Showing 87001 words to 90000 words out of 294767 words

Chapter 30 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

gaske yana rayen kenan kamar yadda goumar yasha gaya mata?.......kenan hakan yana nufin watan watarana zai dawo zuwa cikin rayuwarsu?,ama tasan yana raye?,yana kuma kusa dasu?,aba fa?" Tambayoyin da sukayi mata tsaiwar mashi aka kenan,saidai daga bisani zuciyar ta bata tabbacin

"Basu sani ba!,duka tambayarki amsarsu basu sani ba" kanta ta sanya tsakanin cinyoyinta,sai taji kawai babu abinda take sha'awar yi irin kuka,kuka data jima da ajeshi cikin rayuwarta,ta tattara duk wani koke koke tun daga sanda ta soma hankali cikin hassan Ibrahim gwarzo ta ajjiye ayau shi ya dawo mata sabo fil,ta sakeshi a hankali ya soma fita da wani zazzafan tsohon miki.

Daga cikin swissotel tun daga first floor zuwa floor na qarshe baisan adadin sau nawa ya duba ba,daga nan ya sake maida qafafunsa zuwa cikin haram bayan zuciyarsa ta gaya masa ta tafi tayi addu'a,ya zagaye haram har qafafunsa suka soma gaya masa tafiyar ta soma yawa akan wadda ya saba yi.

Duk wani tunaninsa ya kulle,abinda kawai yake iya tunawa sultana ya gani,kuma ita yakeson ya lalubo,baiji gajiyar zaryar da yakeyi ba har sai da zuciyarsa ta ladabtar da dukka gabansa,ya sulale ya samu waje cikin reception din gaba ya zauna bayan ya shafe awanni yana abu daya.

Wayarsa kawai ya sake zarowa,ya lalubi number yayi kira. Cikin nauyin bacci suhail ya daga kiran ya saka a kunnensa

"I thought kayi bacci tun tuni,ko murnar ganin dream twins dinka ya hanaka?" Idonsa ya lumshe yana jin bugawar da zuciyarsa takeyi,shi kam ya manta ma da batun yaga yaran,abinda ya gani yanzun duka ya shafe wannan

"Inason kayima mutanen nan magana,nijer da Nigeria duka nakeson shiga,banzan ainihin inda zan sameta ba,a rage lokacin da aka dibamin,bazan iya kaiwa har sannan ba.......next week zan bar nan".

Duka zantukan sai suhail ya kasa ganesu,don baisan komai akan abinda maina ke magana ba

"Wacece zaka samo?,me zakayi a nijer kuma?"

"Kayi yadda nace please,ayi arranging komai saboda idan na shiga bansan ranar fitowa ta ba sai Allah" yayi furucin duk wani qarfin gwiwa da yake tunanin zai samu yana narkewa daga zuciyarsa

"Are u okay maina?"

"Yes iam" ya bashi amsar dashi kansa yasan ba ita bace haqiqanin gaskiyar yana zare wayar daga kunnensa,sai kawai ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing,idanunsa naci gaba da bibiyar kai kawon mutane cikin wajen,yana jin kamar ya tabbata a wajen har sai ya gano ainihin location nata.

Maida dubansa yayi ga ma'aikatan dake wajen,yayi imanin da zai bincika akwai komai nasu cikin hotel din muddin a nan din ta sauka,to amma bashi da yaqinin daga ina take?,ina ta tafi?,wajen wasu tazo?,duka bai samu wannan information din ba. Number goumar da ya rasa shine mafi girman rashi da yayi a wancan shekarar,ya daina jin komai,komai ya yanke,baisan kuma ta yaya zai sake samo wani abu da zai sadashi da goumar din ba. Abune me wahala su bada information na wani room,ba zasu bada ba,hasalima zai sanya sunyi zarginsa da wani abu. Wannan tunanin ya sakashi qarasa debe duk wani tsammani nasa,ya maida idanunsa ya lumshe,sai ya dinga jin sunayen Allah na zuwa kanshi. Fara maimaitasu yayi daya bayan daya,yana yi a hankali yana samun nutsuwar zuciya da kuma ta ruhi.

