Showing 291001 words to 294000 words out of 294767 words
Chapter 98 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
abu.
"Daddy...."
"Shshshsh......koma ki kwanta" ya fadi mata a raunane. Haka kawai ta kasa masa musu,ta miqe ta koma saman gadon ta kwanta din. Ta rufe idanunta yafi sau shurin masaki amma ko alamar wani abu me kama da bacci bata ji ba,sai kawai ta bude idanun nata ta azasu a kanshi wanda yana zaune ne saman abun sallah amma kanshi yana qasa.
Batasan adadin lokacin da suka dauka a haka ba,tadaiji kiran sallah. Tana nan har ya miqe ya sake alwala
"Ki shirya Idan na dawo daga masallaci zamu fita" kasa tambayarsa tayi har ya juya ya fice. Kawai dai taji jikinta gaba daya yayi sanyi kamar an zare mata laka. Duk da tana da alwala amma saita koma ta sake dauro wata.
Tana idar da sallar kawai taji kuka ya qwace mata,kukan da batasan dalilin zuwansa ba,ta kuma kasa tsaidashi. Ko sanda taji ya bude qofar ta kasa daga kanta ta kalleshi,tana jinsa ya dauki key da wayarsa ya jefa a aljihu,sai ya miqa mata hannu ya tayar da ita
"Sulthana" ya kirayi sunanta kai tsaye abinda ya jima baiyi ba. Daga kanta tayi ta kalleshi
"Kukan na meye kuma?,uhmmmm?"
"Inaji a jikina akwai abinda yake faruwa" ta fada muryarta a rarrabe da muryar kuka. Jikinsa ya jawota ya rungumeta tsam yana kiran sunayen Allah daya bayan daya. Yadda taji zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri ta tabbatar ba lafiya ba,amma albarkacin kiran sunayen Allahn sai taji nutsuwa ta saukar mata.
Kusan mintuna goma sukayi a haka sannan yaja hannunta,ya bude ma'ajiyar takalmanta ya bata takalmi yaja hannunta suna ficewa daga dakin.
Bai tashi kowa ba cikin gidan,kamar yadda yaran ba wanda ya tashi,koda birra da ba kasafai ta fiya baccin safe ba. Daya daga cikin motocinsa qanana ya bude ya tabbatar ta shiga seat din driver sannan shima ya zagaya ya shiga ya zauna ya tayar da motar. Baiyi horn ba daya daga cikin security dake gadin mansion house din nasu yana bakin aiki,don haka ya zuge masa gate din suka fice a hankali.
Tun a farkon MAYAK'I street take ganin motoci kadan kadan har suka isa qofar babban gate din da zai sadaka da cikin gidan. Gabanta ya yanke ya fadi,tunda take tun kuma tasowarta bata taba ganin gate din gidan nasu a wangale haka ba,sai taji gaba daya hankalinta yayi cikin gidan kamar ana tunzurata.
Ya fahimci hakan,don haka yayi parking dole a waje,yaje ya bude mata ya kama hannunta zuwa ciki. Idanunta sunga almu sunga atta sun kuma ga saddi, kowannensu kuma kuka taga yanayi,duk kamar an wanke mata kai ta bisu da kallo daga bisani zuciyarta tayi wani irin bugawa data sanyata saurin kama kalmar
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, astgafirullah ya Allah" ta dinga maimaitawa.
"Wa muka rasa?,waye ya rasu?,karkuce aba,kada kuce ama,kada kuma kucemin bibi!" Ta tsaresu atta da tambaya. Kiran sunan bibi din ya sanyasu juyawa,hakan ya sanyata neman birkicewa.
Isowar inna murjana 'yaruwa ga Bintou kakarta wajen ya sanyashi sakin qatuwar ajiyar zuciya baisan ta yadda zasu fuskanci wannan babban tashin hankalin ba,shi ko sultana.
