Showing 117001 words to 120000 words out of 294767 words
Chapter 40 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
zuciyarsa ba dadi na tsakin da tayi masa
"Goumar" ya kirashi kai tsaye
"Kay...."
"Shshshsh.......wannan ba huruminka bane,kayi kaman bakaji ba,zanyi handling abun...... BINTOU da NADEEYA keson sanin waye daddynsu?" Ya masa tambayar yana maida wayar free. Murmushi mai sauti ya fito daga bakin goumar har sautin nasa yana bayyana
"Kaine daddynsu....... wanda na taba nuna musu uncle haidar shine daddy maina daddy aliyyu,ya dawo daga tafiyar da yayi,kuma dama ya musu alqawarin zai dawo din" kamar shiri kamar hadin bala'i dukkansu suka saki qaramin ihu suna ruqunqumeshi. Kashe wayar yayi yana murmushi ya hadasu dukka shima ya rungumesu.
A nan saman cinyarsa suka kwanta,ya shiga basu labarin quruciyarsa da na sultana saidai kuma iya abubuwa masu kyau da zasu basu dariya ko suyi musu dadi yake gaya musu. Sannu sannu dukkansu bacci ya daukesu,ya miqe ya kwashesu gaba daya ya maidasu saman gado ya kwantar,sai ya kasa tashi,ya sanyasu a gaba yana kallonsu,hannunsa cikin tafukan hannayensu.
Tunda Allah ya jarabceshi da soyayyar yaran yake tambayar kansa why?,me yasa yake mutuwar sonsu haka?, duk tarin twins din dake Instagram me yasa sai su?,jikinsa yasha bashi ba'a banza ba, zuciyarsa kuma ta taba raya masa sau daya TABBAS YANA DA DANGANTA DASU TA KUSA KOTA NESA,saidai kuma ya qaryata hakan, din yayi lalubensa kaf baiga ta inda zasu hada dangantaka ba.
Murmushi ya sake kufce masa,ashe ubangijinsa ya cika masa muradinsa ba tare daya sani ba?,yara matan da yasha alwashi ya kuma jima yana yiwa ama alqawarin kyautar mata dasu ashe Allah ya jima da cika masa burinsa?,ya sani koda ba'a gaya masa ba sunsha gata da kalar kulawar da ba kowanne yaro ke samu ba.
Tsakinta na dazu ya sake dawo masa fes a kunnensa,sake cije lips din nasa yayi ya girgiza kansa kadan,bata canza bane ko da saura?, Ya jefawa kansa tambayar. Lallai zai dauki komai amma banda raini, wadannan tsakin akwai buqatar nuna mata bai kamaci tayi masa shi ba,tabbas.........
*_maina sarkin son girma😂,me karatu kada fa ya qara b'aro wani aikin muzo mu hadu da wasu twins din?,ba ruwan HUGUMA dai_*
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 62
Cikin jikinsa yaja yaransa bayan ya gama shafa'i da wuturi,ya rungumesu tsam suna jin dumin juna yana sauke ajiyar zuciya. Sai yanzu yake sake tabbatarwa lallai jininsa ne,lallai wani bangare ne na jikinsa. Ni'imtaccen bacci yayi wanda ya jima baiyi irinsa ba cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,haka yaran suma,babu wadda ta motsa a cikinsu haka suka qarar da daren.
Juyi kawai ta dinga yi tana tuna yaran,sam bacci ua qauracewa idanunta,tana tsoron kada ya aiwatar sa abinda ya fada din,don ta gama sallamawa shegen kaifin maganarsa guda daya kafiya da taurin kansa. Batasan haka take qaunar yaran har cikin jininta, batasan haka zuciyarta ke mutuwar qaunar yaran nata ba,bata taba kuma kawowa haka take jinsu a ranta ba sai a wannan daren,ta jima tana juyi kafin daga bisani baccin yayi awon gaba da ita.
