Showing 198001 words to 201000 words out of 294767 words
Chapter 67 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
na wani sakanni,sai yayi hanzari janye idanunsa yana juya ciki jikinsa a mace.
Duk wani feeling nashi da yake qoqarin dannewa yana controlling nasa tasa kakkaifar qwayar idanunta cikin qasa da second sittin ta rusashi,gaba daya ta saukar masa da kasala,ta tayar masa da wani irin abu cikin sassan jikinsa,amma duk da haka da yake namijinne da gaske, sai ya yaqi hakan saman fuskarsa,ya koma cikin yaran ya zauna sosai abinsa kamar dazu.
Da qyar ta daga qafanta ta sanyo kai cikin falon tana yin sallama,kallo daya ama tayi mata ta karanci ba cikin daidai dinta take ba
"Sannu da gida ama" ta furta tana qoqarin qaqalo murmushi,don ita kanta taji idanunsa har cikin tsakiyar jikinta,wani kakkaifan kallo daya tayar da kowacce tsiga ta jikinta,ya aike mata da wani irin saqo me nauyi,saqon da taji inama ace zaya shimfida mata kyakkyawan qirjinsa ta samu masauki a ciki,tana ji tana kuma tsammani a nan ne kawai zata samu sassaucin abinda takeji,a nan ne kawai zata samu nutsuwar da take da buqata.
"Yauwa sultana......lafiya kuwa?" Ta tambayeta tana tattara hankalinta a kanta sanda ta matso kusa da ama din tana kwashe mata takardunta da suka zube a qasa
"Laf.....fiya ama,na gama abinda najeyi ne" amsar data bawa ama din sai data sanyashi lumshe kyawawan idanunsa. Yanzu haka a wannan safiyar miliyoyin maza nawa ne suka kalle masa fuskarta?,anya zai qyaleta a haka kuwa?,zai iya ci gaba da yi mata wannan zurun?.
"Gajiya ce kenan?" Ta sake tambayarta,saita gyada kai kawai ba tare da tace komai ba
"Saiki shiga ciki ki kwanta ai ki huta sosai,may be idan kika samu bacci zakiji kin ware"
"To ama" ta amsata tana riqe kayanta da kyau. Sai sannan benazeer da batoul da hankalinsu yayi nisa a wasa da daddynsu sukayi mata sannu da zuwa. Tadan saci kallonsa na abinda yayi qasa da second biyu sannan ta watsa musu harara
"Sai yanzu kuka ganni?,banason sannu da zuwan" murmushi ya qwacewa ama,har sai data dora hannunta saman bakinta kadan ta maida jikinta bayan kujera tana lumshe ido
"Yaro man kaza" ama din ta fada qasan ranta. Tanajin yaran suna fadin
"Am sorry mommy.....am sorry mommy".
"Naji" ta fadi,cikin dakewar da takeson nuna tsananin kamun kanta tace
"Barka da rana" saidai tayi maganar ne tana kallon gabanta. Kamar baijita ba haka yayi mata,yasan daya daga cikin abinda bataso kenan.
"Ina wuni" ta sake maimaitawa wani abu yana tsaya mata a wuya
"Maina bakai ake gaidawa ba?" Ama tayi saurin kawo qarshen drama din
"Oh.....sorry ban ganta ba,kina lafiya?" Ya amsa yana duba letter A cikin tarkacen building blocks din. Kasa amsa masa tayi,don tayi imanin idan ta bude baki kuka zata sake masa,sai kawai ta qara wuta ta wuce dakinta.
Tana maida qofar suka hada idanu da ama,har tayi kaman ta jefa masa harara sai kuma ta dauke kai saboda wani tunani da tayi,bata harareshi ba amma ya fahimci harara taso jefa masan,sai ya qunshe dariyarsa yana dauke kai,ya maida kai ga yaransa.