Ita ta riqeta,sai ta bita kamar raqumi da akala har suka wuce sassan bibi din.
Duk wanda yake falon tabi da kallo,kowa yana nan,kowa ya hadu,dukka uncle's dinnata dama yaran gidan kowa zata iya cewa ta ganshi a falon,inna murjana taci gaba da jagorantarta har bedroom din bibi. Bai yarda ya barsu ba sai yabi bayansu.
Dukka matan su oncle issofou suna wajen,tana dauke idanunta daga kansu sai ya sauka akan abinda ya dimautata gaba daya.
Tana kwance cikin lullubin farin abun rufa,wanda a take zuciyarta ta gaya mata bibi ce,babu wadda ke kwance a wannan wajen sai bibi,taga kowa a gidan banda ita. Taga fuskar kowa amma bata ga ta bibi ba,duk wata jijiya dake jikinta ta gama shaida mata hakan,don haka bata tsaya jira ko sauraren kowa ba ta nufi inda take kwancen.
Tana daga mayafin saman fuskarta ta fita tarwai. Cak taji komai nata yana neman tsayawa,kama daga bugun zuciyarta zuwa fitar numfashinta.
"Alhayyul qayyumu!" Ta fusgi sunan da wani irin qarfi,cikin cikakkiyar ma'anar sunan nashi kuwa sai numfashinta ya dawo daidai,saidai gaba daya jikinta yayi rauni don haka ta zube ta saitin kan nata
"A yanayin da naji jikina na tabbatar wani bangare na rayuwata ya tafi,na rasa wani sashe na rayuwata,wani mummunan abu zai faru dani,ashe kece zaki tafi bibi,ke zaki tafi ki barni,me yasa bibi?,ban shirya rasaki ba.....ban shirya rayuwa babu ke ba......ashe da kikace min aliyyu ne madadinki?,maina ne makwafinki abinda kike nufi kenan?,ashe da kikace kin barwa Aliyyu ni wasiyya ce kike yimin?,ashe tafiya zakiyi da gaske ki barni?.......me zan miki bibi idan ba addu'a ba?" Take kaman an zuba mata wani abu tasirin hassan gwarzo ya dawo mata,tarin addu'o'in da aka koya musu da yadda ya kamata ka yiwa mamaci.
"Ya ubangiji gata nan.....me yawan zumunci ce.....me jin qan marayu ce......me kula da bayinta ne......wadda bata yarda zumunci ya samu tasgaro,ya ubangiji kajiqanta da mafi girman jin qai,kayi mata rahama cikin tarin rahamarka......ya Allah......ta kula da maraicina.......dama na sauran marayun dangi wanda ta sani da wanda bata sani ba......ya Allah,ka cika mata alqawarin nan da annabin rahama ya yiwa duk wanda ke kula da marayu na zama maqoci ga shugaban halitta a aljanna......Allah kasa kabarinta ya zama dausayi daga dausayin aljannah......Ya Allah ka san ita wacece a wajena.......Allah kafi kowa sanin irin girman rashin da nayi.....Allah ka bani ikon jurewa......bibi ki yafemin dukkan wani bacin rai da fargaba dana sakaki,daga randa kika karbeni a tsumman goyo har zuwa yanzun nan......Allah ka sanyamin dangana da haquri akan rasa bibi.....rashi na har abada......" Daga nan numfashinta ya qwace mata,ta tafi luuu ta kifa saman fuskar bibi da tayi wani haske kamar ka kirata ta amsa.
Kafin kowa ya isa wajen shi ya isa,ya saka hannunsa gaba daya ya dagota luuuu. Gaba daya jikinta ya cika,ba alamun numfashi a tattare dashi. Kiran sunanta ya fara yi yana jijjigata cikin tashin hankali,sai kuma ya fara keta mutane da sassarfa yana fita daga dakin ba tare da yana fahimtar abinda suke fadi ba.
