Showing 99001 words to 102000 words out of 294767 words

Chapter 34 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

Tsam almu ya tsaya daga bakin qofa ba tare da maina ya buqaci hakan ba, cikin jikinsa yaji bazai iya jerawa da maina ba,yana jin bazai iya jure hukuncin kallo kadai da maina zai iya fara maraba dashi daga dukka iyayen nasu ba. Bai waiwaya ya kalli almu ba,kaman ma baisan almun ya tsaya ba ya doshi babbar qofar falon. Ya tube tsadajjen sau cikin qafarsa,ya sanya qafafunsa dake saye da safa cikin falon yana janye labulen gefe bakinsa kuma dauke da cikakkiyar sallamar

"Assalamualaikum warahmatullah". Wani dogon numfashi almu ya saki yana qamewa jikin bango gami da runtse idanunsa. Ya rantse da Allah.....tabbas inda shine ya maina bazai iya sanya kansa ga falon nan ba,ya rantse da Allah bazai iya fuskantarsu ba saidai idan tara tara za'a yi masa,wanne irin qarfin zuciya dakiya da jarumta ke gareshi?,ko kuwa dai baisan girman laifinsa bane a garesu?.

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" sukayi hadin bakin amsawa,saidai kuma ba dukkansu bane suka samu cikakkiyar lada da daman amsa sallamar.......kamar yankewa zubar ruwan sama sauran amsa sallama ta tsaya saman harshen aba......yayin da oncle umar shima sauran furucin suka tsaye masa cak. Wani irin rawa zuciyar aba tayi bayan daukewar sallamar daga bakinsa,a nutse kuma sai ya dauke kansa daga kallon qofar falon ya maida ga takardar kilishinsa ya soma qoqarin nannadeshi.

Cikin qasa da second biyu da shigowarsa dakin da fitar sallamar daga bakinsa idanunsu suka gauraya waje daya. Haduwar idanun data zame musu wani abu na bazata dukkaninsu. Batayi zaton ganinsa ba.....baiyi tsammanin samunta a wajen ba......hasashe ko tunaninta bai kawo.mata ganinsa a nan kurkusa ba. Wani wawan birki taja a matuqar Hautsine,a hankali taji hankalinta yana neman firgita,nutsuwarta na shirin yin qaura daga ganganr jikinta. Wannan haduwar dai dai take da MUGUN GANI a wajenta...... mummunar rana da kuma mummunan lokaci......maina cikin gidan?,a wannan daren?,a kuma irin wannan lokacin?. Tambayoyin da suka kusan tsayar mata da gudun numfashi tsakanin qirjinta da zuciyarta zuwa hunhunta kenan.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 53


Dukkan zagayayyun lion eyes dinnan nasa ya kafeta dashi. Karon farko......lokaci na farko da sukayi gaba da gaba dashi. Karon farko yau gashi tsaye a gabanta,a gaban wata sultanar da ko kusa ko alama baiga tayi masa kama da wancan sultanar da ya bari shekaru biyar baya ba. Wani irin qaton abu yake ji yana gangarowa daga zuciyarsa me matuqar nauyi yana kwaranyewa zuwa sassan jikinsa.

Da wani zazzafan karsashi ta janye idanuwanta,wata irin wuta na ruruwa cikin qahon zuciyarta. Har tsakiyar qirjinta takejin wani irin zafi yana sauka,ta soma takawa cikin bawa kai qwarin gwiwa ta kewayeshi tana nufin fita daga dakin, zuciyarta na jaddada mata bata da hadi dashi,ruhinta na gaya mata cewa bata sanshi ba......bata ma taba saninsa a rayuwarta ba,tana kuma sake bawa kanta yaqinin bata da wata alaqa dashi.

Dukkan kowanne sashe na zuciyarsa muradin binta da kallo yakeyi,abinda ya gani qasa da second goma cikin qwayar idanunsa ya matuqar razanashi,to amma sanin da yayi cewa abinda ke gabansa da kuma mutanen dake zaune cikin falon din dai dai yake da tunkarowar yaqi cikin rayuwarsa sai ya tattara dukka wani abu daya taso ya tsaye masa a wuya yayi musu muguwar hadiya,hadiyewar daya haifar da ciwo a qirjinsa da kuma jirkicewar ainihin launin qwayar idanunsa.

