Showing 27001 words to 30000 words out of 294767 words

Chapter 10 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

bacin rai da kuma zato....."

"Wanne zato kike magana akai hamdiyya?,bayan ga zahiri?,ga zahirin da duk me hankali yasan inda ya dosa?,ya kuma san abinda yake nufi?"

"Aba.....don Allah ka tsaya mu tattauna.....bai kamat......"

"Meye bai kamata ba?,shin kinsan mummunar illar dake tattare da barin hawaye yana zuba a idanun maraya?,kinsan illar kukan maraya?" Kai ta girgiza da sauri

"To ya isheni hakanan,aliyyu yayi abinda rai da shaidan ya raya masa ko?,to nima banga abinda zai hanani daukan mataki a kansa ba".

Ta sanshi farin sani,ta sanshi magana daya yake,ta kuma sanshi cewa kaifi daya ne,tunda yahau dokin naqi bazai saurareta ba,to amma ita din cikin jikimta da zuciyarta taqi gamsuwa da hasashen aba akan maina,bawai don tana daure masa qarqashi bane,a'ah......ita kanta taci alwashin hukuntashi a duk sanda ya bayyana cikin gidan,to amma kuma wannan shirun fa?,ba kwana daya ba biyu ba?,ba sati daya ba ba biyu ba?,shi din ba gwanin yin nesa da gida bane,hakanan ba gwanin son yawace yawace ba. Baya shan komai bashi kuma da abokan banza,ina yayi da nesa haka?.

Ita daya cikin dakin nasa bayan aba ya fice ya bata guri takewa kanta wadannan tambayoyin. Sai kawai ta fidda wayarta ta soma laluben numbers din mutum biyu cikin abokansa kuma roommate dinsa,wato faisal mus'ab.

Suna gama gaisawa suka cillo qorafin daukewar maina daga makaranta,bayan ya sani lokacine da suke dab da fara jarrabawa,ana da buqatarsa,jarabawa ce me matuqar muhimmanci wadda zata bashi damar shiga gaba ta biyu ta karatunsa,gabar kuma da zata baka tabbacin sake samun gurbi da kuma gindin zama cikin karatun.

Jikinta a sanyaye sukayi sallama dasu suma suna jimanta batun,wai ba'a san ina maina ya shiga ba?,kamar qaramin yaro?,hankalinsu yadan dagu saboda basusan ainihin abinda yake faruwa ba,sundai yima ana alqawarin bincikoshi muddin yana niamy cikin makaranta ko wajen makaranta.

Ji tayi kaman ta sanya hannunta saman kanta tayi kuka. Jarabawar da zasuyin yanzun ya jima yana bata labarinta tare da buqatar addu'arta. Ta tabbatar bawai qanqanin abu bane zai sanyashi tafiya ya barta ba,amma kuma tana saka ran ko ina ya shiga jarabawar dake tsaye a ranshi zata koro musu shi.

Da daya da daya take kiran duk wanda tasan zata iya samun wani abu game da maina,saidai har ta gama kiran aqalla mutum ashirin cif ba wanda yaga koda gittawarsa. Dole ta sare ta kuma tabbatar zaiyi wuya idan ba wata GAGARUMAR K'ADDARAR bace ke shirin sake tunkarota.

"où est-il allé?(ina ya tafi?)" Ta yiwa kanta da kanta tambayar da itama amsarta take nema.


********K'arfe sha daya ne na safiyar ranar asabar wadda ke dauke da yanayi maras zafi duk da cikin yanayin zafin ake. Saidai a ranar sosai zafin ya sassauta saboda alamu dake bayyana yiwuwar samun ruwan sama kowanne lokaci. Cikin gidanma babu wata hayaniya,don kusan duka yaran gidan sun fita da safen saboda yin siyayyar komawa makaranta a ranar litinin dinnan me zuwa.