Sai daya zagayo zai shiga motar bayan ya sanyata a ciki ya lura tuni almu na mazaunin driver,aminata na bayan tana kuka sai kawai ya koma ya umarci aminata ta koma gaba ya maye gurbin aminata yana sanyata a jikinsa.
Gudu almu yake tsalawa amma gani yakeyi kamar tafiyar hawainiya yake. Bai dauke idonsa kona minti guda ba a kanta har suka isa babban private hospital da suke zuwa.
Suna dagata don shiga da ita ciki saiga jini ta qasan doguwar rigar baccin jikinta,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna cikin reception yana kiran sunan Allah. Neman agajin ubangiji yakeyi,ko menene zaya faru ubangiji ya bashi qwarin zuciyar karba da hannu bibbiyu. Cikin qasa da minti.biyar wannan zuciyar ta aliyyu haidar ta dawo ganganr jikinsa,ya yunqura cikin matuqar jarumta kai tsaye ya wuce dakin da suka shigar da ita.
Dashi akayi komai,kuma shima da kanshi ya fahimci cikin ne yake barazanar zubewa,dole ya amince akayi mata daurin mahaifa. Dr Noor ta qara masa haske da bayanin yadda za'a kula da ita,ta samu hutu sosai ake buqata da kuma zama waje daya.
Basu wuce awa biyu ba wasu daga cikin yan gidan sukazo ganin yadda take,ama bata samu fitowa ba amma ta kirashi kusan sau biyu. Zuwa lokacin ya tabbatar an binne bibi,sai ya zauna kawai yana nazarin rayuwa
"Yanzu bibi ta zama tarihi?" Ya tambayi kansa da kansa. Ta yaya zai mance da bibi?,itace qashin bayan nasararsa a rayuwa,itace qashin bayan komai,itace tushiya masomin dawa.
Da kuka ta farka,hankalinsa ya sake tashi saboda ba'a son wanann tashin hankalin daga gareta. Oncle issofou yana gurin da oncle tahir,su suke da qwarin gwiwar fara dorata akan bigiren tayar da imaninta ta fannin yarda da qaddara.
Bawai bata yarda da QADDARA ba,amma tana ganin komai kamar ba haka bane,kamar a mafarki ne,yau cikin duniya babu bibinta,uwa kuma kaka sannan mahaifiyar kaka duka a wajenta.
Dole aka dakatar da masu zuwa dubiya,aka barshi daga shi sai ita. Ya bata dama sosai tayi kuka,har shima ya dinga hadiyar zuciya yana sauke ajiyar zuciyar a jejjere. Sai daya tabbatar ta samu sassauci da rangwame duk da yasan mutuwar bibi abune da ba zaya taba barin zuciyarsu da rayuwarsu ba,sannan ya fara lallashinta da kalaman da suka sake zabge wani kaso na zallar tashin hankali da damuwarta.
"Zan zame miki bibi kamar yadda na zame miki momma nafessa da abba hamani da abba mohmoud...... nayi miki wannan alqawarin ba zaki sake kukan rashin bibi ba daga yau,saidai ki tunata kiyi kewa ki mata addu'a" hannayensa ta kamo ta riqe da kyau
"Kayimin alqawarin ko meye na haifa indai mace ne khadeeja ce kuma bibi"
"Ko biyar kika haifa kikeso a saka musu sunan shi za'a saka musu,amma muddin kinaso ki cika wannan burin saikin kwantar da hankalinki,lafiyar abinda yake cikinki ya inganta,ki haifota da cikakkiyar lafiyarta wadda ita zata bada wannan damar ta sanya sunanta" wata ajiyar zuciya me qarfi ta furzar tana kwantar da kanta saman kafadarsa tana kuma sake gayawa kanya dole ta samawa zuciyarta nutsuwa,tana da buqatar haifarwa bibi ta kwata yadda sunan zaici gaba da wanzuwa a ahalinta.