Tamkar gagarumin me laifin dake takawa zuwa gaban alqalin da zai yanke masa hukuncin mutuwa ko rayuwa haka yaci gaba da daga qafafunsa da kuma saukesu yana tunkarar mutanen da ya tabbatar suke da matsayar ci gaba da fuskantar rayuwarsa a yanayin daya kamata ko akasin haka. Dukkaninsu idan ka dauke mutum daya tal wato ABA idanunsu yana kanshi,kowa yana dubansa ne da zallar tarin mamaki da kuma bazatar bayyanarsa a irin wannan lokacin.

Dai dai sanda ya zube a tsakaninsu aba ya miqe,ko sau daya ko alama bai nuna yasan da shigowarsa ko wanzuwarsa cikin dakin ba

"Issoufou idan kun gama ka sanya yara su shiga dakincan su fidda komai,zan din shiga ciki na kwanta goben ina tunanin zan riga kowa fita don ina da baqi a gidan baqi na". Ba maina kawai ba,dukkansu sunsan wannan miqewar da yayi bawai ya yita bane saboda yana nufin abinda ya fada din,ya yita ne kawai saboda baya buqatar hada numfashi da maina,ya yita ne saboda isowar maina gurin,don a zaman tattaunawar da sukayi duka duka basuci koda rabin abinda suka zauna su tattauna saboda shi din ba.

Kaman yadda ya yiwa ama haka ya miqe cikin zafin nama ya tari gaban aba sannan ya sulale a gaban nasa.

"Waye wannan?,ku gaya masa ya matsa daga gabana!" Aba ya furta da wata irin kakkausar murya da duk sanda ta fita da irin wannan sautin......duk wanda ya sanshi to yasan cewa yakai maqurar fushinsa kenan

"Don Allah aba.....don girman Allah......!" Bai barshi ya qarasa magiyarsa ba sai saukar zazzafan mari da sautinsa ya karade falon. Kaf dinsu jini ya dauke a jikinsu,don ba wanda ya tsammaci irin wannan zazzafan hukuncin haka tashin farko daga wajen aba,kasancewarsa mutum ne bame yawan kaiwa koda yara hannu ba bare maina da a yanzun ya zama cikakken mutum

"Kaci gaba da tsayamin bisa hanya kaga yadda zamu kwashe dakai mahaukacin banza!......zaka matsamin ko sai na tattakaka a wajen?" Aba din ya kuma fadi cikin fushi. Cikin hanzari oncle umar ya miqe ya janye maina wanda ko gezau baiyi ba,hasalima baiso oncle umar din ya janyeshi ba,zaifi masa dadi ya barshi a wajen aba yaci gaba da dukansa wataqila ita daya ce sassauqar hanyar da aba din zaiyi saurin sassautowa ya saurareshi.

"Zauna nan,kada ka sake tsaiwa masa a hanya aliyyu" oncle umar da zuciyarsa shima ta fara motsawa ya fada cikin nasa fushin.

Kafeshi oncle umar din yayi da idanu,kaman yadda oncle bashar da oncle issoufou suka kasa motsawa,idanunsu dukka akan maina din,saboda wani abu ne da yazo musu a bazata gaba dayansu.

A hankali idanuwansa suke sauya launi saboda abinda ke motsa masa cikin zuciya,wani irin yanayi maras dadi qunci da zafin zuciyar da shi daya yasan me yake fuskanta.

"Yaushe ka dawo?, yaushe ka shigo gidan?" Oncle bashar yayi qarfin halin tambayar maina. Sanda ya dago fuskanshi da zummar amsa masa dukkansu saida kowa yasha jinin jikinsa. Wani irin yanayi fuskar tasa ta sauya,gaba daya kamanninsa sun canza.

