Showing 66001 words to 69000 words out of 294767 words
Chapter 23 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
da laushi......amma a nata hancin kama yakeyi mata da qamshin MUTUWA.....Tabbas inda mutuwa tana da wani qamshi na daban......wannan qamshin shi ya dace a baiwa wannan sunan.
Waige waige ta fara yi jikinta yanason fara rawa, hankalinta kuma nason yin qaura daga gangar jikinta
"Ki nutsu,ba kowa a wajen nan,ba shi daya aka qerowa turaren ba,bashi daya kaf duniya yake siyan turaren ba......ki nutsu kada ki ruda kanki sultana" zuciyarta ta fara rada mata cikin kunnuwanta yayin da qirjinta ke wani irin bugawa da tsananin qarfi har numfashinta yana rarrabewa.
"Sultana mohmoud mayak'i" ta sake ji an kirata,kiran sunan da ya hautsinata gaba daya ta waiwayo da wani irin sauri. Wata dalibar ce cikin daliban da suke ajin farko wato J.s one ke nufota. Hannunta riqe da wani babban abu da ya yima sultana zubi da kwali. Har ta iso gabanta sultana na dubanta qirjinta kuma bai fasa dagawa ba,sai ta miqa mata kwalin tana kallonta bayan ta rusunawa sultana din kamar yadda yake doka ne na makarantar dole na qasa ya rusunawa babba
"Wai gashi" bin kwalin dake hannun yarinyar tayi da kallo sannan ta maida dubanta ga fuskarta tana tattaro ragowar miyau din bakinta,da qyar ta tambayeta
"Wai inji wa?" Kai ta karkada yarinyar
"Ban sani ba,nima wata daliba ce ta bani tace itama wata ce ta bata tace a baki" fuska tadan motsa kadan,abun yadan daure mata kai,tayi kaman ba zata karba ba,to amma yadda yarinyar ke rusune sai taga bai kamata ta barta a haka ba
"Ya sunan wadda ko wanda ya bada?"
"Nima na tambaya tace bata sani ba,wancan din tace me bada saqon sunanki kawai ya kama yace a baki"
"Kodai aba ne yake sauri bazai iya tsaiwa ba ya bayar a kawo?" Wannan tunanin ya sanyata miqa hannu ta karba,yarinyar ta juya da sauri sauri tana barin gurin don kada azo mata ba'a sameta ba,sai itama sultana din ta soma takawa tana riqe da kwalin tana barin wajen zuwa nana aisha hostel,har a sannan hancinta yana jin qamshin nan data yiwa maqurar tsana*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 35
Tana tafe a hanya tana juya kwalin,ba qato bane hakanan ba qarami ba,yana da matsakaicin girma,amma kuma yana da dan nauyi. Kai tsaye ta koma hostel dinsu,sanda ta isa dakin da yawa an yoye,kowa ya fita waje,wasu gurin family dinsu,wasu kuma suna jiran tsammanin isowar 'yan uwan nasu.
Gefan gadonta ta zauna a nutse,ta aza kwalin saman cinyarta ta fara budeshi.
Sannu a hankali ta kammala yage takardar jiki tsaf,wani irin kwali ne na musamman tamkar qaramin akwati,sai daukan idanu yakeyi da wani irin santsi da tambarin dolce and Gabbana ko ina a manne a jiki.
Doki ya kamata,muddin wannan kyautar daga hannun aba take to ko shakka batayi tafiya yayi ya kuma tuna da ita
"Allah sarki ubana,maganin kukana" ta furta hawayen qaunar aba na cika mata idanu.
