Showing 144001 words to 147000 words out of 294767 words

Chapter 49 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

idan zaki fita.....bazan iya jurewa ba naga ana kallonki.......you are not a baby now......kin zama babbar mace.....zuciyata ba zata iya dauka ba.....ki killacemin please"

"N killace maka me?,waima......meye hadinka da dukka rayuwata iyeee...... please stay away from me" ta fadi da qwarin gwiwa tana son banbare hannunsa daga qugunta,don wani mummunan saqo me tsayawa a zuciya da qwaqwalwa kawai yake aikewa gangar jikinta a haka. Tana jin wayarta na vibration amma bata ma da qarfin duba me kiran.

Hankalinsa kwance yake kallon qwayoyin idanunta,akwai wani kakkaifan abu a ciki da yake sanyashi nazari yadda zai kaudashi daga zuciyarta,ta riqi abubuwa masu yawa a ranta da alama,and shi kuma bazai iya kallonsu tattare da ita ba,dole ya kawo qarshensu. Sakinta din yayi a hankali saidai kuma ba salin alin ba,don sai daya zira hannunsa cikin aljihun rigar tata ya zare wayarta,wanda bata lura da hakan ba sai daya daga wayar yana qoqarin cire code din kai.

A tsiwace ta bude bakinta zatayi magana amma sai maganar ta koma inda tafito sakamakon turo qofar dakin da akayi da dan sauri.

A tarw suka juya suna duban bakin qofar,ama ce sanye da qaramin hijab mahadin pyjamas dinta,fuskarta tayi kyau qwarai cikin kalolin kayan,sun kuma fidda quruciyarta sosai saika dauka duka duka bata wuce shekara talatin ba.

Wani irin abu sultana taji kaman an watsa mata cikin jikinta

"Subhanallah" ama ta furta qasa qasa da sauri,sai sultana din tayi hanzarin ja baya cikin zafin nama tana nesanta jikinta daga maina. Zuciyarta na bugawa kamar wadda aka kama da laifin sata dumu dumu,idanunta dukka sun nuna tsantsar tsoronta da ganin da ama tayi musu tsaye cikin mugun kusanci da juna ita da maina din. Daga subhanallah ama bata qara komai ba ta saki handle din ta juya tana ficewa daga dakin cikin abinda duka bai wuce second biyar ba,dama zuwa tayi taga yanayin yaran ta wuce itama ta kwanta,wanda hakan sabonta ne,duk dare takan dubasu kusan sau hudu ko biyar,musamman idan aiki yama tanja yawa ko ba'a nan zata kwana dasu ba.

A fusace ta juyo tana duban maina wanda ko dis babu wani alamun tashin hankali tattare dashi,hasalima sai taga kaman wani tattausan murmushi ne yake fita daga saman fuskarsa. A yadda taga hankalinsa na akwance tasan ko meye zata fada ma batawa kanta lokaci ne kawai zatayi,sai kawai ta juya da gaggawa tabi bayan ama kamar wadda keson cimmata.

Wani murmushin ya kuma saki bayan ta bacewa ganinsa,ya matsa gaban yaran ya sake dubasu,ya saita musu ac din dakin sannan ya kashe duk wasu kayan wuta ya rufe musu ya fice abinsa.

Yana ratsa farfajiyar gidan iskar dake kadawa tana sake sanya masa nishadi har cikin zuciyarsa,idanunsa ya dinga lumshewa yana tuna qamshinta da laushin fatarta,wani irin dumi da fatarta ke dashi wanda kusan ya jima da haddace wannan,tun tana mitsitsiyarta ma......lokaci na farko da ya fara saninta a matsayin diya mace,sanda tana sultana qwaila. Wani murmushin ya sake subuce masa daya tuna ranar,rana ce da tazo musu a rikice ba tare da shiri ba,rana ce da bai taba hasashen faruwar abinda ya faru din ba a sannan,tana dauke da wani irin memories masu nauyi da bazaiyiwu zuciya ko kwanya su manta dashi ba.....amma duk da haka yakan tuna wasu baiwawwaki da ya sameta dasu da suka girmi shekarunta.

