Showing 195001 words to 198000 words out of 294767 words
Chapter 66 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
sukayi suka gama har suka rabu.
A daren yau din saita samu kanta da sauraren bakin qofarta wai ko zataji kusurkusur ko motsinsa,ta dinga juyi saman gadon ita daya,daga hannun dama zuwa hagu. Bacci taketa buri da fatan tayi amma yaqi zuwa mata,gefe guda ga wani muguwar kasala da mutuwar jiki data saukar mata,sai kace wadda aka yiwa dukan tsiya,ko ina na jikinta ta dinga ji yana mata ciwo,duk burin da taci nayin bacci isashe don ta samu gabatar da program dinta a gobe cikin karsashi da fara'a dukka ya zagwanye. Bata taba ji jikinta na mata ciwo irin haka ba,ba kuma wai bata da lafiya bane,batasan meye dalili ba. Wannan abu biyun su suka taru sukayi mata rubdugu suka nakasa baccinta,don ba itace bacci ya dauka ba sai da biyu na dare ya raba.
Da sassafe taso fita a washegari wai ta shammaceshi kaman wancan karon,to saidai yanayin da takeji jikinta na kasala ya sakata shiryawarta dama komai nata ya zama a sanyaye. Koda ta buda break din da tanja ta hada mata sai taji cikinta ya cushe ta kasa ci,don haka taja tissue kawai ta goge hannunta,ta dauki key dinta da hand bag tayi hanyar fita,daidai sannan ta kalli agogo. Duk saurintama ya tashi a banza,don a irin wannan lokacin yake shigowa gidan. Amma kuma sam bataga alamun gidan a bude ba ko kuma da mutum a ciki.
Tana shirin tashin motar kiran bibi ya shigo,ta zauna daga gaban motar tana amsa wayar, jifa jifa idanunta nakan qofar gidan,tamkar wadda ke tsammanin fitowar wani ko wata,saidai qasan zuciyarta ta tabbatarwa kanta babu wanda take tsimaye. Sukayi sallama da bibi,ta ajjiye wayar a gefanta tana sake kallon qofar gidan,sai taja siririn tsaki ta tayar da motar a kasalance tana barin layin nasu.
Sanda ta isa tv station din ta samu ma'aikata sosai,don yau batayi sammakon da tayi jiya ba,duk inda ta gifta saita gaisa da mutane,batasan da wanne irin farinjini ta shigo tv station din ba,qauna suke nuna mata sosai,duk kuwa da cewa ba ita daya bace 'yar Africa a wajen.
Bugun zuciyarta ne ya dinga qaruwa sanda take lalubar key tana qoqarin bude office din,sai takeji har cikin zuciyarta kaman zata taras da wani a cikin office din,kamar wancan lokacin......kamar waccar ranar.....
"Maina?" Wata zuciyar ta tambayeta
"Ban sani ba" tayi saurin amsawa kanta da kanta rana murguda baki kaman ita da wani ne.
Sanda qofar ta bata sautin ta budu daita aza hannunta saman qofar tana jin yadda bugun zuciyarta yake qaruwa,sai data kulle idanun nata taja numfashi da kyau sannan ta tura qofar a hankali ta sanya qafafunta.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 104
Dukka idanun ta wara sanda ta shiga office din, zuciyarta na bada sautin bugun da har ya take iya jinsa ga kunnenta. Office din fetal yake,babu kowa babu ma alamun an shigo tun bayan gama gyara mata shi da akayi. Sosai ta wara hancinta wai ko zata jiyo wani baqon qamshi daban,ba qamshin komai saina freshner da ake mata using nata cikin office din. Jinta tayi kaman an buge mata gwiwarta,haka kawai taji ta sare,qwarin gwiwarta ya sake raguwa,dannkarsashin data samu daga qasa zuwa hawowanta sama dukka babu ya zagwanye.
Jikinta a sanyaye ta isa cikin office din,ta ajjiye tarkacen hannunta taja kujera ta zauna tana maida numfashi. Ta sake bude idanunta,sai suka sauka saman kujerar,inda ya zame duk kayan jikinta da inda ya zaunar da ita,tsigar jikinta tayi wani irin tashi,ta runtse idanunta tana kiran sunan Allah hadi da lullube fuskarta da tafin hannunta. Sosai takejin zafi cikin zuciyarta,tayi imani yarinyar ce ta tareshi,qilan ma yanzun haka suna tare,ai hakan bai taba faruwa ba sai yanzu,sai yanzu da tazo qasar.