Tana ajjiye jakarta saman gado taji damshin hawaye ta eyelashes dinta,takai hannu ta tabosu,ta dawo da dubanta kan yatsun nata
"Kuka kuma?,na me?" Ta tambayi kanta cikin qarfin hali,duk kuwa dacewa sosai takeji wani abu yana damunta a zuciya
"No" ta fadi tana girgiza kai,tana gayawa kanta kada tayi kukan,tayi qoqarin hadiye komai,sai kuma taji zuciyarta tana bala'in tashi.
Gefan gadon ta samu ta zauna,ta dinga jan numfashi me zurfi tana kuma fesar da wani,dukka a qoqarinta na daidaita damuwarta. Ta kusa kashe minti ashirin a haka sannan ta danji dama dama,sai ta tashi ta cire kayan jikinta,ta nemo riga da skirt free size masu taushi ta saka.
Idan zata iya tunawa wunin yau babu abinda ta sanyawa cikinta,bata kuma jin yunwar kwata kwata,a cushe takejin cikinta,to amma kuma koma meye bai kamata takai har irin wannan lokacin ba tare da taci komai ba,don haka ta sanya baby hijab saman kayan ta fito kitchen ko zata samu wani abu taci.
Qin yarda tayi kwata kwata ta kalli sashen da suke,ta maida dubanta ga qofar kitchen din da take tunkara,saidai duk da haka hakan bai hanata jiyoshi yana gayawa ama saqo ba
"Zuwa dare idan Allah ya kaimu ayana zata iso,nace bari na gaya miki,zanje daukota around 8,don munyi magana da uncle tahir ya bani ita........" Bata bari ta gama jin sauran abinda yake fada ba ta shige kitchen din da sassarfa,ayana.....tasan ayana sosai,kusan mate ne ita da ayana din,duk a sannan ayana din ta bawa sultana shekara daya. Ama nason ayana don 'yar yayanta ne uwa daya uba daya,sannan a baya tasha jin uncle tahir yana tsokanar maina zai bashi ayana.....tun maina din yana dan makaranta.
A birkice ta dauko fresh milk,ta bude da zummar tasha ko zata wuce da abinda ya tsaya mata a maqoshi,amma data sanya baki sai taji ba zata iya ba,don haka ta dauki qaramar tukunya ta juyeta a ciki,ta jefa citta da kanunfari da cardamom da kuma mint fresh mint leaves da basa rabo dashi,ta rage wutar can qasa,ta goye hannayenta a qirji ta zubawa tukunyar idanu tunaninta kuma yana lulawa wata duniyar ta daban.
Sanda ama ta tashi tana shiga dakinta dauko wasu files ya samu ya miqe yana miqawa batoul gidan daya hada mata
"Ina zuwa,bari na samo ruwa" ya fadi yana gyara bottom na rigarshi,ya soma takawa zuwa kitchen din. Tunda ta wuce hankalinsa yayi can,yadda ya karanci sultana yayi imani koda mahaifiyarta a yanzu da zata dawo duniya ba zatayi mata karatun da yayi mata ba,ya tabbatar daga jikinta har zuciyarta bata jin dadinsu,to amma wannan hanyar daya biyo ita daya ce sassauqar hanyar da zata kawo musu qarshen komai,don dukka wata jarrabawa da zaiyi game da ita ya gama yinta,ya kuma gama fahimtar inda ta dosa gaba dayanta.
Tun kafin ya qaraso yaga madarar ta cika tukunyar tana kuma zubewa,yayi mamakin ganin tana tsaye a wajen amma bata lura da hakan ba,yadan qara sauri kadan ya isa bakin gas din ya kashe.
Gilmawarsa ta sanyata ankara da shigowarsa amma saita gaza motsawa daga wajen,tana kallonsa ya dauki rariya da cup ya tace madarar,ya dawo kusa da kitchen cabinet inda take tsaye,ya bude ya dauko zuma ya zuba ya sanya spoon ya barta a wajen. Ya qarasa bakin freezer dake daya side din ya fiddo ruwa mara sanyi cancan sannan ya juya yana barin kitchen din.