********Tunda sukayi sallar asuba washegari basu koma ba,shi dasu zaman hira sukayi,duk wata tambaya idan sukayi masa haka zai amsa musu,hakanan shima ya sakasu gaba da tambayoyi. A nan din ya samu information sosai akan sultana,wasu abubuwan da bai sansu ba sakamakon yankewar sadarwa tsakaninsa da goumar dukka yaji a bakinsu benazeer. Shuru yayi yana sauke boyayyar ajiyar zuciya,tausayinta yana sake illata masa zuciya. Yana da buri sosai a kanta,burin da yasha banban da burinsa na baya,amma kuma dukka abinda zai gudanar dole saida hadin kanta.
Yana tsaka da wannan tunanin wayarsa ta dauki tsuwwa,batoul dake game a ciki ta miqo masa a nutse yasa hannu ya karba yana mata murmushi. Daddy ne,alhj Bello Muhammad mahaifin sardauna......mahaifin kuma laila..... Mutumin da ya zame masa bango jigo kuma makwafin mahaifi. Tashi yayi ya zauna sosai yana jin wani iri,bai kyauta ba kwata kwata,duk kansa ya shiga kawuna,sam baiyi kiran daddy din ba tsahon kwanaki,abinda kuma bai saba ba.
Yana qoqarin gaidashi shi kuma yana qoqarin tambayar lafiyarsa
"Lafiya alhamdulillah daddy"
"To ma sha Allah......'yar rigimarka ce ta sakani a gaba,wai na binciki lafiya kake?,ka zama wani mugun busy kwana biyu" sumarsa ya yamutsa,laila tana daureshi da jijiyar jikinsa,duk sanda ta hada lamarinsu da daddy din a ciki sai ya zamana kamar ta masa dabibayi ne. Ko dazun bayan asubah da ya tashi yaga saqonta,yayi mata reply ne ya zame masa jidali har kawo yanzu.
"Lafiya alhamdulillah nazo wajen family nane.....ina da buqatar lokaci ne daddy,akwai matsaloli da nakeson gyarawa" ajiyar zuciya ya saki yana jin farinciki yana ratsashi. Tunda suke da maina din tsahon shekaru uku bai taba zancan gida ba,hakanan shima bai taba tilastashi game da komai nasa ba,amma a matsayinsa na uba kuma mahaifi ko yaushe yana da wannan tunanin a ransa,dole kuwa a yanzu yayi farinciki
"Ma sha Allah, alhamdulillah,to Allah ya yaye damuwa ya shiga lamarin"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu daddy na gode sosai " ya fadi har qasan ransa yana jin kimarsa tana sake qaruwa. Mutum ne me tsananin dattako,kamili na gaske wanda yasan abinda ya kamata
"Gashi karbi" daddy ya fada yana miqawa laila wayar. A dan kunyace ta karba sannan ta miqe tana barin wajen,ta tabbatar yau din zata samu kulawa data d'ara wadda ta saba samu.
"Yaa maina.......barka da warhaka" ta furta tana karyar da murya
"Barka kadai laila......kina lafiya?"
"Uhmmm......to, lafiya alhamdulillah,amma ba lafiya sosai ba"
"Me yake faruwa?" Ya tambayeta cikin son nuna kulawa
"I missed you so much yaa haidar,and it's killing me wallahi" tayi maganar tana fita daga tsakiyar zuciyarta da gasken gaske. Ido ya lumshe sannan ya budesu,bayason yadda kullum kwanan duniya take sake zurmawa cikin soyayyarsa,baisan ta yaya akayi ta fara sonshi ba,baisan kuma yaushe ba,tabbas ba shakka da bazai barta ta fara ba. Har yanzu zuciyarsa jaririya ce akan soyayya,yana jin kamar rainonta yake, zuciyarsa batayi fadi da girman amsar kalolin soyayya ba
"Ina gida as i said......ina wajen family na......ga 'ya'yana su gaisheki" ya furta da zummar cimma manufar dake qasan ranshi
"Yayanka?,when...... yaushe ka haihu?" Murmushi me sauti ya fidda
"It's a long story........ batoul ga aunty laila" ya fadi yana hadasu da wayar yayin da ya koma yayi relaxing jikin kujera yana kallonsu.
A qalla sun kusa mintuna biyu kafin su miqa masa Wayar,ya karba ya saka a kunnensa
"Yayanka ko yaran cousins naka ko yaran sisters dinka?"