Sosai taji yadda idanunta sukayi nauyi suke mata kuma mahaukacin radadi,ko da bata duba ba tasan sunyi kumburin da duk wanda ya kalleta zai fahimci kuka tayi ba na wasa ba.

"Ya hayyu......ya qayyumu..... birahmtika astageesu....hasbiyallahu lailah illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ta dinga furtawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba mugun kusanci bane a tsakaninka da ita kunnuwanka ba zasu iya jin abinda bakinta ke furtawa ba.

Sanda ta duba agogon wayarta sai tayi mamakin yadda lokaci yaja dare kuma ya fara nisa,tasan zasuyi tsammanin ta koma haram ne saboda sun santa da nacin addu'a idan akazo wajen. Ta saba raba dare a wajen,baccinta kuma qalilanne,wannan dalilin tasan shine kadai ya sanya basu nemeta ba.

Dukka wani kuzari da za'a samu jikin dan adam babu shi a jikinta,a haka ta dinga takawa har ta maida kanta swissotel.

Ta samesu dukkansu sunyi bacci,yaran na jikin bibi duk su biyun,da alama tatsuniya ko labaran data saba basu take basu bacci ya daukesun. Taji dadin hakan qwarai,saita lallaba ta daura alwala,daga zaune tayi sallah raka'a biyu amma ta kasa roqar komai,ta maida kanta ta kwantar saman qafafunta wasu hawayen na zirarar mata.

Wani irin wahalallen dare yayi cikin wani yanayi dashi kansa baisan taqaimemen inda ya dosa ba......baisan me gobensa ke tanadar masa ba,kuma har yanzu baisan da fuskar da zai kalli ama ba,ta bibi me sauqi ciki cikin sauqi ma......amma aba fa?. Yafi kowa sanin waye din aba,ya sanshi tamkar yunwar cikinsa,shekara biyar ba wasa bace.....ya sani aba bazai taba aminta da cewa ba GUDUN K'ADDARA yayi ba.....bazai taba yarda cewa SHIKE BIBIYAR QADDARAR BA.....cikin kowacce dama daya samu.....daidai da second daya bai taba daga qafa ba saidai idan DAMAR ta kubce masa.

Yadda ta tashi da zazzabi me zafi haka ya tashi da mugun ciwon kai,saidai ko sau daya bai matsa daga bakin tafekeken window din dake dakin ba me kamanceceniya da qofa,idanunsa dukka cikin sashen harami,shine abu guda daya dake sanya masa nutsuwa da kuma juriya.

Kiran sallar azahar daga masallacin haram shine abinda ya tasheta. Ta bude idanunta a hankali tana qarewa dakin kallo. Ta tabbatar cikin dakinsu take na hotel din,abinda ya bayyana mata inda ta ganta a yanzun mafarki tayi.

Shareren fili ne dake dauke da wani irin farin yashi iya ganinka,ba kowa cikin filin daga ita sai maina din. Wasu fararen kaya ne a jikinsa farare qal matuqa da sukayi kusanci da yashin dake shimfide qasan qafafunsu. Sutura ce irin ta asalin buzaye,ya kuma qawata shigar tasa da nadi irin na asalin ba'abzine,nadin farin rawani shima tas dashi wanda ya sake qarawa fuskarsa wani madaukakin kyau da kwarjini. Tsakaninsu duka duka taku ne baifi biyar ba,ita dinma kuma cikin shigen shigarsa take na fararen kaya,kanta babu dankwali sai iska dake wasa da gashinta daga hagu zuwa dama. Suna tsaye carko carko,kallon kallo sukema juna su duka,a duk sanda maina yadan motsa sai ta matsa baya,sunyi hakan ya kusa sau goma,daga qarshe ta jita caraf a hannunsa,kafin kuma tayi kowanne yunquri ya lullubeta da faffadan qirjinsa. Mutsu mutsun qwatar kanta ta dinga yi amma hakan ya gagara,yanason rada mata wani abu a kunne ne amma taqi bashi dama,daga qarshe ta soma cizonsa tana yakushinsa amma tamkar ba jikinsa takema haka ba........sai muryar benazeer ta bayyana tana qwala mata kira,kiran nata da tayi shi ya sanyata farkawa daga baccin ya kuma yanke mata mafarkin.