Cak ta tsaya tana duban kyaututtukan da aka shirya cikin box din. Tarin tsagwaron chocolates,dukka kalolin wasu chocolate da takesha babu wadda ba'a zuba ba a cikinta. Wani siririn agogo da take da tabbacin zaiyi wuya chain dinsa idan ba gold bane a jiki. Turaren da take amfani dashi sanda tana sultana dinta wanda a yanzun ma tuni ta sauya zuwa wani kalar daban. Biro da wasu qananun notebook masu masifar kyau da tsari,sai wata memo itama daban da zata baka damar tsara komai na rayuwarka da date da komai,sai wani greeting card da duka rubutun jiki layi qwaya daya ne tal
"Best wishes" kadai ke rubuce daga tsakiyansa.
Bin budadden box din kawai takeyi da kallo,cikin jikinta ta dinga jin wannan kyautar ba daga hannun aba ta fito ba,batama dace da ace daga aba din take ba,to anya ba batan suna sukayi ba?,tunda dai daliban makarantar ba suna da yawa qwarai,kuma bazaiyiwu kaf makarantar ace ita daya ce qwallin qwal me suna sultana mahmoud ba. Juya bayan katin tayi,a nan ta samu amsar tambayarta,cikakken sunanta harda na qasarta ne rattabe a bayan,hakan yana nufin me aiken yanason bata tabbacin saqonshi ne.
Wani abu me kama da bacin rai ya biyo bayan mamakinta,ta sake juya katin ko zataga alama koda ta sunan me saqonne amma babu,tsoro da shakka suka kamata,daidai sanda ameena aleeyu ta shigo da sassarfa
"To kizo ga duka 'yan gidanku nan gaba daya,har mun gaisa da aba ma,ama nada maqurar kirki,atta da almu suna yanayi dake" ameena din tace da sultana cikin nuna zallar zumudi.
Da sauri ta tashi hae box din dake saman cinyarta ya watse a wajen,sam batabi ta kansa ba tayi hanyar waje duk da tana jiyo ameena na fadin
"Kinyi barna,wannan agogon me tsada .......Allah yasa baki fasa glass dinshi ba".
Tana tafiya zuciyarta na nanata tambayarta daga ina wannan gift din ya fito?,indai har ga aba yazo to waye ko wace ta aiko da gift din?.
"May be dai still aba dinne" zuciyar dake neman nutsuwarta ta fada tana bata tabbaci.
Tun daga nesa data hangosu murmushi ya subucewa fuskarta,kasa jurewa tayi ta isa garesu a hankali sai ta dan saka da sassarfa,ta qarasa ga ama ya fada jikinta tana riqeta da kyau,bakinta har rawa yakeyi wajen fadin sunanta
"Ama.....sannu da zuwa ama"
"Wato ama dinki kawai kika gani ko?,ni baki ganni ba?" Muryar bibi ta doki kunnenta. Waiwayawa tayi da sauri tana duban bibin,sai ta saki ama ta nufeta itama ta fada jikinta tana qanqameta
"Ban lura da bibi na ba,bibi tun daga nijer kikazo ganina?" Ta fadi tana murmushi. Harara ta balla mata
"Kuma gashi an yanqwanani ko ganina ma ba'a yi ba?" Ta fadi tana yatsina baki,saidai kuma qasan zuciyarta na mata wani irin sanyi saboda sauyi muraran da take gani tattare da sultanarta. Baya taja tana duban bibin
"Ni ya kamata nayi fushi bibi,kina can kina qiba abunki aba yana baki kayan dadi,ina nan kin barni da abinci da horon boarding" ta dan taba tsokanarta wanda abune da kusan dukkaninsu kunnuwansu sun manta rabon da su jishi daga bakinta,sai suka sanya dariya,wanda muryar aba ta fito a ciki,sai a sannan ta ankara dashi shima,abinda ya sanya tadan yi qas da kanta ta kuma nufeshi da hanzari.