Cikin qawataccen falon ama din wanda ke dada qara nuna alfarmarta da alfarmar dawwamar arziqin masu gidan,tamkar ma basu taba wani zamani da kalmar babu ta ratsa ta tsakaninsu ba. Sultana ce zaune saman daya daga cikin royal chairs na dinning din.

Cikin wata irin nutsuwa take zaunen,tana sanye da wasu cotton kaya hot pink. Gown ce me gajeran hannu data saukar mata har gwiwa,sai wandonta da ya lafe a jikinta. Kanta off_white silk scarf ne da ya lullube asirin sassalkan gashinta wanda ke daure a siririn band, yafi qarfin boyuwa ta cikin scarf din don haka ya fiddo ta qasansa ya bazu zuwa sassan kafadunta.

Warwaraye ne sirara guda hudu da ama ta siya mata a nigeria masu kyau masu kalan gold jere a kyakkyawan hannunta,ta sanya yatsanta guda daya tana wasa dasu ta hanyar warasu da kuma hadesu waje daya.

Tun daga qofan kitchen da ama ke takowa dauke da kofin madara take qare mata kallo. Cikin wata biyu da faruwar abun qaramin fadi tashi tayi ba wajen ganin sultana din ta farfado. Ciki kuwa harda dauketa da tayi sukabar nijer gaba daya suka tafi nigeria. A nigeria dukka tayi wasu yaqin,ta kuma samu nasarar don sultana din ta soma komawa hayyacinta. Burbushin damuwa da suka ragewa zuciyarta kusan dukka ta ciresu,ta karbi zaman Nigeria da kyau,ta canza sosai,abinda ya yiwa kusan kowa dadi. Duka duka basufi sati guda da dawowa ba.

Yanayin zaman da sultanan tayi saman kujera ya tabbatarwa ama wani tunanin takeyi. Abinda kuma sam bataso kenan,amma dan adam ne,duk yadda takai ga qurewa wajen ganin ta bata kulawa dole akwai abubuwan da bata isa ta hanata ba,dadin da takeji cikin ranta kawai shine sauyi da take sake samu,ta soma yin wani irin fresh,haskenta tamkar ana qara mata shi,qiba ce har yanzun babu ita sam.

"Tunanin me akeyi?,a bawa ama labari" ama ta fadi sanda ta isa gabanta tana jan kujera guda daya dake kusa da sultana din tana zama.

Dago fuskarta tayi suka hada idanu,sai sultana din ta dan saki murmushi,alamun kunya dukka suna nunawa cikin qwayar idanunta. Zata iya cewa ba zata iya tuna zaqi ko dandanon soyayyar uwa ba,amma adan tsukin da tsautsayin ya saukar mata ta samu dukkan wata kulawa da d'a ke samu wajen uwa. Wani irin sabo me tarin yawa ya shiga tsakaninta da ama irin wanda bai taba hadasu ba,har wasu lokutan idan ta kebe take mamakin ashe dama haka take da kirki?,ashe da gaske ne abinda su aminata ke fadi a kanta a baya?.

"Ba komai" ta fada da wani irin sanyi wanda ya soma zame mata dabi'a,sanyin da abaya sam sam sultana bata sanshi ba cikin rayuwarta.

"To Allah yasa,maza ungo" aman ta fada tana miqa mata mug din hannunta me dauke da madarar shanu data tafasa mata ita da duminta.