"My biological daughters" d'if tayi na wasu sakanni kafin ta furzar d numfashi
"Okay...... okay,it's ok,see you later?,zaka kirani?,ko ni zan kira?" Ta tambayeshi tana karyar d wuya,maganarsa ta yanzu kuma tana dukan zuciyarta
"Idan kinji shuru zaki iya kiran nawa na bada dama" qaramin murmushi ta saki
"Thanks,bye.....ka kula da kanka please"
"Na gode" ya amsa mata a taqaice,sai ya zame wayar yana kallonta.
Yayi tsammanin daya gaya mata wannan zata rude ne,ya dauka zata katse wayar,ya kira kuma taqi dagawa,ya zaci zatayi fushi,sai yaga dukka babu wannan a tattare da ita.
Har rana yayi kawai yana zaune cikinsu suna sabgoginsu,yayi musu doki,ya dora wani a bayansa wani a qafafunsa,suyi wasan buya dukka. Abinda ya sake haifar da wani irin shaquwa tsakaninsu qasa da awa ashirin da hudu. Sukayi wani mugun sakewa da shi,qauna da soyayyar nan dake tsakanin mahaifi da 'ya'yansa ta sake bubbuga sosai,duk wata soyayya ta motsa qwarai. La'asar liqis suka baro hotel din,ba kuma gida ya nufa dasu kai tsaye ba,yayi kiran hadiminsa ya bashi jan motar suka wuce wani qaton mall dake garin marad'i.
Siyayya ya dinga yi musu harda ta hauka,sosai yake jin kansa a matsayin mahaifi,yake kuma son ya soma taka wannan rawar,yake muradin ya amsa sunansa na mahaifi din. Sanda yake musu 'yan tambayoyi don sanin abubuwan da ba lallai ya jisu daga bakin ama ko wani a gidan ba.....sai zuciyarsa dukka ta raunata,ya fahimci tsantsar gatan da ama ta nuna musu,kulawa da sadaukarwar da aba ya musu. Ya sani koshi ne a wajen ba lallai ya musu irin wannan gatan da suke samu, zuciyarsa sai ta sake rauni,qauna da soyayyar mahaifiyarsa ta sake cika masa zuciya. Ita din ta daban ce......mahaifiya soyayyart daban ce kamar yadda take ta daban. Yawan siyayyar motarsu tayi kadan ba zata iya cinyewa badon haka suka zuba abinda zasu iya dauka,sauran kuma ya bada location dinsa sukace zai taras da kayansa har qofar gida in sha Allah.
Daga nan ya sake biyewa dasu ya cikasu da kayan maqulashe,hakanan ya tsinci kansa da yiwa driver umarni suka dauki hanyar wajen tsohon me namansu da bibi da ama ke so sosai,bama su kadai ba harda aba din.
Suna dosar wajen komai yana dawo masa sabo,wajen da yayi silar wanzuwar komai cikin rayuwarsu,muhalli da daga nan aka fara qulla zaren saqar K'ADDARARsu,daga nan komai ya fara.
Daga nesa kadan ya sanya yayi parking,yace su benazeer su zauna cikin motar,sai suka maqale wuya
"Daddy ba zaka dade ba?" Kai ya jinjina yana murmushi
"In sha Allah" ya fadi yana shafa sumarsu,shi kansa yana jin inda zaiyiwu ko na second daya bazaiyi nesa dasu ba,ya janye jikinsa driver ya maida murfin ya rufe.
Lokacin da yayi sallama yana kan hadar hadar killace naman da aka samu gasawa,bayan dadin da namansu ke dashi suna da matuqar tsafta qwarai,wannan ya sanya maina din duk iyayinsa da zabe zaben abinci da yake dashi bai taba challenging namansu ba.
