Showing 21001 words to 24000 words out of 294767 words

Chapter 8 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

suka kwana. Tun sanda Dr chafa'atou ta shigo sultana ta farka,amma data fahimci ba su kadai bane cikin dakin harda aba sai ta kasa bude idanunta,saidai kukanta data dora ta hanyar fidda qwalla,wanda sam basu lura ba sai da Dr chafa'atou tasa hannu ta juyo da fuskarta tanason ganin yanayin idanunta.

Ta fahimci ta farka kuma kuka takeyi,sai kawai ta yagi tissue tana goge mata hawayen cikin takatsantsan din kada ta fama mata fuskarta,tasan tana tsananin yanayin da take ciki,so ba buqatar ayi maganar da zata ji ta takura ko a tilasta mata boye damuwarta ko don gudun kamuwa da depression da tayi imanin indai ba'a yi da gaske ba tana iya tsintar kanta a ciki muddin ba'a kula da kyau ba

"Dr ina fata komai lafiya" aba ya tambayi Dr chafa'atou kai tsaye. Sai data dan juyo kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga fuskar sultana

"Eh lafiya alhamdulillah,saidai idanun nan nata inajin anjima kadan sai an dubashi sosai,don yaqi sauka daga kumburin da yayi,sannan da alama ma kamar bata iya budashi da kyau ma ko?" Tayi tambayar tana me neman amsa daga wajen ama. Kai aman ta gyada mata tana bata tabbaci.

"Oh.....bayan abinda ya aikata kuma har sai daya hada da illatamin idanun yarinya?" Aba ya fadi da wani irin tune,wanda sai a yanzu ta gama fahimtar inda aba ya sanya gaba akan case din.

"Ba matsala in sha Allah" Dr chafa'atou ta fadi don ta kwantar masa da hankali. Kai ya jinjina da qarfin gaske hannayensa zube a aljihun wandonsa

"Kuyi mata cikakken bincike,idan da wani matsala inaga zaifi kyau ku bani ita na fita da ita waje ayi mata dukkan abinda ya kamata" Ya fadi yana hadiye wani abu me daci dake taso masa,tsantsar tausayin yarinyar da kuma rashin imanin maina qarara yana bayyana a idanuwansa.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 11
_______________________________
*_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_*

*_SUTURA ABAR TUNQAHO_*

*_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_*

_Magana akeyi ta_

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

*UMMU MAHNOOR LUXURIES*

_GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_

*_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_*

*_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_*

*_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_*

*KYAU*

*QUALITY DA DAUKAN HANKALI*

*LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA*
*GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA*

*_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*

08135142610

*INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES

*FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA

*_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_*

*_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_*

*_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_*

*TASTED AND TRUSTED*πŸ‘ŒπŸ‘ŒπŸ‘Œ
_____________________________



"karka damu alhaji,in sha Allah zamuyi duka bakin qoqarinmu" kai kawai ya jinjina sannan ya waiwaya yana duban ama

"Na kirashi yafi sau shurin masaki ban sameshi ba,ban sani bama ko blocking dina yayi?,me yiwuwa tunda ke uwarsa ce bazai iya miki haka ba,idan kin sameshi ki shaida masa saqon da yabar mana ya riskemu,munga result kuma a qasa mun gode" daga wannan ya sanya kai ya fice,sai ama ta bishi da kallo baki sake. Me aba yake nufi ne?,baisan yadda suke nemansa itama hakan bane,ta kirayeshi bata sameshi ba?,sannan tayi zaton zaiyi maganar ya dawo gida ne ya karbi hukuncin da ya dace dashi,a maimakon hakan sai taji wata magana ma yakeyi daban wadda a nata ganin a yanzun ba nanata maganar bane ya kamata a dinga yi,abinda yafi kyau shine asan meye abu na gaba da ya kamata ace an aiwatar.

K'arfe bakwai da rabi sai ga bibi an kawota,ita da matar oncle umar. Jikinta sanye da lallausar bubu cotton 'yar saudiyya,hannunta riqe da casbahar da kana gani kasan itama ita ta kwana ja. Dukkansu suna a gaban gadon sultanar suna mata sannu,saidai ba wanda ta tankawa,hasalima ko qwayar idanuntan taqi ta bude ta kalli koda bibi dinne,sai hawaye da suke bulbulowa ta qasan idanun. Juyin duniya bibi tayi ta bude ido amma ta qiya,duk da dama daya idon ba wani buduwa yakeyi sosai ba,koda ta bude dinma bawai ganin komai tarwai takeyi ba.

