da zamewa nan cikin kujera ta kwanta lamo tana taya ama kallon News,duk da bawai burgeta labaran tashar yakeyi ba,tunda labarai ne na duniya,hasalima bata fahimtar me suke haskowa,tana dai jin ama time to time tana salati ko qorafi. Wayarta da kuma bakin qofar da take yawan kalla sune suka janye hankalinta.

Mintuna suka yita shudewa suna bada awanni amma tana kwancen a nan,can qasan ran ama tanata mamakin abinda ya zaunar da sultana din,tunda zaiyi wuya ka shigo gidan ka sameta a falo.

Door bell na kadawa gabanta ya yanke ya fadi,ta lumshe idonta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,lamo tayi taqi tashi,don zuciyarta na raya mata shine,har sai da tanja ta fito ta bude qofan sanda ama ta qwala mata kira tana gaya mata ta bude din sultana bacci ya dauketa.

Qasa qasa ta bude idanunta sanda su benazeer ke shigowa da school uniform,sunata fada akan wani dan qaramin notebook. Soror tayi,haka kawai kuma tana jin ba wai,bata tsammaci su bane,kawai zuciyarta tana raya mata shine,daya zamana kuma bashi din bane duk sai taji abun wani iri.

Maida idanuntan kawai tayi ta sake rufewa,a hankali a hankali tun tana jiyo hayaniyarsu ama nata fama dasu har wani bacci ya sake saceta. Bata farka ba sai da aka sake buga qaraurawan. Ta bude idanunta tana kallon tanja dake bude qofar. Ayana ce,tanja ta matsa ta bata waje ta shigo,saita zube takardun hannunta nan tsakiyar falon tana kallon ama a marairaice

"Ama aikin babbane,ba sauran abubuwa da bas qarasamin bane,ya maina babu abinda yayi min,ashe yace musu ne zanzo nayi komai da kaina don nasan darajar karatun" ta qarasa fadi kaman zatayi kuka

"Yanzu idan bai tausayamin ba waye zai tausayawa?,sannan ama harda samarmin wajen zama,ya barni mana na zauna a nan" ta qarasa maganar muryarta na nuna bacin rai. Kai sultana ta dauke,don dukansu tasan ba lura da farkawarta,sai kawai ta maida idanunta ta kulle ba tare da tace komai ba, saidai kuma kunnuwanta suna jin komai.


_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 113



"bai kyauta ba..... tun farko sai yayi bayani baiyi komai ba ki samu ki shiga da wuri ki gama aikinki.......har yanzu haidar yana nan da halinsa.....amma kuma na tabbatar tunda yafiso ki zauna cikin dalibai yana da dalilin hakan,nasan halinsa sarai" y ayana tayi tana sake ajiyar zuciya,ta dauka ama zatabi bayanta ne,don kwata kwata batason tayi nesa da gidan,ko ba komai idan tana zaune a nan din hakan zai kawo kusanci tsakaninsu,kusancin kuma da take fata ya tabbatar mata da burinta. A yanzun tana gayawa kanta tayi gefe da matsalar sultana,kowa yaji da kanshi kawai,kuma wanda ya iya allonsa ya wanke.

Bata sake cewa komai ba,sai falon ya danyi shuru sai hayaniyar yaran daketa hada litattafansu na islamiyya,don malaminsu dake daukarsu karatun addini yana dab da isowa. Sosai suke karatun addini ama bata bari sun zauna haka ba,kudi ta kashe me yawa take biyan malamin,yanzu haka suna da haddar izifi goma goma cas a kansu. Yaran nada wani irin budaddiyar qwaqwalwa da kuma baiwa data sanya ama tsaiwa tsayin daka akan karatunsu na addini,don duk bokonta bata yarda da tsurar karatun boko ba,wannan ya sanya cikin family house na mayaki komai na ama dana yaranta tun usul ya fita daban.

Ama ce ta miqe ta wuce ciki saboda wayarta dake ringing,wannan ya bawa sultana damar bude idanunta a hankali ta kuma miqe ta zauna sosai, benazeer da batoul suka matso suna cikata da surutun sun dawo tun dazu tana bacci. Qaramin murmushi ta saki kawai tana shafa kawunansu.

"Ga ya shaik can ya qaraso" ta fadi musu sanda bell din ta kada

"Allah ya bada sa'a" ta fadi zuciyarta cike da qaunarsu sanda suke rige rigen zuwa su bude qofan. Suna fita ta miqe tana wuce dakinta,ayana ta bita da satar kallo. Duk yadda takeso ta amintar da kanta ta daina jin d'ar game da sultana din amma ta gaza haquri,muddin xasu hada inuwa daya koda sultana cikin kayan bacci take sai taji ta raina kanta,duk kuwa da yadda qawaye da samarinta ke kambama kyanta da ajinta,bata tana tunanin zataga wata diya mace taji ta raina duka wadannan abubuwan nata ba.

Duk yadda batason zaman falon ko don ayana amma ranar a falon ta wuni. Dukka hankalinta yana kan qofa da duk wata bell da za'a kada don neman izinin shigowa gidan,batasan tana yi ba ita a karan kanta sai daga baya ta fahimci kamar akwai wani abu da takeyi out of dabi'arta data saba da ita a gidan. Ta lalubi kanta kaf don neman ba'asin wannan qwaqwafi da takeyi amma ta rasa amsa,koda wani sashe na zuciyarta ya gaya mata nashi hasashen sai ta bashi amsa da

"Wannan babbar qarya ce!" Abinda ta gayawa kanta da kanta kenan. Ta aza hakan kawai akan ta gaji da zaman waje daya,tana buqatar sabbin mutane da sabon waje,saidai kuma har a cikin zuciyarta wannan dalilin yaqi gamsar da ruhi da kuma zuciyarta.

Har fargabar zuwan dare ta dinga yi,don batasan yadda zai risketa ba. Daren jiya tasha wahala sosai,bayan kasalar jiki zuciyarta da ruhinta dukka tamkar jinya sukeyi,bata da qarfi a jiki da kuma zuciyarta gaba daya,wannan ya sanya daren ranar yafi zuwa mata da tsananin da yafi na jiya. Don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login