Samun kanta tayi da binsa da kallo,yana qarasa ficewa sai taji hawaye ya silalo mata,ta shafo hawayen tana kallonsu
"Again?" Ta tambayi kanta muryarta tana rawa,kawai saiga wasu hawayen sabbi suna sake fitowa.
"No.....no" ta fadi sau biyu a jere tana girgiza kanta,saita matsa gaban fanfo dake kafe a sink ta kunna,ta fara tarar ruwan tana wanke fuskarta dashi. A qalla ta kusa mintuna biyar a haka kafin ta samu nasarar tsaida hawayen,saidai abinda takeji a cikin zuciyarta bai sauya ba.
Da kadan kadan take kurbar madarar,sai taji tana zauna mata sosai,a hankali ta shanye,wanda tun kafin takai ga ajjiye kofin jikinta ya sakeyin weak,wani kasala ya sake sauko mata,saita ajjiye cup din a daddafe ta fice a kitchen din. Yaga fitarta,ya rakata da idanu har ta shige dakinta saiya fidda ajiyar zuciya a sirrance yana dauke kanshi.
Sosai ta duqunqune cikin duvet tana jin sanyi cikin qashinta kamar wadda zazzabin cikin qashi yake neman kamawa,ta lumshe idonta tana fidda numfashi,ita kanta zuwa yanzu ta tabbatar ba lafiya lau take ba,ta dinga karanto addu'o'i cikin ranta,cikin ikon Allah sannu sannu wani irin mahaukacin bacci yazo yayi awon gaba da ita.
Batasan tsahon lokacin data dauka ba,itadai ta farka ta jiyo maganganu sama sama daga falo,da alama baqi ke dasu a gidan. Ta kalli agogo,saita miqe da dan hanzarinta zata wuce toilet,mararta taji ta murda,tadan dafeta tana yamutsa fuska,a hankali kuma saita saki,ta miqe ta wuce bandaki don daura alwala ta biya bashin sallar da yake kanta.
Koda ta idar bandakin ta koma,tayi wanka da ruwa me dumi sosai sannan ta shirya cikin wata doguwar rigan kayan bacci me taushi. Ta taje gashinta da kyau ta dameshi cikin band,saita tsaya tana kallon fuskarta. Skin dinta ya sake fresh sosai,hakanan idanunta ma kaman sun qara girma da haske. Yunwa taji tana dan ji,hakan kuma ya mata dadi,don tanaso taci abincin sha'awar cinne bata jinsa. Juyawa tayi ta dauki wayarta ba tare data daura dankwali ba ta nufi falon,sam ta manta da batun zuwan ayana,hakan wannan lokacin tasan lokacine da daga su saisu a gidan.
Sai data bude qofan ta soma isa falon sannan tunaninta na daxun ya fara dawo mata. Benazeer da batoul da kuma maina suna zaune saman carfet,sun sake sosai sun kuma yiwa wajen abinda suke so,sun batashi da abinci,ayana na duqe a gabansu tana qara musu miya da lettuce. Muryarta da tasu benazeer kadai ke tashi,alamun da zai bayyana maka lallai ita din ba baya bace wajen surutu da karadi. Yayin da hannun maina na hagu ke riqe da waya yana daddanawa tamkar hankalinsa baya kansu.
Idanunta dukka ta zube akan ayana din, shirt ce a jikinta inner da top me budadden gaba,sai palazzo madadin kayan,wata irin hula ce kawai saman kanta,wannan ya sanya sumar da ta danyi gadonta ta fito ta qasan hular. Tayi kusanci da yawa da maina,ko luma bata sani ba idanunta ne suka nuna mata hakan?,koma mene sai taji ci gaba da kallonsu bashi da wani alfanu face wani abu me zafi da yake saukar mata saman zuciyarta. Tana zare idanunta daga kansu yana dago kansa suka hada idanu,tun fitowarta fitinannen qamshinta ya ziyarci.hancinsa.