Da bibin ta gaji ta koma lallabata ta tashi taci abinci,abincin da tafiso ta sanya tanja ta dafa mata tun sassafe,shima har bibi din tayi ta gama bata ko motsa ba bare ta nuna tasan me sukeyi,daga qarshe ma sai ta gyara kwanciyarta ta basu baya ta fuskanci bango sanda 'yan dubiya suka fara isowa dakin.

Ita daya tasan me takeji cikin zuciyarta,wani baqinciki da wani abu me tauri ne tokare tsakiyar maqoshinta. Kunyar kallon kowa takeji,hakanan kuma haushin kowa takeji. Ta tabbatar inda bibi bata biyewa umarninsa ba ta sakata a gaba sun tafi yadda suka saba da yanzun babu abinda ya sameta. Kusan ta tarkata dukka laifin ne ta azawa bibin,tana ganin sassaucin da ta yiwa maina dinne har ya samu qofar aiwatar da mummunar nufinsa a kanta.

Wasa wasa sai gashi takai har qarfe biyu na rana bataci komai ba,maganinta ma babu wanda tasha a ciki sai uban kuka data saka gaba. Duk wani motsin sultana din yana kan idanun ama,a yanzun tana sake jinta ne kamar saddi,tana ji kuma har cikin rai da zuciyarta nauyinta ce sultana,dolenta ce sultanar.

Biyun da 'yan mintuna su yasmine da aminata suka shigo da abincin rana. Muryoyinsu kadai suka sake haifarwa da zuciyarta wani sabon rudanin. Yanzun fa kenan itan ba daidai take dasu ba?,dukkansu sun fita walwala nutsuwar zuciya da kuma 'yanci?,a cikinsun yanzun itace daban kenan?. Har suka gama leqata suka mata sannu bata motsa ba kaman yadda takewa kowa. Hankalin ama yana kai,don haka bibi na fita sallah ta sanya kowa yabar dakin,ta maida qofa ta rufe sannan ta tako a nutse inda sultanan ke kwance.

Kiran sunanta tayi amma bata amsa ba,bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta durquso saman kanta ta kuma sanya hannayenta dukka biyun tana dagota daga kwanciyar tana fadin

"Haba sultanan bibi.....subhanallah" ama ta fadi kuma daga baya bayan taji yadda jikinta ya dumame da wani mugun zazzabi. Zagayowa tayi ta zauna sosai kusa da ita tana riqe tafin hannunta idanunta akan rufaffun idanuwanta

"Yanzun da wannan zazzabin a jikinki kike kwance?,sultana kinason kashe kanki ne?,kinaso yayi miki dariya yace yayi winning a kanki?,kinaso yaji cewa burinsa ya cika na cusguna miki?,kinason sanyawa bibi hawan jini ne?,ko kinaso aba ya shiga matsananciyar damuwar da zai dinga kasa komai?" Shuru bata amsa ba,saidai kukanta yanzun ya qaru ya zama me sauti ba kaman daxu da take yinsa silently ba. Tana jin inama ace ama zata iya farka qirjinta ta cire mata zuciyar daga qirjinta ko zata samu sassaucin abinda takeji,inama ace mutum yana iya shafe rayuwarsa gaba daya ya sake rubuta sabuwa,inama ace ta rufe ido ta bude taga ba itace sultanar familyn MAYAK'I ba

"Sultana.....babu ci babu sha babu shan magani,me kikeson yi idan ba kisan kai ba?,kina azabtar da kanki bayan shi wanda yayi miki laifin har yanzu bai waiwayi gida ba bare yasan kinayi,me yasa kike azabtar d kanki da kanki?,duba......yanzu lokacin sallah ne amma tunaninki ko kiyi sallar baya baki?" Sake barkewa tayi da kukan tana cusa fuskarta tsakanin cinyar ama tare da qanqame ama da kyau. Kuka takeyi sosai me sauti,sautin kukan dake fita da wani irin mugun radadi da ciwo da zukata suka tara. Sosai ta sake karya zuciyar ama,sai ta dora hannunta saman kanta tana shafa sassalkan gashinta da ya zama kamar na tsohuwar mahaukaciya tsakanin jiya da yau saboda tsananin firgici da tashin hankalin da take ciki. Sumar da ake bata lokaci wajen gyarata da qalqaleta amma a yau bata da maraba da radaddagaggen zare cikin tarin tarkacen bola. Ta yarda da maganar Dr chafa'atou sai anyi da gaske akan sultana din,idan ba haka ba depression din tsaf zaya kamata. Bata dakatar da ita daga kukan ba,saidai itama tata zuciyar tayi nisa wajen tunanin yadda zata tafi da yarinyar.