Sai data tattara nutsuwarta sannan ta miqe a hankali,ta zauna sosai tana duban jikinta da kyau. Haka kawai ta dinga jin kamar qamshinsa ne cikin jikinta,wannan ya sanya kanta yaso sarawa,ta saka dukka hannuwan nata ta dafe kan nata bacin rai yana ratsa zuciyarta.

Ta tabbatar kuma jikinta yana bata masaukinsa yana a wahen,ko cikin hotel din ko kuma wajen hotel din,muddin kuwa haka ne ya zame mata dole tayi takatsantsan ta kuma kula da kyau harsu kammala kwanaki hudun da suka rage musu subar qasar. Ba zata taba bari wani yaji labarin wai ta ganshi ba,hakanan zatayi duk me yiwuwa ta tabbatar baiga yaranta ba. Wannan tunanin ma ya sanya ta janyo wayarta ta kira number ama.

Bugu daya ta daga, muryarta adan dakushe tayi sallama

"Kin tashi kenan?,mun dan fita siyayya kina bacci,zazzabin ya sauka?" Boyayyar ajiyar zuciya ta ya sauke

"Ya sauka ama,batoul suna tare dake?" Tayi mata tambayar dake qasan ranta

"Eh muna tare....." Ta bata amsa matuqar mamakin tambayar sultanar tana kama ama,saboda abune da bata taba yinsa ba

"Akwai wani abu ne?" Ama ta kasa shuru ta tambayeta,da sauri ta girgiza kai kaman tana wajen

"Ba komai,kawai jiya sai da na fita nemosu ne ama,suna nisan kiwo sosai" mamaki ya sake kama ama,yau sultana ke magana haka akansu batoul kai tsaye?.

"Kinfi kowa sani muddin cikin haram ne ba abinda zai faru,just relax....." Aman ta fada murmushi yana subuce mata. Sautin murmushin ama din ya sanya kunya tadan kamata,saita wayance dayi musu adawo lafiya,ta maida wayar ta ajjiye gefanta tana sauke ajiyar zuciya.

Har yanzun kallon kallon da suka yima junansu a daren jiya ya kasa barin idanu da kwanyarta,hakanan kallonsa na cikin mafarkin me kama dana jiya. Qatuwar tsaki taja,wani irin tsanarsa yana ratsata,ba abinda fuskarsa ke tuna mata sai zallar azaba qunci da jarrabawar daya afka rayuwarta a ciki.

*_Masu karatu......marabanmu da isowa gaba😂😂😂.......wasan zaya fara,sai nace Allah ya hadamu ranar litinin muji_*

*Waye zaiyi nasara?"

*Waye zaiyi giving up?*

*Ta yaya maina zai fuskanci mutum hudu zuwa biyar?*

*Ama*
*Aba*
*Bibi*
*Benazeer batoul*

*Me gayya me aiki SULTANA?*

_ASHA HUTUN QARSHEN MAKO LAFIYA_


*HUGUMANKU CE*🥰*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 47



A nutse ya rufe mas hafin qur'anin dake hannunsa,yayi addu'o'i na wasu sakanni sannan ya maidashi ya ajiye. Wayarsa ya jawo ya bude,makeken hoton benazeer da batoul dake saman screen din wayarsa ya bayyana. Sunyi matuqar kyau cikin wasu pink gown,komai dake jikinsu pink ne,hatta ribbon da aka musu adon ka dashi da qananun dan kunnayen azurfa masu pink din duwatsu ne.

Ajiyar zuciya ya sauke karo na babu adadi,fuskoki ukun wunin yau duka su suka hanashi kuzari ko wani karsashi. Fuskokin yaran da baisan meye hadinsa dasu ba yakejinsu da wani irin qauna me zurfi a zuciyarsa,da kuma fuskar sultana.