Bata musa ba ta miqa hannu ta dauka,a nutse takai bakinta sai kuma ta sauke tana duban cup din

"Yaya dai?" Ama data dauki wayarta tana son duba calendar don ganin yau din adadin kwanaki nawa maina ya qara rabonshi dasu ta furta tana kallon fuskar sultana

"Na qoshi" ta fadi a sanyaye tana dan dora hannunta saman wuyanta. Da mamaki ta dubeta

"Amma kaman ke kika cewa bilki a kawo zaki sha ko?" Kai kawai ta dagawa ama,sai ama din ta sake maida hankalinta kanta,cikin sassauta murya tace

"Sultana banaso ki dawo da dabi'ar qin cin abinci fa,don Allah karki maido mu baya kinji?,na lura tunda muka dawo nijer kike gujewa abinci,idan nijer dinne bakiso mu koma nigeria ne gaba daya to" kai ta girgiza mata alamun a'ah,sai kuna wasu siraran qwalla suka biyo fatar idanunta. Ita batasan yadda zata yiwa ama din bayani ba,kwata kwata kamar an cire mata sha'awar abinci,tanason ci amma da ta kaishi bakinta sai taji gaba daya ta qoshi,idan kuma ta tilastawa kanta din dai amai ya fara taso mata.

Ama ta lura da hawayen,hankalinta yadan dagu ta ajiye wayar tata saman table

"Idan kina da damuwa ni mamarki ce ki gayamin sultana" ta fadi mata tana ritsata da idanu.

"Ba komai,kawai qoshi nayi" ta bata amsa tana saka yatsunta tana dauke hawayen

"Ko madararki za'a kawo miki?,yanzun sai nayi waya niamy su sakota a jirgi don tafi saurin zuwa?" Kai ta sake girgiza mata alamun dai a'ah. Duk yadda ta rayu da qaunar madarar da shauqinta da kuma jin gardinta gaba daya yanzun bata burgeta

"Zansha wannan din anjima"

"Kinyi alqawari?"

"Eh" ta amsa mata,sai ama ta gyada kai sannan ta maida dubanta ga calendar din.

Lissafinta dai dai yake,kwanakin shurawa suke tamkar cikin mafarki,duk yadda take tunanin zuwa lokacin zai nemesu zai waiwayi gida zai dawo zai kirata koda a waya ne abun ya sabawa tunaninta,babu ko daya a ciki. Tayi cigiya iyakar yinta,har a kafafen tv da radio amma shuru kakeji. Aba kuma ya nade hannunsa yana kallonta,baice komai ba bai kuma sanya baki ba. Koda yaje Nigeria ma acan din su yaaya abdulhakeem fada suka dinga zabgawa kaman su ari baki

"Kuna wasa ne,dan mutum guda kamar batan nama a miya?" Sun kira aba amma har suka gama fadansu baice komai ba,daga qarshe yace dasu

"Aiba yaro bane qarami,ya fimu sanin ciwon kansa ma yanzun,duk inda yaje zai dawo tunda dai ba qanqanin jariri bane" ran uncle abdulhakeem ya baci qwarai,saboda ya fahimci kamar m abun bai dameshi ba. Hayatudden ne ya karba da yake ya fishi sanyi da sauqin kai yayi masa magana shima

"Kuma iyayensa ne,na baku wuqa da nama yaaya,kada ku damu" jin ya fadi hakan sai ya rabu dashi kawai. Cigiyar suma suka baza sosai,amma har suka gama zamansu suka dawo da nijer din da Nigerian ba wani bayani.

Tana shiga fargaba wasu lokutan,tana shiga tunani me zurfi kan yana ina,wanne hannu zai fada?,da waye zai hadu?,sai ta furzar da iska me zafi daga bakinta daidai sanda suka hada ido da sultana. Maida wayar tayi ta ajjiye cikin zuciyarta tana maimaita addu'ar data zama sirri tsakaninta da ubangijinta na ya bawa aliyyun tarbiyyarsa dama lafiyarsa kariya,kada ubangiji ya kamashi ko ya jarabcesu silar zubar hawaye a idanunsu.