"Idan yazo meye zaiyi miki?,ina ruwanki dashi?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar
"Aifa" ta sake bawa kanta amsa. Knocking din da akeyi ya sanyata miqewa tana nufar qofar,gabanta nadan faduwa tana tunanin ganin wani abu da zai wanke mata wannan kai kawon da zuciyarta keyi. Saidai kuma sanda ta bude din da
Dioura ce da fuskar nan tata ma'abociyar fara'a. Qoqari tayi ta tattaro dukka fara'ar dake kan fuskarta dama qasan zuciyarta tana mata sannu da zuwa cikin harshen abzinanci. Ta amsa mata itama ta bata waje ta shigo.
Shigowar dioura ya debe mata kewa sosai,qarasa tattaunawa da kuma tsara daukan program din suka qarasa yi.
Ita daya cikin dakin sauya tufafin na musamman da aka tanadar mata a cikin office dinta,tayi wani fitinannen kyau cikin laffayar me azabar kyau da tsada,idan ka ganta a sannan zakayi tsammani shuwa ce,duk suturan data sanya yana karbarta ainun haka jikinta yake.
Fuskarta take kalla,tanason bawa kanta qwarin gwiwar shiga studio din. Ta jima tana zumudin randa zata gabatar da al'adun kanuri saboda yadda abubuwansu suke burgeta,yau ranar yazo,amma kaf ta rasa duk wani walwala da nishadi da take da buqata. Ga kasalar da take sake saukar mata,tana jin kanta da idanunta tamkar wadda ta tara bacci na shekaru aru aru a kanta.
Siririn tsaki taja sanda akayi knocking qofar dakin,sannan kuma tace
"Ina fitowa" ta sake juyawa tana gyara fuskarta,tana ambaton sunan Allah a hankali a hankali wai ko zata samu sassauci daga dukkan abinda takeji din.
"Wow......bansan wanne shiga bane yafiyi miki kyau,na last week ne ko na wannan satin?" Dioura ta fadi da kwantaccen murmushi da gurbatacciyar hausarta tana kallon sultana. Dan murmushi da yafi kama da na yaqe ta saki tana maida abubuwan hannunta data cire cikin jaka.
Har sun soma ficewa ita da dioura saita tsaya,tana buqatar wani abu da zai dawo mata da karsashinta cikin jikinta,idan ta fita a haka tabbas ba zata taba bada abinda program din yake buqata ba. A nutse ta koma ta zauna,ta fidda wayarta ta soma kiran layin ama.
Dab da zata katse ta daga da sallama a bakinta
"Good morning ama"
"Morning sultana,ban tashi da wuri ba yau din,tanja tacemin har kin wuce"
"Eh ama......"
"To ma sha Allah.....ina fatan komai lafiya?" Ta tambayeta saboda yanayi muryarta daya bata kaman akwai wani abu
"Lafiya alhamdulillah,zan shiga program.......ina buqatar addu'a" ta qarasa fada muryarta na danson yin rawa. Tausayinta sai ya saukarwa ama,ta dinga ji a ranta inda mahaifiyarta tana raye tabbas ita zata kira ta nema addu'a kaman haka,maraici ba dadi komai gatan da zaka samu,gatan uwa daban yake,mahaifiya kuma ba madadinta.
Sai muryar ama da jikinta dukka sukayi sanyi,cikin nuna kulawa tace
"Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya.......zaki magana dasu batoul ne?"
"Eh ama" ta fadi qasa qasa cikin dan jin nauyi
"Gasu" ta fadi tana miqawa yaran wayar.
Da zumudinsu suka soma magana da ita don yau basuje school ba saboda jikin benazeer,koda batoul taje ita daya ba lallai ta zauna,shi yasa ama tace a barsu duka,ta dinga murmushi tana biye musu,a qalla sun kusa mintuna goma da ita tana biye dasu kafin tace su bawa ama wayar sukayi sallama.
Iska ta furzar daga bakinta tana kallon fuskar wayar,ta samu relief kaso hamsin cikin dari,amma ta rasa gane dalilin da ya sanya wannan gurbin ya gaza cikewa,ta rasa me yasa ta kasa samun satisfaction dari bisa dari?. Idanunta ta rufe tana karanto addu'o'i,tana jin zatayi managing da 50% din data samu,don haka ta miqe tana fita daga office din.
Ita kadai tasan yadda tayi forcing kanta tayi program din,a fuska ne kawai take da karsashi da kuma kuzari,amma cikin zuciyarta da gangar jikinta wani irin emptiness take ji.