Idanu ya zuba masa sanda yake amsa sallamar,kamannin maina din suna masa yawo a ido,saidai wannan din ba yaro maina bane yake gani,cikakken saurayi da Hankali ya game jikinsa,me cikar zati halitta da wani uban kwarjini dake yawo saman fuskarsa
"Ka ganeni?" Ya tambayeshi yana qaramin murmushi
"Eh to.....magana ta domin Allah naso na shaidaka,amma kuma ina tantama idan kaine din,kamar dai maina ko?,dan gidan alhj hamidou mayak'i?" Kai ya jinjina yana murmushi. Murna ta cikashi ya ajjiye kayan hannusa yana cewa
"Kai,Allahu akhbar....... ashe rai kanga rai,shuru babu kai ba dattijuwar arziqi?" Mamaki yadan kamashi,kenan bibi ma tabar aikowa a siya mata kenan tun bayan da yabar gidan?. Gaya masa yadda yakeso ayi masa yayi yace ya aiko masa dashi mota yanzu zai jirashi. Jikin yahuza na rawa ya soma aiwatarwa,don ya tabbatar yau qila dukka kudin namansa ne zasu fito daga jikin maina din. Kamar yadda ya zata din kuwa,don sai waiwayowa yayi kawai yaga ya ajjiye masa bandir daya da CFA,wanda yayi imanin sun ninka kudin namansa ma,don haka ya zage shima ya cikashi da naman da yafi yawan wanda ya buqata,yana sake jinjina kyauta irin ta jinin 'yan gidan da kirkinsu.
Yinin ranar duka cikin rashin sukuni ta yishi,ta kasa zaune ta kasa tsaye tsakanin sashen bibi dana ama,damuwa ce sosai cikin rai da fuskarta,wanda sai kana da mugun nazari zaka kula da haka. Ta dauka da sassafe aba ama ko bibi zasu tasashi gaba da sababi ya kawo mata yaranta,ko kuma shidin ya kawosun amma sai taga ba wanda ma yayi batun yaran. Sanda taga har azahar ta shigo tana shirin ficewa damuwarsa da fargabarta sai ya qaru,idan ma barin qasar ne tasan zuwa yanzu sun jima da ficewa. Qaruwar damuwar ya ankarar da ama,tana sane,tasan ya kwashesu tun jiyan bai kuma dawo dasu ba,ta fahimci kuma sultana din a dame take,tayi shuru ne saboda ko yaya dai a bashi chance shi da su da zasusan shine mahaifinsu,susan suna da mahaifi,ya kuma yi duk hirar da yakeson yayi dasu din. Idan shi me laifi ne su ai basuyi laifin komai ba,basusan kuma komai ba,bai kamata a lullube musu ubansu ba, shi kadai yayi laifi,shi kadai zai amshi hukunci,abinda ke tsakaninsa da mommynsu kuma ba hurumin yaran bane bare a tsundumasu a ciki basuji ba basu gani ba,bayan suma kawosu akayi cikin rigimar da basusan da zamanta ba.
Yamma lis ta sameta a kitchen tana qoqarin diban abincin rana da bataci ba,don ko na safenma dai tsakurarsa tayi. A iya safen zuwa yanzun aman ta fahimci itama me qulafucin yara ne,wani dalili ne kawai dama yake sawa take nuna halin ko in kula dasu,amma tana qididdige da dukka motsinsu da takunsu.
"Lafiya kike yau kuwa sultana?,ko bakya jin dadi?" Kai ta girgiza,sai taji zuciyarta tadan tsinke,aman bata san abinda ke damunta ba kenan
"Lafiya lau nake ama,kawai kasala nakeji"
"To Allah ya qara lafiya,Alla ya rufa asiri" ta amsata tana ajjiye plate din data shigo dasu ta gama abinda zatayi sultana din na satar kallonta qasa qasa har ta juya ta fice. Ajiyar zuciya ta sauke tana ajjiye abincin data debo din,ta rungume hannayenta ranta na sake baci,magariba na dosowa ya kwashe mata yara tun jiya har yanzu ba duriyarsu?, bacin ran ya sanyata jin qwalla ta cika mata ido,sai tayi qarfin halin son maidasu amma duk da haka sai da suka zubo,ta daukesu tana yiwa kanta fadan
"Ashe har kwanan gobe shike cin nasara a kanki tunda baki daina masa kuka ba,bai daina saka hawayenki zuba ba" wannan maganar ta sanya dole ta jawo jarumta ta azama zuciyarta,ta zuba abinci me yawa kaman da gaske zata iya cinyewa sannan ta juya ta fice.