Sai da tayi shuru don kanta sannan ta dagata tana cewa

"Banaso daga yanzu ki sake irin haka sultana,idan maina ya tsaneki ya zalunceki ya kuma cusguna miki mu dukka nan ke mukeso,mu dukkaninmu walwala da farincikinki mukeso,kuma zaya dawo ya fuskanci mafi girman hukunci,hukuncin da kuma kece zaki zabeshi da kanki". A duk sanda ta furta sunan Aliyyu ko maina sai taji wani abu tsakiyar kanta yana mata yawo kamar ana sakatar qwaqwalwarta,ambatar sunansa kadai yana sake sanya mata wata mahaukaciyar tsanarsa da takejin tamkar zuciyarta zata tsage ta fado,to amma batun hukuntashi dake hannunta kamar yadda ama ta furta sai ta samu kanta da laluben amsa,cikin manya manyan hukunce hukuncen da akema dan adam cikin rayuwa batasan wanne iri zata zaba masa ba,take kuma taji kanta ya sara kamar zai rabe biyu,tunaninsa ko daya bata qauna cikin kwanyarta,karon farko ta bude bakinta a hankali muryarta na fita da wani irin sarqaqqen amo

"Ama don Allah.....kibar kiramin sunanshi.....kaina kamar zai rabe biyu" ta qarasa maganar dukka jikinta yana kakkarwa saboda wani sabon zazzabi me cakude da ciwon kai daya sake saukar mata.

Yadda taga jikin nata yana rawa tilas ta kiranyi likita,a sannan dr chafa'atou ta fita sai dr nadra. Dr nadra tafi Dr chafa'atou fusata da lamarin,ta sake checking sultana da kyau tace a dakatar da shigowar masu dubiya,idaninta kuma da magariba likitan idanu Dr nouhou zai shigo zai dubata. A barta ta huta kawai,a qyaleta duk abinda take so tayin,shine zai sanya zuciyarta samun sassauci daga abinda takeji.

To ba'a sake matsa matan ba,saidai duka ranar ama din tana tsaye akan sultana din,sai yamma liqis ruwan da suka sanya mata ya qare,ama ta lallaba ta sanyata tayi alwala tayi sallah daga zaune saboda dinkin da yake jikinta,ta hilaceta da qyar ta samu tasha tea cokali uku,na hudun kuwa dawowa yayi bai iya shiga cikinta ba. Ganin hakan sai ta qyaleta,tana fatan gobe tasha abinda yafi hakan.

Suna tsaye daga bakin window inda zasu dinga hangota sosai ita da bibi din data gagara tafiya guda tun safen. Wayarta na hannunta dai still ya zuwa yanzu batasan adadin sau nawa tayi kiran layin maina ba. Duk sanda zata kira akace mata wayarsa na akashe sai taji ranta ya ninninka baci akan na baya. Me yaron yake nufi?,ya maishesu mutanen banza kenan?,yayi aika aikarsa ya wuce gararin gabansa babu abinda ya shalleshi?,baya tunanin a yanayin da ya barta ma ya dawo ya tabbatar da ingancin rayuwarta ko kuma akasin haka?.

Isowar likita gab da dakin ya sanyasu motsawa,yace a dauko wheelchair a kawota ya duba idanun nata. Numfashi ama ta sauke tana duban bibi,dukkansu a firgice suke,sannan kowannensu kana kallon fuskarsa zakaga yayi wata rama tsakanin jiya da yau kawai

"Bibi dare yana yi, inaga ya kamata ki wuce gida hakanan kodon yanayin jikinki,na miki alqawarin zan bawa sultana dukkan kulawa tamkar yadda mahaifiya zata bawa d'anta na cikinta kulawa"




*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 12
__________________________________
*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba_*

https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
________________________________


Ko daya bibi bata da haufi da ama,kaf yaran gidan a gabanta aka haifesu,kuma babu wani wanda ya taba kuka da ita. Abu daya ne da ita,bata daukan raini ko qanqani,bata kuma son sakarci,duk wanda ya santa ya santa da wannan halin,don haka babu haufi bibi din tabar mata sultana,saidai kafin ta tafin tabar musu tanja saboda ama din kanta ta samu sauqin zirga zirga,sannan kuma tace da ama din

"Kome ake ciki banason ki boyemin,daga maina har sultana dukkansu jini na ne,kuma jikokina ne"

"In sha Allah bazan boye miki komai ba" ama ta furta tana lanqwasa yatsunta tana jin wani nauyi bibin ta sake aza mata.