Yes,sultana ce,ba wani abu ba kuma wasu shekaru yanayi ko zamani da zai iya hanashi ganeta,halittar daya raina da hannunsa ya bata dukkan kulawa. Ko ina yaronsa?,da waye yake kama?,ya girmansa yanzu?,duk bai sani ba,yana kuma daya daga cikin burikansa a yanzun. Yayi zirga zirga yau din tsakanin haram zuwa cikin hotel tsakanin kowacce sallah amma baiga wani abu da yayi kamanceceniya da ita ba. Ciwon kan da yake fama dashi duka yau bai barshi zama a masallacin ba,dole idan ya idar da sallah yake dawowa daki ya kwanta,amma yanzun da ake shirye shiryen kiran sallar isha'i sai yaji yana da muradin sake fitan. Yanason sake ganin yaran,ko suma sun nemeshi oho?,ko a wanne hotel suka sauka?,duka bai sani ba.

Alwala ya sake duk da wancan bai baci ba,ya feshe jikinsa da turarensa ya sanya qaramar hular da bahaushe ke kira tashi ka fiya naci saman kansa sai gashi ya fita a balarabe sak,ya sanya takalmansa ya fito a dakin.

Yana takawa har zuwa cikin haramin zuciyarsa na masa saqe saqe iri iri,bakinsa da kuma zuciyar tasa duka ambaton Allah sukeyi. Zuwa yanzu yanajin kamar ya rufe ido ya bude ya ganshi a nijer,yana jin ya shirya facing duk wani challenge.....duk wani tuhuma da kuma kowanne hawa da sauka bore da kuma bijirewa daga gurin koma waye.

Cikin tsantsan sawa kai nutsuwa da kushu'i akayi sallan isha'i da shi,ya kammala dukka addu'o'insa,sai ya samu kansa da zama a hanyar da sukayi clashing da yaran jiya,saman wata concrete chair.

Yana lazumi a hankali iskar wajen kuma tana ratsashi, cikin ruhinsa kuma yana jin kewar yaran,sai ya dinga hango fuskokinsu a jiya,daga shi har cikin yaran a cikin nishadi suke,dukka moment da sukayi spending tare ya zame masa memorable.

"Uncle haidar....... uncle haidar" ya jiyo muryar dab da shi. Kaf qasar a yanzun yasan su daya ne zasu kirashi da wannan sunan,don su kadai ya gayamawa wannan suna,a ko ina da aliyyu maina yake amfani,idan yaso ya qara da MAYAK'I.

Idanuwansa ya bude yana waiwayawa,dukkansu suna sanye da jilbab daidai jikinsu da yayi matuqar haskasu ya kuma qara musu kwarjini. Daga benazeer me giggiwa har batoul miskila murmushi sukeyi masa,alamun dake nuna sunji dadin ganinsa qwarai da gaske.

"U are highly welcome my BB" kafin ya gama kaiwa qarshen zancan ma benazeer ta zagayo tana neman gurin zama kusa dashi

"Dama na cewa batoul zamu iya ganinka fa,tunda aunty bata kiramu ba mu duba ko zamu ganka kafin lokacin komawa gida yayi" murmushi ya saki yana juyawa wajen batoul,yayi mata alama da hannu kan ta taho. Bata musa din ba ta zauna a daya gefan nasa,ya basu hannu sukayi musabaha dukkansu yana gaidasu da larabci. Ga mamakinsa sai yaji sun responding masa,yadan zaro idanu

"Wanne yare da wanne kukeji?" Dariya benazeer ta bushe dashi tana kallonsa,saita nuna masa yatsa hudu

"Ehnn......wanne da wanne?" Ya tambayeta irin amazingly dinnan yana fidda murmushi

"Hausa,english,arabic....... France small small" dariya sosai ta bashi da yadda ta fadi small small din tana daga qaramin yatsanta.