"Lafiya kake murmushi kai daya?" Muryar suhail dake zaune cikin falon yana duba wata jaridar qasar France ya fadi yana kallon fuskar maina.

Sai a sannan ya lura dashi,yayi qoqarin gyara mode na fuskarshi yana neman wajen zama

"Lafiya mana....." Tashi suhail yayi sosai ya zauna yana ajjiye newspaper din

"A'ah,inafa lafiya,kafimin kama da mutumin da soyayya ta yiwa mummunan kamu fa malam" harara ya watsa masa yana qoqarin bude wayar sultana din daya taho mata da ita

"Hakane.....tunda kowa ma irinka ne wanda bashi da aikinyi sai soyayya" sai ya gyara zamansa sosai yana shiga cikin wayar ya soma dube dubensa. Baku suhail ya sake yana kallonsa kafin ya saki murmushi daga baya

"Ni ka tunamin,i got her phone number......bari na gwada kiranta" kaman an fusgeshi ya daga idanu yana duban suhail,so yake ya tambayeshi wacece amma kuma ya kasa,sai idanu kawai daya zuba masa,zuciyarsa na harbawa kadan kadan.

"Yeey.....ta shiga" ya furta with excitement yana gyara zamansa. Ga mamakinsa wayar sultanan dake hannunsa ne ya fara harbawa,a nutse ya dauke dubansa daga kan suhail ya maida kan wayar,saiga numbers a jere reras suna harbawa.

Iya adadin yadda suke harbawar haka zuciyarsa ke bugawa fiye da kima,a nutse ya maida dubansa ga suhail bayan kiran ya katse yana sake qoqarin kuma kira.

Kaman dai dazun haka yaga kiran ya sake shigowa,da gaske ne wannan ba wasa ba, numbers din sultana ke gareshi,kuma ita din yake kira,waye ya bashi number wayarta cikin gidan?,ya yiwa kansa tambayar da baisan amsarta ba

"Still dai taqi dagawa.......tana da aji da yawa,da gaske sai nayi yaqi da gasken gaske zan sameta...... lemme try again" ya furta yana duban screen din wayarsa yana sake qoqarin kiran.

Hannu ya sanya ya latse wayar gaba daya ya kasheta duka yana jin wani abu yana riqe masa waya

"Oh no!" Ya sake ji suhail ya fada da sautin damuwa cikin muryarsa

"Ta kashe wayar.......wai man.....me yasa ba zaka shigemin gaba ba?,na tabbatar sister dinka ce don akwai kamanni a tsakaninku......i love her wallahi with all my heart.....zan kula da ita i promise"

"Mahaukacin da ya baka digit nata bai gaya maka matar aure bace!" Ya fadi a tsawace har sautin tsawar nasa na fita farfajiyar corridor dinsa. A mamakance suhail ya fidda idanu yana duban maina,kafin daga bisani ya rage kaifin kallonsa a kanshi,ya kuma tattaro dukka jarumatarsa yana masa duba nakai tsaye*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 75



"Please banason irin wannan wasan,wanne magana kake haka?,matar aure kamar yaya?,ta ina ta zama matar aure?,ina mijin?"

"Eh.....yes matar aure ce harda yaranta" dariya suhail ya saki yana doka qafanshi a qasa

"Kaga,cool down man.....kawai kacemin kaima kana cikin 'yan takara bawai kayimin qaryar matar aure bace...."

"Na taba maka qarya?" Ya jefa masa tambayar yana jin zafin jifansa da qaryar da yayi

"No.....amma akan mace ai ba abinda mu maza ba zamu iyayi ba muddin dai muna sonta"

"Shut your mouth please suhail......sultana matata ce..... benazeer da batoul are my kids!" Yakai qarshen maganar yana dukan hannun kujerar da yake kai.