Zamewa tayi ta tsugunna a qasa tana gaidashi
"Barka da warhaka aba,ina kwana?" Ba wanda bai dubeta ba yadda take komai cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa. Yana dan saki murmushi ya amsa mata
"Lafiya qalau sultana,tashi a qasa kada ki bata uniform dinki,ga abun zama can an shimfida mu qarasa" tanja ce ta riqe hannunta,saita waiwaya tana duban tanja din
"Kina Nigeria ko kina nijer tanja?" Ta tambayeta bayan ta gaida tanjan itama cikin rusunawa,abinda sultana din bata taba mata shi ba koda wasa,kai kwata kwata ma ba zatace ga sanda sultanar ta taba gaidata ba,ba zata iya tunawa ba.
"Inaaa......ina nan gurin iyayen dakina,in tafi nabar 'yan biyu?,ai bazan iya ba" ta amsa mata tana murmushi. Sai a sannan hankalinta yakai kai,bataga benazeer da batoul ba,idanu ta shiga warewa can qasan zuciyarta tana jin shauqin ganin yaran,amma ko me kama dasu bata gani ba. Duka sai taji zuciyarta ba dadi,ta dinga nacin kallon inda goumar yake amma bataga alamun suna tare ba,har goumar din ya lura da yawan kallon da takeyi,sai ya saki murmushi ya watsa mata hannuwansa,qasa qasa kuma yadda babu wanda zaiji yace da ita
"Me na satar miki ne kuma yau?,mutumin da ko kallon fuskarsa ba'a sonyi yau shi aketa kalla?,ki bude baki kawai ki cewa ama ina 'ya'yanki ko?" Harara ta watsa masa gabanta yana faduwa,salon maganarsa sak yaa maina,kusan wasu abubuwan nasu suna bala'in kamanceceniya da juna,kamannin fuska ne sam Allah bai sanya sunyo daya ba. Qaramin tsaki taja tana dauke kanta ta maida ga sashen su ama daketa bata labarin abubuwan da suke wakana bayan batanan,sai muryar goumar ta motsa cikin dariya
"Allah bibi wannan 'yar jikanyar taki ladabin qarya tayi muku,qanzo ne ya sanyata yin laushi,bata canza hali ba ashe rashin kunyar nan tana nan,yanzun nan ta gama min tsaki harda harara" ya qarasa fadi yana dariya sosai. Harara bibi ta watsa masa
"Qaniyarka sarkin sharri,ta ina ta hararekan dukkanmu muna nan idanunmu suna gani?"
"Wannan idon naki ai ya kusa rubewa,don inda kina gani sosai da a yanxun kinga wani abu da ni kadai nake hangowa" ya furta maganar yana kallon wani guri daban. Ba tare da Bibi din ta waiwayo ba tace
"Kaji dashi ja'iri" saita jawo wani mazubi ta miqawa sultana,wanda ba komai ciki sai kayan ciye ciye da tasan tafiso.
Cikin wata irin sassanyan nutsuwa ya maida wayar tashi me bango biyu ya manneta guri guda ya rufeta. Qirjinsa da zuciyarsa tana masa wani irin nauyi,da gaske goumar yakeyi bazai taba ganin yaran ba?,da gaske yake,yau din rana ce da zata iya sake nesantashi da damar sake ganin kowa da komai da ya shefeshi ko ahalinsa.
Yayi kwadayi qwarai wajen sakasu a idanunsa,yaso ya samu wannan damar koda zata kasance dama ta qarshe a garesa,tunda bai san yaushe ba?,baisan sai wanne lokaci ba.
Wannan babbar dama ce a gareshi da muddin ta gushe masa baisan sai yaushe zai sake samun wata damar makamanciyarta ba,zaiyi komai zaije zai kuma aiwatar dukka domin sa,domin ahalinsa.
A hankali ya isa dab da motar da mutumin da idan baka matso kusa dashi qwarai ba zaka tsammaci mutum mutumi ne. Yana isowar ya sanya hannu ya bude masa bayan motar,ya zura gangar jikinsa cikin wata irin kasala da galabaita tamkar wanda yayi watanni yana aikin kauda duwatsu ba tare da ya huta ba. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta subuce masa,ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin kamar ajiyar zuciyar zata fita ne tare da zuciyar dake qirjinsa,ya maida bayansa jikin kujerar yayi relax yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugawa sanda motar ke gangarawa tana barin wajen.