Kanta ta dauke,daidai sanda ayana itama ke qoqarin dauke kanta daga kan fuskar sultana, fuskar data rudar da ita da kwantaccen zallar sassanyan kyau. Tun sultana batakai haka ba tasan ita din me kyau ce,don kaf iyalin MAYAK'I ba wanda ya kamo qafarta, mutum daya ne suke gogayya,ya haidar din,aliyyu maina,to amma a yanzun zallar kyau aji da kuma nutsuwa me cakude da kwarjini da take gani tattare da ita yaso firgita zuciyarta.
*_tofa,wanne ne ba wanne ba?,ga sultanar ama?,ga AYANA da take matsayin diya a wajen ama,wacce AMA da MAINA zasu zaba?_*
*_tayi masauki cikin gidansu,kuma kusa da gidan MAINANTA,ya zata kaya?_*
_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 106
Daga ayana har shi ta bawa banza ajiyarsu,taci gaba da takawa da nutsuwarta har ta isa dining area sannan ta dubi batoul cikin muryartan nan dake saurin janye hankalin me sauraro
"Ina ama?"
"Ta shiga wanka" benazeer sarkin karadi ta baiwa sultana amsa. Kai kawai ta gyada,saita maida idanunta ga kayan abincin dake saman dining din tana nazarinsu,daidai lokacin tanja ta fito daga kitchen dauke da nata kwanaon abincin.
"Uwar daki kin tashi kenan" wani qaramin murmushi da baikai zuci ba sultana tayi tana dan shafa kwantaccen gashinta,murmushin da ya kusa sanya maina kasa controlling kanshi,don tunda ta fito ta wafci hankalinsa da tunaninsa,kowacce gaba dake jikinsa tana amsa kallon da yayi mata sau daya tak
"Wallahi tanja......yunwa nakeji,kuma na rasa meye zanci a ciki" tayi maganar tana taba warmer din da tafi kusa da ita.
"Ba zaki rasa ba kam,bari na bude miki ki gani"
"Na gode tanja" sultana ta fadi cikin girmamawa da qauna. Matar ta jima tana hidima wa rayuwarta,ta dade tana nunawa rayuwarta kulawa da soyayya.
Dukka abincin ta bude,ta zuba musu ido tana ci gaba da nazari kafin tace
"Inajin pepper soup din catfish dincan zanci"
"Yauwa nasan ba zaki rasa ba" tanja ta fada tana daukan plate ta soma zuba mata tana bata labarin program dinta na yau data kalla. Murmushi kawai takema tanja din,don sai taji haka kawai batason dogon magana,duk da taci gaba da surutanta da yaran,amma jikin sultana yana bata daga ita har maina din hankalinsu yana kanta,wanda ko sau daya bata waiwaya sashensu bama bare ta basu damar tunanin tasan sunayi.
"Da kin zauna ai" sultana tace da tanja wadda ke nufin sauka tabar wajen
"To ai sai na tayaki hirar" tanja din ta fada tana jan kujera ta zauna. A hankali da kuma kadan da kadan take diban pepper soup din tana sawa a bakinta suna hira da tanja. Duk da bakinta babu dadi amma sai taji ta samu appetit sosai,kafin wani lokaci sai gashi ta cinye tas
"Yayi dadi tanja,xan samu qari?"
"Me zai hana?" Ta amsata tana murmushi,sai tana plate din ta sake qara mata harma yafi na farko yawa
"Zan iya cinyewa kuwa?"
"Mummy zanci......"
"Nima mummy zanci" muryoyin benazeer da batoul suka bata amsa. Baki tadan bude tana dubansu ba tare data bari ta hada idanu da wani tsakanin maina da ayana ba. Kafin ma tace komai har sun iso saman dining din,suka sanya hannu suka fara ci,sai batace komai ba ta maida kai tana cin tana musu qananun mitoci
"Idan kika cinyemin ban qoshi ba tam,ni daku ne" tanja na zaune tana dariya,gami da mamakin cin kifin sultana,don ba abune data fiya damuwa dashi ba,dashi da nama duka basu wani dameta ba da zatayi musu cin qoshi.