"Yanxu oncle......yanxu na shigo,ama taqi saurarona tace saidai na sameku...... shima aba haka"

"Ba zasu saurareka din ba,don bakayi abinda zasu saurareka haka ta sauqi ba aliyyu" oncle umar ya fadi da wannan yanayin nasa dake nuna zafinsa. Idanu maina ya maida kan oncle umar din yana da zafi shima qwarai,har wani lokaci bibi ke ganin ta wajenshi ya gado zafi da kafiya,saidai nashi zafin da ya tashi ya ninka na dukka uwayen nasa. Duk da zafinsa idan ya gama spark ya sauka yana da budaddiyar zuciya,yana da zuciyar sauraro dake iya fahimtar mutum ta kuma bashi uzuri,yana da kafiya da qoqarin fahimtar da aba harma da bibi a duk sanda suka hau dokin naqi,ya hangi nasara ya idanuwa da bangarensa,don haka ya zamo a hankali ya gurfanar da kansa a gabansu

"Bansan da wanne baki zan fara baku haquri ba......bansan wadanne kalmomi ne zasuyi tasiri a kanku wajen wanke fushina dake zuciyarku ba...... abinda zan iya fada kawai shine......ina me neman afuwa da yafiyarku akan yanayin dana sanya zukatanku.....zullumi da fargaba dukka.......sannan gani a gabanku kuyimin dukka hukuncin da kuke ganin ya dace kan cutarwar da na yiwa jikarku" kalamansa sun dakesu sosai sun kuma sanyayar da jikkunansu. Dakin ya dauki shuru,kaman yadda basuce komai ba hakanan shima bai motsa daga tsugunnon da yayi ba,har sai da oncle umar ya magantu

"Koma ka zauna maina" kasa motsawar yayi yana jin nauyi da kunyarsu,yanajin nauyin abinda ya aikata din da yayi sanadin barinsa gida,yanajin kamar a yanzune komai ya faru,har sai da oncle issoufou ya kama hannunsa sannan ya matsa gefe ya sake zama sosai.

Fada sosai oncle umar ya balle masa dashi,don dama shidin baya barin ko ta kwana,sha yanzu magani yanzune ko akan waye,sai da yayi mai isarsa bashar da issoufou suna tayashi sannan ya rufe da fadin

"Abinda ya faru tsakaninka da matarka za'a iya cewa me sauqi ne inda ka zauna baka nuna ragwantaka ba...... za'a iya cewa rabo ne ya kawo haka,shi kuwa rabo baya tsallake rana da loakcinsa......ba kuma wanda ya isa ya hana wannan rabon fita sai ya fita a sanda ubangiji ya tsara......abu mafi muni shine tafiyarka,tafiya bata sati daya ko biyu ba,bata wata daya ko biyu ba,bata shekara daya ko biyu ba.....shekaru aliyyu,shekaru a qalla biyar?,wanne irin rago ne aliyyu?me yasa ba zaka tsaya ka fuskanci koma meye ba?,duk tsiya ba haramun dinka ka afkawa ba,me yasa ka tafi?" Ya jefa masa tambayar da alama tafiyar tasa tana daya daga cikin abinda ya sosai zuciyarsa.

Tabbas yasan cikin bacin ran dake danqare aran oncle umar ne kadai ya sanyashi ya jefeshi da kalmar RAGWANTAKA......saboda duk gidan yafi kowa sanin TSORO yana daya daga cikin abubuwan da bai baiwa muhimmanci a rayuwarsa ba JA DA BAYA basa daga cikin kafatanin dabi'unsa,duk yadda zai musu bayanin yadda yaji a sanda abun ya faru.....duk yadda zai kwatanta musu yadda qaddara ta dinga janshi tana tilasta masa ficewa daga gidan ba zasu gane ba.......daga bayan barinsa gidan kome daya faru dashi ya sakashi a mizanin wannan QADDARAR da tayi sanadin fitarsa a gida..... wanda yayi imanin banda hakan ta faru......da tuni a yanzun ba shine ALIYYU MAYAK'I da ake magana a kai ba,da tuni ba shine MAINA da yaketa qoqarin binne daukaka da matsayin da ya samu ba,bayan tarin qalubalen da ya gamu dashi sanadin fitarsa a gida