Har ta rako su aba bakin mota,suka kuma fidda komai da komai da suka kawo mata cikin zuciyarta bata kasa juya batun box dinnan ba,daga ina yake?, itace tambayar da taketa nacin nanatawa.
Tana nan tsaye har suka kammala shiga motar. Ama ya sauke glass din bangarenta ta miqa ma sultana wani box. Kallonsa tayi sannan ta sanya hannu ta amsa. Madararta ce,madara mafi soyuwa a gareta,madarar da tana begenta amma kuma tana nisantata da rayuwarta saboda tuna mata da takeyi dashi
"Gashi inji benazeer da batoul da baki tambayesu ba,sunce suna gaidaki" wata irin kunya ce ta saukar mata,tanason tambayarsun amma batasan ta yaya zata fara tambayar tasu a gaban ama da aba din ba,uwa uba ga bibi a gefe,ga kuma dan sanya ido goumar
"Ace ina gaidasu" ta fada da sassanyan muryarta
"Basa amsawa,sai da aka roqa musu" goumar ya fadi cikin salon tsokana. Harara kawai ta samu damar binsa dashi saboda tashin da motar tayi bata samu daman maida masa raddi ba.
Duk wata kujiba kujiban zuwan masu visiting lokaci yana yi aka rufe gate din makaranta,doka kuma taci gaba da aiki. Suna saman gadonsu kowa na kintsa wajensa da gyara kayayyakin da aka kawo masa daga gida,dakin nasu fal kaya saboda dukkansu kusan daga gidan iko da wadata kowacce ta fito,babu wadda ta fito daga qaramin family.
Da wuri sultana ta gama komai,tana daga saman gadonta ameena aleeyu ta qaraso da box dinta ta miqa mata
"Ga box dinki nan" binsa tayi da kallo tana jin shakkar amsa,sai ta maida dubanta ga ameena
"Bansan waye ya aiko dashi ba,ki ajjiyemin kawai zan nema maishi saina karba"
"To ya wuce saurayinki?" Ta tsokaneta tana dariya. Dukanta maganar tayi har tsakiyar zuciyarta,sai ta daga kai tana kallonta gami da jefa mata harara
"Ba saurayi ba dattijo" ta fadi cikin hushi. Yanayin yadda tayi maganar gauraye da harshen qasar nijer cikin kuma fushi dukkansu ya basu dariya,bata sake ce musu komai ba ta janye qafafunta zuwa gadonta ta juya musu baya.
Iyakar tunaninta kaf ta gaza canko wanda zai iya aiko mata da saqon
"To kodai goumar ke yimin wasa da hankali?" Tayi tunanin haka daga qarshe,sai ta cije lebanta tana jin qamshin gaskiyar hasashenta. Tabbas da ta tuna hakan kafin su tafi saita yayyaba masa magana,ta fuskanci kamar yana yawan son yiwa rayuwarta shishshigi.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 02 page 36
**********Sannu a hankali rayuwa taci gaba da tafiyar mata,tana sake hankali tana kuma sake fahimtar me ainihin rayuwa ke nufi kadan kadan.
Sosai kwanyarta take budewa,a hankali kuma ta fahimci gatan da ama tayi mata data kawota makarantar. Kafin takai ga zuwa ss3 ta zama wata sultana ta daban. Azkar ya kama bakinta ainun,karatun qur'ani da wata nutsuwa dake nuna sanin haqiqanin rayuwa. Tabbas! Ilimi wani irin haske ne da babu irinsa,wani abu ne dake busawa zuciya da rayuwa wani ruhi na musamman. Hatta da kamanninta sun sauya,sun cika da wata irin nutsuwa da wani sirtaccen kyau nata dake boye. Idan ka kalleta a sannan babu abinda zakaji cikin zuciyarka dangane da ita sai tsananin burgewa,saboda wata kamala annuri da kwarjini da ilimi ya zuba mata,komai nata sai ya zama cikin nutsuwa da kuma kamun kai. Kalaman bakinta sun canza sosai,hakanan mu'amalarta,saidai kuma tun wancan sanyin da tayi.....tun wancan sauyawar......tun a wancan lokacin har zuwa yanzu sai ta zama me matuqar sanyi,miskila mara yawan surutu hayaniya ko kuma kwarafniya kwata kwata.