Nannauyan ajiyar zuciya ayana ta saki a boye,ita kadao tasan me takeji cikin qirjinta. Duk yadda takeso kada ta saci kallon sultana koda a boye ne amma ta kasa,ta kalleta ta kalleta har ta dinga jin ta raina kanta da kanta,a yanxun da take xaune tsakiyar yaran nata suna cin kifin saita dinga jin inama ace itace?,inama ace yaranta ne ita da maina?. Babu wanda zai kalleta yace itace mamarsu,haihuwace irin ta quruciya,quruciyarma iya quruciya ko ciwon kai ba'a gama sani ba bare ayi maganar girma. Tana jin kamar zata sare da maina din amma wata zuciyar tana bata qwarin gwiwa,abu daya ne da bata sani ba......har yanxun yana nan a matsayin mijinta,tana nan a matsayin matarsa ko kuwa?,bata da amsa,batasan kuma waye zata tambaya ba ta samu hasken da zai haska mata kalan takun da zatayi.
Maida hankalinta tayi ga maina tanason janshi da fira,saidai kuma hausawa sukace miskili kafi mahaukaci ban haushi,gaba daya attention din da take buqata daga garesa ta gaza samunsa,wayarsa ya bawa kusan dukka a hankalinsa a idanunta,amma kuma ta wani gefen sultana ke daukan hankalinsa. Ya qware qwarai wajen iya satar kallo,wannan ya sanya ba lallai ka fahimci ita yake kalla din ba.
"Alhamdulillah,ku matsa ku bani waje na wuce" sultana ta fada tana miqewa daga saman dining din bayan ta kammala cin kifin.
"Idan ama ta fito kice mata na koma daki,zan duba program na next week in sha Allah"
"To ba laifi" tanja ta fada tana matsa mata hanya.
Tana sauka daga dining area din ama na fitowa,cikin shigar BOUBOU na wani material sassauqa ruwan bula wanda ya zauna mata sosai,ya kuma boye shekarunta,tamkar ba itace ta haifi maina ba,daya daga cikin dabi'un ama din dake burgeta qwarai wato ado da kwalliya,ta kuma tasirantu sosai dasu a iya tsahon zamanta da ita
"Ama zan wuce daki,sai da safe" sulta tayi saurin fada sanda taga ama din tana kallonta
"Zan duba wasu ayyuka" ta sake bawa ama uzuri don batason tace mata ma ta zauna a falon
"To Allah ya taimaka.......ayana......ga yayarki kun gaisa kuwa?" Ama dake shirin zama saman kujera ta fadi.
"Sultana ga ayana" aman ta kuma maimaitawa ganin sultana kamar bataji ba tana nufin wucewa ciki. Tsaiwa tayi da tafiyar ta juyo,idanunsu suka gauraya waje guda karon farko tun shigowarta falon. Zubin halittar idanun sultanar na dabanne,suna da wani irin kyau da koke mace kika kallesu sai sun burgeki,sun kuma bar miki kishi me yawa a zuci muddin akwai abinda ya hada tarayyarku ta fannin kishin
"Barka da dare kina lafiya?" Ayana ta fadi tana qaqalo murmushin dole
"Sannu ya kike?,ya garin?" Sultana din ta fada itama tana qoqarin arowa fuskarta sakewa.
"Lafiya qalau,ya paris?" Ayana ta sake tambaya
"Paris normal alhamdulillah.......kema gaki a cikinta"
"Yes....... gaskiya ne,Allah dai yasa tana da dadi" ta sake fadi tana kuma karantar duk wani motsi na sultana. Qaramin murmushi ta saki mata,ta gaji da wannan tambayoyin marasa fa'ida da