"Meye ra'ayinki kan komawa makaranta?" Tayi maganar tana monitoring mode dinta. Ambatar makarantar kadai kuwa ya canza yanayinta din,tayi qas da kanta,saidai kafin tace komai sai ga yasmine ta shigo,rungume da ledar data tabbatar siyayyyar da suka fita yine

"Sultana ga mariam inoussa ita da aicha ousmane,muna dawowa muka gansu wai basusan a nan guraren kike ba,'yan uwan gidansu alhaji saddam ne ashe". Kaf walwala da fara'ar fuskarta ta dauke,ta saki baki kawai tana duban yasmine kafin tayi magana a hankali

"Ki dakatar dasu ki gaya musu bacci nakeyi" ta fadi maganar da iyakacin gaskiyarta ne,saboda a yanzun bata qaunar hulda da duk wadanda ta sani a baya,musamman qawayenta na makaranta dama na cikin unguwa gaba daya. Gani takeyi kowa ma yasan meye ya faru da ita?,kuma kowa kallonta yakeyi da abun.

Turus yasime tayi tana duban sultana,kwata kwata ta canza,ko su dinma ba komai take shiga nasu ko ta sanya baki ba

"Yasmine,jeki ki gaya musun" ama ta yiwa yasmine magana,sai ta amsa tana juyawa tare da barin falon.

Tun a nan ta fahimci tana da buqatar canjin makaranta ne,don haka a washegari lahadi tayi mata register da wata makarantar daban. Makaranta ce me mugun tsada wadda har tafi waccan tata ta bayan tsada kuma tsari. Tasan muddin idan ba hakan tayi ba ba zata sake ba,gwara ta kaita cikin wadanda bata taba sani ba,yadda ba zatayi dari dari ko ta kasa sakewa tayi karatu cikinsu ba.

Duka a ranar lahadin ta sauya mata komai da komai,hatta da ruwa da drinks na zuwa makaranta da zata iya buqata kamar wata 'yar free nursery.

Duk dai a ranar ta fidda mota guda cikin motocinta duk da dama already sultanan akwai motar kaita makarantar,amma tace a ajjiyeta,saboda tana da burin ta sake sabuwar rayuwa,batason komai nata data taba amfani dashi a baya yanzun a dawo dashi,don hatta da sutturu duk uban tulin kayan sawarta ta sanya tanja ta fiddasu,batasan rabawa sukayi tsakanin ma'aikatan ba ko menene oho,itadai duka tayi mata juyen closet nata.



*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 15


*_les jumeaux_*(the twins)???



K'arfe biyu da rabi motocin yaran gidan dake jigilar kaisu makaranta suka fara saukesu,a lokacin ama tana zaune a samanta,tana jin motsi da kai kawonsu,saidai aikin da takeyi ya dauke mata hankali,batajin zata iya saukowa a sannan,saddi ne yana yima kansa komai don ba qaramin yaro bane bare tace zai nemi wani abu daga gareta,sai sultananta da tasan ita dinma indai ba wani abu ta buqata ba ba lallai ta nemi ganinta. Waya ta dauka ta kirayi bilki me aiki tace ta duba mata sultana ta dawo?. Ba jimawa ta sake kiranta

"Ta dawo hajiya"

"Yauwa to,ki bincika ko akwai wani abu da take buqata,idan babu shikenan,sai la'asar ni zan sauko"

"To hajiya" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar. Mintuna biyu rak bilkin ta sake kiranta

"Hajiya qofarta rufe take" dan shuru ama tayi

"Lafiya?"

"Eh kaman lafiya gaskiya don na danji motsinta"

"To yayi,ki rabu da ita wala'alla hutawa takeyi,sai na sauko din"

"To a sauko lafiya" bilki ta amsa mata.

Wayar ta aje tana dan nazari kadan tare daci gaba da aikinta da take gab da kammalawa. Lissafin shekara shekara ne,wanda bayan ta kammala din take fidda zakka haqqin Allah.

Tana gamawa din yadda taso ta zauna ta huta sai tayi sallar la'asar kuma amma sai taji hankalinta yayi kan sultana. Kashe mini laptop din tayi,ta zura tausasan slippers dinta ta miqe tana nufo stairs din.