Ana kiran magariba suna isa qofar gidan,kaman ko yaushe ya sallami driver din ya karbi tuqin motar ya nufo bakin gate din da ita. Horn daya hudu ya qaraso,yaja da baya cikin girmamawa ya bude masa ya shige da motar.
Parking lot na gidan gaba daya cike da motocin 'yan gidan,alamu dake gwada kusan kowa yana gida kenan. Ya tsaida tasa motar ya juyo yana kallonsu benazeer
"Zaku shiga ciki,kuje wajen ama da bibi kuce dukkansu ina gaidasu, benazeer ki bawa ama wannan, batoul ke kuma bibi,zanyi sallar magariba zan shigo daga nan"
"Kada ka dade daddy" batoul ta fadi a raunane. Murmushi ya saki,tausayinta yaji ya ratsashi, yarinyar da alama tana da tsananin qulafuci akan abinda takeso,kamar dai yadda yake,yana fata kada Allah ya bawa mamansu galaba a kanshi,zayaso su rayu tare cikin aminci
"Kada ki damu B na,magarib da isha'i zanyi,zanzo muci abinci tare a wajen ama ko bibi" dan qaramin ihun murna suka saki, murmushi ya kubce masa,sai ya sauka ya bude musu qofar motar suka fice sukayi cikin gidan. Yana shirin kulle motar yaji maganarsa a bayansa, goumar ne da alama shima masallacin zashi,ya qaraso yana dubansa cikin bashi girma kuma yace
"Barka da yamma" yayi gaisuwar yana karantarsa. Daga jiya zuwa yau daya dauki yaran kadai walwalarsa ta qaru,kai idan ma idanunsa sun gani da kyau nutsuwarsa ma ta ninka ta jiyan
"Barka kadai malam oumar me qarya" ya qarasa fada yana dagowa daga rufe motar da yakeyi. Sunan da ya bashin ya sanyashi bushewa da dariya harda dan ranqwafawa,wannan ya bawa maina daman buga masa duka a tsakiyar bayansa, goumar ya gantsare yana jin zafi yana ratsashi. Tun ba yau ba sunsan hannun yaa maina bashi da dadi,shi yasa ba kasafai suka fiya son yi masa laifi ba
"Bayana yaa maina"
"Eh,ai bansan me zanyi maka na huce ba,ashe kaima da nake ganinka me imani ba imanin gareka ba,twins fa?,ashe nawa ne?,nayita kwana ina tashi da begensu?,kacemin yaro guda ta haifamin,ashe jaruma ce ita din" ba shiri goumar ya qyalqyale da dariya. Wato har wani sunan jarumta ya bawa sultanan,saboda baisan ainihin fadi tashin da akasha kafin yaran su rayu ba a cikin mahaifarta,tashin hankalin data dinga yi,saidai duk da haka yanason bashi abinda zai karya lagon bibi sosai
"Eh to,zaka iya kiranta da hakan......amma kasan banda tsananin rabo da tuni bibi ta sanya an markade maka yara tun suna 'yan tayi?" Dif wuta ta dauke masa,Girarsa ya tsuke saboda kasa fahimtar abinda goumar ke shirin gaya masa
"Kaman yaaya?" Ya tambayi goumar din yana sakin wuyanshi da ya riqe,miqewa tsaye sosai goumar din yayi yana gyara rigarsa
"Eh,so tayi a zubda cikin,wai sultana tayi qanqanta,wannan ai shine silar tafiyarsu Austria da nace maka sunyi a sace" Ajiyar zuciya ya sauke tamkar zata fito hade da zuciyarsa,sai yaji qafafunsa sun kasa daukarsa,ya koma ya jingina da motarsa. Ba komai goumar yake gayanmasa ba kenan,akwai abubuwa da yawa da bai bashi information akai ba. Inda bibi ta aikata masa hakan ya tabbatar babu wani abu da zatayi wanda zata wanke kanta,kuma yasan tabbas a lokacin da goumar ya gaya masa abinda bibi ke shirin yi kenan......yayi imani duk yadda yake