Sak suhail yayi yana kallonsa cikin mamaki,yayin da shima maina din suhail yake kalla fuskarsa na sake bayyana zallar kishinsa.

Qaramin dariya suhail ya saki yana komawa baya ya zauna sosai

"Nasan ka qware wajen dakiya,cin magani,zafin zuciya da kuma zallar miskilanci......to amma bansan sanda ka zama dan wasan kwaikwayo ba,yaushe kukayi auren?,har ta haifa maka wadannan bula bulan twins din ma sha Allah tubarkalla,son kowa qin wanda ya rasa?,idan su din yaranka ne me yasa tsahon shekarun kaketa begensu kake sonsu amma kuma muke yawan maganar bakasan inda suke ba a fadin duniya?,ko nufinka duk cikin rainin hankalinka ne?" Ya amsa tambayar cikin salo na shashantarwa. Tsam ya miqe daga inda yake zaune din

"Duka wannan bani da lokacin maka bayaninsa,kaje wanda ya baka phone number din ya maka bayanin,kuma ka gaya masa nace ya warware maka komai ta yadda a Karan kanka zakasan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.......zan iya jure komai amma banda abinda zai tabamin mutuncin iyali na.......kada ka kuskura mu ssmu matsala dakai akan haka,je répète(na sake maimaitawa)sultane est ma femme(sultana matata ce),reste loin d'elle(ka fita hanyarta)" daga nan ya tsugunna a nutse ya dauki wayoyinsa da nata ya soma takawa kai tsaye zuwa bedroom dinsa.

"Wannan duka matsalarka ce,ko ba wajenka ba zan zauna a gidan MAYAK'I,sannan idanma kayi hakanne don ka hanani sonta so yanzu na fara sonta......" Maganar ta sakashi cin burki sanda ya sanya qafarsa a dakin ya waiwayo ya zuba masa wani kallo me cike da kashedi da gargadi ba tare daya sake tofa masa kanzil ba ya juya ya qarasa shigewa ciki.

Saman bedside drawer ya zube wayoyinsa,ya cusa hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,wanne irin jarrabawa ce wannan takeson kutso kai tsakaninsa da abokinsa na kusan shekaru hudu?,Ta yaya zai iya ci gaba da mu'amala dashi?,yanason matarsa?,uwar 'ya'yansa?,me yasa suhail yaqi yarda da bayaninsa ne?,bayan yasan tsahon zamansu da shekarun da sukayi tare bai taba kwatanta yi masa qarya ba?. Kiran sunan Allah yayi a jejjere yana fatan zugin da zuciyarsa ke masa ya sassauta.

Bayason yayi treating suhail in a wrong way,koba komai kusan qarfin zuwansa marad'i saboda shine,ya baro familynsa a niamy ya zabi zuwa wajensa,bai dace ace yayi masa wani ba dai dai ba,amma shima ya dace ya fahimceshi,ya fahimci maganarsa da kyakkyawar fahimta.

***********Kaman wata maras gaskiya haka take takowa zuwa dakin ama,tun daren jiya data samu ta shige daki ko motsi me qarfi bata sakeyi ba saboda nauyi da kunyar ama din. Batasan me zata ce mata ba,duk da komai data gani kawai yazo ne ba zata,amma sai abun ya zamana kamar an tsarashi ne,bataso ama ko wani cikin gidan ya fahimceta bai bai.

Wata off-white gown ne a jikinta chiffon da aka yiwa budadden dinki,sosai kalan yayi mata fatarta kyau wadda keta fidda qamshin milk cream nata da take amfani dashi. Da safen sumarta ya dameta,ta zauna bayan ta fito daga toilet ta rabashi gida biyu ta kalbace kowanne,sai jelar ya biyo ta bayan kunnenta, fuskarta yayi wani irin kyau kai kace daga qasar hindu ta fito.