"Dukka ka yiwa kowa laifi,amma tamu me sauqi ce,kuma mun yafe maka,a yanzun babban qalubalenka, zamuyi iya abinda zamu iya wajen nema maka sasaauci,amma saukowarsu wannan tana hannunka,tunda bamu isa mu tilasta musu su yafe maka ko mu goge abinda ke ransu ba......" Ko iya wadannan kalaman na oncle umar kadai sun samar da wani sasaauci cikin gurbin zuciyarsa,sun kuma haifar da wani dan qaramin hope

Baisan ta yadda zai gode musu ba, matsayin nagartattun kawunnai a wajensa,ya miqe da zummar barin falon,yana kuma wassafa ta inda zai fara tunkarar wannan gundumemiyar matsalar........ babban yaqi da zai zama madubin rayuwarsa muddin ya cimma nasara.

"Kaje zuwa da safe koma meye zamu qarasa magana akai......gobe daurin auren qannenka biyu"

"Waye da waye?" Ya samu kansa da jefawa oncle umar tambayar saboda wani fargaba daya kamashi. Dukka sai suka dan tsaya suna dubansa kafin oncle umar din ya bashi amsa

"Aminata da yasmine" qas yayi da kansa kuma yana jin nauyinsu,yana jin kamar yayi tambaya akan makomar aurensa da sultana......to amma kuma hakan kamar zai zama da gaggawa,karbarsa da sukayi bawai yana nufin yanzun shi bame laifi bane a wajen kowa ba...... a'ah......yasan sun karbeshi ne saboda tsananin zumunci irin nasu da yadda suka tashi da soyayyar junansu data yaran da suka fita daga tsatsonsu.

"Aliyyu" oncle issoufou ya kirayeshi da sassaucin nan nasa,don shi din mutum ne da bashi da zafi sam,duk cikinsu yafi kowa sanyin hali

"Ka kama bibi,ka tabbatar ta zame maka tsani" kai ya girgiza wani busashen murmushi na fita daga saman labbansa,tamkar oncle issoufou din ya shiga zuciyarsa,bibi ce kawai last hope dinsa da yayi imanin tana da power din da zata maida komai bisa saiti,ko meye zatayi duk wani borenta bazai bari ya dameshi ba,zai runtse idanunsa,zai kuma gwada mata shi dan yau ne,domin yasan halin bibi sarai,zuma ce sai da wuta,amma kuma yana da babban yaqini a kanta.

Daidai inda sukayi kacibus ya kalla sanda yake fita a falon,yaja dogon numfashi daya sauka har tsakiyar hunhu da zuciyarsa

"SULTANA" ya maimaita sunan kamar yaune ya fara jinsa. Akwai babban game tsakaninsa da ita,yana tunanin itace abu na qarshe da zai cimma,a yadda ya tsara itace zata kasance matakalar qarshe,yaya zaije mata?,ta yaya zai risketa?,dukka bai san wannan ba......abu daya ya sani,ya kuma haqiqancewa kansa shine........duk RINTSI......duk yadda za'a je a dawo ba zaya taba yarda da abinda zai shafi igiyoyinsa ba

"Idan suna nan har yanzu?" Wani sashe na zuciyarsa ya jefa masa tambayar data tilasta masa riqe hannun almu dake zaune zuwa yanzu a gefan qofar falon saman wasu qananun kujeru dake wajen don ya gaji da tsaiwar jiransa

"Idan har yanzu sashe na yana nan......ina buqatarsa,ka gyaramin koda iya wajen da zan ajjiye kayana" ya fada adan birkice,don har yanzun bayajin cikakkiyar nutsuwa a jikinsa. Kai almu ya gyada yana miqewa,har yayi taku biyu mainan ya kirashi,sai ya dawo ya tsaya cak gaban maina yana kallonsa

"Bayan tafiyata ciwon kurumta ko bebantaka ya sameka ne?" Ya masa tambayar yana duban idanunsa. Kai ya girgiza sannan ya matso taku hudu da sauri ya fada jikin mainan yana cewa

