Showing 267001 words to 270000 words out of 294767 words

Chapter 90 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

aikin?" Ama ta tambayeshi. Kai ya gyada mata

"Eh na gama"

"Yauwa,tashi ya rakaki kije ki kwanta sultana,kada ki yarda don kin shigo cikin mutane ki dinga stressing kanki da yawa,kuje idan akwai abinda kike buqata ki gaya masa zai kawo miki" kaman zata nutse a wajen ta miqe tana mata sai da safe.

Suna tafe a hanya ita da atta suna hira,hirar duka data shafesu ne abubuwan da suka faru da basa kusa,har suka isa qofar sassan yayi mata sallama ya juya ya koma.

Kusan wanna shine karon farko da zata fara kwana a sassansa,duk sai ta jita wani iri,ta samu saman sofa ta takure tana qarewa sassan kallo. Sassa ne dake basu fargaba a baya,ba kuma kowa ke sbigarsa ba don me wajen bayason hayaniya ballantana shirme. An gyarashi fiye da zato,an qawatashi an kuma sake zuba komai sabo,bata sani ba aikin ama ne kona me sashen.

Tana tsaka da wannan saqe saqen ya murda handle din yayi sallama,hannunsa dauke da 'yan qananun abubuwan amfani,kanta a kwance saman cinyarta tana jinta kamar a baqon waje ta amsa sallamar,sai ya qarasa yana ajjiye komai a muhallinsa,sannan ya tattako a nutse zuwa inda take zaune,saiji tayi ya dauketa cak daga saman kujerar yana fadin

"Wannan zaman kin takura da yawa" bai mata masauki ba ko ina sai saman gadonsa,yasa hannu yana zare mayafin wuyanta,tadan motsa zata riqe ya girgiza mata kai

"Ki kwanta kiyi bacci,nina na gaji,karki sake gajiyar dani da musunkinnan" daga haka ya juya yana ficewa daga dakin. Aqalla ya kusan mintuna talatin kafin ya dawo dakin,ta cikun dim light take kallonsa,ya dauki pillow ya haye saman sofa ya zube a hankali sabida gajiya yana ambatar sunan Allah saboda tsantsar gajiya. Tun tana sauraren saukar numfashinsa a hankali har itama baccin yazo yayi awon gaba da ita.

*******Tana zaune daga gefan gado,yayin da yake tsaye daga gaban madubi yana sanya links na rigarsa.

Wata zubabbiyar dakakkiyar shadda ce a jikinsa ya sanya wadda ta amsa sunanta wajen kyau da tsantsar tsadar da basai an gaya maka ba.

Yana danyin komai a gaggauce ne,alamu suna nuna jiransa akeyi,minti bayan minti yana duba agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa.

Tunda ya dora babbar rigar kayan saman jikinsa komai ya ida tsinke mata. Yayi wani irin fitinannen kyau,mahaukacin kishin da batasan tana dashi ba ya soma taso mata kamar zatayi amansa ta bakinta.

Dafaffiyar madara take sha amma sai takejinta kamar ruwan madaci. Ya kammala shirinsa tsaf,ya kuma wadata jikinsa da sassanyan turarensan nan me tsayawa a zuciya.

A nutse ya tako gabanta yana kallonta da narkakkun idanunsa dinnan dake nuna bai samu isashen bacci ba daren jiya. Taji tashinsa yakai sau nawa,taji shigarsa toilet ya kusa sau uku,duk fitowa kuma da alwalarsa yake fitowa,wannan ya sanyata samun yankakken bacci itama. Tana tsoron kada yayi ciwo irin wanda yayi a paris.

Cikin kulawa ya duba mug din tea din dake ajjiye a gefanta,shi ya sanya aka dafo madarar,don ko yaya yake sauri yanason duk lokutan cin abinci ya zamana shi ya fara sanya mata wani abu a cikinta,hakan yana jin kamar yana wanke kansa ne daga tarin yunwa amai da wahala daya barta a cikin lokacin cikinsu benazeer.