Kai ya jinjina sosai suna sake burgeshi,da alama sun samu background me kyau ta kowanne fanni na rayuwa

"Za'a yimin magana da kowanne?" Kai suka gyada kusan lokaci guda,sai ya saki murmushi yana gyara zamansa sosai a gaskiyarsu,yana jin zuciyarshi da ruhinsa yana masa wani irin dadi,yana jinsa tamkar a tsakiyar ahalinsa

"Bari na gayawa kowa abinda zaice" yana rufe baki benazeer ta maida masa da arabic,sannan ta sakeyi da sauri ta maida da France,sannan ta sake maida masa da english

"Daman da hausan ka fada" ta qarashe zancan da fadin hakan. Dariya ne ya kamashi,fararen haqoransa dake a jere ras suna sheqi suka bayyana.

"Na yarda....yanzun muje na bada gift na wannan abun" ya furta yana miqewa. Duk sai yaga basu motsa ba,ya waiwaya yana dubansu

"Oya...... muje"

"Aunty zatayi fada uncle" batoul ta fada tana maqale kafada. Dawowa yayi ya zauna ya dafa kansu

"Idan zatayi fada kuce uncle ne ya baku sabeel.....kun gane?"

"Idan mukace haka ba zatayi fada ba?" Kai ya gyada yana murmushi,duk sai suka sauka da karsashinsu suka bisa.

Kaman jiya ya musu siyayya,saidai yau din ya siya musu dai dai daidai yadda zasu iya cinyewa ma a gurin,gudun kada ya sanyawa iyayensu rashin nutsuwa a zuciyarsu da kuma ayar tambaya. Tsakiyarsun ya zauna sunata ciye ciyensu suna qananun fadansu da ba'a raba sako da sako,wani lokaci kuma su sakashi a ciki ya raba ko su jefashi a hirar su har suka gama.

Sanda ya niyyaci rakasu suka fidda idanu,suna tsoron ya hadu da sultana,don ko jiyan susan banda sun iso da wuri data fito nemansun nan saita gansu,sun tabbatar kuma zasusha fada qila harda punishment

"Uncle zamu iya zuwa da kanmu" idanunsa ya lumshe yana gyada kansa

"Goodnight"

"Goodnight uncle" suka maida masa,zukatansu dukkansu cike da shauqi,kowanne a cikinsu yana jin kamar kada ya rabu da dan uwansa.

Sai daya qara wasu awanni a wajen,ya sake addu'a sosai yana neman ubangiji ya shiga lamarinsa. Sai kusan sanda dare ya raba sannan ya wuce masaukinsa.

A dakin kusan abun jiya ya hanashi bacci. Fuskar sultana da a yau yayi mararin su sake ganin juna,da kuma yaran. Baisan wacce jarrabawa ce take bibiyarsa akan yaran ba,amma yana jin wata irin tsaftatacciya kuma tatacciyar qaunarsu cikin zuciya da ruhinsa.

*******Dukka kwanakin da suka rage musu cikin makka din a darare take,kowanne motsi sai take ganin kamar zata ganshi a masaukinsu kowanne fita da yaran zasuyi sai taji kaman zasu hadu,kaman zai kwashe yaran a nemesu a rasa,kowanne fita tata cikin kaffa kaffa takeyi da lura da duk inda zata gifta din. Tun daga rabar bata sake bin elevator ba ta gwammace tayita bin stairs har takai qasa,wanda idan ta fita din sai tayi zamanta cikin masallaci,idan ta dawo ciki kuma ta dawo din kenan sai kuma washegari. Duk sanda tayi hanyar elevator sai taga kamar zasu sake haduwa,kaman zata sake ganinsa irin yadda ta ganshi rannan.

Kwana hudu kacal da suka rage subar makka su wuce nijer sukayi wani irin sabo dashi,hakanan shima yayi wani sabo dasu ta yadda har bai tuna haduwa sukayi kuma kowanne lokaci shi ko kuma su wani zai iya tafiya yabar wani. A jikinsa yake jin kamar gurin zamansu daya,kamar wani family ne shi dasu dake rayuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login