Ita daya ta koma office ta zare dukka kayan data gabatar da program din dasu duk da cewa sun zama mallakinta. Haka kawai taji bata da buqatar barinsu a jikinta,ta maida kayanta data taho dasu ta koma saman sofa tana maida numfashi. Kanta ta juya tana kallon agogon wayarta,ta gama abinda ya shigo da ita gidan don haka tana tunanin komawa zatayi gida,don kasalar dake jikinta koda ta zauna ba zata barta tayi komai ba. Komai nata ta tattare tayi sign-in ta wuce parking lot,ta zuba duka tarkacenta cikin motar ta shiga ta tayar da ita ta fice daga gidan.
^^^^Motsa jiki yayi a safiyar na tsahon mintuna talatin da biyar,sosai yake jin kanshi fresh a safiyar,don jiya ya samu yayi bacci isashe ba laifi. Direct ya wuce toilet yayi wanka,ya dawo ya shirya kansa cikin long sleeve shirt da dogon trouser. Yayi wani fresh sosai kaman yadda zuciyarsa yake jinta da sauqin damuwa a ciki. Ta falo ya dawo yana duba abubuwan da suhail yayi kafin ya fita a gidan,bai jima ba yaron dake musu share share ya qaraso,sai ya matsa bakin window ya bashi space don ya gyara gidan.
Idanunsa saman gidan,yana kallon abun hawa aba,abinda yake tabbatar masa da aba bai fita ba kenan. Yanason shiga yaga batoul da benazeer,ya kuma gaida ama,amma bayason aba din yasan da wanzuwarsa a unguwar,har yanzu wannan lokacin baiyi ba, yafison yayi nesa dashi,ya tabbatar hakan zai sanyata yaci gaba da jin kewarsa.
Idanunsa ya mayar side din window dinta,idan ya rantse bazaiyi kaffara ba ya tabbatar ta wuce wajen aiki ne,barin hali sai mutuwa,sai kuma yanzun da ya tasamma sauyata. Murmushi ya kubce masa sanda ya tuna yanayinta a jiyan,indai har da gaske ne abinda yake gani cikin idanunta kishi ne hakan yana nufin akwai soyayyarshi koda bame yawa bace a zuciyarta?. Ajiyar zuciya ya saki,yana jin kewarta sosai cikin kowacce jijiya dake dauke da alhakin zagayawar jini a jikinta,to amma yanajin dole yadanyi step down kadan don yayi taste akan irin nata soyayyar a kanshi.
Matsawa yayi daga jikin window din sanda wayarsa ta dauki tsuwwa,ya juya a hankali yana nufar wajen wayar,a yadda ya tsara din yau gaba daya bazai fita ba saboda shirye shiryen tafiyar da zasuyi shida suhail na sati uku. Haka kawai bayason yin tafiyar,don bayason yayi nesa da ama da twins dinshi,to amma kuma hakan ya zama dole,don daddy ya nema alfarma a wajensu su wakilceshi,daddyn kuma yafi qarfin kowacce kalar alfarma a wajensu.
Tunda ya fita ya dawo ma bai duba wayar ba sai yanzun,tarin miscals ya samu,ciki harda na ayana wanda ya kusa guda goma. Yadan tsuke gira kadan,yana shirin yayi deleting na miscals din wani kiran na ayana ya sake shigowa.
Hakanan ya daga ba don ranshi yana so ba,surutunta har hawan masa kai yakeyi,baisan inda ta gaji surutu ba,tunda dai shi yasan uncle tahir ba haka yake ba.
Da dakakkiyar muryar nan tashi yayi sallama,sallamar data sanya ayana shiga taitayinta,murya ce me ratsa zuciya da qwaqwalwar wanda ake magana dashi
"Good morning yaa haidar"
"Morning,kina lafiya?"
"Lafiya Lau nake,na kira ne na gaya maka yanzu haka ina airport,yau ne taho wana,transit daya zamuyi kuma,ina saka ran nan da wajen dare anan paris in sha Allah ina Paris"
"Yayi kyau,Allah ya tsare hanya....."
"Amma ya haidar......baka manta dai da alfarman da daddy ya nema min ba ko?"