Washegari suka sallamesu don ta tilastawa kanta haqurin dole kodon lafiyar abinda yake cikinta. Ta koma gida akaci gaba da karbar gaisuwa da ita,tayi qoqarin cika zuciyarta da tawakkali,saidai ko sassan bibi ta kasa shiga har akayi komai aka gama. Duk abinda Sharia tace game da rabon gado da sauransu aka aiwatar,inda aka samu kaso tsoka da bibi din ta ware ta rubuta da sunan sultana koda bayan ranta. Dukkansu sunfi qarfin haka,sultana kuma tafi qarfin komai a wajensu,aka tattara dukkan abinda ta bata din aka damqa mata,saidai tashin hankali ya hanata daga idanu ta karba,sai maina ne ya tsaya akan komai.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 157
*_Bayan shekara uku_*
Kyakkyawar farfajiya ce da ake wareta cikin wani sashe daga sassan MAINA HAMIDOU mansion house aka mata wani irin yanayi na musamman da fararen duwatsu masu daraja da tsada,aka sanya mata rumfa da kujeru na kaba masu dadin zama da baiwa zuciya nutsuwa da ruhi.
Kyakkyawar farar ba'abziniyar nan,ma'abociyar shimfidadden kyau me matuqar jan hankali da wani qira ta jiki da baya nuna tsufa ko adadin shekaru wato SULTANA HAMANI 'yar jaridan gidan Tv paris amma ta bayan fage wadda camera bata nuna fuskarta,amma ayyukanta da sunanta ya warwatsu a ko ina.
Takardu da suka system ne masu yawa warwatse a gabanta tana aikin daya janye mata hankali,saidai duk da hakan daga nan inda take tana iya jiyo daddadan muryar benazeer tana karanta suratuttauba,surar dake dauke da bankadar asirin manufukan madeena da suka cutar da ma'aiki S A W sosai. Daya daga cikin yanayi da lokuta kenan da take yawaita godewa Allah da godewa ama data kaita makarantar data qara fahimtar da ita addini ta kuma fahimci alqur'ani da kyau har tana iya fahimtar ma'anarsa sanda ake karantashi,ta kuma cusa mata qaunar qur'ani ta yadda batayi sake ba har sai data tabbatar benazeer da batoul din sun kasance cikin mahaddata qur'ani suna da shekaru sha uku uku a duniya,yanzun shekaru biyu kenan.
Benazeer da batoul sune suka zama madubin aseem waseem da birra,wadanda keda shekara takwas takwas a duniya,suke kuma da haddar izifi talatin kowannensu bisa jagorancin malaminsu na islamiyya da kuma taimakawar benazeer da batoul.
Ta muskuta tana gyara zamanta kenan ta hangi tahowar batoul. Matashiyar budurwar buzuwar nijer usul data gado tsaho da kuma murjewar jiki. Ta qasan idanu take karantarta,tafi kowa kwaso dabi'u na mahaifinta,komai nata a nutse yake har ta iso gabanta ta ajjiye tray din hannunta saman table din gefan sultana din tana murmushi.
Murmushin itama ta saki ta ajjiye takardun hannunta ta zauna sosai,ta saka hannu ta bude tray din da aka lullube tana fadin
"Bari muga me besty yau ta girka.....anata karatu besty tanata girki" sultanar ta qarasa fada tana dariya. Sunayen data basu kenan ita da benazeer saboda tsantsar sabo dake a tsakaninsu. Duk da 'ya'yan ama ne halak malak,amma duk weekend na duniya indai suna qasar wajensu sukeyi,bama su benazeer ba,kusan duka yaran sunfi ganewa zama wajen ama din,don saisu kwashi sati biyu ma basa gidansu suna gidan ama ko family house na MAYAK'I.