A falon ama din su zuwaira keta kai kawo suna kawar da abubuwan dake buqatar a kauda su din,tabbacin dai da gaske goben tafiya ta tabbatar musu. Don duk wani abu da zai iya datti ko qura anata cireshi ana alkintashi. Ta gaisa dasu cikin mutuntatawa suka amsa mata cikin girmamawa da kuma qauna da sanin darajar juna,sai ta zarce dakin ama, wanda tun daga bakin qofa takejin muryoyinsu benazeer,da alama yauma sammakon tashi sukayi kenan.

A kunyace ta tura qofar dakin bakinta dauke da sallama. Ama dake yiwa batoul stretching da mini stretcher dinsu ta amsa tana waiwayowa. Suna hada idanu sultana tayi saurin dauke idanunta saboda sosai takejin nauyin ama,itama ama din saita basar taci gaba da tsaga sumar batoul tana cewa

"Uhm.......sai kuma me ya faru?" Da zumudi take ci gaba da bata labarin,wanda sai data zauna sannan ta fahimci labarin daddynsu take bawa ama din,ita kuma ta tattara dukka hankalinta tana saurararta.

"Barka da safiya ama" ta fadi kaman wata baquwa

"Barka kadai.....mun tashi lpy?" Ta amsa mata yadda suka saba gaisawa ba tare data juyowa ba

"Lafiya alhamdulillah" zamowa dukka benazeer da batoul sukayi suka gaidata,ta amsa musu tana dan dubansu. A kullum cikin zuciyarta sake jin alfahari takeyi da yaran,a kullum kwanan duniya wani kusanci zuciyarta take samu da yaran,ko yaushe nutsuwa da tarbiyyar da suke samu yi mata dadi takeyi a rai,ba wani guri da zasu baqunta su zauna ko su gifta saisun samu masoya,wani irin farinjini garesu,sai kuma Allah ya hukunta suka zama wasu irin nutsatstsu masu hankali,idan ka dauke surutun benazeer wanda shi din kaman a halittarta yake,saidai kuma duk surutun nata yana da limit,bata soki burutsu KO maganganun da suka shallake shekarunta.

"Dame dame ama za'a hada?" Sai a sannan tadan waiwayo

"Ni kuma?,ai na kammala komai,saidai ke,abinda kikasan baki hada din ba ki hada,goben in sha Allah by 10 zamu tashi zuwa Nigeria,four kuma zamu wuce in sha Allah" ta fadi sanda benazeer da batoul keta hayaniyarsu basuji ma me take fada ba. Kunya tadan sake kamata,ta sadda kai qasa tana matsa hannayenta,sai ta miqe sum sum

"Zamuje lalle,ba zakije ba?" Ama ta tambayeta. Batajin zata iya hada wajen zama da ama na wasu awanni,don ame laifin take jin kanta,don haka tace da ita

"A tahomin da kayan hadin kawai duka,koda mun isa can zan saka da kaina"

"To yayi" ta amsa mata tana qoqarin hadewa batoul gashinta guri guda.

Agogon fata na kamfanin D&G shine abu na qarshe daya daura a hannunsa,kuma shine cikamakin kwalliyar da yayi cikin bugaggiyar shaddar qasar mali fara qal dake jikinsa. Shadda ce da aka zubawa wani irin kwantaccen aiki daya dace da kalar dakakkiyar hular kansa,ya daga zagayyayun lion eyes dinsa yana duban fuskarsa ma'abociyar sassanyan kyau da wani irin shinfidadden kwarjini wadda ta qawatu da baqiqirin gashi daga gefe da gefen kumatunsa zuwa habarsa.