A nutse ta sauka ta kuma nufi sashen dakunan dake qasa. Tana ratsa falon suna gaisawa da masu aikinta da yau duka basu samu ganinta ba,tana amsa musu tana dosar dakin,har ta isa qofa.

Murdata tayi har yanzu tana kulle,ta kira sunan sultana din sau biyu bata amsa ba,sai ta juya yana yiwa fainusa magana kan ta duba store ta ciro mata spare key.

Cikin qasa da minti daya fainusa me aiki ta dawo da key din ta miqa mata,ta karba ta soma gwadawa har ta samu na dakin.

Dundum yake kamar ba rana ba,cikin mamaki ta kunna fitilar dakin haske ya gauraye,idonta ya sauka kanta sanda take nade tsakiyar gado lullube da qaton duvet. Mamaki ya kama ama ta kira sunanta tana takawa ciki hadi da cewa

"Bakijin zafi zaki rufa haka?,wanne irin bacci ne wannan sai an rufe kai?" Ta furta tana janye duvet din.

Razana tayi ganin yadda sultana din ke qudundune guri guda tana rawar sanyi sosai. Farar fuskarta ta sauya launi zuwa pink color kaman yadda tasan tanayi a duk sanda take zazzabi irin wannan ko wani ciwo. Tun bata kai hannunta ba take iya jin hucin dake fita daga jikinta gaba daya,duk da hakan sai ta miqa hannunta da sauri tana taba sassan wuyanta. Saukar hannun ama a jikinta sai taji kaman an qara mata ciwon,ta maqale wuyan wasu siraran hawayen suna fita daga idanunta

"Ya salam ya Allah" ama ta furta,zafin dake jikinta yayi yawa qwarai,sai ta dauki remote na ac din dake gefan gadon ta soma da kasheta,sannan ta juyo ga sultana din tana zama sosai a gabanta

"Dama dashi kika dawo daga makaranta?,tun yaushe ne?" Ta tambayeta cikin tsananin damuwa

"Tunda na shiga classe(class)" kai amma ta girgiza tana jin hankalinta yana daguwa

"Bari na kira Dr chafa'atou,zafin zazzabin yayi yawa" ta fadi tana sauka daga saman gadon sannan ta koma zuwa sassanta da gagggawa.

Qasa tayi da kanta tana lumshe idanuwanta bayan fitar ama. Wasu hawayen masu zafi kwatankwacin zafin zazzabin jikinta suka biyo kuncinta. Ita daya tasan me takeji cikin jikinta,tanajin kamar ana kama qasusuwanta ana ballasu daya bayan daya,kowacce gaba ta jikinta ciwo take mata sosai. Wasu sabbin hawayen suka kuma biyo idanunta,tun daga wancan ranar...... tun daga randa yayi mata fyade......tun ranar da ya zalunceta ya cuceta bata sake samun lafiya ba......bata sake jin qarfi cikin jikinta ba,ya tafi da dukka kuzarinta,ya tafi da walwalarta da kuma farincikinta,tana jinta a cikin jikinta ita karan kanta kamar ba sultanan bibi ba,kamar ba itace ke rayuwa a wannan gangar jikin ba.

Dukka wayoyinta ta debo ta dawo dakin tana gwada layukan wayar Dr chafa'atou. Bude qofar dakin ya sanya sultana bude fararen idanunta da suka sauya kala saboda tsabar zafin zazzafin dake fita a jikinta

"Sannu sultana.....sannu" ama ta fadi cikin kulawa ainun tana zama saman bedside drawer tana kuma sauraren wayar Dr chafa'atou dake ringing.

Dab da zata katse ta daga,cikin girmama juna suka gaisa

"Jikin patient dinki ne ba lafiya médecin(Dr)"

"Tofa,me ya sameta kuma?" Dr chafa'atou dake shirin zama saman kujerarta daga can


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login