"Name?" Ya tamabayeta don shi bilhaqqi ya manta
"Habba ya haidar........daddy fa ya gaya maka,kaine wakili na......ya wakiltaka akan al'amurana a cikin Paris"
"Oh......,karki damu,muna tare da ama,kuma nasan She will do her best to take care of you.......ina da harkoki da yawa,ba komai ne zan iya concentrating akai ba" shuru ta danyi jikinta yana sanyaya,anya abinda take gani me sauqi ne zayazo da sauqin kuwa?.
"I know yaa haidar....but kulan mace da namiji ba daya bane......"
"She's the one who raised me......so that tana iya kula da 'ya'ya dari ma" ya datsi numfashinta. Yanajin yadda ta aje numfashi,sannan muryar qasa qasa tace
"It's okay,saina qaraso"
"Safe flight"
"Thank you" ta amsashi tana jin dadin fatansa na qarshe a gareta.
Iska ya furzar,ya soma gajiya da wadannan abubuwan,ga laila sai kuma ga ayana ta taho......ayana me sauqi ce a gareshi,laila dince yake komai da takatsantsan a kanta,ta yadda komai idan ya tashi qarewa tsakaninsu za'a yishi cikin girma da mutunci. Wayarsa ya mayar aljihu,ya koma bakin window din ya duba,ba motar aba,hakan kuma yana alamta mishi ya fita kenan,don haka ya koma ya zura lallausan fluffy dinsa yana fitowa daga gidan,yana buqatar ganin ama.
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 105
Ya samu qofan a bude,don haka ya turata kawai ya shiga da sallama. Suna saman carfet sanye da wasu pink loungwear,an raba musu sumarsu me tsaho gida biyu,kowacce an kameta da pink din ribbon da ya dace da kayan jikinsu,sun yiwa building blocks baja baja a falon sunata qoqarin hadawa. Ama na zaune saman kujera,gabanta dan madaidaicin table ne da system akai,da alama wannan lissafe lissafen nata da ya santa dashi shekara da shekaru takeyi,akwai madaidaicin tray daga gefanta,da alama late breakfast zatayi ko kuma takeyi din.
Building blocks din dake saman cinyarsu suka watsar sunata qoqarin tararsa. Tsaiwa yayi yana kallonsu murmushi ya subuce masa,kafin su iso sai ya goce,sannan kuma ya miqa hannu ya dauki benazeer. Baya batoul tayi tana kyabe baki alamar zata saki kuka
"Daddy nifa?"
"Benazeer ce bata da lafiya,baki gani ba har wadannan kumatun sun zazzage?....." Ya fada yana jan kumatunta wadanda da gaske sundan ragu,sai kuma ya dora da cewa
"Kin manta kuma ke din babbace,qanwarki ce ita fa" hakan daya fada sai ya faranta mata ta fara tsalle,ya saku murmushi ya duqa yana miqa mata hannunsa,saita riqe ta tattakashi itama ta haye kafadarsa suka nufo ama,wadda a haka zaka dauka batasan me yake faruwa ba,saidai tana karance dasu. Duk sanda irin hakan zata faru ita kadai tasan farincikin da takeji, addu'a daya takeyi Allah ya sanyaya zuciyar sultana,tana da matuqar buqatar tarin jikoki,musamman da bata haihu da yawa ba,takanji kamar ta yiwa almu da saddi aure,saidai sunyi qanqanta sosai,amma tana ji a jikinta ko shekarun maina ba zasukai ba zata aurar dasu da ikon Allah.
Da qyar suka bari ya gaisa da ama,suja tattaro masa blocks din sukace lallai shima ya hada nasa aga waye zaiyi abu me kyau. Yanata murmushi ya fara diban nasa,yana sane ya dinga hada shirme sunata masa ihu,sai ya narke fuska shima kaman qaramin yaro ya dubi ama
"Ama kinga abinda sukema danki ko?" Tun bata kulasu har dole ta dinga sanya baki a ciki,ita ta dinga raba maki ba yadda ta iya. A daidai lokacin qararrawar qofa ta buga,tanja ta baro kitchen zata bude yace ta koma taci gaba da aikinta,ya tashi yana gyara hannun rigarsa daya tattare ya nufi qofar.
Bata kawo komai ba sanda ta danna bell,don haka tana tsaye sosai tana jira a bude mata,duk ta qagauta ta qarasa cikin gidan,kwanciya kawai take da buqatar yi ko zata samu mode dinta da abinda takeji a jikinta ya koma daidai.
Shi da ita duka basu tsammaci ganin juna ba,idanunsu suka sarqe waje guda,kowannensu sai ya kasa janye nashi idon,kamar masu kallon quda