"Are you okay?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta. Har tsakiyar zuciyarta takejin wannan tambayar idan yayi mata,me yasa wai bazai tsaya ya kalli qwayar idanunta ba?,me yasa wai bazai karanci komai daga idanunta ba?.

Kai ta gyada masa tana kuma basarwa tare da qin yarda ta kalli idonsa. Ture mug din yayi gefe,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda sabbi CFA masu yawa ya ajjiye mata yana fadin

"Zamuje Nigeria gidan uncle tahir,ni da Sardauna da oncle issofou da oncle umar......amma ina sanya rai a yau din in sha Allah zamu dawo". Mummuar faduwa gabanta yayi,taji zuciyarta na wani irin rige rigen bugawa.

"Me zasuje yi?,gidansu ayana?,nema masa auren ayana ko me?,da gaske yake?,......d gaske ya daga mata qafa?,da gaske ya barta kenan?,da gaske ya zabi AYANA DA LAILA a kanta?,kada dai ya zamana tsaiwar da sukayi da niamy auren LAILA ya karba?". Duk sauran abinda yake fada bata jishi ba,abu daya taji na qarshe saukar tattausan lips dinsa me sanyi saman goshinta,sai kuma qarar rufe qofar bayan fitarsa.

Ji tayi kaman zata dimauce,duk yadda taso ta zauna a dakin ita kadai ta kasa,duk yadda take tunanin babu soyayyarsa ko digo a zuciyarta a yau din ta qaryata kanta sau babu adadi.....a yau kuma ta tabbatarwa kanta tarin TSANA DA QIYAYYAR da take tunanin tanayi masa ba komai bace face zallar soyayya fara sol mara sofane.......wajen waye zataje taji dadi?,waye zai rage mata abinda takeji a ranta?.

Idanunta a rurrufe ta zura slippers a inda suke aje slippers nasu ta nufi hanyar fita,saita samu kanta da wucewa zuwa sassan bibi kai tsaye,tana jin itace dama me tallafar damuwarta,a yanzun ma ita zata taya idaniya da zuciyarta kokawa.

Aba oncle issofou da oncle umar harda oncle bashar da shi kansa maina dinne zaune a falon,sun kammala karin kumallo suna yin sallama da ama da sauran dan maganganu da suka shafi yan uwa. Daga gefe su aminata ne da yasmine suke tsaye atta da saddi suna musu gyaran daya daga cikin freezer din bibi suna kwashe ruwa da lemukan ciki don sunaso suyi snacks su ajjiyeshu fresh,don dukkansu basu kadai bane,kuma kamar sultana suma basa iya jure yunwa,a nan sassan bibi ne kawai kuma suke da tabbacin zai tsira.

Yadda ta shigo din kusan yaja hankalin kowa a falon,banda bibi daketa faman mita wa maina. Ita dinma idanunta basu gane mata kowa ba,ba wanda ta gani sai bibi kadai wadda hankalin da tunanin dama zuciyar gaba daya dama sun taho ne dominta.

"Yauwa yaki nan" bibi ta fada tana yafitota. Dukka hankalinta ba abinda ya bata sai bibi ta kirata ne ta qara jaddada mata batun auren ayana da laila da maina zaiyi tare da bikinsu najma

"Wai ke kika bawa wannan ja'irin damar tafiya Nigeria zuwa........."


"Wallahi bani bace bibi........bani bace,bibi don Allah ki hanashi......ki gaya masa kada yaje.......inasonsa wallahi......ina qaunarsa bibi.......zuciyata ba zata iya jurar ganinsa da kowa ba......ina sonsa......kice masa nace ina sonsa,ina mutuwar sonshi fiye da yadda yake sona.....nafi sonshi bibi akan son da yakeyimin......yace aure zai qara.......laila da ayana yakeso yanzu......zaije Nigeria neman auren laila bayan ayana kuma...... wallahi bibi bazan iya jurewa ba" ta qarasa fadi hawaye yana sauko mata.