Tana S.S3 ama ta saka su benazeer a free nursery,surutu da wayonsu ya isa,wani irin wayo ne dasu da yafi na shekarunsu,duk da batoul nada kalar nata miskilancin,amma tun kafin shekarunsu su fara nisa kamanceceniyar halayya wajen yawan surutu rigima da rawar kai na sultanan can baya benazeer ta kwafe tsaf!,wannan ya sanya ama tafi maida hankali akan benazeer din sosai,tanaso dukka wadannan halaye da Tayo gadonsu su kasance kan tsari da kuma cikakkiyar kulawar tarbiyya. Saboda kwadayin ingantar tarbiyyar yaran ya sanya gaba daya ama ta daina tunanin komawa nijer,tafison a nan din inda suke suyi tasu quruciyar da wayon,saboda itace babbar shaidar banbancin tarbiyyar da qasashen biyu ke dashi.
A shekararta ta qarshe a makaranta ta yiwa kanta gata me tarin yawa. Tayi joining classes da akeyi na musamman bayan wadanda suka zama wajibi. Litattafai ake musu na addini masu yawa,zazzafan karatu ne da ya sanya da yawa daliban basu fiya joining ba sai masu wayo da masifar nacin so karatu irin sultana. Yadda zazzafar qiyayyar karatu ta juye mata zuwa zazzafar soyayyar karatu tana bawa ama mamaki. A duk sanda sukayi hutu tazo gida yakan zamana kamar ba hutu ta samu ba. Duk bayan kowacce daqiqa tana maqale da litattafai,wani lokaci hadda takeyi wasu lokuta kuma tilawa. Ta samu hadisai sosai,wasu ta haddacesu ne,musamman wadanda keda alaqa da mu'amala da kuma rayuwa,wasu kuma a yayin da aka karanta mata ta iyasu a rubuce kuma tana tsintar wasu tana amfana dasu. Kosu benazeer bata basu lokacinta kamar yadda take bawa litattafanta. Sai ya zamana ba wata shaquwa bace can can a tsakaninsu da ita. Da ama suka budi idanu,ama itace mommansu,ita sultana AUNTY kawai suke kiranta,kuma suna mata kallon auty dinsu ce,saboda tsakaninsu hukuntawa ne da tsawatarwa idan za'a yi ba dai dai ba tamkar na qaramin yaro da babbar yayarsa.
Watannin qarshe da suka rage musu a makarantar,dab da zasu fara jarabawa sukayi saukar alqur'ani me girma. Kyawawan qira'o'i dukka guda bakwai din da muke dasu babu wanda bata iya ba. Karatu take tartilan babu gargada,babu bata,zakayi tsammanin ta jima da saukeshin a yanzun maimaici kawai takeyi. Tana cikin zaqaquran dalibai guda goma na farko da aka fidda cikin ajinsu.
Sanda suka fara jarrabawa dukka tunaninta sai ya sake fadada akan qara nisan zangon karatunta,batajin zata zauna haka,yanzunne ta soma jin gardin ilimi,ashe ilimi dadi ne dashi har haka?,ashe muddin kana da ilimi kuma kana aiki dashi basai an zauna ana fama wajen gyaraka da saitaka ba?. Sau tari idan su ameena aleeyu sukaga tana zaune guri daya tana murmushi sukan cika da mamakin meye yake sata nishadi yayin kadaicewa ita daya?.