"Barka da dawowa ya maina,Tu nous manques(munyi kewarka)"

"merci(na gode)" ya ambata da raunanniyar muryar nan yana daga almu daga jikinsa yana kallonsa. Shima almu din kallon fuskar maina yakeyi,yana mamakin yadda ya mainan nasu ya sake komawa. Babban mutum da wani irin shinfidadden kwarjini da nutsuwa saman fuskarsa. Abinda shima maina ke wassafawa a ransa kenan,almu din da ya tafi ya bari da sauran quruciya ya zama saurayi

"Ka girma almu,ina fata zaka taimaka wajen kawo wani haske komai qanqantarsa tsakanina da ama"

"je promets in sha Allah(nayi alqawari in sha Allah)" kai maina ya jinjina,yana a tsaye har almu ya tunkari tsohon sashensa da baiga wani abu daya sauya ba ta wajen,saima gyara da wajen ya samu da kuma kulawa.

A yadda idanunta suke a rufe sam bataga bibi dake zaune cikin falon ba tana kallo saboda raguwar jama'a daga sassan nata. Sanda ta shigo din daga kai kawai bibi tayi ta bita da kallo,yanayin taku da tafiyar sultanar dukka ba sune tattare da ita ba

"Ikon Allah" bibi ta fadi har zuwa sanda ta tura qofar dakin dake kusa da ainihin dakinta ta shige

"Allah ya kyauta.......itama wannan ja'irar na fuskanci ta zama baudaddiya" ta fadi a bayyane tana maida toothpick din data zaro bakinta taci gaba da sakacenta.

Kamar daga sama taji sallamarsa,saita maida dubanta da hanzari bakin qofar qawataccen falon nata. Yadda ya zuba mata idanu haka itama ta zuba masa tana jin kamar cikin mafarki take ko kuma majigi take kalla

"Wannan kamar maina" ta fadi cikin tantama duk da yaqininta yafi yawa akan tabbas shi dinne. Qafafunta dake saman kujera ta sauke,har yanzu bata dauke dubanta daga kanshi ba kamar wadda taga fatalwa. Ta waiwaya kadan tana qwala kiran sunan

"Tanja!,ke tanja!!" Tanja tana kusa,don tana kitchen din bibi din zata zuba abinci taci,saita saki abinda takeyi din,don yanayin kiran da bibi ke qwala matan baiyi kama da kiran lafiya ba,uwa uba kuma tanata juya dawowar maina a daidai wannan lokaci.

Dashi idanunta suka fara cin karo,yana tsaye abinsa qyam daga bakin qofar,a dan rude ta kalli tanja

"Wancan dake bakin qofar a tsaye ba aliyyu maina bane?" Tayi tambayar bihaqqi tana neman sani.

Tanja bata ma dubi wajen ba ta bawa bibi amsa

"Shine" kammala fitar haruffan guda biyar yayi daidai da miqewar bibi tamkar bame fama da ciwon qafa lokaci lokaci ba,sai kawai ta soma jan zaninta tana daurin qirji dashi idanunta fes bisa fuskar maina da sai data miqe din take sake qare masa kallo abinda daga maina din har tanja suka gaza gane abinda take nufi da hakan

*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 54


Idanunsa fes bisa kanta,yasan dukkan wani kalar rigimarta,yasan meye zata iya aikatawa da wanda ba zata iya aikatawa ba,yasan kuma lagonta qwarai da gaske.

"Billhuwallazi lailah illa huwa idan ma fatalwa ce ba aliyyu ba ni bibi nafi qarfinta.......idan kuma har da gaske kaine.......da idanuwanka guda biyu a bude na rashin kunya ka iya dawo mana cikin gida to dai dai nake dakai,shege ka fasa ni da kai" ta fadi cikin daukaka murya tana sake gyara daurin zaninta da kyau tamkar me shirin yin dambe dashi. Dolen dole badon yaso ba murmushi ya subuce masa yana kallonta,da gaske take tattara dukkan qarfinta kamar wadda ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login