Dif wajen yayi,kunya ta kama aba qwarai da gaske har ya kasa motsi,yayin da bibi mamaki ya kamata,sai kuma a sannan ta fahimci lallai hankalin sultana yayi gaba,bata kula da kowa a cikin falon ba sai ita.

"Zo nan ja'iri,don qaniyarka abinda ka gaya mata dama kenan?,baka ko lura da ba'a gayawa masu juna biyu tashin hankali irin haka ba.?" Zancan bibi ya sanya aba zare jikinsa cikin dabara ya lalubi hanyar barin falon tun kafin sultana ta watsatsake ta sameshi a wajen.

Wani irin sassanyan abu ya soma ratsa zuciyarsa yana narkar da wannan dunqulallen abun me zafi da quna daya tsaye masa a wuya tun ranar farko data soma ware idanunta ta kalleshi tace

"Bana sonka!,bana qaunarka!,i hate you"

"Dakai nake kaketa fama murmushi kaman wanda aka bawa tallan maclien"

"Bibi" ya kirata a tausashe da wata irin murya da farinciki yake gauraye da ita

"Ni nace mata ina neman auren ayana ma bare laila?......da bakina na taba gaya mata haka?…...sultana" ya kira sunanta yana takowa gabanta

"Yau da zan fita na gaya miki ni zan nemawa kaina auren laila?......bibi kaman bakisan zancan suhail da sardauna akeyi ba kin manta?" Dif wuta ta dauke mata,a hankali idanunta suka fara washewa daga rufewar da sukayi,ta fara hango uncle bashar da yayi qasa da kansa,gefe oncle issofou ga kuma oncle umar.........*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 143



Dukkansu suka lula wata duniya......duniyar da basa gane kowa sai kawunansu,duniyar da a lokacin suka manta da kowa da kuma komai. Sirrikan zuciya ne kawai ke tona kawunansu cikin wani irin jirkitaccen yanayi wanda dukkansu su biyun basu taba fuskantarsa ba. Gigicewar qwaqwalwa da dimaucewar tunani.....ba abinda ke tasiri sai QAUNA me wani irin matuqar qarfi dake wanke laifuka ga zukata,ta kuma goge kowanne irin tabo bacin rai da kuma quncin zuciya.

Suna tsakiyar wannan yanayin wayarsa ta fasa qara. Cikin zafin nama ya miqa hannu da zummar kasheta don baya buqatar komai da zai katse masa wannan yanayi me matuqar tsada a gareshi...... yanayi mafi soyuwa a gareshi fiye da dararen farko ga angwaye. Akayi rashin sa'a ya daga kiran a maimakon kashewa harda guzurin shigar da wayar handsfree.

Muryar suhail ta fito fes ta cika dakin,cikin wata muguwar kasala ya zare jikinsa daga gareta a hankali yana sauke numfashi a jejjere kaman wanda yayi tseren gudu da dawakai

"Zamuyi missing flight fa......kana duba time kuwa?" Lion eyes dinsa da suka qara girma suka kuma sauya kala ya lumshe yana furzar da iska,qoqarinsa ya daidaita numfashinsa kada yayi magana suhail ya fahimci yanayin da yake ciki

"Hello.....maina"

"Ina jinka" yayi qoqarin fadi

"Wulaqancin naka ne ya motsa?,don baqinciki saida layi yazo kaina sannan zaka tsiri mugun halinka?"

"Ni kake gayawa haka?" Ya furta calmly yana nuna qirjinsa da yatsarsa.

"An gaya maka waye kai?" Ya fada da sautin dariyar da ake qoqarin boyewa.

"Alright......to na fasa zuwa bazanje ba......kayi duk abinda zakayi,Allah yasa su hanaka lailan muga ta tsiya...."