Comb ya dauka yana sake gyara gashin fuskar tasa da kyau,duk kuwa da cewa a kwance yake yana sheqi,sheqin da zai gaya maka qololuwar tsafta da kulawar da yake samu. Siririn murmushi ne ya subuce saman labbansa dake da wani irin color me jan hankali daya qarawa habarsa da kyakkyawan hancinsa kyau,daren jiya ya tuna,yayi mafarki sosai da ita,mafarkin da ya sakar masa da matsananciyar sha'awarta me cakude da wata iriyar narkakkiyar qauna da ya tashi da ita da safennan. Wani irin so ne me nauyi da yaji tamkar an qara mizanin nauyin zuciyarsa,t bashi memory me dadi da ya tabbatar zaiyi masa rakiya zuwa niamy ya bashi kuma dukkan karsashi har yaje ya dawo. Abu daya zuciyarsa ta tsaida masa,wanann tafiyar idan yaje ya dawo,zaya zauna ayi komai ya qare tsakaninsa da aba ama harma da sultana din. Bazai juri yana rayuwa da ita gida daya ba amma batasan girma da nauyin igiyarta dake kansa ba.

Knocking qofar da kuma fitar sautin suhail shi ya Katse masa komai

"nous allons rater le vol(zamu rasa jirgi)" ya fadi da harshen faransanci. Bai amsa masa ba sai ajjiye comb din da yayi,ya dauki wayarta data kwana a hannunsa ya zura a aljihunsa,sannan ya saka hannu ya jawo luggage dinsa dake dauke da kayan sawarsa na kwana daya tak da zasuyi ya fito.

Zuciyarsa yakai nesa sosai ya miqawa suhail hannu. Ga mamakinsa shi kaman ma komai bai faru ba ya bashi hannu shima suka gaisa yadda suka saba

"petit-déjeuner(breakfast)" suhail ya fada yana nuna masa warmer din kayan karin kumallon da Bibi tasa aka shirya musu. Kai ya kada alamun a'ah

"Kasan yayi safiya yanzun,zan shiga muyi sallama da su ama"

"Saika fito don ni already ma munyi,har 'yar tsohuwa ma ta bani wata kyauta wallahi,naji dadin.kyautar nan" ya fadi yana murmushi gami da satar kallon maina. Sarai ya ganshi,amma sai ya share kaman bai ganshi din ba,ya taka a nutse yana fita daga sassan nasa.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 76


A gaggauce yake amsa gaisuwar masu aikin saboda shi kansa yasan lokaci yana dab da qauracewa. Sanda yake duban agogonsa yana nufar dakin ama kai tsaye lokacin ta sanya santala santalan fararen qafafunta da suka dan nuna ta qasan material din jikinta. Qafafun nata ya soma gani kafin ya kai idanunsa har zuwa qaurinta don rigar bata sauka har qasa sosai ba. Tsigar jikinsa ya zuba,wani abu ya tsarga mishi har cikin jininsa da ganin kwantaccen baqin gashi saman qaurinta,wanda bame yawa bane,wannan din sai ya zama tamkar ado saman farar fatarta.

Da sauri ta kauce masa sanda yake sauke idanunshi a kanta. Kalbar kanta ta dauki hankalinsa sosai lokacin da take giftashi da hanzarinta,don batason ma wani abu ya hadasu. Da kallo ya bita har ta bacewa ganinsa,sai ya maida idanunsa ya lumshe,yana jin tsananin kewar tattausan qamshin da jikinta ke fiddawa,ya qarasa ya murza handle din dakin ama ya shiga.

Tana amsa sallamarshi ta dauke kanta tana ci gaba da hada hadarta,ta fahimci gaba daya kaman kunya ce takeson yin qaura daga jikinsa,shi yasa ta hade ranta da kyau. Daga benazeer har batoul basu barshi ya qarasa shigowa dakin ba suka taho da gudu,kowacce na qoqarin fara hawa jikinsa. Murmushi ya subuce masa,wani farinciki yana ratsa zuciyarsa,ko iya wadannan princess din da sultana ta bashi kadai ya isa ya siya mata matsayin da bayajin duk duniya baya ga ama akwai wata mace data isa ta sameshi,ya tsugunna dukkansu ya basu daman hawa kanshi da kyau kamar bai damu da farar shaddar dake jikinsa ba,sannan ya miqe dauke dasu yana qarasawa wajen ama.

Har qasa ya tsugunna bayan ya ajjiyesu yana gaidata,ta amsa masa ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login