"Delicious.....anya ba catering zaki koma ba?" Ama ta fadi tana gutsirar pizza din dake gabanta. Dariya batoul ta qyalqyale da ita tana cewa
"Mummy ko asa miki waigi santi kikeyi?" Sai ta saki dariyar itama.
"Bibi!bibi!" Muryar birra ta karade kunnuwansu da kiran sunan KHADEEJATU BIBI da takeyi.
Dukkansu suka waiwaya inda suke jiyo sautinta. Birra din ce ta biyo yarinyar da gudu gudu wadda duka duka ba zata haura shekara biyu da rabi ba. Hannun yarinyar cukuikuye da jilbab dinta tanata tsala gudu,bata kuma tsaya ba har ta iso gaban sultana ta fada jikinta tana ruqunmeta,kafin daga bisani birra ta iso cikin fushi ta tsaya a gaban sultana tana haki.
"Me kuma ya faru?" Sultana ta tambayeta hannunta saman lallausar sumar bibi
"Mummy.....wallahi yarinyar nan batason makaranta kwata kwata,tun dazu nake maimaita mata ayar da anty B tace na koya mata amma taqi fada?"
"Gado ba karambani ba" muryarsa ta ratsa wajen. Dukkansu suka waiwaya suna dubanshi fuskokinsu dauke da murmushi,yayin da bibi dake kwance cinyar sultana tuni ta fincike ta tsinka da gudu ta nufeshi.
Aliyyu hamidou MAYAK'I,a responsible father.....uba ba ga 'yayanshi kawai ba.....hatta ga matarshi da sauran ahalin MAYAK'I. Cikin shigar ba'abzinen asali harda rawaninsa,shigar da take qara mata soyayyarshi,take kuma sake fidda sigar kyansa haiba kamala harda kwarjininsa. Tun da safe da zai fita yayi shigar take masa tsiya.
"Wannan kakar tawa ta musamman ce.....ku barmin abata,gadon qin son ecolé tayi,ku barta da sannu zata fara so tunda 'yanuwanta suna so". Kafada birra ta maqale
"Dama tace ba zaka bari ayi punishing nata ba daddy"
"A'ah zanyi kuwa muddin taci gaba da qin makaranta" ya fadi yana kama kumatunta,ita kuma ta qyalqyale da dariya tana boye kanta,daidai sanda 'yan samarin tagwayen guda biyu aseem da waseem sanye da shiga sak irin ta mahaifinsu suka shigo hannunsu dauke da leda.
"Ku kaiwa anty batoul ko anty benazeer ta bawa kowa nashi" ya fadi bayan ya karbi leda daya ya sauke musu birra. Ciki suka dunguma sunata hayaniya irin ta 'yan uwa a tsakaninsu,dashi da ita suka bisu da kallo cikin jin alfahari da yaran nasu har suka bacewa ganinsu.
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsawa saman kujerar da take kai ya zauna daura da ita fuskarshi shimfide da murmushi ya miqa mata tattausan hannunsa me dauke da zara zaran yatsun hannu
"Barka da gida rabbatul_bait" nata hannun ta cire ta miqa masa,ya sanyashi tsakiyar nasa hannun,dumi da taushin tafin hannun nata ya ratsashi. Komai nata na dabanne na musamman kuma,ya tabbatar ko iya yanzun da zai shanshana tafin hannunsa ya gogi wannan lallausan qamshin da tafin hannunta baya rabo dashi
"Barka kadai abul_bait......barka da dawowa cikin iyalinsa" murmushi ya subuce masa yana shaqar daddadan qamshin KABBASA da kowacce sutura tata takeyi
(Sirrina kenan)
"Na gode......har yanzun kinqi gayan sirrin wannan qamshin,qamshin da nake fita dashi cikin qwaqwalwata na dawo kuma na tarar dashi" murmushi ta sake masa,yanason qamshin turaren matuqa,kuma koda ta sauya wajen siya saiya gane
"Tafiyayye ne daga Nigeria,NAI perfumes"