"Mugu saboda kai ka samu?....." Bai tsaya ya gama jin abinda zaice ba ya katse kiran gaba daya ya kuma kife wayar. Bai taba kawowa dukkansu zasu amshi batun laila da ayana haka da muhimmanci ba,koda yake ya sani wani abu ne kawai da ubangiji ya shiga cikinsa, bayan dimbin tarin addu'a daya dinga yi dare sur akan ubangiji ya kawo daidaito a tsakaninsu.

Already an bashi laila,amma kuma madaurin aurensu yana Nigeria,sai suka yanke zuwa gaidashi hade da nemawa sardauna ayana. To amma shi suhail dinma yafi sardauna matsuwa da damuwa,kamar wanda akace an fasa bashi lailan.

Da wani irin narkakken kallo ya waiwaya gareta,bai samu ganin fuskarta ba don ta duqunqune waje guda,ya sanya hannu ya birkitota,daidai sannan aka soma knocking qofar.

Wani wawan tsaki ya saki yana sake adanata a qirjinsa da kyau,tana jin yadda zuciyarsa ke fat fat fat,ta lumshe ido tana jin sautin cikin kunnenta

"Sulthana" ya kirayeta da wannan salon kiran da tayi imani duk duniya babu wanda ya kaishi iyawa

"Anya zan iya ci gaba da zama cikin gidannan?,.a tabbatar bazasu barmu mu mori amarcinmu ba?" Kunyace ta kamata da abinda ya fada,wanne irin amarci da yara biyu ga tsarabar wani cikin ma?.

Kafin wani a cikinsu ya sake magana aka sake knocking qofar sosai. Wani dogon tsakin da yaf na dazu ya kuma saki,jikinsa a matuqar mace ya miqe yana maida bottom na rigar shaddarsa da tuni tayi squeezing sosai,ya taka a hankali ya fita yana mita a fili.

Numfashi taja sosai tana qanqame pillow tana jin yadda mararta ta daure sosai. Har ga Allah itama an shiga nata haqqin,kowanne bangare a jikinta yana buqatarsa,batasan haka tayi mahaukacin kewarsa ba sai yanzu,batasan haka ta zama addicted to him ba sai yanzu.

A zafafe ya bude qofar,almu yaja da baya yana rabewa,ya sani ko ada ba mutum bane meson a yawaita masa knocking ba.

Jirkitattun idanunsa ya kafeshi dasu,har sai shakka da tsoronsa suka saukarwa almu.

"Ama tace na gaya maka aunty sultana ta shirya,ga dr noor nan zata shigo ta dubata" idanunsa ya maida ya lumshe yana dora hannunsa saman goshinsa. Bayajin zamansu cikin gidan zaici gaba da dorewa gaskiya,yasan muddin suna zaune ko iya kulawar ama garesu ba zata basu cikakken lokaci ba. Qofar ya tura kadan sannan ya taka yana komawa ciki. Yadda yayin. Ya ishi almu amsa,don haka ya juya yana barin wajen gami da sakin ajiyar zuciya

"Allah ya soni". Ya fada a fili yana yiwa kanshi dariya qasa qasa.

Cak ya dagota yana kallon qwayar idanunta ita kuma tana qoqarin boyewa,ya saki dariya a hankali yana tura fuskarshi cikin fuskarta yana laluben kunnenta

"Baby yayi missing daddynshi?...." Riqeshi tayi da kyau kunya tana dawainiya da ita tana kuma boye fuskarta a jikinsa

"Wait....." Ya furta yana qoqarin dagota,saita hanashi,wannan ya sanya hankali kwance ya sauketa gami da zaunar da ita saman sofa. Tana qoqarin kwanciya ya tallabota ta zauna sosai,sai ya sulale a gabanta ya duqa bisa dukka gwiwoyinsa,yasa tattausan tafin hannunsa ya riqe hannuwanta yana kallon tsakiyar qwayar idanunta

"Sulthana" da fararen idanuwanta ta amsa masa,abinda ya sanyashi hadiyar yawu da qyar,ya tarkato sauran nutsuwar data rage masa yaja numfashi sosai sannan yace