Sun kusa a qalla awa biyu harda wani abu kafin Dr cha'aibou ya kammala gwaje gwajensa. Ya daga result na gwajin da aka yima idanun nan cikin asibitin yana kalla sai ya maida takardar saman teburinsa yana duban ama

"Ta samu matsalar rainin gani a idonta guda daya,jijiyoyin dake dauko haske sun tabu saboda duka da ya samesu ko buguwa....." A firgice ta juya tana duban sultana saboda yadda sakamakon ya daketa da kyau. Idanunta fes ta zubewa sultanar,tana zaune saman lallausan kujerar da Dr din yace ta zauna akai,ko motsi kyakkyawa batayi ba bare wani reaction,itakam meye wai ya rage mata?,ita a yanzu ko cewa akayi maina ya kasheta dawowa tayi sam ba zatayi mamaki ba

"Amma ba damuwa in sha Allah,zamu dorata saman magani zuwa wani lokaci mu gani?,idan kuma akwai buqatar ayi mata glass zuwa lokacin zamu gani" ya fadi yana zaro takarda yayi rubuce rubuce akai.

Hawaye kawai idanun ama keson xubarwa amma tana dannewa,don ta tabbatar muddin ta zubda hawaye akan maina alhali yana raye ko a macen ma tamnar ruwan masifa ta fidda masa. Tsananin tausayin sultanar kamar ya fasa zuciyarta. Cikin qasa da awa ashirin da hudu duka yarinyar kamanninta sun jirkice,tayi wata irin wawuyar ramar da hatta rigunanta basa zaunar mata sosai a jikinta.

Da qyar da daren ta lallabata tasha madararta,madararta ta amana wadda muddin bata shata ba kaf gidan babu me rintsawa,amma sai gashi wai yau lallabata akeyi tasha din.

Kamar jiya bacci ya riga daukar sultana kafin ita,kaman jiyan dai haka ta zauna,gefe qur'ani gefe wayarta tana tusa kiran maina amma dai komai bai canza ba.

Batafi awa biyu da zama ba sultanan ta farka firgice tana kiran sunan maina din da qarfin. Da ita da tanja da itama ta fara bacci batasan waye ya riga wani isa gareta ba. Kuka take sosai dafe da kanta,ta ture hannuwan ama dake riqe da ita da qarfi,sai ama din ta fahimci kaman batason ganinta. Bataji komai ba don tasan situation din da take ciki,kuma Dr chafa'atou ta mata bayanin komai,zata iya tsintar kanta cikin razana da firgita da kuma miyagun mafarkai na abubuwan da suka faru da ita. Don haka ta yiwa tanja alama taja da baya ta basu waje.

Sun kusa kwashe wata awar tanja na lallabata da hikimomi da dabarun data saba mata kafin ta samu kukan yaja baya,ta bata ruwa tasha saita maida bayanta kawai ta kwanta hawayen na ratsa gashin idanunta yana jiqasu da hawayen dake diga har cikin kunnenta.

A wannan daren ma sam ama bata iya bacci ba,tunani ba kalar wanda batayi ba,a haka asuba ta rusketa.

********Kwanaki bakwai kenan da faruwar abun amma babu abinda ya canza. Al'amarin da ya haifar da rashin walwala rashin kuzari da karsashi cikin family din MAYAK'I. Kusan dukka sa'aninta dake gidan tamkar suma sun shiga alhini na abinda ya farun. Cikin dangi kuwa masu zuwa dubiya ne keta zarya,dadinta daya Dr chafa'atou ta hana shiga wajenta saboda tana buqatar hutu da qarancin hayaniya. Abinda ya daurewa ama kai shine fitar zancan, saidai bata da tabbacin sunsan ainihin abinda yayi silar kwanciyartata.

Daga ama har bibi babu wanda bai rame ba,kada ma ama taji labari wadda kullum dare tausayin sultana yake sanyata a gaba. Kowanne dare yarinyar cikin firgici da kuka take yinsa,idan an dace bacci ya dauketa kuma tun batayi nisa ba take farkawa a razane,muddin tayi wannan razanar kuma nata baccin ya qare itama.

Fargaba zullumi da rashin isashen bacci ga jinya suka taru suka yiwa ama din yawa. Gefe guda ga aba wanda bata sake ganin walwalarsa ba tun daga wancan ranar. Kullum rana zai shigo da safe ya duba sultana din,ya jima da ita yana tambayarta me takeso?,saidai babu um ba um um,hakan da dare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login