"A bedroom...... sulthana nakeso gani zahirinta...kin fahimta?" Wuya ta langabar tana narke masa fuska gami da turo lips dinta na qasa saita girgiza kai kadan

"Ya salammmm" ya fadi da sauri yana runtse idanunshi. Yadda tayi masan gaba daya ta sake tsomoshi,sai yaji yana craving nata qwarai da gaske,kamar ya toshe kowacce qofa da zata sada jama'a dasu

"Exactly wannan sultanar!" Ya fadi da karsashinsa yana nunata da yatsansa idanunsa cikin nata.

"Sultana shagwababbiya....... sulthana sakakkiya........sultana mara jin magana........ sulthana mara kunya.......amma dukka a bedroom dina.......akan gado na......." Sai kuma ya sassauta murya can qasa

"......idan mun fita waje kuma ki zama mummyn twins.......matar aliyyu maina.....the owner of my heart,my life and my breath.....kiyimin alqawari" ya fadi idanunsa yana lullumshewa.

Kai tsaye a yanzun ta kalleshi da fari qal din qwayar idonta.

"Ka fadi ko meye kakeso......ka fadi ko meye kake da buqata daga wajen sulthana......nayi maka alqawarin zaka samu fiye dashi" fuskarsa ya kifa tsakiyar tafin hannunta,hannunsa ya shaqi wani irin launin qamshi daya banbanta da qamshin jikinta,ya daga kansa a hankali yana sake kallonta da narkakkun idanunsa

"Kiyimin alqawarin bani sabon ruhi......kiyi alqawarin bani sabuwar rayuwa......kiyi alqawarin lullube rayuwata da tsaftatacciyar soyayya..... kiyimin alqawarin rayuwa dani har abada..........ki sadaukarmin da raywarki sulthana gaba daya".

Gaba daya kalamansa sun qarasa kashe mata jiki,har taji kaman qwalla zata fito daga idanunta,sai kawai ta zamo daga saman kujerar itama tana riqe da hannuwan nasa

"Rayuwar sulthana naka ne yaa maina......ka manta da wadannan hannuwan ka raineta?,ka manta kaine ka kafa tubalin rayuwarta?,ka manta kaine ka bata dukkan wata rayuwa data dace da ita?,kaine ka bata qwarin gwiwar rayuwa ka kula da komai nata......kaine sulthana......kaine rayuwa da komai na sulthana,kaine numfashinta.....ka manta jininka ke yawo a jikin sulthana?,ka manta jininka aka zubawa sulthana ta miqe taci gaba da rayuwa?...." Idonsa ya sake lumshewa yana jinsa tamkar yana yawo cikin iska.......yana jin wani abu daya zarta farinciki yana dawainiya dashi

"Zan baka fiye da rayuwar daka sanya rai a kanta.....zan baka sama da farincikin da kake mafarkin samu......zan zame maka tamkar uwa.....zan zame maka tamkar 'ya zan kuma zame maka mata......in sha Allah"..

Duk dauriyarsa ta qare,babu wani sauran juriya ko dagiya tattare dashi ya jawota yayi mata wata wawiyar runguma. Sai digar hawayensa taji kawai tsakiyar kanta daya ratsa sassalkan gashinta dake tarwatse a gadon bayanta.

Zuciyarta tayi wani irin laushi,jikinta ya mutu murus. Ya haidar da babu wani abu da za'a ce ya taba sanyashi kuka a iya tsahon sanin da akayi masa?,yau shine yake kuka a kanta har karo na biyu?,ya haidar me kafiya da tsaiwa akan raayi,me kuma tsatstsauran ra'ayin da baya canzawa yau shine duqe a gabanta yake kuka?.

"Ba GUDUN QADDARA nayi ba sulthana.......ki yafemin......please......bansan da wanne idanu bane zan kalli su aba da bibi......na taba marainiyarsu......na taba ajiyar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login